Free chapter · Read without an account

Chapter 16.

by JamilaUmarJanafty · IDAN AN CIZA..!

*IDAN AN CIZA..!*


*Wattpad:Jamilaumar315*

*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*

*Mallakar:Janafty*


*SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA*


*Page 16*


*4rd May, 2022.*

_Abuja, Thursday_

*03:40Am*


Tun ranar mandoy ɗin da ta gabata Mommy ta so su je Gombe kamar yadda Abi ya bukata amman kuma tana jagorantar wani case a kotu sai ta ga gwara ta tsaya ta gama kafin su tafi. Dole ya sanya ta kira Sulaiman tace ya dakata da Bucking ɗin su ya bari sai ranar jumma'a tunda ranar Alhamis ne karshen shari'an nasu.Sun gama tsara na su amman shi Abin da Ubangiji ya tsara ya sha bambam da tunaninsu.


 A daran Alhamis duk wani shirin tafiya Brr.Murjantu ta gama yin sa saboda Sulaiman ya kirata ya faɗa ma ta jirgin ƙarfe goman safe za su bi zuwa Gombe in Allah ya yarda shi ya sa tunda ta dawo daga wajen aiki ta kasa zama sai faman shiri take yi musu tunda wannan ne karo na farko tun bayan abin da ya faru da shi da zai kara takawa zuwa jiharsa.


 Alhaji Hamza kawai ta kira suka yi mgana Saboda shi zai tura musu motar da za ta ɗauke su daga filin jirgi zuwa gidan Hajiya, Lafiya lau ta gama duka shirinta a daren Abi yace mata ba ya jin daɗin jikinsa yana so ya yi wanka ita ta rarrafa ta ɗora shi saman keke ta kai shi tiolet ta taimaka masa ya yi wanka sannan ta gunguroshi zuwa ɗaki ta shirya shi, sannan ta zo ta yi masa shirin kwanciya a daren sun kwana a jikin juna a baya bata ɗora masa nauyinta saboda yanayin laluransa sai ranar kuma da kansa ya bata umarnin ta matso kusa da shi bayan ta matso sai ya saka hannunsa mai motsi ya jawota gefensa har kanta na matsuwa da ƙirjinsa.


 Manganganun da ya yi ta gaya mata sun bata mamaki da tsoro sai dai ba ta taɓa tunanin tafiya Habibi zai yi barta ba. Ya jadaddamata in har bai samu zuwa Gombe da kansa ba ta taya shi neman yafiyar Hajiya sannan ta yi masa alƙwarin neman yaro nan ta bashi hakuri sannan ta yi masa alkwarin samar ma Mimi farinciki da kuma ba ta abin da take so, a lokacin kallonsa ta yi cikin mamaki kafin Ta ce.


 "Ka daina faɗin haka Habibi in sha Allahu gobe za mu je Gombe, kuma da kanka za ka samu damar neman gafaran Hajiya, sannan kai da kanka za ka yi magana da Mansoor ka nemi yafiyar sa."

Mirmishi ya yi mata ba tare da ya yi mgana ba sai dai ta ga ya yi mata wani iri duk ya sauya mata. Ta san ya yi shekaru yana jinya ƴan'uwanta ba duka ba ne su ka bata goyon zaman jinyar Major Kabir ɗin ba, gani suke zata yi wahala da shi tunda ba ranar warkewa. Ita kuma me ya rage mata a duniya ban da ta zauna ta kula da Mijinta uban Ƴaƴanta domin ta samu rabauta ranar gobe kiyama, Shi ya sa ba taɓa nuna masa gajiyawarta ba tana Ƙoƙari a kansa da amanar gidansa da ƴaƴansu


 Sun jima kafin su kwanta yana ga ya mata wasu irin mganganu ma su kama da kamar mutum yana barin wasiyya sai hankalinta ya tashi ganin haka ya sa sai ya bar mganar ta rumgumshi ta ce su kwana su yi barci gobe suna da tafiya a gaban su.

Barci ne mai nauyi ya kwasheta acan cikin barcin ta yi mafarkin ta ga an taru gida ya cika ana ta kuka kuma taga wai an saka Habibi a makara za'a fita da shi ita kuma ta rike tana ta kuka.


  Kamar an wancakalar da ita haka taji ta a gefe ta bar jikin Kabir, sai da ta tashi a firgice dai dai Lokacin da ta ji ya na tari ba kakkautawa. A firgice ta miƙe ta laluba hannunta ta kunna hasken ɗakin sai ta ganshi kwance in da ta kwantar da shi sai dai kuma tari ya sarƙe shi yana yi kamar numfashinsa zai ɗauke hankalinta ya ta shi sai ta tuna mafarkin da ta yi, ai da gudu ta diro daga kan gado ta isa gare shi tana riƙe shi ƙokarin tarairayosa take yi ta ji yana faɗin"ruwa! ruwa!

Ba tare da tunanin komai ba ta sake shi sai ta kwashi gudu kamar za ta faɗi zuwa falo fridge ta buɗe ta ɗauko masa ruwa mara sanyi tunda Saboda shi ba ta kunna fridge ɗin falo sai dai na Kitchen. Abin da ya sake ba ta tsoro ko da ta koma har ya faɗo daga kan gado ta ruɗe ga ta ita kaɗai ta nufe shi da sauri tana kiran sunan shi.


 " Habibi, Subhanallah!"


 Haka ta ke faɗi dakyar ta iya ɗago kansa domin sai taji ya kara yi mata nauyi ta kafa masa goran a baki ta na bashi ruwan abin da ya sa ka ta fashewa da kuka shi ne ganin ruwan gefe da gefe sai zubewa yake yi kaɗan ne ma ya ke shiga bakin sa.

Cikin muryan kuka ta ce"Na shiga uku ni Murja me ya same ka haka Habibi?

Shi kuma sai ya kauda kansa ruwan ya suɓuce daga hannunta ya ganganra ƙasa inda su ke zaune gabaɗaya ya jiƙa su ita a koƙarinta ta mikar da shi ta maida shi saman gado kamar yadda ta saba dubarunta. Amman yau sai ya gagareta shi kuma tarin na neman ƙara sarƙe shi cikin muryan da ta fara karyewa ba ta ma wani jin sa sossi ta ji ya kira sunan ta.


"Murjanatu.."


"Murjanatu.."


 Da sauri ta amsa da "Na'am Habibi me kake so? Ko na je na kira Megadi ya zo ya taya ni mu ɗora ka saman keken ka?

Sai ta ga ya girgiza mata kai lokaci ɗaya yana riko hannunta cikin sarkewan numfashin da ba ta lura ya fara sama da ƙasa ba ya fara mgana"Murja ki yafe min kin ji? Sannan ki tayani neman gafara Hajiya da kuma afuwar Mimi domin na zalunceta sannan ki yi min alkwarin za ki nemi yaron nan ki ba shi hakuri kuma ki yimin alkwarin yi ma Mimi duk abin da take so saboda farincikinta." Yana mgana cikin In ina saboda mumfashinsa na sarƙewa Mommy ta fashe da kuka kafin tavce"Ka daina faɗin irin haka sai na ga kamar mutuwa za ka yi ka barni Habibi?


 Cikin ƙarfin hali ya ce" Naso na samu damar neman yafiyar su da kaina sai dai lokaci ya kuremin Murja, na amimta dake nasan za ki kula da ƴaƴana ki yi min alkwari guda uku na farko ki tayani neman gafaran Hajiya na biyu ki nemi yaro nan ki tayani neman yafiyarsa, na uku ki yi min alƙwarin yi ma Mimi abin da take so Murja"

Mommy na kuka ta ke ɗaga masa kai lokaci ɗaya tana faɗin"Na ɗauka amman dai in sha Allahu tare za mu je duk ka nemi gafaran su."

Hawaye ke fita ta gefe da gefen idanuwansa ya ce"Ko bayan raina ban amince ki bar gidan nan ba Murja, ko da aure za ki sake yi ki zauna nan ne gidanki domin ki kula da yaran mu."

 Mommy kuka ta ke yi har da majina ta kasa mgana sai da taji ya kara riƙo ta da karfi lokacin tarin ya kara sarƙeshi faɗi yake yi

" Na yafe miki duka laifin da kika taɓa yi min Murja wanda kika sani da wanda ba ki sani ba , nima ki yafe min duk zaman kuncin da na yi da ke a baya ki yafe min Murj...'

Sai ya kasa karisawa domin tarin ya sarkeshi kuma yana tafiya da numfashinsa yadda Mommy ta ruɗe ne yasa ba ta fahimci lokaci ya kure ba. Domin a lokacin ana kokarin zare ran Abi ne, ita a tunaninta ba ta makara ba ya sa ta sake shi ta mike a guje ta fita haraban gidan tana kururwan kiran ma'aikatan gidan.


 Allahu akbar ko da suka taso da gudu suna tambayan ta ko lafiya ta rika nuna musu cikin gida tana faɗin sunan Habibi tana wani irin kuka yasa su ka kwashi gudu zuwa cikin gidan har vikin bedroom ɗin su suka iske Abi kwance a kasa idanuwa sun kafe ba ya motsi. Megadin gidan dattijo ne na yanzu tun bayan yin ritayansa shi ya duba Abi ya tabbatar da rai ya yi halinsa itama kuma a koƙarin Mommy a kama mata shi su je asibiti har ta saka mayafi tana faman kiran can asibitin in da Dr Ashiru ke aiki. Megadi ya kalleta duk ta fita hayyacinta sauran ma'aikatan ma maza tuni sun fara salati matan kuma kuka suke ganin yanayin Hajiya duk ta fita hayyacinta ta ruɗe.

 Tsawa ta daka musu lokaci ɗaya tana faɗin"Ku kama min shi mu fita waje,asibiti za mu je a duba shi."

Kai Baba Megadi ya girgiza kafin ya ce"Hajiya sai dai mu yi hakuri Allah ya yi ma Alhaji rasuwa."


"Rasuwa? Habibi ne ya rasu?


 Ai ba ta san lokacin da ta yi kansa tana kiran sunan shi ba, lokacin har megadin ya saka hannu ya shafe masa idanuwansa, Allahu Akbar Kullu Nafsin Za'ikatul maut kowani rai sai ya ɗanɗani zafin mutuwa Allah ya sa mu dace.

Mommy kamar ta zare ko na ce ta yi hauka haka ta ke rike gawan Abi tana wani irin kuka ta surutai faɗi take yi"Habibi me ya sa ka yi min haka? Ka tafi ka barni Wayyo Allah na shiga uku na lalace."

Ma'aikatanta mata ne ke tare da ita mazan daman guda uku ne megadi sai direba da mai kula da haraban gidan. Matan kuma mai girki wata bakatafiya ce saira sai mai gyaran gida wata yar matashiyace mai suna Aina'u daga can gidan su kano aka aiko mata da ita saboda su taya ta taimakon gidanta da mijinta. Har gwara Saira da shekarunta ita ke ba ma Hajiya hakuri su kansu ma kukan su ke yi Aina'u kuma sai mutuwar iyayenta suka dawo mata sabuwa itama gefe ta samu ta zauna ta na faman rusa kuka jikinta sai rawa yake tunda take a duniya ba ta taɓa ganin gawa ido na ganin ido ba sai yau.


 Abi ya cika misalin 3: 50am na daren ranar Jumma'a ne kuma Mommy ba ta iya kiran kowa ba saboda tashin hankali har aka kira sallar asuba gwan Abi na jikinta ta rumgume ta yi kuka har muryanta ta daina fita tunaninta gabaɗaya ya toshe, da ita da su Sara tare su ka yi wannan zaman acikin ɗaki tana kuka suma suna tayata.

Sai wajen shida saura na safe sannan Megadi da su Habu suka sake shigowa ganin halin da Hajiya ke ciki ya sa Megadi ya durkusa a gabanta yana faɗin" Hajiya ki yi hakuri ki daina kuka don Allah, ya kamata ki kira waya ki sanar da su abin da ya faru ya kamata a suturta Alhaji domin a yi masa gata a kaisa makwancinsa na gaskiya."


 Mommy ta kalleshi da Idanuwanta suka rine saboda kuka sai a lokacin ta fahimci abin da ya kamata ta yi, ta kuma kara samun tabbacin Habibi ya tafi ya barta, Dole ta janye daga gareshi suka kamashi suka matsar gefe suka rufa masa zanin gado suka rufe shi su Sara kuma sai su ka koma falo suka zauna jugum tare da su Habu. Mommy kuma wayarta ta ɗauka amman ta rasa wanda za ta kira a daidai wannan lokacin sai kira ya shigo wayarta ta na dubawa sai ta ga kamar Alhaji Hamza ne saboda ba ta ma wani gani sosai da hanzari ta ɗauka ba ta jira maaganarsa ba ta faahe da kuka tana faɗin

"Abban Jaheed Habibi ya rasu, na shiga uku na lalace Habibi ya tafi ya barni."

Haka ta ke faɗi muryanta na sarƙewa saboda kuka.

Daga can bangaren Sulaiman ya yi zumbur ya miƙe daga kishigiɗan da ya yi cikin wani irin razana yace"Innalillahi wa'inna ilahirraju'un Mommy Abi ne kika ce ya rasu? Sai a lokacin ta fahimci ba Alhaji Hamza ba ne Sulaiman ne. Sai kawai ta koma ta sulale a kasa ta na kara fashewa da kuka Lokaci ɗaya tana fadin"Sulaiman kun zama marayu yau Abin ku ya tafi ya barmu."


 Ta ma kasa mgana sai wani irin gunjin kuka kawai take yi. Daga can Bangaren Sulaiman ya katse wayarsa da Salati mai ƙarfi a bakinsa wanda ya taho tare da hawaye masu zafi daga kuncinsa.

Matarsa Jawahir na Kitchen tana Koƙarin yi musu abun karyawa tunda zai fita da wuri yana da tiyata karfe takwas ɗin safe sai dai taji salatin mijinta da karfi da yasa ta baro kitchen din da gudu zuwa Bedroom ɗin su nan ta iske shi zaune a kasa dafe da kansa da sauri ta ƙarisa gabansa cikin tashin hankali ta kira shi da sunan da take kiran shi.


"Darling me ya faru na ji kana ta salati haka?


 Sai ta ga mijinta uban ya'yanta gwarzon namiji irin Dr.Sulaiman ya ɗago fuskarsa ta yi kaca kaca da hawaye cikin razana ta ce"Innalilllahi Darling me ya faru?

Cikin Wani irin sauti ya ce"Jawahir na rasa mahaifina, Abi ya rasu."

Cikin wani irin sauti ta furta"Hasbunallahi wa'imal wakeel, Innalillahi wa'inna alaihirraju'un."

Ta faɗa lokaci ɗaya a na ƙariswa gare shi ta zauna kusa da shi ta rumgumosa sai kawai ya faɗa jikinta ya fashe da kuka yana faɗin "Mommy na can ita kaɗai ba kowa a wajenta, Jawahir na zama maraya Ƙannena sun zama marayu mahaifiyata ta zama bazawara Ƴayana sun rasa kakansu, ki shirya su Momi bari na yi mana bucking ɗin jirgi yanzu nan."


 Da sauri kuma ya mike ya ɗauki wayarsa sai da ya sama musu Jirgin da zai tashi zuwa Abuja da Safa nan sannan ya kira asibitin su ya shaida musu halin da a ke ciki, dole a ka sauya sunan shi da wani Dr Ishaya, sannan daga baya ya kira Alhaji Hamza Saboda Mommy mace ce yadda ma ta ruɗe ya tabbata ba za ta iya kiran kowa ba shima ya tashi yana jin wani irin kasala a jikinsa kiran da ya yi daman ya gaisa da iyayen na shi kamar yadda ya saba duk safiya kafin ya fita aiki.


 Alhaji Hamza ya ji mutuwar ɗan uwansa ya na tare da Anty ne lokacin da Sulaiman ya kira shi ya na sanar da shi yayansa Major Kabir ya rasu jiya da daddare.

Salati kawai ya ke ta maimatawa ba shi kaɗai ba duka matansa da ya'yansa sun ruɗe da jin wannan mutuwar daman Sulaiman ya ce ba ya tunanin Mommy ta kira wani shi ya je ya sanar da Hajiya shi kuma yanzu zai kira su Madiha ya sanar da su. Allah ya taimaake shi wayar mijin Madiha ya kira ya sanar da shi abin da ke faruwa shima ya ruɗe yace bari ya nema musu Jirgi.


 Dr. Sulaiman cikin wani yanayi ya ce"Ka ga ya ma Madiha cikin hikima saboda kada ta ɗaga hankalinta."

Cikin tsananin tausayin su ya ce"In sha Allahu Dr, Allah ya jiƙan Abi."

Ya amsa mata da Amin wayar mijin Khadija ya kira sai kuma kawai ya ji ita ta ɗaga Wayar cikin karaɗinta ta ce"Dr yau ni aka tuna shi ne a ka kira mu da sassafe?

Sai ya kasa gayamata ya ce ta mika ma Mijinta wayar, yanayin muryansa ya sa sai da gabanta ya faɗi cikin in ina ta ce" Dr me ya faru? Jawahir da yara suna lafiya ko?

Kai tsaye ya ce"Ki ba ma Muhammad wayar da shi zan yi mgana."

Tun daga nan ta san wani abu mara ɗaɗii ya faru sabo ba ta mantawa lokacin da Abi ya samu hatsari Dr Sulaiman ɗin ne ya kira sannan ya ƙi magana da ita sai da Muhammad. Daman ya shiga Tiolet ne ya na fitowa jikinta na rawa ta mika masa wayar ta kuma lafe a kunnensa domin ita jikinta ya bata wani abu ne ya faru.

Sai dai ta yi nadamar yadda ta kara kunnenta ta jiyo ma kanta abunda ya kusa tsaida numfashinta.

Ihu ta rika yi da kuka tana faɗin "Innalillahi Abi ne ya rasu? Na shiga uku na lalace"

Muhammad ke kokarin lallashinta amman kuma taki sauraran shi. Ba su samu jirgi ba sai suka shirya tafiyan mota tunda daga kaduna ne zuwa Abuja. Khadi sun yi mgana da Madiha kowacce murya ta shake suna yi ma juna gaisuwan rashin da suka yi madiha ta ce yanzu za su taso ita kuma Khadija ta ce suma ga su nan a hanya. Khadi ce ta kira wayar Mimi sai dai tana ta ringing ba'a ɗauka ba wayar Hajiya ma haka , sai ta kira wayar Mommy sara ta ɗauka ta ce Mommy na cikin ɗakin da Abi yake, Sai khadija ta kara rushewa da kuka ta kosa su isa Mommy ba za ta iya ɗaukan wannan rashin ba ita kaɗai ba.


 Ko kafin takwas na safe a kafafan Sada zumuta duk an saka rasuwar da sauran duk wanda ya kamata yaji rasuwar Major Kabir ya ji, musamman gidan Talabijin na Karamchi a Safiyar ranar suka tashi da wannan alhinin domin ko da Alhaji Hamza ya isa gidan Hajiya Mimi ta bar gida zuwa wajen aiki tunda labaran Safe gareta.

Tana ɗakin Labarai ana gyara mata fuskarta Wayar Daddy ta shigo mata sai da gabanta ya faɗi a lokacin ba ta ji kamar za ta faɗi ba sai da ya ce ta bar komai ta taho gida ita ta sadakar Hajiya ce ta rasu daman ta barta kwance ta na gayamata ba ta jin ɗadin jikinta. Haka ta bar wajen aiki a afujajan sai dai abin da ta je ta ji ne yasa ta ruɗe ta kasa mallakan kanta

Hajiya kuma sai ta yi dauriya ita ke lallashin Mimi Alhaji Hamza kuma ya na amsa wayoyin mutanen domin in za'a saka rasuwar Major Kabir sai an ce Yayan Alhaji Hamza tsohon Sanatan jihar Gombe.

Rukky ne ta yi ta kiran wayar Mimi ba ta ɗauka ba, saboda su san abin da ke faruwa sai Mimin ta rubuta sako ta tura mata.


"Rukayya ki sanar da Manaja Abuja za mu wuce yanzu Allah ya yi ma Abi rasuwa."


 Allahu Akbar zukata sun raunana yawancin mutane ma sanarwa da gidan talabijin na karamci ta yi ne su kasan abunda ya faru ciki har da Inna Meri da ta na ma cikin ɗaki lokacin suna cikin karanta labaran duniya na Safe bayan sun gama suka sanar Walida ce ta rugo ɗaki da guda tana haki ta ce"Inna yanzu nagani a Tibi ana faɗin Allah ya yi ma mahaifin mai karanta labaran na rasuwa Mimi."

Da Sauri inna Meri ta mike ta fita falo Sai ta ci karo da hoton Major kabir cikin kakinsa Soja ana sanar da rasuwarsa jiya da Daddare za'ayi jana'izarsa yau Jumma'a bayan an sauko daga sallar Jumma'a a gidansa dake Gwarimpa a Abuja.

Ba za ta manta da fuskarsa ba ta gane shi Allah Sarki rai bakon duniya daman ai ƴarsa ta ce ba shi da lafiya duk sai jikin Inna Meri ya yi sanyi a fili ta kaɗa kai kafin ta ce"Allah ya jiƙan sa da Rahama mu kuma Allah ya kyautata ta mu bayan tasu."


 Walida ta amsa da Amin ita ba ta san shi ba amman ai ta san Mimi budurwan yayansu ne a baya kuma Inna Meri ta san su shiyasa ba ta yi mamakin ganin yadda jikin Inna Meri ya yi sanyi ba. Suna zaunen Baba Ɗanjuma ya shigo cikin shirin fita yana ga ya mata shima Jana'iza zai je ƙanin Mallam Hashimu ne ya rasu.

Ta yi salati kafin itama dire da faɗin "Kai Jama'a ana ta tafiya nima yanzu nake ganin sanarwan rasuwan mahaifin yarinyar nan da Baban Inna ya so mai karanta labarai anan yanzu suke faɗi jiya da dddare ya rasu." Baba Ɗanjuma ya ce"Innalillahi wannan Sojan? Inna Meri ta gyaɗa masa kai sai kawai ya jinjina kai kafin ya ce"Allah ya jiƙan su da rahma Allah yasa Aljanna makoma"

Shima yana tunawa da shekarun baya ne har an zo an gama jin ɗadin duniya kuma an koma. Kai Allah yasa mu dace, Allah ya sa mu mutu muna masu Imani Amin.


******


Kamar yadda aka sanar an yi Jana'izar Marigayi Major Kabir Sulaiman Dabo a gidansa bayan sallar Jumma'a Alhamdulillah ya samu jama'a kama daga yan siyasa abokan hulɗar Daddy tare da Abokan aikin Abi sojoji ritayas kamarsa har da masu kakin a lokacin sannan tare da mazajen yayan shi da kuma sai yan'uwa da abokan arzuka tare da dangin Mommy daga kano aka sallace shi zuwa gidansa na gaskiya. A ka bar mata acikin gida suna kuka sak abin da Mommy ta gani a mafarki shi ya faru ta riƙe gawan mijinta tana wani irin kuka sai da ƙanwarta Zainabu ta zo ta riƙe tare da sauran yan'uwanta da su Mama ko da aka fita da shi sai ta faɗi a sume ita da Mimi. Madiha da Khadi kuma sun kasa mallakan kansu ma.

Alhaji Hamza da Sulaimam suka yi ma Major wanka suka haɗashi saboda nisan makabartan sai bayan la'asar suka dawo daga kaishi. A makabarta Sulaiman ya sha kuka shi da Alhaji Hamza Jaheed ma ya iso da shi akayi jana'iza.

Shi ne ya rike sulaiman ɗin ya tada shi daga gaban kabarin Abi likita ne mai dakiya amman ya yi rashin bangon da har abada ba zai iya maida kamarsa ba.

Suna dawowa aka kafa tantuna a haraban gida domin zaman makoki.


 Hajiya kuma ta yi tawakkali tana zaune da hijabi da carbi ko hawayenta ba wanda ya gani Lokacin da aka tafi kai shi bayan Mommy ta farfaɗo ta fara surutai tana faɗin

"Habibi yace na nema masa gafara wajen Hajiya, Hajiya ki yafe masa ya rasu da niyar a yau mu je Gombe ya durkusa ya nemi gafaran ki, ke ma Mimi da ke ya rasu kina bakin shi faɗi yake yi Murjanatu ki yi min alkwarin yi ma Mimi duk abin da zai saka ta farinciki ciki har da neman yaron nan ku rokesa gafaran ya yafe min."

Sai da Mama ta rufe mata baki sai sakin maganganu take yi kamar ba ta cikin hayyacinta.

Sai a lokacin Hajiya ta yi hawaye cikin kuka ta ce"Na yafe masa duk laifin da ya taɓamin da wanda ya sani da wanda bai sani ba, ina masa fatan salama da aminci da kuma dacewar wannan rana ta Jumma'a mai daraja Allah ya jiƙan ka Kabiru".

Sai Hajiya ta fashe da kukan da take ta rikewa Mimi ta koma jikinta ta kwanta suka haɗe suna ta gunjin kuka. Mommy faɗi kawai take yi" Habibi ya rasu? Ni murja ina zan sa ka kaina a gabana fa ya rasu Allah ya jiƙan ka Habibi."


 Ƙanwarta Zainabu ta ce"Ki daina kiransa da wani suna in ba sunan shi ba mala'iku da sunan shi suka san shi ba Habibi ba, ai yanzu wani Habibi ya kare Murja gafaran Ubangiji zaki yi ta neman masa shi ne kawai gata da Soyayyar da za ki nuna masa"

In ka kalli Ahalin nan sai ka tausaya musu, duk da yanayin Abi amman fa tsayayyen Uba ne mai yin komai saboda ƴayan shi, shi ya gina su har su ka kawo matsayin da suke a lokacin kowacce ka gani ido ya Kumbura murya ta dishe saboda kuka, 

Mutanen arziki daga ko'ina sun zo musu gaisuwa daga Gombe Rukky tare da Salim Bunza da Na Misau da wasu daga cikin ma'aikatansu da aka wakilta ranar biyu sun zo musu gaisuwa, Rukky ma nan ta kwana sai ranar uku ta koma Gombe ita ma Khadi abokan aikinta da na mijinta duk sun zo musu gaisuwa haka Dr. Sulaiman sannan Jawahir ma yan'uwanta suna ta zuwa.Haka dangin Mommy su ma sun yi mata kara kwarai da gaake.


 Ana ta zaman gaisuwa manyan manyan mutane nata zuwa gaisuwa su kuma shiga har cikin gida su yi ma Mommy gaisuwa wacce ta za ma abun tausayi.

Mimi ta samu wayoyin mutanen da ba ta san wasu ba ma, a rana ba ta san adadin masu kira su yi mata gaisuwa ba, kaf ma'aikantan su har da masu Inten ba'a bar su a baya ba. Sannan ba ta yi tunanin za ta samu kiran wayar su Nasir ba.

Sai ga shi Mu'azzam ne ya fara kiranta ya yi mata gaisuwa ya ce a kafafen sada zumunta ya gani sai kuma da ga baya Usman ke faɗa masa, sannan Usman ya kirata Ahmad ma tare da Nasir sun yi mata gaisuwa kuma ta ji daɗii kwarai. Sai dai Aji bai kirata ba kuma tana da tabbacin ya sani rashi fa ta yi rashin kuma na Mahaifi, tunda ta karɓi lambarsa ba ta samun kwarin gwiwan kiransa ba. Sai ta ce bari ta gani zai iya yi mata gaisuwa?. Sai ta ɗauki wayarta ta tura masa sako.


 "Aji Nah Abi ne ya rasu yau kwana biyar."

Mimi ce Fatima"


 Ita kanta ta san bazai taɓa mata gaisuwa ba, tunda ya kasa mantawa da abin da ya faru a baya, abunda ba ta sani ba tun a ranar yaji rasuwar domin a daren ya je gaida Inna take gaya masa a cikin ransa ko a fili bai ce Allah ya jiƙansa ba.

Sai da Inna ta ce"Kanin ma mallam Hashimu shima ya rasu yau. Allah ya jiƙan su da Rahma."

Ba saboda shi ya amsa ba sai Saboda ƙanin Mallam Hashimu amman yadda yake jin tsanar wannan mutumin ba zai iya nema masa jinƙai wajen ubangiji ba, ba domin ya na musulmi ba da sai yace Allah ya kara nauyin kasa.


 Kuma Mu'azzam ya kira sa ya gaya masa ya ce to ina ruwan sa? Bayan nan har Makama sai da ya kirasa yana gaya masa ya yi tsaki ya kashe wayarsa ya rasa waye ne baban Mimi a wajensu da suka damu da Mutuwarsa. Nasir ne da ya kirasa sai da suka yi faɗa kamar abun arziki Nasir ya ce"Ya ƙarin haƙurin mu kuma Aji?

Aji ya ce"Ni babana ya ji ma da rasuwa, Innata kuma da ranta sannan Babana uban riƙo na yana cikin koshin lafiya."

Nasir ya yi dariya kafin ya ce" Gaisuwan Major mana baban Mimi, ya kamata ka kirata ka yi mata gaisuwa sanda na kirata sai da ta tambaye ni ka sani kuwa?

A fusace Aji ya ce"Nasir ba domin kai ba ne wallahi da sai na zage ka, kada ku ƙara kirana da irin wannan shirmen na ku"

Nasir ya ce"Aji rasuwa fa aka yi? mutuwa ce fa" ƙaramin tsaki ya ja kafin ya ce"ka bari in ka mutu in ta kirani ta min gaisuwa sai na haɗa na yi mata a lokacin."


 Daga haka katse wayarsa ya bar Nasir da sakin baki, Kuma a daran ta turo masa saƙo. Mamaki ya kama shi wato kenan sun ba ta lambar sa kenan.

Goge saƙon ya yi ya kuma ɗauki lambar ya saka ta a blacklist duk abunda zai haɗasa da abin da zai hana shi barci yana kokarin yin nesa da shi. Ko alama bai ji tausayinta domin wai ta rasa mahaifinta ba, shi a tunaninsa wannan in ya rasu ma abun murna an rage mugun iri a kasa ne, sauran kaɗan ya maida mata amsa da cewa Allah yasa kasa ta kara danne shi sai kuma ya fasa shuru ma ai amsa ce ga mai hankali.





*Janafty*


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.