Free chapter 路 Read without an account
Page 10
by Nanameera 路 BA ITA BA CE
*BA ITA BA CE!..馃挅馃挅*
*NANAMEERA*
*MIKIYA WRITERS ASSO...*
```Page 10```.
# *The war*
"I'm sorry eesha amma ya kamata ace kin tsaya kin fahimci abinda zan fa蓷a miki wlh isn't my fault banida za蓳i na auri Ramlah ne saboda babu yanda zanyi ni ne nake kula da ita nd kuma yanayin lalurarta dole idan ta ce tanason abu ayi mata shi idan ba haka ba za'a ga ba daidai ba wannan shine dalilin kawai" girgiza kai tayi tana raba jikinta da nasa ta ce"A'a yaya Khalil kaima kana sonta yasa ka aureta idan ba haka ba bazaka mance al茩awarinmu cikin sau茩i ba, karka damu nima yanzu inada wanda nakeso kuma nake shirin aure saboda haka..." hannayensa ya sanya yana rufe mata baki cikin zafin rai ya ce"wlh baki isaba eesha ke tawace ni ka蓷ai kuma babu wanda ya isa ya aureki ina raye kuma na barshi nasan kin gane abinda nake nufi"ture hannunsa ta yi tana harararsa ta ce"da kenan amma yanzu na shige wannan level 蓷in kuma har abada zan cigaba da kallonka matsayin marayaudari wanda yaci amanata" ta 茩arashe maganar tana rufe bakinta saboda wani kuka daya zo mata da gudu ta fice daga 蓷akin. Jingina ya yi da wall 蓷in 蓷akin yana dafe kansa gaba蓷aya ya ji duniyar tayi masa zafi furzar da wani irin zazzafan numfashi ya yi sannan ya juya ya fita. Zaune ya tadda ta kan royal cusion 蓷in parlon sai kuka take kamar ranta zai fita, hannayensa zube cikin wandonsa ya 茩araso gabanta sannan ya tsuguna 蓷ago fuskarta ya yi cikin sanyin murya ya ce"eeshana" kallonsa tayi da idanunta da suka sauya kala zuwa jaa bata ce komai ta cigaba da kukanta cikin son ya rarrasheta ya ce"now tell me kina sona?" da sauri ta 蓷ago ta kalleshi sai kuma ta janye hannunsa daga kan fuskarta ta mi茩e tana kallonsa ta ce"a baya dai na soka yaya Khalil naji kamar bazan iya rayuwa idan babu kai ba nayi mararin kasancewa matarka kamar yanda ka kwa蓷aitamin" numfasawa ta yi sannan ta cigaba da fa蓷in"amma yanzu na ha茩ura dakai na barka kayi rayuwa mai da蓷i da matar daka aura nima ina fatan nasamu wanda zai soni sona har 茩arshen rayuwa"ta 茩arashe maganar tana goge hawayen kan fuskarta, mi茩ewa tsaye ya yi yana kallonta zuciyarsa fal tausayinta ya ce"Ma'eesha nasan nayi kuskure amma dan Allah karki 蓷auki haka matsayin makamin da zaki cutar da rayuwata har yau har gobe ina sonki kuma inada burin aurenki 茩addara ce ta rabamu amma nayi miki al茩awarin wannan karan bazan bari ta rabamu ba"
"Aikuwa kayi ka蓷an kuma kayi 茩arya domin 茩addara ta rigada ta gifta tsakaninku babu kai babu ita har abada matu茩ar ina numfashi wlh Khalil bazan bari ka zauna da ita ba ko a baya ina fa蓷a maka balle kuma yanzu da ka rigada kayi aure" hankali tashe yake kallon Mommy bashi ka蓷ai ba hadda Ma'eesha wacce tazama kamar statue a wajen kenan har i Wannan lokacin Mommy bata daina tsanarta ba?, har yanzu tana nan akan bakanta na son ganin bayanta?, a baya ta saba da cin zarafin Mommy a gareta tun bata san tsanarta Mommy tayi ba har tayi girman da ta fahimci komai amma tsananin so da 茩aunar da takewa Khalil ya sanya bata iya fushi koda yaushe tana hanyar zuwa inda suke. Bakinsa na rawa ya 茩arasa wajen Mommy yana kallonta ya ce"haba Mommy i think ai mun shige wannan level 蓷in mene haka please?, mene ne aibunta da kika tsaneta har haka?, ya kamata ace ko dan saboda ni ki daina yi mata irin wa蓷annan abubuwan yanzu fa ba da bace Ma'eesha ta girma tasan kanta zata fahimci duk abinda kike mata dan Allah Mommy stop it" juyowa ya yi da niyyar yiwa Ma'eesha magana saida ko inuwarta babu tun sanda ya bar gabanta ta fice daga parlon, dafe kansa ya yi sannan yabi bayanta.
Tsaye ya sameta jikin corridor tana goge hawayen fuskarsa gudun kada General ya gani, rungumeta ya yi ta baya hakan yasa ta sake fashewa da wani sabon kukan na takaici jan hannunta ya yi bai ce mata komai ba ya bu蓷e wata 茩ofa suka shiga kai tsaye kuma waje suka fito motarsa ya bu蓷e ya zurata ciki sannan shima ya shiga ya yi mata key suka bar gidan, kwafa Mommy tayi tana sakin curtains 蓷in ta ce"dani kake zancen wlh" ta shige bedroom ta 蓷auki wayarta ringing 蓷aya matar ta 蓷auka Mommy ta ce"kina ina Hajiya?" daga 蓷aya 蓳angaren ta ce"kin ganni nan ina gida lafiya?" girgiza kai Mommy ta yi ta ce"gobe ki zo zaki rakani unguwa" okay kawai ta ce sannan ta kashe wayar ta shiga safa da marwa cikin 蓷akin sai kuma ta fita.
Tura 茩ofar tayi ta shiga wani ha蓷a蓷蓷en bedroom 蓷in ya yi kyau sosai zaune ta hangeta tana danna wayarta hankali kwance tsaki Mommy ta yi sannan ta 茩ara sa gabanta tana fincike wayar 蓷ago kanta tayi tana turo baki sai a sannan na kalleta fara ce tasa amma ba wata kyakkyawa ba kana ganinta kasan idanunta a bu蓷e suke tasan duniya zama Mommy tayi gefenta ta ce"shashasha kina nan kina danna waya bakisan halin da ake ciki ba" turo baki tayi ta ce"to dan Allah Mommy me zanyi ai bansan meya faru ba kuma kinzo kina min fa蓷a" girgiza kai Mommy tayi ta ce"to idanma zaki daina wannan shashancin ki daina idan kuma ba haka ba nan da 拼an kwanaki kiji ance mijinki ya 茩ara aure" da sauri ta mi茩e zaune tana kallon Mommy da manyan idanunta ta ce"Mommy kamarya mijina?, mene ya samu mijin nawa aure kamarya?" ajiyar zuciya Mommy ta sauke ta ce"kamar yanda kika ji na fa蓷a miki dan Khalil na gab da 茩ara aure" mi茩ewa tayi tsaye tuni attachment 蓷in kanta ya wargaje ciki tashin hankali take cewa"dan Allah Mommy ki daina yimin irin wannan wasan haba, ina Khalil 蓷in yake?" kama hannunta Mommy ta yi ta zaunar sannan ta ce"bari kiji na fa蓷a miki kinsan yarinyar da yake so da can baya har na sanya yabar 茩asar saboda kada ya aureta to yanzu daya dawo tazo gidan nan 蓷azu da babanta kuma Khalil ya nuna har yanzu yana sonta kuma yanda ya nuna ma nan gaba ka蓷an zai aureta" 蓷ora hannunta tayi a ka cikin tashin hankali take cewa"nashiga uku Mommy wayyo Allahna dan Allah ki hanashi wlh bazan iya zama da kishiya ba" tsaki Mommy tayi ta ce"ke amma anyi shashashar yarinya Macen kikewa kuka?, kishiyar da ba'a yi miki ba?, to ni bazan lamunci kiyi kishi da wata ba bare kuma Ma'eesha dana tsaneta tun tana 茩arama kibar komai a hannuna daga wajenki kawai inason ki tubure ki nuna ke ciwonki ya tashi karki kuskura ki bari ya gane ba ciwon gaske bane ya tashi nikuma duk sauran zanyi" jikinta na rawa ta mi茩e tsaye zata yi waje Mommy ta ce"gidan ubanwa zaki?" "Mommy zanje na kwanta ne kafin ya dawo" murmushi Mommy tayi sannan itama ta mi茩e ta fice.
*Riyadh*
*Al Olaya residence*
Yana gama breakfast 蓷in ya fito cikin cikin wata jallabiya ash colour gashinsa ya sakeshi ya kwanta kan bayansa kallonta ya yi ganin yanda take hawaye har sannan, girgiza kai Zaki ya yi sannan ya 茩araso gabanta yana kallonta ya ce"tashi tsaye" girgiza masa kai ta yi tana yarfe hannu ya ce"bazaki tashi ba?" kamar zatayi kuka ta ce"ni to bazan iya tashin ba 茩afana yana zafi sosai" dan 茩aramin tsaki ya yi sannan ya sanya hannunsa ya 蓷auketa ya fice daga parlon. Kallonsa Muhaira tayi sai kuma ta kalli doctorn kawai ta fashe da kuka ha蓷e ransa ya yi ya ce"zakiyi min shiru ko saina bige bakin?" ko saurarensa bata yiba ta cigaba da kukanta tana ganin likitan ya gama ha蓷a allurar ta mi茩e da gudu tana rungume Zaki tana sakin wani irin kuka gaba 蓷aya sun rigada sun gama gano abinda ya sanyata kukan hakan yasa Zaki ya ce"kidaina wannan abun ki fito ko ranki ya 蓳aci" sake zagaye hannayenta tayi a jikinsa ta ce"dan Allah kar ayimin allura wlh naji sau茩i babu zafi yanzu" cikin son shawo kan rigimarta ya ce"babu zafi?" gya蓷a masa kai tayi ya ce"to zo naga" da sauri ta dawo gabanshi ya sanya hannunsa ya jawota jikinsa ya rungume ya ce"to fa蓷amin mene yake damunki da?" cikin sanyin murya ta ce"茩afata ce tana ciwo sai kuma kaina, gashi 茩irjina yana min zafi sosai kuma..."maganar ta tsaya sakamakon allurar da taji an tsaka mata da sauri ta sake shigewa jikinsa tana sakar masa cizo murmushi kawai ya yi sannan ya ajiye sringe 蓷in yana shafa bayanta ya ce"shhhh ki daina kukan ya isa haka" kamar yana sake tura ta haka ta cigaba da yi masa kuka ya ce"Shikenan kiyi shiru zan siya maki chocolate da ice-cream" cikin shashshekar kuka ta ce"ni a'a banso ka maidani gurin Baba banason nan Papi" shafa kanta ya yi bai ce komai ba yana ji har ta fara sauke numfashi a jikinsa alamar bacci ya 蓷auketa. Cikin nutsuwa likitan yake masa bayani ya ce"Sir yarinyar nan tana 蓷auke da cutar Asthma sannan kuma reason 蓷in dake sawa ta dinga ciwon 茩afa jininta AS ne babbar matsalar kuma ita ce tanada ciwon zuciya wanda yake gab da kaiwa matakin 茩arshe" da sauri Zaki ya kalleshi sai kuma ya kalli Muhaira wacce take rungume 茩irjinsa Allah mai iko wannan 拼ar 茩aramar yarinyar da ciwon zuciya abun akwai tausayi sai a sannan maganganun aljanun jikinta suka dawo kansa kenan idan da gaske suke ita 蓷in batada kowa kenan?, amma kuma ai a wajen 蓷an uwanta ya siyeta something fishy!.
Maganar likitan ce ta dawo dashi daga tunanin daya tafi ya ce"Sir akwai bu茩atar a dinga kulawa da ita da abinda zata ci da wanda zata sha sannan kuma kada a dinga yawan 蓳ata mata rai dan hakan zai iya haifar da matsala" duk wannan maganar da ya fa蓷eta ne da harshen labarci, gya蓷a kai Zaki ya yi sannan sukayi sallama ya fito daga asibitin kai tsaye kuma gida ya nufa da ita.
*FCT, ABUJA*
Hannunsa ri茩e cikin na Ma'eesha ya ce"idan Allah ya kaimu gobe zan zo dan Allah eesha ki cire komai daga ranki karki bari wani abun ya samu lafiyarki" gya蓷a masa kai kawai tayi sannan ta sauka daga motar ta shige gida, saida ya daina hangota sannan ya juya ya bar gidan zuciyarsa har sannan cike take da 蓳acin rai koda wasa bai ta蓳a zaton abun zai zama haka ba da bazai ta蓳a barin Ma'eesha ba a wancen lokacin. Kallonta Farooq ya yi har ta 茩araso gabansa tana shirin shige shi ya ce"Ma'eesha!" yanda ya fa蓷i sunan nata ne tagane something not good hakan yasa ta dawo ta tsaya amma bata ce komai ba, mi茩ewa tsaye ya yi yana kallonta ya ce"uban wane ya kawoki gida?" shiru Ma'eesha tayi masa dan idan ranta yana 蓳ace to bata iya magana, sosai shirun nata ya tunzura Farooq hakan yasa cikin 蓳acin rai ya ce"kee dan ubanki ni nake miki magana kina jina?" wani kallo tayi masa sai kuma ta haye sama da sauri batareda ta bashi amsa ba, kwafa Farooq ya yi ya tsaya for some minutes sai kuma ya bi bayanta.
Kwance ya tarar da ita sai rusa kuka take kamar wacce aka cewa Mami ko General ya mutu, cikin 蓳acin rai Farooq ya ce" bari na sanar dake wani abu duk ranar dana sake ganinki da wannan guy 蓷in wlh sai na lahira ya fiki jin da蓷i sai na 蓳ata miki rai fiyeda tunaninki ki dinga kula 蓷an iska yaro saboda kinason jawo mana abun magana" a fusace ta mike tana kallonsa cikeda tsiwa take cewa" wlh saina kulashi babu ruwanka da wanda zan kula da kuma wanda bazan kula ba abinda nakeso shine wanda zan yi ba wanda kai ka za蓳amin ba tunda kai ba ubana bane nayi maka biyayya a baya wacce hakan ta jefani cikin wani hali har yanzu kuma ban fita daga cikinsa ba saboda haka wannan karon bazan ji maganarka ba indai akan Khalil ne" ta shige toilet tana buga 茩ofar da 茩arfi. Kwafa ya yi sannan ya juya shima ya fita daga dakin yana buga 茩ofar, jingina tayi da kofar ban蓷akin ta fashe da wani sabon kukan inama bata bi Father ba, inama tayi zamanta a gida wata茩ila bataga abinda zai tayar mata da hankali ba inama ace mafarki take wanda zata farka yanzu nan, ganin lokaci na tafiya yasa ta 蓷auro alwala ta fito tayi sallah sannan ta kwanta kan gado ko zata samu sau茩in abinda takejin yana yi mata yawo cikin ranta.
*Al Olaya residence*
Da mamaki Zaki yake kallon tarin motocin da suka yi parking harabar gidan ta蓳e bakinsa ya yi sai kuma ya 蓷auko Muhaira wacce har sannan take bacci ya shiga takawa da ita cikeda isa. Turus ya yi sanda ya shiga parlon saboda idanu biyu da sukayi da Dmash wanda yake zaune kan kujera shida tawagarsa a gefe, yana ganin ya shigo ya mi茩e tsaye kana ganin fuskarsa kasan ransa a 蓳ace yake yana zuwa bai yi wata wata ba ya sauke masa lafiyayyen mari a fuska ji kake tassssss, runtse idanuwansa ya yi lokaci 蓷aya jijiyoyin kansa suka tashi above 2mins kafin ya bu蓷e idanunsa yana kallon Dmash wanda yake tsaye gabansa da sauri Muhaira wacce 茩arar marin ya tasa ta fashe da kuka tana rungumeshi ta ce"Papinaaaa" gam Zaki ya ri茩eta a jikinsa yana kallon Dmash ya ce".
*Dommmmmmmmmmm馃槀*.
# *Unconditional love*
# *Trafficking*
# *Incident*
# *Destiny*
# *SQUAD 2024*
# *Nanameera ce!鉁嶏笍*.