Free chapter · Read without an account

Chapter 60

by AMEENATOU MUHAMMAD ALHASSAN · Destiny love

*DESTINY LOVE*

         Daga alƙalamin

             *Oumyasmeen*

Watt pad @Aminaoumyasmeen

Arewabooke@oumyasmeen

          

            Perfectly pen's ✊

KING AND QUEEN WRITING CHAMBER👌✊

Duk meson ci gaba ya shiga link ɗin nan ku yi following ɗina domin samin ci gaba da zarar na ɗora ku danna min VOTE ngd

Episode 60

A hankali wanda yafi kowa sata ya lallaɓo ya ɗauke ni washe gari ana ɗora mata tallah guna tazo haka rayuwa ta cigaba da gudana tun tana jin tsorona har ta dena kwasam

                      sai ga cikina a jikin ta nan fa ta shiga tashin hankali ta sanadin haka mahaifiyar ta ta kore ta gida na kama mata mu ka ci gaba da aikata masha'ar mu cikin dake jikinta tuni na bata magani ya zube

Ganin tana sha'awar karatu na kaita makaranta amma fa da biyu na kai ta tagged ɗina shine yar da za'ai ta sami kusan ci da lion kin san fa mun daɗe muna farautar sa da yake shegen me wayone ko wacce gada muka samai sai ya tsallake ta


                            duk a cikin tagged ɗin nane nasa ta ta zama ƙawar safna tana gama karatu da yake uban gidan lion shine me gidan radiyo ya ɗauke ta aiki amma na manufa mun gama tsara duk yarda za ai amma shegiyar yarinyar nan ta wargaza shirin mu

abin da na fuskanta bani kaɗai bahijjah

kewa aiki ba sannan ta kamu da son lion mutumin da natsana sama da mutuwata....abin da ya ƙara dagan hankali shi ne saboda ya saki jiki da ita tare ake tura su aiki sun saba har tana koƙarin bayyana masa sirrrin mu nida former governor da sauran ta wagar mu

Murmushi ya saki yace

"Lion yana da taurin kai former governor yana da gidan saida jarirai da manyan mutane to agarin binciken sa ya gani da yake shi uban iyane dan bin kwaukwafi ne sai ya je ya gano wa idonsa yayi mana tirere a gidan Radio

                             uban gidan sa Sanusi ya hanashi suka zagaye zasu je su fito da su sukuma faɗawa al'umma wane shi...na tura yarana

                              kash akai rashin sa'a ya gudu ita kuma da hannuna nasa kibur na shaƙeta har sai da ta mutu ashe ya laɓe da gowar da zanyi sai naga yana ɗaukar video kafin in ankare ya jefamin dutsai a idona har gwayar idona ta fashe idon ya tsiyaye


Ajiyar zuciya ta saki tace

"Ina mahaifiyar bahijjah...?,

Dariya yayi yace

"Au na manta in faɗa miki ta je ta bata haƙuri har ta haƙura bayan duk wata lalacewa da bahijjah tayi da sa hannun ta tana da kwaɗayi ta nan bahijjah take siyeta..,

Wai yaron nan bayan na koma gida sai ga yan sanda sun zo kamani a daran na fito shi kuma ya shiga sahun mutanan da zan kashe.... Har yanzu ina mamaki dalilin da yahana shi saƙin video kashe bahijjah ba,

Gawar ta aka kaiwa mahaifiyar ta .....tayi kuka a bu na biyu bani na kashe Sultan amma ina ganin kamar

gargaɗi akai mai amma beji ba

            uku kuma mutuwar bily I really miss you bily tana so ta kara zamame min bara zana shiyasa na kawar da ita...

Tashi tsaye tayi tace

"Duk wayan da kake neman ransu ba abin da sukai maka musamman bahijjah bata cancanci haka ba daga gun ka.. sai..bily me son farin cikin ka saboda kai..,

a fusace ya nuna mata hanya lokacin agogo ya buga ƙarfe 2:30 na dare yace

"lokacin ki yayi yana gama faɗar haka ya juya ya fita jakar ta ta ɗauka ta fito har kofar gate matashin nan ya rakata da katawa tayi ganin su nucy tabbas mahaifin nucy besan nucy tana tare da babban yaron saba masu iya magana sun ce....

                                        duk wanda ya ce tukunyar wani bazata tafasa ba to tashi ko ɗumi bazata yi ba kaɓata ɗan wani kai ma a ɓata naka tabbas da gayya goga ya janyo nucy cikin harkar nan    

                 domin ya koyawa mahaifinta hankali ya killace ya'yan sa yana lalata ya'yan wasu buɗe motar ta tayi ta shiga da gudu tabar gun tunani ta shiga yi wa ya kashe SULTAN.....

ganin bata da me bata amsa ta kawar da tunanin...

  

              Three days ago



Ummi ya kamata ki faɗa mana abin da kike ɓoyewa shekara da shekaru barin kashi aciki baya maganin yunwa cewar Aziz.

ta gumi ta zare tace


"Aziz lokaci nake jira da zan faɗa muku ya kusa amma ba yanzu ba nima ina ganin inna faɗa muku zan sami salama a zuciya ta,


kai ya jin jina yace

"Insha Allah zaki samu,

kallonsa tayi tace

"Aziz banji kana maganar aure ba ...,

Sosa ƙƴeya yayi yace

"Ummi lubna nake so gani nake yanzu tayi yarinta da soyayya ga karatun ta jira nake ta gama..,


pillow case ta ɗauka ta buga mai a goɗon baya tace


"Ya Allah ai daman nace maka za'a zo gun ka dinga cewa yarinya me majina yanzu ita kuma kake so...? to ko ba karatu bama son ka,

Marairaice'wa yayi yace

"Please ummi wallahi na tuba..,

uhmm tace lubna ce ta fito ita da nur suna hira zama sukai lubna tace

"Lah ya Aziz yaushe ka dawo...?,

kallon ta yayi riga da skirt ne a jikin ta na atamfa super Holland taci ɗauri irin na zamani lubna akwai kwalliya kau da kansa yayi yace

"ɗazu..,

Gyara veil ɗin tayi ta ya fashi a kafa ɗa tace

"Please ɗan Allah ka kai ni Alheri radio..,

cikin mamaki yake kallon ta yace

"Me zaki yi acan...?,

ɗan yamu tsa fuska tayi tace


"Zan yiwa king of journalist sannu da zuwa yau kwana hudu da dawo warsa amma banje ba....,

kallon mamaki yake mata tuni zuciyarsa ta shiga zullumi karɗe soyayya suke amma da yake namijin gaske ne sai ya waske yace

"Me ce alakar ki da shi....na sansa mutumina ne...,

waro ido tayi tace

"Dan girman Allah..,

shan tuka yayi yace

"Ina yi miki wasane..?,

girgiza kai tayi tace

"A'a,

                tashi yayi yace

"Ba inda zaki ki bari gobe zai zo duba lafiyar sa amma ba gidan Radio da zan kai ki shima sai kin faɗan alkarki da shi inna gamsu in kai ki,


sanyi jikin ta yayi tace

"To,

Anan shiga kitchen sukai ita da nur da ummi suna taya ta girki har suka kammalah Ummi na lura da su inda sukai ba daidai ba ta gyara musu....


************


Ayshe POV*****




lallaɓatayi har tayi bacci a hankali ta kwantar da kanta dake cinyar ta miƙewa tayi 

              fita tayi daga ɗakin ta koma nata tana shiga wayar ta tayi ƙara da take bedsite drower banza tayi da'ita ɗan tana kyautata zanton wannan shegiyar mayar ce....

                   

             Uncle Nasir ne ya shigo yace

"Wai tareek ya baki ajiyar yarinyar da yazo da ita...?,

cikin mamaki take kallon sa tace

"Kai da baka gidan nan a ina ka sani..?,

          Waskekewa yayi yace

"yanzu ake sanar dani,

          Hmm kawai tace domin tun da aka kashe ɗanta tafara zargin mijin nata musamman wasu abubuwa da yake wa'yanda bata yarda da suba tana tsoron randa zargin ta zai tabbata ɗaukar wayar ta tayi ta fita komawa floor tayi...again sai ga wani saƙo kamar haka

_ƙar ki ɗorawa kowa alhaƙin kashe miki ɗa wayan da suka kashe miki basa tare da ke saidai akwai shu'umai wa'yanda sunfi gubar muciji...saurin isar da saƙo azzalumai maciya amanah nice baby_

                    ta kusan jefar da wayar to wake mata wannan text message ɗin ba number a kullum da irin maganar da zata zo mata da ita kuma dai-dai da tuaninta

Firgigit ta ɗago sakamaƙon shigowar hafsa tace

"Aunty lafiya kike tunanin...?,

            Ajiyar zuciya ta saki tace


"Ba tunani nake ba kaina ke ciwo,

Ayyah sannu ina bakuwar tamu..?,


tashi tayi tace

"Tayi bacci dan Allah kar ki wani kwakƙaran motsi da zai ta sheta kinga jiya bamu yi bacci ba yau anci sa'a ba tayi rigima ba ..,

"to, bedroom ɗin ta shiga duban basma tayi tace

                "Malam fa ya zo,


Tsaki basma tayi tace

"Yau bani da ra'ayin karatu,

Inda saboda hafsa ta saba juyawa tayi ta fita bata ce mata ƙanzul ba


Mayafi aunty Ayesha ta ɗauka da mukullin mota da yake tareek ta turo mata kuɗi na siyayyar kayan abrar ɗakin uncle nasir ta shiga bata tsaya knocking ba ta murɗa handle ta shiga da sauri ya rufe laptop ɗin sa

              jikin ta ne yayi sanyi zuciyar ta tace

"zan tafi siyowa abrar kaya...,

Cikin yaƙe yace


"Masha Allah Allah ya kiyaye...taking care,

Kai ta ɗaga mai ta juya bata nuna mai ta ga abin da yake ba daman tasan ko mun daran da ɗewa zai nema wa kansa mafita amma bata irin hanyar nan ba ko aure ne yayi baza ta tauye mai hakki ba tunda ita ta kasa..

            da wannan zancen ta fita

Bedroom ɗin su basma kuwa cikin bacci abrar taji wani irin ciwon mara kuka tasa har ta tashi basma da ta fara kailula (baccin rana) cikin faɗa basma tace

"Ke wai wacce irin mara hankali ce..? baki da aiki sai kuka nasha faɗa miki tareek ba zai dawoba ba yanzu ma haka ya manta da rayuwar ki yana tare da amaryar sa yar dangin arziki ba irin yahudawa ba .....


yanzu kam tana jin hausa saboda zaman su da hafsa taji me tace abrar hakuri ne da ita dan haka bata tanka wa basma ba

                    dafe marar ta tayi tana juyi ita tasan irin ciwon da take ji ...



IN BRIEFLY


Amarya da ango

Yau kwanan safna hudu a gidan tareek tun da aka kawo ta ko kallon bata ishe shi ba bama ta ganinsa abin duniya ya ishe ta ko wacce amarya sarauniya ce a gidan mijinta amma ban da'ita tayi baƙi ta rame ga jaraba nacin ta iya gyara mom hafsa tayi mata....

tsaki taja abin da bata so ta fara aikatawa shi zata fara bata so tareek ya gane ita ba buɗurwa bace amma inta nemi mata fa....ai bazai gane ba shawarar nucy zata ɗauka ga mon hafsa tace mata har yanzu boka na aiki be kamo zuciyar sa ba duk randa ya kamo sai ta juya shi son ranta

"ga sitti itama yanzu ta lura sitti ta sauya mata akwai wani abu da take ƙullawa wanda ita bata sani ba alhalin da ba haka suke ba kallon ko ina na shashin nasa take abin sha'awa

                dawowar nan da yayi har ya fitar da komai ya canza wani ko ita da aka zubawa dukiya ya fita komai yau indai be biya mata hakkin ta ba zata kira nucy ta amince da wacce zata haɗa ta da ita amma ai'nucy ba sona take ba ,....ƙar dai tuggu take haɗa min..

Shashin wata zuciyar ya mata amsa tuni takawar da zancen ai sun shirya har ta bata haƙuri gyara zama tayi tana duba agogo karfe

                 5:30 ya shigo cikin ƙasai ta abin mamaki shashinsa abuɗe da sauri ya ƙarasa dawa zai yi tozali lallai dole ya koyawa yarinyar nan hankali...

Cikin ki ɗima ta juyo jikinta na rawa yawa mazari saboda ganin ya koma yawa ma yunwacin zaki har ta briefcase ɗinsa ta sulale a ƙasa......✍️


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.