Free chapter Β· Read without an account
002
β¦ π¦π¨π‘π π¦ππππ₯ ππππππ₯π π§π β¦
πππΎππ π°π½π³ πππΈπππ΄π½
π±π π΅π°ππ΄πππ°π°π·ππ°π·
ππππππ ππππππ'π πππππππππππ
Ψ¨Ψ³Ω Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
Book 1
π·πππ 6_10
-
-
π½π°πΈπ±π°ππ°, πΊπ°π½πΎ, π½πΈπΆπ΄ππΈπ°.
Garin damuna ne sanyin safiyar Asabar garin babu hayaniya sosai sakamakon ruwa da aka kwana anayi kowa yana gida. Gida ne Safe Content mai tsananin kyau tun daga waje zaka san gidan ya tsaru iya tsaruwa. Daga cikin gidan kuwa Palour ne madaidaici da Ιakuna guda huΙu a ciki sai kitchen da toilet. Zaune suke ita da Mijinta a palour'n ta Ιora kanta akan kafaΙar sa abu yake nuna mata a waya suna hira hankali kwance banko Ζofar Ιaki akayi mace ce ta shigo sai huci take yi doguwa ce amma ba sosai ba dan za'a iya kiran ta da gajeriya masifa ce take cin ta ta hau cewa
"Ni zaka ci amana TAHEER yau kwana na amma ka bige kana hira da wannan matsiyaciyar" ta faΙa tana nuna wadda ke zaune kusa da shi da janye kanta daga jikin sa tayi dan bata son tashin hankalin Jalila masifaffiyar Kishiyar ta wadda ta fison kullum suyi ta faΙa ana jin su a waje
Mijin nasu ne ya tashi tsaye yana cewa "Jalila me yake damun kine? Kullum kin fison ayi ta jin mu a maΖota"
Kusa da shi ta dawo tana huci da hura hanci ta cigaba da cewa "Ehh na fiso, baka da kirki Taheer inacan nema maka abinda zaka ci amma ka taho Nan cin amana ta"
"Komai a gurin ki cin amana ne" ya faΙa kamar ya dake ta
"Ehhh Ιin" ta faΙa tana Ζara daga murya, nufo wadda ke zaune tayi tana ruΖo wuyan rigar ta
"Na tsane ki FAKEEHAH bana Ζaunar ganin ki a gidan nan wllh" ta faΙa tana zare mata ido
"Da mijina kika zo kika sameni bani na same ki a gidan nan ba. Ζaddara ce tasa ya aure ki"
Fakeehah ce ta nuna Taheer tana cewa "Taheer ka faΙa wa matar ka ta sake ni ko in mata abinda bata yi zata ba a rayuwar ta, shiru hauka ne? Ko wane irin shirme ta Ιauko sai ta sauke shi a kaina"
"Ko an faΙa mata kowa jaki ne mara ilimi ne kamar ta?"
"Kinga Fakeehah yi haΖuri ki shiga Ιaki, ke kuma Jalila kike ki haΙa mana breakfast"
Cika ta tayi ta wuce bagazam-bagazam zuwa kitchen. Kusa da Fakeehah ya dawo kalamai na rarrashi yayi ta faΙa da Ζyar ta haΖura ya tasa ta a gaba suka shige Ιaki.
Fito wa tayi daga inda ta LaΙe ta nufi Ιakin Fakeehah buga musu Ζofa ta fara da Ζarfi Taheer ne ya buΙe Ζofar yana kallon ta harΙe hannu a Ζirji yayi yana cewa
"Lafiya kike wannan bugun?"
Harara ta Ιalla masa sannan tace "Ita tasa haka Taheer ka fita a ido na"
Ζara tsuke fuska yayi sai ya ce"Jalila wai kece mijin ne da kike min irin haka? Kowa na jin mu"
"Why Taheer? Meyasa kake min haka, kalle ni daga sama har Ζasa mace ce ban cika ba ko me ranar gurki na kana gurin kishiya ta"
"Sai aka ce miki wani abu muka yi? Lallashin ta nake yi kin mata laifi"
"Lallashi Amma Kai Ιan kutumar Uba ne Taheer, naci uwar lallashin ta fashe ma, wa yace ta kula min miji ranar girki na? Ita ta jawa kanta" ta faΙa tana Ζara hararar sa
Tsaiwar sa ya gyara yana zaro Ido ya Ζara kallon ta da kyau "Ni kike zagi Jalila?"
KaΙa kai tayi tana wani yamutsa fuska tare da gyara zaman Ιaurin dankwalin ta gashin ko kyan gani ba gyara sannan ta ce "An zage ka Taheer, Ubana ne kai ko Uwata? Zaman hakuri kawai nake da kai kasani?"
Shiru yayi mata sai kuma ya ce " Ni zance zaman haΖuri nake da ke Jalila Ζazama dake ba ladabi ba biyayya kullum gani na kike kamar sa'an ki amma shikenan Kije na sake ki" ya Ζara sa faΙa muryar sa wani iri kamar wanda zai yi kuka
Hannu Jalila ta Ιora aka tana sakin ihuu "Wayyo Allah, Innalillahi wainnaillaihir-rajiun na shiga Uku ni Jalila Taheer ni ka saka" ta faΙa tana nuna kanta. Bangaje shi tayi ta shiga Ιakin. Fakeehah na zaune a gefen gada jaririya ce a hannun ta tana shayar da ita kamar bata jin abinda ke faruwa a waje ba nuna ta Jalila tayi hawaye na zubowa daga idon ta tana cewa
"Kinji daΙi ya sake ni Koh? Ban saku ba wllh" ta faΙa tana sakin makirin murmushi sai kuma ta cigaba da cewa
"Fakeehah ki sa a ranki sai na dawo ke kuma zaki fita wannan dole ne" fuuuu ta fice daga cikin Ιakin.
"Allah ya fiki In Sha Allah"ta faΙa tana raka bayan ta da harara
"Kisa a ranki karki cire wallahi sai na dawo ke kuma ki fita harabada ke da gidan Taheer Indai na dawo" ta faΙa tana jan akwatin ta.........
πππππππππ
A gajiye ta dawo daga gidan Aunty ba kowa a tsakar gidan yanzu Ιangaren su kawai ta nufa a Ζofar Ιaki ta tarar da Yaya Basaam da yara guda biyu ko kallon inda yake bata yi ba ta shige ciki da sauri ya tashi ya bita cikin shima a tsaye ya tarar da ita tana cire mayafi Rafi'at na zaune tana danna waya kusa da ita yaje ya tsaya Ιagowa tayi Mari ya Ιauke ta da shi bata yi zata ba kawai tayi Mari a fuska lailayo wani ashar tayi tana cewa
"Kutumar Uba, kamare ni" ta faΙa a fusace
"An mare kin, ko zaki rama ne?" Ya bata amsa
"Ba zan rama ba amma zaka gani, Ιazu ma haka kayi min wannan haukan koh? Saboda na maka shiru shiyasa koh" ta faΙa tana huci dawo da kallon ta tayi ga Rafi'at tana cewa
"Ke kuma" ta faΙa tana nuna Rafi'at
Sai kuma ta cigaba da cewa "Ζazu Maamah ta kira ni sharrin da kika min kenan a gurin ta"
"Ni ban mata waya ba Allah" ta faΙa tana zazzare ido
"Da kin mata waya da baki yi ba ke ta shafa, to ki sani tunda yau ya Ζara marina wallahi sai munje Hisbah tunda ba mutunci ne da shi ba mtwsssss" ta faΙa tana shigewa Ιaki ta barsu cirkwai-cirkwai......
ππ«§ππ«§π
Kwance take akan makeken Royal Bed Ιin ta Bacci take yi sai juye-juye take yi bakin ta sai motsi yake alamun magana take amma bata fita sosai gumi duk ya jiΖa jikin ta
"Muhammad wannan rayuwar yanzu ka zaΙa wa kanka? Shaye-shaye Muhammad ba halin ka bane please ka daina" ta faΙa tana Ζara juya kan nata shiru tayi sai kuma ta cigaba da cewa
"Tafiya zaka yi ba zaka dawo gida ba Muhammad? Ina bukatar ka a kusa dani ka dawo gida dan Allah" ta Ζara faΙa tana miΖa hannu alamun tana miΖa wa wanda take kira hannu ya riΖe ta
"Muhammad karka tafi ka barni, ina cikin wani hali please karka tafi yarona" ta faΙa tana sakin Ζara........
#π΅π°ππ΄πππ°π°π·ππ°π·π―
Comments & Share Fisabillah π₯°π
Book 2 300
Book 3 300
*Littafin sune silar Ζaddara ta 500 ne kacal, dukanshi Book Ιin Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*
9047574404
Fatima Abdulhadi Garba
Opay
*bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ku tura ta wannan number 07077791941*
Zaku iya samu na ta wannan number 07077791941
π½πΈππΌπβ€πΈπΈββπΈββοΈ