Free chapter · Read without an account
Chapter 8
***
✨ *ALLON* *ƘADDARA* ✨
*OUM FATIMA*
*DASHEN ALLAH* *WRITERS* *ASSOCIATION*
*PAGE 8*
Addu'a sosai Baba Malam yayi suna amsawa kafin yayi shiru Hajjo ta fara magana "Ba wani abu bane dalilin kiran akan maganar auren Nabeel da Safiyya ne" da sauri Momy ta ɗago har tana harɗe harshe wurin cewa "wane Nabeel ɗin?, Ba dai nawa ba".
"Habeeba!" Abba Mukhtar ya faɗa a matuƙar tsawace "rabu da ita Mukhtar aure ne dai sai an yi shi ba fashi don haka na yanke sati biyu masu zuwa za'a ɗaura auren, sai kuyi shirin da zaku yi" Hajjo ta faɗa tana ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya "in da mai magana zai iya faɗa".
"Ban amince ba ba kuma zan taɓa amincewa ba, yanda na ɗan-ɗani baƙin ciki akan uwarta itama sai ta ɗan-ɗana!" Momy ta faɗa tun kafin Hajjo ta gama rufe bakinta.
"Habeeba!!! Ranki zai yi mummunan ɓaci idan na ƙara jin bakin ki a wurin an!" Abba ya faɗa ransa na tafasa da halin matar sa, ace mahaifiyarsa na magana tana maida martani tsabar rashin mutunci. "Ko mai zaka yi Alhaji sai dai kayi, amma har abada bazan bari jinina ya haɗu da na Harira ba, har abada!" Tana gama faɗin hakan ta tashi ta fice daga ɗakin.
Binta da kallo kawai Abba yayi har ta ɓace ma ganinsa kafin yace "zan nuna maki nike da iko dake da abinda kika haifa". Hajjo ya kalla yace "me zai hana a ɗaura auren kawai gobe in yaso daga baya ayi koma miye?".
"Inaga abi komai a hankali kar ayi gaugawa" cewar Baba Malam da tun da aka fara maganar baice komai ba. Kallon mu Alhaji Babba yayi yace "kowa ya tafi ya kwanta" tashi duk muka yi muka fice ya rage saura mazan kawai. Nasiha sosai Baba Malam yayiwa Nabeel akan yabi komai a hankali sannan yabi mahaifiyarsa a hankali da rarrashi inaba Allah komai zai yi dai-dai. Kai kawai ya gyaɗa ya kasa magana. Ya rasa mai ke damuna Momy? Meye a tsakaninsu da Ammy?, Kullum Waɗannan tambayoyin suke a ransa da zuciyarsa.
Sosai suka ƙara tattaunawa suka tsai da maganar a sati biyun kafin su miƙe kowa ya nufi sashen sa. Hannu Jabeer ya miƙawa Nabeel suka yi musabiha yace masa "Congratulations Bro Allah yasa alkairi"
"Ameen Brother, na gode" ya faɗa a sanyaye. Jabeer motarsa ya shiga ya tafi gidansa shi kuma ya nufi ɗakinsa jikinsa a sanyaye yake sosai da fargabar abin da Momy zata yi. Duk da ƙasan zuciyarsa danƙare take da farin cikin zai mallake ta nan da sati biyu, sai dai fargabar dake zuciyarsa ta hana farin cikin bayyana.
*** Ni kuwa a nawa ɓangaren farin ciki ne bayyane a saman fuskata na samun cikar burina da zan yi. Sai dai yanayin da naga Ammy ta wuce ɗakinta ya sanyaya min jikina, A sanyaye nabi bayanta zuwa ɗakin nata saman gado na sameta tana kuka. Tana gani na ta maza ta share hawanta, zama nayi kusa da ita na riƙe hannayenta nace "Ammy kuka kike yi? Ko kema bakya son auren ne?" Hannuna ta riƙe itama tace "ba auren ki da Nabeel bane ban so Hanan halin da zaki jefa kanki nake gudu, na san halin Habiba da kafiya a kan ra'ayinta na santa farin sani tunda tare muka tashi tun ƙiruciya har girma kafin abinda ya faru ya datse alaƙar dake tsakaninmu" cikin zaƙuwa da son jin abinda ya raba su nace "Ammy kina nufin da ku ƙawaye ne? Amma miye ya shiga tsakaninku ya lalata alaƙar da kuka daɗe a cikin ta?".
"A kan soyayya ne"
"Soyayya?" Na tambaya da mamaki "Ammy ban gane ba?".
"Ki manta kawai Hanan jeki kwanta ki tabbatar kin yi addu'a kafin ki kwanta".
"To Ammy" na faɗa ba don naso ba, Allah ya sani ina matuƙar son sanin abin da ke tsakanin Ammy nah da Momyn Nabeel. Amma sai dai duk sanda na tambayi Ammy sai ta kauda maganar, haka naje na cancza kayana na kwanta ina ta saƙe-saƙe. Kiran da Ya Nabeel ya minne yasa na manta da duk wata damuwa muka sha soyayyar mu, inda shima kaso da yawa na damuwar sa ya goge
★
Washe gari na tashi jikina da sauƙi sosai don haka na shirya na tafi wurin aiki, sai da Ammy tace in bari in ƙara warkewa nace mata bana jin daɗin zaman gidan. Rabuwa tayi dani sabo da itama gidan ya ishe ta tana son fita ta shawo iska don haka ta tambayi Baba Malam akan zata kaiwa Aunty Ade ƙanwarta ziyara. Bai hanata ba sabo da yasan a halin da ake ciki tana buƙatar shawara da makusantan ta, kuma a Kano daga ita sai ƙanwarta Sa'adatu da suke kira Ade. Iyayen su Allah ya masu rasuwa sai kuma dangi da suka rage suna can Katsina asalin Mahaifar su.
Don haka tare muka fita da Ammy na sauke ta gidan Aunty Ade da yake kan hanya tane na wuce wurin aikina akan inna tashi zan samu Ammy acan mu yini.
Yau sai da kowa ya fahimci ina cikin farin ciki a ma'aikatar mu har masu sauraro ma sun fahimta sabo da yanda na riƙa saka waƙoƙin soyayya masu daɗi ina binsu har ana jin sautin muryata. Lokacin da aka bada damar kira da turo saƙo haka aka yi ta tambayata "Malama Hanan da alama yau kina cikin nishaɗi, ko dai albishir ɗin kujerar Hajji kika samu a safiyar yau" ire-iren waɗannan tambayoyin nayi ta samu in da nake ce musu alkairi ne ya tunƙaro ni insha Allah kwana kusa zasuji dadaɗan labari.
Haka nayi ta samun saƙonnin fatan alkairi har na gama na dawo ofishin mu inda Samha ta sani a gaba da tambaya har sai da na faɗa mata abin da ke faruwa. Sosai ta taya ni murna tun da ta san soyayyar dake tsakaninmu da Ya Nabeel.
"Amma Hanan ya zaki yi da Faisal?" Samha ta tambaye ni.
"Ya ko zan yi da shi, ai dama ban ce masa ina son sa ba, ban kuma ɓoye masa cewa ina da wanda nake so"
"Haka ne amma shima yana sonki sosai"
"To ya zaiyi tunda ni bana sonshi sai yayi haƙiri" na faɗa ina jin hirar ta fara gundura ta "baki da kirki ƙawata" Samha ta faɗa tana dukan kafaɗata "bana munafinci dai" na faɗa nima muka saka dariya tare.
**** A can gidan Aunty Ade kuwa bayan sun gaisa Aunty ta kawo mata ruwa da abin motsa baki, zama tayi kusa da ita tace "Yaya lafiya kuwa na ganki haka?, Kamar kina cikin damuwa sosai fa". Ajiyar zuciya Ammy ta sauke kafin tace "an tsaida ranar auren ƴarki nan da sati biyu".
"Masha Allah, Allah ya nuna mana lokacin, amma sati biyu bai yi wuri ba kuwa?" Ammy tace "ba wannan ne damuwar ba Ade kin san fa halin da ake ciki game da Habiba kin san abin da ke tsakanina da ita, don bakiji irin furucin da tayi ba a gaban Hajjo lokacin da aka tsaida ranar!" Ta ƙara sa faɗa cikin damuwa.
"To sai me Yaya don Habiba bata so tunda bata isa ta hana ba?, Ai yanzu ma ita ke da faɗuwa kamar yadda kika shiga gaban ta a baya wallahi, ai ba tsoro zakiji ba nuna mata zaki yi kinfi ƙarfinta kuma ko da yaushe kece a gabanta aure dai sai an yi shi insha Allah ɗan baƙin ciki sai dai ya mutu, mudai farin cikin ƴarmu muke so" Aunty Ade ta faɗa tana rangaɗa guɗa.
"A'a fa Ade kin san halin Habiba da kafiyar kan tsiya, bakya ganin zata hana ta farin cikin da kike magana koda anyi auren?"
"Ki kwantar da hankalinki Yaya ba abinda zai faru sai alkairi".
Haka suka yi ta tattaunawa har muka tashi daga aiki nazo na same su. Ina shigowa Aunty Ade ta taso ta rungumeni tana sakin guɗa "Masha Allah ɗiyata ta kusa zama amarya, Allah dai ya nuna min wannan lokacin za'a sha kallon rawa a wurin Uwar amarya" Aunty Ade ce ke maganar tana taka rawa. Gaba ɗaya dariya muka saka ni da yaranta guda uku ƴar budurwar ce babba mai suna Afiya sai guda biyun maza Umar da Abdul. Ammy ma sai da ta dara da halin Aunty Ade na barkwanci.
A nan muka yini sai da dare zamu wuce Aunty tace ai ni nazo kenan zata sa direba ya kai Ammy gida daga nan ya amsomin kayana zata fara min gyaran jiki kasancewar ta ƙwararriya a fannin.
Ammy bata yi musu ba tace zata faɗa wa Baba Malam ɗin in ta koma. Raka Ammy muka yi har inda direba ya fito da mota na buɗe mata ta shiga suka tafi mu kuma muka koma ciki ina riƙe da hannun Abdul ƙaramin ɗan Aunty.
Kamar yadda Aunty ta faɗa direba ya dawo da kayana cikin ƙaramin akwati da Ammy ta haɗo min ta bashi ya kawo, tun a daren Aunty ta fara kwaɓa abubuwa ta shafamin a jikina sai da yayi mintinan da take buƙata kafin ta haɗa min ruwan ɗumi nayi wanka sannan na kwanta. Ya Nabeel ya kira ni muka sha hira kafin bacci ya ɗauke ni....
*OUM* *FATIMA*