Free chapter · Read without an account
Page 1
💎↪️YARA MANYAN GOBE↪️💎
ILLAR TALLA
Alhamdulill, da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, tsira da amincin su tabbata a bisa shugaban mu Annabi Muhammad S AW, ina godewa Allah bisa ga wannan dama da ya ba ni ta fara rubuta wannan littafi, kamar yadda na fara Allah ya ba ni ikon ganin ƙarshensa, Allah ya sa saƙon da nake son isarwa zai isa ga al'umma da kuma masu karatu gaba ɗaya, kuskuren da ke ciki Allah ya yafe mana, ya kuma katange nasu karatu daga fahimtar sa.
Na sadaukar da wannan littafi ga dukkan matasa masu tasowa, da kuma iyaye waɗanda kullum su ke iya bakin ƙoƙarin su don ganin cewa sun tarbiyyantar da ƴaƴansu bisa ilimi da kyawawan halaye.
Sannan bayan haka ga wani ɗan tsokaci game da sana'ar talla, Talla sana'a ce amma sai ka/kin dage da riƙo ga tarbiya da kuma kamun kai. Ban yi wannan rubutun domin daƙushe talla ko ince bai da kyau ba a'a, talla sana'a ce mai kyau amma tana da ƙalubale da rashin amfani kamar yanda take da amfani sai dai rashin amfanin ta zai iya fin yawa. Ban daƙushe ko nace talla bata da kyau ba, talla tana da kyau amma abin da aka fi so iyaye su lura shi ne: su riƙa bin kwakkwafin inda ƴaƴan su masu talla ke zuwa da kuma irin abokan da ƴaƴan su ke hulɗa da su. Su riƙa lura da halayen ƴaƴan su tare da bincikar duk wata baƙon hali da suka ga ƴaƴan su na ƙoƙarin ɗauka, sannan suyi saurin yi wa tufkar hanci domin gudun abin da zai biyo baya. Ina fatan duk wanda ya karanta wannan littafin zai yi ƙoƙarin ɗaukar darasi mai kyau da ke ciki. Nagode"
Page 1.
Meye dalilin da yasa kike hana ni talla a baya Umma? Waye mahaifina? Ina yake? Yana raye ko ya mutu? Meye ya sanya baya tare da mu idan bai mutu ba? Meye yasa Ć´an uwan sa basu neme mu ba? Ina Ć´an uwanki???.
Waɗannan su ne tambayoyin da na ke son yin su ga Umma bisa ga wannan halin da na ke ciki, bayan bijirewa umarnin ta cewa ka da na yi talla, yanzu ga matsalar da hakan ya jawo gare ni, matsalar da ba za ta taɓa guguwa daga tarihi na ba.
A duk lokacin da na tuna da halin da na tsinci kaina a ciki sai na ji hawaye ya fara gudana daga cikin idanunta zuwa saman fuskanta, nadama ta mamaye zuciya ta, tabbas na yi kuskure a rayuwa ta, ina fatan hakan zai zama darasi gareni da ma sauran mutane gaba É—aya.
Suna na Rahma. Mu uku ne a wajen mahaifiyar mu, ban san mahaifin mu ba tunda na taso, haka kuma ban san dangin sa ba. Ban taɓa ganin sa ba saboda baya tare da mu kuma bamu san a ina yake ba. Dalilin kuwa, shi ne na taso ne a gun kakata ta ɓangaren uwa, ban wuce shekaru bakwai ba a duniya Allah yayi mata rasuwa, tabbas na yi matukar baƙin ciki da rasuwar ta, ba don komai ba sai saboda tana matukar so na, ba na cin komai sai abinda na ke so, haka zalika duk abinda na so shi na ke yi, daga nan na koma wajen mahaifiyar ta da zama, kasancewar banda wurin zuwa da ya wuce nan ɗin.
Lokacin da na dawo, mahaifiyata kaɗai na samu da ƙanne na biyu mace da namiji, macen sunan ta Rahima, sai kuma namijin mai suna Abdurrahman , don haka ban san waye mahaifina ba, daga wannan lokaci wata sabuwar rayuwa ta faro a tarihin rayuwa ta.
Mu talakawa ne irin talakawan da ko naira biyar ma sai sun sha wahala kafin suke samu, Mahaifiyata bata sana'ar komai, sai dai tayi wa mutane aikatau ko wankau su biya ta kafin muke samun abin da zamu ci na ranar, don haka ba ta da halin samun jari balle ta yi sana'a, ba ta da dangi balle ta roƙe su, ba ta hangen abin mutane don haka ba ta son roƙar kowa wani abu a rayuwar ta, mahaifiya ta jajirtacciya ce da a kullum duk da halin da mu ke ciki ba ta rabuwa da yi mana nasiha, akan cewa mu guji duniya da hangen abin mutane, mu yi farin ciki a halin da mu ke ciki.
Idan aka bar maganar abin da mu ke kaiwa bakin salati, wanda kullum mu ke ta fafutukar ganin mu samu ko da wanda za mu ci sau biyu ne a rana, sai kuma kayan sawa, wannan kuwa, ba'a magana saboda ko sabulu ma da ƙyar muke samu wani lokacin idan tayi wanki ya rage, sai su bar mata.
Ba ma iya sayan sabbin kayan sawa, idan ka ga mun samu kaya sai dai fah, idan makwabta ko ƴan unguwa sun fid da kunce sun ba mu, haka mu ke karɓa cike da farin ciki muna godiya, don kuwa ga ni mu ke tamkar an biya mana aikin hajji, ka san abinda ba ka da shi, baka da halin samunsa ko da kana buƙata, idan a ba ka dole ka yi farin ciki , duk da kuwa cewa mafi yawa kayan sai sun fara yagewa ko sun koɗe su ke iya ba mu amma a haka ake lallaɓawa.
Rayuwa kullum ƙara girma ake yi, tunani yan canzawa, a ko da yaushe burika suna ƙara cika zuciya, hangen abin mutane da son ganin an zama kamar su yana ninkuwa, ko da kuwa mutum ya san bai kai matsayin su ba, ba ma taɓa duba matsayin da mu ke ciki, wannan halaye na ɗan adam su suka fara yin tasiri a kaina, bi sa ga wannan dalilin a hankali a hankali na fara jin cewa bana son irin kayan da suke ba mu, saboda ina rainawa idan sun bani, sai na ga cewa kenan ma hakan raina ku su ka yi, don haka wasu lokutan ma ba na iya yi musu godiya, wani lokacin kuma idan aka ba ni sai kawai na jefar da shi a bola, ko kuma idan na tabbatar kaya za'a ba ni ko da an kira ni sai na ki zuwa, idan sun tambayi dalili sai na ce musu babu komai.
Dalilai biyu ne su ka sanya na fara tsirar waÉ—annan halaye:
Na farko dai a matsayina na wacce ko da yaushe ta ke ƙara zama budurwa amma sai ya zamana cewa duk kayan da su ke ba Ni tsummokara ne, komai wanki da gugar da zan yi musu ba za su taɓa yin kyau ba, wasu ma sun yage, shin me ya sa ba zasu ba ni kaya masu kyau ba wanda bai gama lalacewa ba, sai dai tsummokara, shin bola suka mayar da ni ko ya? Shin zasu iya bari ƴaƴan su su sanya kalar waɗannan kayan, bisa ga haka, a duk lokacin da mutum ya ba ni irin wannan kayan maimakon nayi farin ciki da godiya, sai dai ma daga wannan ranar na ji tsanar sa a cikin zuciya ta, don kuwa bai dauke Ni a matsayin mutum ba, bola ko mahaukaciya ya mayar da ni.
Dalili na biyu kuwa shine tuni rayuwar wasu mutanen ta ja ra'ayina, na fara ganin cewa ni ma daidai na ke da saura, don haka yadda su ke sanya sababbin kaya, ni ma su ya kamata n sanya, yadda su ke ado da kwalliya Ni ma haka ya kamata.
Tom amma tambayar da a ko da yaushe na ke yi wa kaina itace "shin ta ya hakan za ta faru".