Free chapter · Read without an account
{50..}
Da sauri ta sunkuyar da kanta tana jin tamkar ana soka mata mashi a zuciya tsabar takaici, dan kansa ya sakar mata hannun tinda ya lura bakin tsiwar ya mutu, zubewa tayi kan carpet tana jin kamar shoulders dinta zasu zube ta fara shessheƙa a hankali, a bit relief Nurain ya juya ya nufi door, har cikin zuciyarsa baiso hakan ba amma he can't stand it, wnn mitsilar yarinyar tana masa rashin kunya, daga abin alkairi sai ya koma tsiya, ai kwa ta zauna da yunwarta, Hajar ta goge hawayen cheeks dinta, ta kai hannu ta shafa lips dinta waiko ya fashe don har taste din blood ta ringa ji a bakinta, ta ɗago kanta tace "Allah sai ya saka min muguntar da ka min, kuma wllh da bakina ya fashe bazan haƙura ba..", ganin ya juyo yana kallonta da mugun sauri ta wawaki ƙasa ta miƙe ta shige bathroom a guje ta saka lock. girgiza kai kawai Nurain yayi ya bar ɗakin, downstairs ya sauka ya kammala cin abincinsa, ya kashe kayan kallo da bulbs kafin ya haura sama zuwa room dinsa, washe gari tin 8 Nurain ya bar gidan cause Friday ne, ba zai jima a hospital ba baifi yayi spending 2hours ba. Hajar ta fito daga wanka ɗaure da towel da ya tsaya mata a guiwa ta rufa wani towel din a shoulders, kallon fuskarta ta ringa yi ta jikin mirror, fatar idanunta sun ɗan kumbura kaɗan, ta ringa kallon lips dinta kafin ta kai hannu ta shafasu tace "mugu kawaii", shafe shafenta tayi gaban mirrorn, tana gamawa ta buɗe wardrobe ta ɗauki wata doguwar rigar atamfa wacca aka yiwa ɗinki A line, ta koma gaban mirror ta fesa perfumes kala biyu snn ta gogawa lips dinta lip balm. ta murɗa door handle ta fita, kallon floor din tayi jin ta taka dust, ta koma ɗaki ta sako takalminta snn ta sake fitowa, kitchen ta shiga, yau ma dai da electric tayi amfani da dafa abinda take so na breakfast, tana making tea tana tunanin coffee da ta sha jiya, sai taji dama yau ma ta sake samunsa, a rashin samunsa dai zata sha tea, a palour ta zauna taci abincin tana kaffa kaffa da ƙura don palourn is so dusty, kamar yadda ta saba saida ta wanke utensils din da tayi amfani dasu ta gyara kitchen din shima, da sweeper da packer ta haura sama, tass ta share room dinta daman toilet ta wankesa bayan da tayi wanka, fitowa tayi daga ɗakin ta share corridor har zuwa stairs, bayan ta kai ƙasa da sharar ta tsaya tana kallon palourn, ta yamutsa fuska ta fara kakkaɓe cuisine tana gyara zaman trow pillows, within few minutes ta gama share palourn shima, tayi mopping duk inda ta share ko ina ƙal yana kyalli, acikin kayan da Mami ta bata ta fitar da turaren wuta ta watsa a burner dake ɗakinta da kuma palour, a gefen bed ta zauna tana hutawa da wayarta a hannu tana ƙoƙarin kiran Umma, har kiran ya shiga ya katse Umma bata ɗaga ba, saida ta kira sau uku snn ta haƙura ta ajiye wayar tana sauke ajiyar zuciya, wall clock ta kalla taga 11:40, tana zaune dai kamar prisoner taji kamar ana buga ƙofa, after like 5minutes taji bugun ya canza sound da position, tashi tayi ta yaye curtain din window ta leƙa waje, ta ringa kallon compound din amma ba taga kowa ba. Hajiya ta gyara tsayuwar sandarta tana kallon Aysha tace "wai Allah ƙafafuwana zasu ƙarasa kassarewa..", Inuwa mai gadi da ya rakosu ƙofar kitchen ta backyard yace "bari na kawo miki abin zama Hajiya..", Hajiya tace "ai kwa da ka temakamin ɗan nan..", da sauri Inuwa yaje ya ɗakko mata white plastic chair ya kawo, Hajiya ta zauna da kyar tana cewa "yauwa ka temaki makyankyamar nan kuwa yaro, wai mutanen gidan basa nan ne...?, yace "Alhjn dai ya fita Hajiyar kuma na ciki..", Hajiya tace "au toh, bari mu cigaba da aikin bugawa, kai ka koma bakin aikinka kar ɓarawo ya shigo", Inuwa na barin wajen Hajiya tace "danƙwanƙwa Shatu ya kenan gashi nace direba yayi tafiyarsa...?", Aysha ta turo baki don bata so zuwan ba tace "toh ki tashi mu tafi kawai kinga Yayan baya nan..", Hajiya tace "in tashi mu tafi kamarya, nidai ba tafiya nake me nisa ba ƴar nan bare ma yanzu da ciwon ƙafar ya tasar min..", Aysha tace "innalillah Iron lady toh haka za muyi ta zama a nan..?", Da sauri Inuwa ya tashi ya buɗe padlock din gate jin horn din motar mai gidansa, zuge gate din yayi Nurain ya shigo da motarsa gidan, Inuwa na gama rufe gate din ya wuce parking space, Nurain ya kashe motar kafin ya zare key daga Ignition ya buɗe ya fito, Inuwa ya russuna yace "sannu da zuwa Alhj..", Nurain yace "yauwa mal Inuwa, ya aikin...?", Inuwa yace "Alhmdllh", main entrance din gidan Nurain ya wuce ganin haka yasa Inuwa yace "Alhj daman anyi baƙi suna ta can baya a zaune..", Nurain ya tsuke ido sai kuma ya canza direction ya nufi backyard din, tin daga nesa ya gane grandma din tasa, yana zuwa kusa da ita Hajiya tace "Usuman ashe matarka bebiya ce munfi awa uku anan muna dukan ƙofa, har ruwan dutse muka yiwa ƙofar amma ba a buɗe mana ba..", Nurain yayi ajiyar zuciya yace "ai ba ta nan ake shiga ba..", tace "toh babbar ƙofar muka gaji da bugawa shine mai gadi yace yasan hanya ta baya bari ya rakamu ashe itama a garƙame take..", yace "to taso mu shiga ta can..", Hajiya ta danna sadarta a ƙasa ta fara ƙoƙarin miƙewa amma ta kasa, Nurain ya bata support da hannunsa ta miƙe da kyar tana tatata maɗagyas maɗagyas suka wuce gaban gidan, Nurain ya buɗe musu ƙofa, Hajiya ta ringa kallon palourn dake tashin ƙamshi mai daɗi tana gyaɗa kai kafin ta zauna kan sofa, Nurain ya zauna gefenta suka gaisa, Aysha da ta zauna kan one sitter ta zamo ƙasa tace "Yaya ina kwana..", yace "lfy lou Esha, how are you doing..?", tace "fyn alhmdllh..", yace "good yasu Ummi..", tace "suna lfy alhmdllh..", yace "to alhmdllh..", Hajiya da take ƙarewa palourn kallo tace "toh ni ina matar gidan ne munyi wani ƙwamm a palour sai kace namu..", Nurain yayi kamar baiji ba, wayarsa ma ya ciro ya fara dannawa, Hajiya tace "wai ina matar taka ne Usuman..?", yace "nima fa yanzu na dawo daga aiki Hajiya ba nace ga inda take ba..", Hajiya ta saki baki tana kallonsa tace "yau naga ikon Allah matar taka ce baka san inda take ba..?", ya ɗaga kafaɗa yace "tana cikin gidan nan amma bansan a ina ba, Esha dubata upstairs..", Aysha tace "tom" ta tashi ta haura upstairs, da kallo Hajiya ta bita kafin ta dubi Nurain ta jinjina kai, babu jimawa saiga Aysha nan na sakkowa Hajar na biye da ita da hijab a jikinta, suna ƙarasowa palourn Nurain ya tashi ya haura sama, nan ma dai da ido Hajiya ta bisa, kan carpet Hajar ta zauna ta gaida Hajiya cike da ladabi, Hajiya ta amsa tana ƙare mata kallo, jim kaɗan Hajar ta tashi ta shiga kitchen ta kawo musu ruwa da lemo ta haɗo da uban kayan gara plate huɗu, plate din chin chin daban hakama na dubulan Alkaki da nakiya, Aysha taci kayan garar ta abinta tasha lemo, Hajiya kam babu abinda taci yawunta nata tsinkewa, majestically Nurain yake sakkowa daga stairs yana gyara wrist watch dinsa, ya canza kayan jikinsa zuwa wani white yadi mai ɗan uban laushi, gaba ɗaya palourn ya ruguntsume da scent dinsa, yana kallon Hajiya yace "me zaku ci zan fita saina taho muku dashi..?", Hajiya tace "A'a ba mazauna bane mu kam, ai tafiya zanyi, tafi damu ka ajiyeni wajen Muntari..", yace "Ohk, toh muje..", Hajiya ta dubi kayan garar sai kuma ta kalli Hajar tace "nidai idan anyi niyyar bani toh a kwashe min abina a leda na tafi dashi..", a kitchen Hajar ta lalubo leda ta juye kayan garar, tana miƙawa Aysha ledar suka haɗa ido dashi, da sauri ya ɗauke kansa ya fita waje, ta bisa da wata shegiyar harara, a balcony ya tsaya yana jiran su fito ya rufe ƙofar, Hajiya ta fito snn Aysha, har zai rufe ƙofar sai gata nan tsulum ta fito itama tayi tsaye bakin ƙofar tace "ku gaida gida..", Hajiya tace "da nazo da man zafi ai da kin taimakawa ƙafafuwan nan..", Hajar dai tayi murmushi ba tace komai ba, Hajar ta cake bakin ƙofa da gayya taƙi komawa ciki, kallo ɗaya Nurain ya mata ya raɓa ta gefenta ya cire keys din dake jikin ƙofar, ta dubesa da wutsiyar ido ta riƙe ƙugu, front seat ya buɗewa Hajiya ta shiga kafin ya zaga driver seat, kallon main door din gidan yayi, har lokacin Hajar na tsaye riƙe da ƙugu ta banka masa harara, motar ya shiga bayan Aysha ma ta shiga ya ja suka bar gidan, suna fita layin Hajiya tace "da tini na yiwa kaina buƙulu, raina yana son cin kayan zaƙi gashi kuma ina tsoron cikina da bai gama saduda ba, gwara da banyi sagegeduwa da nauyin baki ba nace a zubomin kayana na tafi dashi, gashi kuma yarinyar ba ta da rowa ko kaɗan, ji fa yadda ta jibgo mana kayan zaƙin..", Nurain dake driving yana jinta yace "kar dai kici wnn abun..", tace "a sbd me..?", keenly yace "bashi da kyau ga lfyrki", tace "Eh haka fa, har yaushe ka zama likitan da zaka hanani shan zaƙi, ni da ba ciwon siga ba sai a hanani shan zaƙi, Allah bai ɗoramin cuta ba bazan yiwa kaina cikas ba..", a gidansu ya ajiye su Hajiya, bai ma shiga ba ya juya don zuwa masallaci sallar Juma'a.
★Umma daga bakin gadon da aka kwantar da Mu'azzam, yanxu aka fito dashi daga aikin da aka masa na karayar hannu da gocewar ƙashi a ankle, gaba ɗaya jikinsa bruises ne ga uban bandage da aka nannaɗe masa kai, Umma ta goge kwallar idonta tace "sannu Mu'azzam..?", ya gyaɗa mata kai a hankali, tace "wllh Allah ya isa ban yafe ba Allah ya saka maka cikin gaggawa, duk wanda ya maka haka shima ba zai ga daidai ba..", ta ringa goge hawayen da yake zuba idanunta da ƙasan hijab, yadda taga rana haka taga dare, gashi ba a dubasa da wuri ba saida aka kira police wai ba a duba mutum da irin condition din saida police, Naseer ne yayi ta ɗawainiya har aka samu likitoci suka dubasa, Baba ne ya shigo ward din tare da Naseer, kana ganin Baba kasan shima damuwa da rashin kwanciyar hankali sun samu matsugunni a jikinsa, idonsa ya faɗa ciki kuma yayi ja, gefen gadon ya tsaya yana kallon Mu'azzam yace "sannu kaji", Naseer yace "Umma ko zaki je gida ki ɗan huta zuwa anjima saiki dawo ko..?", Umma ta girgiza kai tace "A'a Naseer ai ban gaji ba..", Baba yace "gida xaki tafi kuwa faɗima, ki kwantar da hankalinki, yanzu haka ma ƴan sanda suna nan suna neman yaran da sukay wnn taɓargazar, insha Allah zasu zaƙulosu..", Naseer yace "ai ƴan daban unguwarmu ne, ni nama san yaran ance Bisi ƙwale da ƙwage sai kuma wasu su uku ne ai, har kangon da suke zama muka je da kuma gidansu tare da ƴan sanda amma basa nan sun gudu, tinda dai an sansu kamasu bazai yi wuya ba insha Allah..", Umma tace "toh me yaron nan yayi musu in banda rashin imani suka masa wnn aika aikar..", Naseer yace "ƙwaya ce ta gaya musu ba daidai ba, a yadda nasan ƴan daba ai basa taɓa wanda ba ɗan uwansu ba, Umma kiyi haƙuri zasu gane kurensu ba bulus suka ci ba..", Baba yayi ajiyar zuciya yace "zo ki tafi gida kin dawo anjima sai ki taho masa da abinci ma...", Umma ta gyaɗa kai ta duƙa tace "Mu'azzam me kake son ci..", yace "komai ma Umma..", wajajen sha biyu Umma ta isa gida, tana shiga ta tarar da Sabra a bakin rariya, ga nan Uban kayan wanke wanke an tula mata tana yi, duk ta jiƙa kayan jikinta sharkaf, Umma ta kama hannunta ta miƙar da ita daga kan ƴar kujerar da take zaune ta wuce da ita ɗaki, tana bata aiki amma wnn ya mata yawa wanke wanke sai kace na gidan biki. Maama ta fito ɗakinta da ɗaurin ƙirji tana kallon bakin rariya tace "ina shegiyar yarinyar ta tafi kuma ga aikin dana sakata bata kammala ba, kaji figaggiyar yariya da tsula tsiya da iya butulci, idan ba butulci ba jiya cikin dare uwarki ta tsallake ta fita ta barki damu muna miki ɗawainiya, shine daga kema za a more ki shine kika gudu, ina kike munafuka..", Sabra ta kwalalo ido waje tace "Maama na kira na..", Umma ta zare mata ido tace "wuce ki zauna a can kar na ganki a tsakar gida" da haka ta cire hijab dinta ta fita, gawayi ta kunna ta ɗora ruwan abinci, tana daf da gama abincin ta kira Anty Jamilah ta sanar da ita abinda ya faru, Anty tace "innalillah wa'inna ilayhirraji'un yanzu kuna wane asibitin...?", Umma ta gaya mata sunan asibitin, Anty tace "Allah ya basa lfy sai munzo.." Umma na katse wayarta da Anty saiga kiran Hajar, ɗagawa tayi snn tayi sallama, from the other side Hajar tace "Umma ina wuni..", Umma ta amsa a takaice tana tmbyrta ya take, Hajar tace "ina lfy Ummata yasu Sabra da Baba da Yaya..?", Umma tace "kowa lfy Hajara..", jimm Hajar tayi kafin tace "Umma ko bakya jin daɗi ne..?", Umma ta numfasa tace "Mu'azzam ne ya gamu da tsautsayi yana asibiti a kwance", idan hankalin Hajar ya kai dubu to ya tashi, zumbur ta miƙe dga kan gadon da take tana tambayar Umma wane asibitin. deeply in thought Hajar ta ringa kewaya ɗakinta, hankalinta duk baya jikinta, handbag dinta ta buɗe ta duba kuɗin da suke ciki, kuɗin basu wuce 5k ba, tin lokacin da za'a kawota Anty ta bata su tace ta riƙe a hannu, wardrobe ta buɗe ta ɗauki sabon hijab ta saka, gaban mirror ta tsaya tayi rubutu ajikin jotter ta fyalle papern tayi folding dinta, daga ƙarshe ta ɗauki handbag dinta ta sauka downstairs, a kan Centre table ta ajiye papern ta doshi main door ta fita compound, mai gadi dake zauna bakin gate ya miƙe ganinta yace "hajiya wani abun za a amso miki..?", ta girgiza kai tace "A'a fita zanyi..", buɗe mata ƙofar yayi yace "adawo lfy..", a zuciyarta tace ai na fita knn a fili kuma tace "ahaa" daga haka ta miƙi hanya ta fita daga street din.
★Da wani irin weird expression Nurain yake kallon Abba dan ya kasa gane laifin da yayi ake masa wnn faɗan, Abba yace "Uthman idan kana son zaman lfy dani kuma kana gudun ɓacin raina toh karka cutar da yarinyar nan..", Nurain ya kasa cewa komai dan bai gano bakin zaren ba, to wace yarinya Abba yake nufi, Abba yace "ka sayi foodstuff din da nace ka siya..?", Nurain da sai yanxu ya fara fahimta yace "Eh Abba na siya..", Hajiya da ke zaune palourn tana kallon Nurain ta saman kantamemen glasses dinta tace "au a haka ne gidan naka da abinci, yarinya gaba ɗaya ta tsumbure ta fige, in banda haske banga abinda ta ƙara ba, tafi kumari da kyan gani da tana wajen Mami, ai kamata yayi tafi kyau a gidan mijinta tayi ɓulɓul abinta ta baje da kyau amma yarinya duk ta fita hayyacinta sai kace wacca ake zuƙewa jini..", Abba ya sauke ajiyar zuciya, tinda yaji Nurain ya sayi foodstuff ya ɗan sakko, Abba yace "kar inji kar in gani akan yarinyar nan Uthman..", Hajiya tace "muje ka mayar dani gida tinda na gama abinda ya kawoni, tin acan gidan naka naso na maka mgana amma banyi ba sanin cewa kafi jin mganar gyatuminka shiyasa nace gwara na gaya masa kuma daman shi ya ɗakko amanar yarinyar..", Nurain ya harareta ƙasa ƙasa ya tashi ya fita, Hajiya ta bisa da kallo tace "jeka mai baƙar zuciya direba ya kaini ko kuma a taro min ɗan sahu..", ƙarfe takwas da ƴan mintina na dare Nurain yayi parking motarsa a gidansa, entrance ya wuce har lokacin maganganun Abba ba suyi fading a brain ɗinsa ba, ya ɗanyi blaming kansa da abinda Hajiya ta faɗa, yess ya kashe gas din da za ta dafa abinci amma duk da yayi hakan still ba a rasa abinci a gidan ba, akwai kayan shayi snn kuma da electric kettle zata iya haɗa tea tasha. mistake dinsa ɗaya da bai gaya mata ba, toh ta yaya zai gaya mata bayan mara kunya ce ta bugawa a jarida. ya ringa ƙarewa palourn kallo, idonsa ya kai kan center table, haɗe gira yayi yana kallon folded paper dake wajen, ya ƙarasa ya ɗauka ya warware a takaice, kamar dai waccan karon rubutun basu wuce 5lines ba, ƙurawa rubutun jiki ido yayi without blinking "Malam na rage maka hanya yanxu abinda ya rage maka kawai shine ka biyoni da takarda ta gidanmu".....✍️