Free chapter · Read without an account

Chapter 55

by AMEENATOU MUHAMMAD ALHASSAN · Destiny love

DESTINY LOVE*


     Daga alƙalamin


       *Oumyasmeen*


Watt pad @Aminaoumyasmeen


Arewabooke@oumyasmeen


      


       Perfectly pen's ✊


KING AND QUEEN WRITING CHAMBER👌✊


ABRAR=me tsoran Allah 






Episode 55



TARÉÉK POV



Sai dai me yawa an ruƙe hannunsa ya kasa dukanta ita kuwa tuni ta firgita ya fashe da wani irin marayan kuka zama jameel yayi be cewa tareek kala ba domin yana iya hango hutar kishi dake ruruwa a idanuwansa gwara inya huce yayi mai magana...


Shiga bedroom yayi wanka yayi tunani duk ya cin kunshe me zuciya gwara ya koma gida ko zai sami salama a zuciyar sa har ya fito be dena tunani ba shirya wa yayi cikin White t-shirt da blue jeans sai ƙamshi yake zubawa wayar da ya siyo ya shiga sai ta mahimman abubuwa sa 


Jameel ne ya shigo yace 


"Malam kabar fa yarinya na jin yunwa,


ɗagowa yayi yace 


"Bata take away ɗaya taci,


Juyawa yayi ya koma floor leda ɗaya ya ɗauko ya kawo ya kawo gaban ta ya buɗe mata tausayin ta ya kama shi 


me lallashi take buƙata gashi Allah ya haɗata da miskilin miji 


bata yi mai musu ta amsa domin itama yunwa take ji komawa yayi ya zauna


tamkar me koyan cin abinci haka ta fara tsakurar sa bawai dan be dadi ba sai dai wannan ba cimar ta bace cimar garin Jordan dan ce 


kaɗan taci ta barsa yago tissue tayi ta goge hannunta ta ɗauki lemo ɗaya ta fara sha ko rabi bata sha ba taji fitsari ajiye wa tayi ta shiga 


bedroom ɗin da tareek yake ta shiga 


Samunsa tayi yana kwance yana latsai latsan waya idanuwanta ne ya ciko da kwallah cikin sanyi murya tamkar ana busa sarewa tace 


"Abbu Abbu ta nuna mai hanyar toilet, 


ɗagowa yayi ya zuɓa mata ido bece mata komai ba ƙasa tayi danata idon dan bazata iya kallan sa ba ta fara wasa da hannunta


haushi ne ya ishi tareek abu kaɗan kuka yawa me takaba bawai ya fahimci me take nufi a'a kawai shigar da ita zai komai ma zata yi tayi wannan shagwaɓar da sangarta ta ishe shi....


ajiye wayar yayi ya sauko daga luxury bed ɗin ya kama hannunta har toilet yawa me ciwon baki yace 


"Taking care taking,


a wannan karan taji me yace dan haka ta ɗaga mai kai tayi har wanka zatayi 



To bayan ta fito tasa kaya duk yana dakin saidai hankalin sa ya kanta lokaci zuwa lokaci yakan ɗago ya kalle ta gamawa yayi ya fara haɗa kayansu dake komai yayi mata ta internet 


yau sai Nigeria ƙasar mu ta gado garin shugaba jagaba 


Fitowa yayi tana biye dashi jameel ma ya shirya kullo dakin jameel yayi sukai kaiwa me kula da dakuna 


Tesxi suka hau har airport ta kai su bincikar kayansu akai da vizar su basu sami wata matsala ba suka shiga jirgi 


Wajan tareek da abrar ɗaya jameel na bayan su baccine yayi a won gaba da ita  a jikin tareek ta kwanta magazine ya ɗauka ya fara karantawa har Allah ya kawo su kano suka sauka a 


AMINU KANO NTERNATIONAL AIRPORT 


checking kayan su akai bare idanuwa abrar tayi tana kallon ikon Allah ruƙe tareek gam tayi tsoron wayan nan bakaƙen mutanan take  


Tun ɗazu wanda zai ɗauke su yazo dan gaka ana gama binciken su 


suka shiga Mota yau sai gidan


BN NADER



GADAN ƘAYA J.R.A


Juyowa driving yayi yana kallon abrar mamakine fal a zuciyar sa ko ina wayan nan mutanen suka samo wannan yarinya..? lalle yau a kwai tashin hankali a gidan nan dama basa rabo dashi to gawa ni nan ya rakito musu sabo fil 


ganin ba me bashi amsa ya mai da hankalin da kan titi har suka iso horn yayi me gadi ya buɗe parking yayi fitowa sukai 


Kallon ko ina abrar take yawa wacce ta warke daga cutar makanta 


jameel ne ya dube SA yace 



"TAREEK wanne bayani za kaiwa su abbie naga ko a jikin ka ?,


Haɗe girar sama data ƙasa yayi yace 


"Wanne bayani kuma..? akan me ..? zan musu bayani..,


murmushi jameel yayi daman yasan za arina shashin aunty Ayesha suka nufa cikin tana zaune a floor da sauri ta tashi jin sallamar su tace 



"sannun ku da zowa na neme ku har na gaji bata lura da yarinyar dake hannun tareek ba ,


Hmm kawai jameel yace domin sun ga mutuwa ido da ido zama jameel yayi tareek ya shigo hannunsa ruƙe da na abrar yawa wata doluwa ta saki baki tana kallon sa kasa haƙura tayi yana zama tace 


"Tareek wace wannan....?,


gyara zama yayi yace 



"Ga a jiyarta zan miki bayani,


Yana fadar haka ya tashi har ya fara tafiya ya tsaya yace 


"Duk abin da take buƙata ki faɗamin in baki kuɗi ki siyo,


daman tasan za'arina shi mutum ne da ba'a sanin cikin sa ba kuma yason shishshigi da shigar mai rayuwa tace 


"Okay ya sunan ta...?,


fita yayi yayin da jameel ya bishi be bata amsa ba 


Kafin ta ankara abrar ta fita tana kuka ta bisu tana Abbu Abbu Abbu da sauri Aunty Ayesha ta bita amma ina gudu take


bata luraba ta bige sitti ruƙota sitti tayi chak jameel ya tsaya banda tareek dama ranta a ɓace yake da tafiyar su yan zun nan hafsa ta sanar mata da dawo war su shine ta zo ta wanke su tas sai ga abin da ta ci karo da shi 


janyota tayi ta sharara mata mari ta dubi jameel tace 


"Kai ina ɗayan takadirin yake wannan kuma a ina ku ka samota....?,


Sosa ƙƴeya jameel yayi yace 


"Uhmm sitti kenan ,


hassala zuciyarta tayi ganin suna shirin raina mata hankali shi dayan ya gudu shi kuma ga amsar da ya bata


maida kallon ta gun Aunty Ayesha tayi tace 


"ke ina kika samu wannan tana zaune a gidan nan ban sani ba ...?,


gaban aunty Ayesha ne ya tsananta bugu tasan tujarar sitti bata ƙarewa bakinta narawa tace 


"Nima yanzun nan tareek ya ban amanarta,


Ihu sitti tasa sakamakon cizo da abrar ta gartsa mata ta zuba a guje ta bi inda taga sunyi sitti tace 


"Innalillahi shikkenan tareek ya dawo mana da jikar aljanu da mayu irin wannan kyau haka to wallahi ba zata saɓo ba ke Aishatou kiramin kowa na gidan nan ya zo babban flooe dole yau wannan aljanar ta barmin gida ,


Jikin Ayesha be yayi sanyi tace 


"To ,


Kallon sama da kasa sitti take mata tace 


"Lafiya kike gyaɗa kai yawa wata gaɗangaruwa ko bazaki bane...? ni inje,


girgiza kai Ayesha tayi tace 


"Zani sitti,


harara sitti ta bita dashi tace 


"Wallahi yau tareek sai ya san faɗa dani ba daɗi ba ya rainani ba..


Besan ni baƙar fura bace faɗan ibilisai 


dole yau safna ta tareek a shashinsa ni anya kuwa ba yarsa ce wannan ba kai biri yayi kama da mutum ya zauna yaƙi aure to wallahi bazan yarda shege ya kara zamar mi a gida ba ,


Inteesar ce ta zo hucewa turus tayi ganin sitti na zuba tujara tace


"A'a sitti lafiya kike magana ke kaɗai...?,


da sauri ta ɗago yace 


"Yar nan zancen zucine ya fito fili yau ran kowa na cikin gidan nan sai ya ɓaci,


Taɓe baki inteesar tayi tace 


"Me ya faru sitti..?gutsuramin kafin a fara faɗan ibilisan da naji kina magana...,


Sarai sitti tasan inteesar ba kunya ce da itaba yanzunan zata mai da ita abokiyar wasan ta ita kuma ta tsani raini tace 


"Uwarki ce ,


Zaro ido tayi tace 


"Sitti nayi nan da alama kenan aljanun gidan nan sun fara taɓa ki ,


Wani uban ashar ta bulmulu tace 


"Ke inteesar wallahi kike yaye ni wanne aljani aini naci dubu sai ce to ,


Zaro Ido inteesar tayi tace 


"Wallahi sitti yi shiru kar yau su hanaki bacci Ni dai nayi nan tayi gaba,


Tsorone ya kama sitti domin bata manta buga kanta da suka dinga yiba da ta shiga toilet aikuwa itama bara tayi wa kanta kiyamul laili 


floor ta takoma ta harɗe kafa ɗaya kan ɗaya dan wallahi yau me rabata da tareek sai Allah ..


💨💨💨 Flash back


Ji yayi an rungume shi kuka take juyowa yayi ya rage tsayin sa ya kura mata ido ga shatin hannun sitti a fuskarta raɗa raɗa


abin ka da farar fata hannu yasa ya share mata hawaye ya ruƙe hannunta suka fara tafiya har shashinsa buɗewa yayi ya shiga 


Jameel ma shigowa yayi ya tsaya a bakin kofa yace 


"Tareek ni na tafi gida yanzun nan hibbah ta kirani hajiya ba lafiya,


Juyawa yayi yace 


"Okay Allah ya bata lafiya,


Amin yace ya fita komawa yayi ya rufo kofar sa


abrar kuwa zama tayi har bacci ya fara ɗaukanta iya gajiya ta gaji 


jingina yayi da jikin kofa


" baya tsoran sitti saboda in da sabo ya saba amma fa mahaifinsa shi zata tusa a gaba da tujarar ta bakuma ya tsoron kowa yasan abrar matarsa ce amma me ai tayi ƙanƙanta da ace babba ce ko dan ya baƙantawa sitti zai zauna da ita suyi zaman aure amma wannan fa da ko kanta bata gama sani ba tabbas yana buƙatar mace amma bashi da ra'ayin tara mata har hudu ga safna matar shige ga abrar wacce ƙaddara ta haɗasu ko me sitti za tayi ba zai taɓa rayuwar aure da safna ba


yana kƴamatar zina yana ƙin meyinta 


alkawari yayi saidai su gaji sunemi saki amma bazai taɓa hada shinfiɗa da itaba....


tsaki yaja lokacin da yakalli a gogo ya ɓata lokaci yana tunani a gurguje ya shiga bedroom ɗinsa ya cire kaya 


ya shiga toilet wanka yayi ya ɓata lokaci yawa wata mace fitowa yayi ɗaure da towel ga wani a hannunsa yana tsane kansa besan da ta shigo bedroom ɗin ba


ya zame towel ɗin dake ɗaure a ƙugunsa wata irin yar ƙara abrar ta saki


da sauri ya maida  towel ɗin idonsa ne ya kaɗ'a yayi ja yanzu yarinyar nan zata raina shi ta gansa ba kaya  


Tsawa ya daka mata ya nuna mata kofar fita da sauri ta fita har tana tuntuɓe 


Cikin sauri ya shirya cikin T-shirt red colour an yi rubutu da baƙi ansa Gucci...


tuni ta haskaka farar fatar sa jeans yasa black colour expensive spray ya ɗauko ya feshe jikin sa agogo ya ɗauko Rolex ya ɗaura 


Ji yowa yayi ana buga kofar sa yawa ba gobe da saurin fitowa yayi ya buɗe kallo ɗaya yayiwa salim ya nutsu yace 


"Kazo abbie na kiranka yana floor sitti,


juyawa yayi batare da yace me komai ba ya kulle kofar


tsaki salim yaja yaso ace yaga wacce sitti take cewa ya kawo ashe shima ya kawo mata me fuska biyu sai ya nuna shima na Allah ne ko da yake dan zina yaƙi zina....


Yana rufe kofar ya nufi wata glasses door zogeta yayi sai ga takalma jere sunfi hamsin ɗauko wani slippers yayi Black colour da yarin ja yasa kallon ta yayi ta haɗa kai da gwuiwa


ba abin da yaki jini irin kuka da zata gane da ta dena gashi bajin hausa take ba balle yayi mata gunta ya je ya ruƙo hannunta domin in ya barta zata kara wani kukan ne ta rikita mai lissafi 


ya kullo shashin sa sai da sukai tafiya me nisa tukun na ya isa shashin sitti baƙin sa ɗauke da sallama ya shiga kowa na zaune duk wanda ya ke kwana a cikin estate ɗin ya hallara agun duk sun zauna ita shugaba tana tsakiya ransane ya ɓaci 


shiga yayi ya zauna a ɗaya daga cikin Luxury royel chairs ɗin dake tabkeken floor ƙasa yayi da kansa 


kowa kallo yabi abrar da shi mamakine ya kusan kar mom amina ina ya samo wannan balarabiyar tab a kwai kura haka ta ayyana a ranta sitti ce zuciyar ta takai har huya tace 


"Kai rasa kunya ɓeran tanka kowa kai yake jira ina kasamo wannan aljanar me idon mage,


ido huɗu sukai da abrar ƙara rukunkume tareek tayi domin tsoran matar ya shigeta haɗe rai yayi abbie da shi ma yake son sanin ko wa wace wannan duk da yayi shedar ɗan nasa bazai taɓa aikata abin da sitti take faɗi ba yace 


"Tareek ina ka samo wannan ba ce min kayi ba aiki aka tura ku to ya akai ka dawo da yarinyar nan ....?,


Safna ce ta shigo yawa an hankaɗo ta wani irin kallon tsana take jifan abrar da shi tamkar dirar miƙiya kamar an ɗiga mata dalma a zuciyar ta da kunnan ta numfashin ta yake kai kawo bata da cutar asma amma a yau fa ta kamu da cutar saboda da numfashin ta dake sama da ƙasa ga bugun zuciya jiiiyi yace......✍️


*_🤔tab akwai kurafa me zai faru gaba to nidai ba ruwana ku yayyafawa safna ruwa 🤗 nayi nan🚵_*


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.