Free chapter · Read without an account

Page 4

by Farnanah · BAZLA❤️

Page 4



Zamansa ke da wuya se ga sallamar wani hadadden saurayi a dakin nasa, amsa masa yayi suka zauna akan daya daga cikin hadaddun kujerun da suke a cikin qawataccen parlorn nasa masu taushi, wanda tsakiyar dakin yake dauke da wani lallausan carpet an daura wani center table mae matuqar kyau da daukar hankali, an daura fruits akae wanda aka tsaftace aka gyara.


“Mutan cyprus barka da dawowa” Abdulhakim ya furta yana mai jindadin ganin aminin nasa

Kamal ya tashi shima cike da shauqin ganin amininsa “yace nayi fushi sai yanzu zakazo”


Abdul yayi dariya yace “afuwan mutumina nayi laifi a yafemin” 

Kamal yayi dariya yace “yasu mamii da mutanen gida” Abdul ya amsa da suna nan lafiya

Suka zauna suna hirar yaushe rabo, Abdul yace “wai ina hafsa da Ahmad ne? Tun da na shigo ban gansu ba, kou mommy bamu gaisa ba”

Kamal yace “duk suna nan, Ahmad yaje gidan anty Hibba hutu” Abdul yace “to bari na wuce, muje na gaida mommy” suka jero suka tafi sashen mommy Abdul ya gaidata ya wuce gida

___________________________

      Washe gari.


Fitowa yayi cikin shirinsa kamar koda yaushe na zuwa aikinsa. Dakin mahaifin nasa ya karasa yayi sallama iyayen nasa suka amsa masa, ya duka har kasa yana me sake gaishe da su cikin ladabi da biyayya, amsa masa sukayi cikin kulawa ya tambayi mahaifin nasa jikinsa ya amsa mishi da”jiki kam Alhamdulillah da sauki, har ka fito kenan?” “Eh Abba nama so in makara ae” “Masha Allah, Allah yayi Albarka ya kuma yi jagora ya kawo babban rabo” suka amsa da Amin ya tashi ya fice bayan ya ajiye musu na cefane.


Yana fitowa ya hadu da Hajara tana shirin makaranta, ta gaishe shi ya amsa mata tare da bata kudin da zatayi break idan taje makaranta, ta yi mishi godiya tana me cigaba da shirinta.

Yana cikin tafiya yaji wayansa tana vibration a cikin aljihu, dubawa yayi yaga Maryam ce sai ya dauka ya kara a kunnensa, sallama tayi ya amsa mata. Bayan sun gama gaisawa take tambayarsa Ko ya fita? “Eh gani a hanya na kusa titi zanje gareji, da wani abu ne?” Ya qarasa yana tanbayarta “A’a dama naji ya jikin Abba shiyassa, anjima inaso zan kara lekawa idan na gama aiki” ta bashi amsa “Abba yaji sauki sosae Alhamdulillahi, nagode sosae da kulawa” tace dashi ai ba komai, sukayi sallama ya katse wayar yana me taron abun hawa.


______________________________


A bangaren Maryam kuwa tunda ya dauki kiran taji jikinta yayi wani irin sanyi zuciyar ta tana bugawa da dan sauri-sauri, tabbas tasan tanayiwa Sufyanu wani irin so da bata taba zaton zatayiwa wani ba a rayuwarta. Bataso sukayi sallama ba amma saboda tasan shi ba ma’aboci yin doguwar fira bane shiyasa bata fiye yawan takura mishi ba.

Kullum akoda yaushe a kuma ko wace addu’a tata roqonta shine Allah ya mallaka mata Sufyanu a matsayin mijinta idan har alkhairi ne gareta.


Tashi tayi tana me sauke nannauyar ajiyar zuciya, ita kadae tasan yadda take jinsa a cikin ranta. Ta gyara dakinta bayan ta gama ta fita taje ta gyara gidan ta hada wuta domin daura abincin karyawa.


___________________________


Baccinta takeyi cikin kwanciyar hankali akan hadadden gadonta, sallama tayi ta shigo dakin ta kalleta sannan ta kalli agogon dakin wanda yake nuni da karfe 11:16am na safiya ta kuma kallon kawar tata. duka ta sake mata a kafarta tana me zama a kusada ita.

Bakinta ta turo cikeda shagwaba saboda a tunaninta Ammi ce, ta tashi tana murza ido tana kara tura baki gaba ta zauna da kyau tana me bude idonta ahankali.

Tar idonta ya sauka akan Yasmeen da take harararta tana tsaki tana duban agogon hannunta, kyakkyawace ajin farko tana sanye cikin red abaya tayi rolling gyalen kayan akan kanta. Tsaki ta kuma ja tana cewa “malama zaki tashi mu tafi ko kuwa?”tana shirin bata amsa ta kuma cewa “fisabilillahi kinsan da wuri zamuje muyi mu dawo amma kika kwanta kına bacci”ta karasa tana harararta.

Tace “yasmeen gajiya nayi ne, bri na shiga nayi wanka na shirya” tace wannan wankan naki ai sai kinfi awa daya baki fito ba” Bazla ta tashi tana dariya ta shiga bandaki 


Ta shirya Itama a cikin doguwar rigarta purple da ta matuqar dacewa da ita, tayi kyau sosaii 

Suka sauko Ammi tana zaune tacewa yasmeen “ku da kuka ce 12 zaku fita ga 2 ta kusa” yasmeen tace “Ammi duk Bazla ce ta bata mana lokaci” Bazla tace “yanzu dai mu tafi” 

Ammi tace “kar ku jima dai, Allah ya tsare” suka Amsa da Ameen suka fita


——————————————————


Sufyanu yana isa ya gaisa da kowa da yake wurin, ya gaida ogansu, Oga Yusuf yace “Ashe Mallam kuma arziki yayi, Allah ya bashi lafiya ya tsare gaba” Sufyanu ya amsa masa da Ameen ya Allah, Oga yace “amma shine baka gayamin ba sai dai Ismail yake gayamin” Sufyanu yace “Oga ayi hakuri” yace to badamuwa Allah ya bashi lafiya 

Ameen Sufyanu yace ya tafi xuwa wurin abokin nasa Isma’il, suka gaisa ya qara mishi ya jikin Baban yace mishi yaji sauqi Alhamdulillah

Oga yazo yace Sufyanu ya taso zai aikeshi karbo wasu kaya

Sufyanu cikin girmamawa ya tashi yaje aiken ogan nasu 


_________________________________


Suna hanya yasmeen tana driving a cikin kwarewa sun saka sauti a cikin motar 

Bazla tace “yasmeen saura two weeks fa mu koma school, wallahi banason komawa in gayamiki” yasmeen tace “kekam Allah ya shiryaki, ke kam meyasa ba kya son school ne” ya tambayeta idonta akan hanya, Bazla tace “bazaki gane bane, kawai dai ni banaso” yasmeen tace “kuma ya zama dole sai an yi ba” Bazla dai bata qara cewa komai ba”


Suka qarasa saloon inda aka fara yi musu gyaran gashi, aka kammala suka nufo hanyar gida

Suna tafiyane sai yasmeen taji motar tana son ta tsaya, tayi tsaki tace “menene haka nasan dai akwai mai a motar” ta samu tayi parking suka fito suka rasa me zasuyi


____________________________________


Mommy ta kira Ammi suka gaisa, mommy tace “hajiya yaushe Alhaji zai dawo ne” Ammi tace “cikin satin nan InshaAllah” mommy tace nifa so nake ayi maganar nan don yau babansu zai dawo a tsayar da magana kawai” Ammi tace ba matsala InshaAllah yana dawowa sai ayi maganar, amma kafin nan ya kamata su fahimci junansu, Mommy tace “hakane kuma zan turo shi anjima da dare” Ammi tace tau shikenan Allah ya kaimu” sukayi sallama


_______________________________



Bangaren su yasmeen tayi kiran bakanikenta amma wayar bata shiga, tacewa Bazla “yanzu ya zamuyi kenan” bata rufe baki ba sai ga Sufyanu yazo wucewa yagansu tsaye murfin gaban motarsu a bude alamun motar tsaya musu tayi

Yayi parking mashin din d yake akai a gefe, yazo yayi musu sallama yasmeen ta amsa 

Yace “motar tsayawa tayi ne” yasmeen ta amsa da “Ey wlh muna tafiya ne kawai ta tsaya” yace “to bari a duba” sai a lokacin Bazla dake danna waya ta dago kai ta kalleshi

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.