Free chapter · Read without an account

16_17

by Hauwau Umar · A WANI COMPANY

***






A WANI COMPANY



BY.

HAUWAU OMAR

CUTIE MEEYRAT.



MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS



Fallow my account.

Arewabook@hauwauomar





Page_16_17





Be ce mata komai ba ya buɗe idanunsa "Kin ɗauka na yi bacci ko shiyasa zaki gudu" girgiza kai ta yi alamar a'a "Jeki toh idan an kusa tashi sai ki dawo" "Okay sir" ta faɗa ta na fita dan zuwa office ɗin Suhailat


Ana tashi ta fito dan nufar office ɗin Mdee a hankali ta tura ƙofar tashiga ganin baya cik i ya sa ta zauna ta na jiransa. Fitowa ya yi cikin wasu fararan cuz masu kyau, tsayawa ta yi tana kallonsa ganin da marron ɗin cuz ce a jikinsa yanzu kuma ya canza kenan da wasu kayan ya ke zuwa Company? ta faɗa ta na cigaba da kallonsa zuwa ya yi dab da ita ya sunkuya "Madam shi kuma kallon fa na menene?" murmushi ta yi tana saurin kawar da kanta "Tashi muje ko?" babu musu ta miƙe tabi bayansa, suna fita su ka shiga cikin motar kai tsaye ya gida su ka nufa. Suna isa ta fita dan shiga gida "Baki jiba" juyowa ta yi danjin mai zaice "Ki gaidamin da Mama" "Toh insha Allah zan faɗamata"



Tsaye ya ke ajikin window apartment ɗinsa, sanye ya ke cikin treecotar black da white riga mai kyau haɗe gashinsa ya yi ya ɗaure guri guda idanunsa a lumshe ya ke wani irin jindaɗi yanayi ya ke garin lileɓe ya ke da hadari mai tafiya da iska mai sanya nishaɗi da gudu ta shigo cikin bedroom ɗin ta na kwala masa kira dafe kansa ya yi wanda ya ji ya sara masa "Ohh ya rabbi wai Jiddah yaushe zakiyi hankaline?" turo baki ta yi Kamar zata yi kuka "Toh ni ba Ammi ce ta biyo ni zata dakeni ba dan na ɗauka mata waya shine na zo gurinka, ka hanata dukana amma ka ke min faɗa ko ya Abrad" ta faɗa hawaye na zuba akan fuskarta "Dan Allah kiyiwa Allah kimin shiru Jiddah" banza ta ma sa ta cigaba da kukan ta tsawa ya daka mata, da sauri ta fita a ɗakin ta na kuka

Ammi da ke nemanta ganin tana kuka ya sa ta tambayarta lafiya? karasawa ta yi ta rungumeta "Wai ke lafiyarki ne kike min kuka?" "Ba ya Abrad bane ba ya yi min faɗa" "Da ya miki faɗa ke me kika masa"? "Ni Ammi babu abun da namasa ki tambayesa"


"Naji maza ki wuce ciki kiyi shiri islamiyya" babu mu su ta nufi bedroom ɗinta dan shiryawa ajere su ka fito ita da Yusra drive ne ya ƙaraso yana buɗe musu motar, shiga su ka yi hannusu ruƙe dana juna. Suna isa Jiddah ta dubi Yusra ta na dariya hararata ta yi "Mie kikewa dariya ke kuma?" "Babu komai kawai ina tuno darun da zakuyi keda ya Ustaz ne" "Toh ina ruwanki nifa Allah bana son gulma" gwalo ta ma ta ta na fita a motar da gudu, bunta ta yi itama da gudu su ka shiga gudu a makaranta Ustaz ne ya ƙaraso gurin ya na mu su magana tsayawa sukayi su na suraransa "Wai ku kullum sai kun shigo kuna gudu haba ya kamata ace kunsa kun girma fa" Jiddah ce ta turo baki "Ni dai Allah ya Ustaz ku daina cewa mun girma nawa mu ke ne nida Sis za'a na cewa mun girma" dariya ya yi kawai yai gaba abunsa dan yasan idan ya biyesuu sai sun bashi ciwon kai.



Ayrah na shiga gida ta sa ki ajiyar zuciya ta rasa mai yasa a yanzu idan ta na tare da Mdee ta ke rasa nutsuwarta ganin sai murmushi ta ke kamar wata zautaciya ya sa Mama da ta ƙaraso gun ta dafata firgigit ta dawo hayyacinta "Ke kuma lafiya kike murmushi?" "Babu komai ni kawai ji nayi ina cikin nishaɗi" "Toh Allah ya kyauta" "ameen" ta ce ta na nufar cikin ɗakin na su kwanciya ta yi saman tabarma ta na kallon silin ɗakin da ya sha wuya ya ke bukatar taimako. Abincin Mama ta ajiye mata "Ki tashi kici abunci kinji" miƙewa ta yi ta na janyo yar karama samira shinkafa ce da wake da mai sai salat da aka yanka, ba Ayrah ba ko ni sai da na yi sha'awar cinta😁 bismillah ta yi ta fara ci dama wata irin yunwa ta ke ji lumshe idanunta ta yi "Wollah Mama wannan abunci na ki ya yi daɗi sosai" murmushi Mama tayi "Kodai na sa miki waigi ne" dariya ta yi ta na cigaba da cin abunci



Su na tashi su ka fito dan tafiya ruwa ne ya fara zuba da sauri Jiddah ta karasa ta shiga motar jan luck ɗin ta yi ta rufe, Yusra da karasowarta kenan ta yi ta yi ta buɗe ta kasa drive ta ce ya buɗe ma ta wani kallo Jiddah ta watsa ma sa "Wallahi idan ka buɗe ma ta ko hmm" shiru ya yi ba ce komai ba "Wai sani me keke nufi ne ba cewa na yi ka buɗemin ba" dariya Jiddah ta yi ganin ruwa na ta dukanta, ganin jikinta ya fara rawa ya sa ta buɗe ma ta, da sauri ta shiga ta na ƙanƙame jikinta ko buntakan Jiddah ba ta yiba sani ne yaja motar su ka tafi. Suna isa gida da sauri Yusra ta fita ta yi apartment ɗinsu ta na shiga ta ga Momy zaune ita da Suhaima da gudu ta yi sama ta na isa ta cire kayan da ke jikinta ta sauya wasu faɗawa kan makeken gadon ta yi ta na sauke numfashi




Washegari da wuri ta fita zaune ta samesa ya na danna waya zama ta yi kan kujera ta na gaidasa amsawa ya yi cikin sakin fuska suna isa suka fito a jare zuwa cikin Company tun da su ka jero p.a ke kallonsu ita ma zuwan ta kenan ta na pearking mota ta ga fitowarsu, ji ta yi hawaye ya gangaro ma ta Allah ya sa ni ta na son Suhail shiyasa bama ta so wani ya raɓesa shin ta ya zata raba Ayrah da Suhail? shine tambayar da taiwa kanta


Ƙwafa ta yi ganin ta rasa mafita ta fito itama dan shiga ciki .Coffee ta aje masa akan table ɗin mug ɗin ya ɗauka ya na kaiwa baki, miƙewa ta yi dan barin office ɗin "Ina zaki" ya tambaye ta "Am dama zanje wajan Aunty Suhailat ne" "Shine kuma ba ki tambayeni ba" girgiza mai kai ta yi da sauri alamar a'a "Shikenan ki je amma karki daɗe dan anjima akwai inda zamu" "Thank you sir" ta faɗa tana murmushi


Da sauri ta ke sauka daga kan stap ɗin ta na sauka ta ga p.a da Oga Abdul tsaye da'alama wani abun su ke wani kallo ya watsa ma ta ya na tsaki da sauri ta ratsa ta gefe ta yi wucewarta "Munafuka ce yarinya nan wallahi" p.a ta faɗa cikin hasala tana isa ta sameta zaune ta na dube dube a laptop.

Zama tayi a kusa da ita murmushi Suhailat ta yi "Jiya ina ki ka shiga ban ganki ba" "Da wuri mu ka tafine shiyasa" "Ohk wai ni kam na tambaye ki man" "Eh ina jinki" "Kina zuwa sloon kuwa?" girgiza ma ta kai ta yi alamar a'a "Gaskiya toh ya kamata yau na kai ki saloon naga idan angyara miki gashi ya zaiyi" murmushi ta yi kawai mikewa ta yi tana kama hannuta "Zo muje kinga mu tambayi Mdee ko zai bari" tashi ta yi tabita su ka fita, su na isa Suhail ya ɗago ya na kallonsu "Sir dan Allah idan ba damuwa zamu fita da Ayrah" wani irin kallo ya ma ta da sauri ta sunkuyar da kanta "Idan kunfita kuje ina" taji ya ambata "Saloon" ta bashi amsa shiru ya yi na wani lokaci kafin ya ce "Shikenan muje na kaiku murmushi jindaɗi su ka yi su na kallon juna



Baya suka buɗe za su shiga su duka "Ni ɗin drive ku ne da zaku shiga baya" "Sorry sir" "Ayrah ki shiga gaban kinji" "A'a Aunty Suhailat ke ki shiga" wani kallota ma ta wanda ya sa ta saurin buɗe gaban ta shiga, murmushi gefan baki ya yi dan dama hakan ya ke da buƙata beauty saloon su ka isa da ke garin abuja babban gurine na musamman wanda ya kayatu, akwai wajan saloon da lalle, wajan make up duk agun, fitowa su ka yi su ka nufi wajan saloon ɗin zama ya yi a gurin su kuma su ka karasa cikin wani glass "Madam gulo ce ta fito ta na tambayarsa abun da ya ke so nuna ma ta su Ayrah ya yi dake zaune cikin glass "Ki tambayesu" ya faɗa ya na ɗora kansa a jikin kujera lumshe idanunsa ya yi wani irin bacci ke fusgarsa

Suhailat ce ta basu umarnin su yiwa Ayrah saloon mai kyau sannan ida sun gama su ma ta kalba kanana zaro idanu ta yi ta na turo baki "Allah ni Aunty Suhailat kar'amin kitso kedai kam anyi raguwa wallahi" "Dan Allah Aunty Suhailat" ta faɗa cikin shagwaɓɓa "Allah fa ke daina marairaice wa dan sai an miki" shiru ta yi kawai ɗago idanunsa ya yi dai-dai lokacin da ake warware mata kai masha Allah ya ambata cikin cool voice ɗinsa, cikin muntina da ba su wuce 30 ba aka gama mata komai bakaramin kyau kalba ta ma ta ba zubawa kan nata idanu ya yi tabbas yarinya Allah ya yi mata baiwa kala- kala "Sir" da sauri ya kalleta ya na mamakin yaushe ta iso nan? mikewa ya yi su ka nufi ƙofar fita su na shiga kai tsaye su ka sauke Suhailat a gida kallon Ayrah ya yi "Kin yi kyau sosai da wannan kitso" murmushi ta yi tana mamakin yaushe yaga kitson na ta "Kina mamakin yadda nagani ko?" ɗaga ma sa kai ta yi dan har ga Allah ta yi mamaki



Buɗe murfin ta yi ta shiga ɗa ga ma ta hannu ya yi ya na murmushi, ta na shiga gida ta ga babu kowa a tsakar gida karasawa cikin ta yi Inna lilahi wainna ilayi rajiƙun

Mai ta ke gani haka








Ina ma'abota sun littfin a wani Company na ce ko kinsan har yanzu ba'a fara wasan ba ko kinsa cewa yanzu ne ƙadarorin Ayrah za su fara ohh ya rabbi ki hanzarta biya danjin yadda zata kaya

Idan kinyi shirin biya

9165855674

Hauwau Umar Abdullahi opay.

Ki turomin evidence ta wannan Number

***

Karki bari a baki labari yar uwata..


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.