Free chapter · Read without an account
Chapter 5
"Khaleel, this girl is very stupid and storborn wallahi, daganin yarinyar kasan cewa bata da kamin kai ko kaɗan, how comes ace kina bin namiji yasoki if not tsabar shaiɗanci, Khaleel abinnan yana bani mamaki, i wonder why za ace mace da Allah yaiwa tarin darajoji tariƙa watsar da mutuncinta beside tunda nace banason yarinyar nan ai se ta haƙura, su suke jawowa maza ke yaudarar su a rayuwa wallahi".
"Hmmm! Aliyu, ai maganin ka kenan irin su ɗin, tunda dai duk matan duniyar nan ka kasa tsaida macen aure, kaga ai se macen ta tsaida kai a mijin aure ƙila ma huta da tuzurantakar nan taka" Khaleel ya ƙarasa mayarwa Aliyu amsa cike da zolaya yana gimtse dariyarsa.
Miƙewa Aliyu yayi cike da zafin rai yanaiwa Khaleel wani banzan kallo, "See this man da Allah, n
i matsala ta dakai kenan mutum yana maka magana in serious address kana wani kawo wata magana, just because you're married to a small girl kake tunanin ka girma, i don't really accept such your small baby girl as a wife gara ma kasani ba aure kayi ba ƙanwa kawai zaka jagwalgwala min ka ɓata, duk da itama Ramlat ɗin bata da kunya banda haka yaushe har ta girma ta isa aure ma? Mtssss". Aliyu yakai ƙarshe da jan tsaki yana mai hayewa up stair da tunanin ya huce haushinsa akan aminin sa Khaleel.
Shi kuwa Khaleel ko a jikinsa tunda dai yasan cewa matarsa matace, tunda tana dauke masa dukkanin bukatarsa gasu ma harda rabon arzikin ɗa, kuma shima bawai yana son waccan Nafisan take ko wace ce ma kawai dai yana so ya daɗa nusar da abokinsa illar zama ba aure ne. Da murmushinsa ya miƙe ya fice ya bar gidan tare da ja masa ƙofar palorn.
"Wallahi nucy sai na auri mutuminnan ko zan rasa sassan jikina yazama ruhina ne kaɗai ya rage, nayi alƙawarin sai ya soni kuma sai na juyashi yanda nakeso". Kai tsaye Nafisa ta faɗa tare da juya ƙan motar zuwa gida wajen prof.
"Mum wallahi inason Haidar kuma idan baku auramin shiba zan iya rasa raina, zafa ku iya rasani Mama ko dan kinga ba ke kika haifeni bane..."
Tassssss! Bata kai ga ƙarashe kalaman bakinta ba Umar ya Zabga mata mari. "Ke fitsarar taki har tawuce ko ina takai ga Mama, to wallah ki shiga taitayinki kuma ki ɓace ki bani waje useless" yana mai ƙoƙarin kai mata kafa ta fice dan Allah ya sani tana matuƙar tsoron wannan mai fuskar kurayen kaman yanda take ambaton Umar ɗin. A fudace ta shige ɗakinta ta tattara abinda take son ɗauka ta zari makullin mota ta fice.
Prof. kuwa kanta tariƙe cike da damuwa, tama kasa cewa komi game da lamarin Nafisa, kuma har cikin ranta ba ta so Umar ya shiga tsakanin su ba, sedai bata son magana hakan na iya janyowa hawan jininta ya tashi. Daga inda take ta kishingiɗe ta kasa cewa da Umar ɗin ko ƙala.
Yau kwanan Nafisa biyu da zuwa Abiya ba tare da sanin Prof. ba, hankalinta kuma ba ƙaramin tashi yayi ba, inda ta ɗora laifin gaba ɗaya a kan Umar, sosai kuma tai masa faɗan zafin zuciyarsa tare da masa kashedi sosai akan tilon 'yarta, bataso Nafisa ta riƙa maraicin uwa a rayuwarta.
Tunda Nafisa ta tafi Abiya Haidar ya birkice kowa ya kasa gane kansa, sosai ya ɗaga hankalin mahaifiyarsa Hjy. Binta tare da sauran 'yan uwansa mata kan lallai-lallai a aura masa Nafisa, Ramlat ce ta dage kan cewa ba sa son Nafisa matsayin suruka a gidansu, ta sanar da Mommy sam Nafisa bata da tarbiyya, hakan yasa Mommy ma tace bazata yarda da auren Nafisan ba.
Lokacin da Mummy ta gano cewa Nafisa 'yace ga Prof. Balkisu da kanta taje nemawa Aliyu auren ta, dafarko prof. ɗin ta turje amma daga baya ganin Nafisan na nutsuwa sai ta shiga tunanin ko dai aure zai gyarata tunda tana son Aliyun, nan danan kuma ba ɓata lokaci aka ɗaura musu aure bayan shan shagulgula.
Tunda Aliyu ya auri Nafisa kullum daɗa ruɗewa yakeyi a fagen sonta, duk sonsa kuma da haihuwa tunda ta nuna masa bataso shima ya alƙarwantawa kansa cewa yabar son haihuwa har mutuwarsa, har zuwa wannan lokaci da Mummy ta ɗaga hankalinsa da na matar tasa.
"Hello Feenah na samo yarinyar fa, cikakkiyar budurwa ce da na tabbatar zata iya ɗaukan ciki, idan muka ƙaraso sai ki sake Kaita a binciki lafiyarta sosai anan dan hankalinki yafi kwanciya amma saida nasa akai komi da ya dace" faɗin Nucy lokacin da ta kira aminiyar tata.
"A haka see this girly, akwai abinda zanyi wanda yafi naki ne banda abinki da har zakice na kaita da kaina, i trust you sosai nucy Allah kaɗai yasan gaskiya ta, kawai ki kawota na yarda da duk binciken da kikai fatan mu dai shine nasara, duk da dai nasan nasara always belong to us and lies upon us" Nafisa ta faɗa tana mai tabbatar wa da kanta samun nasara.
Ba a wani ɗauki lokaci ba abinka da masu ji da kuɗi nan da nan Nucy ta kaiwa Nafisa yarinyar da kanta, kaman kuma yanda takeso yarinyar mummuna ce ta ƙarshe wadda a yanda Nafisa ta gani babu wani ɗa namiji da zaiso kusantarta sabida muni.
Ita kuwa yarinyar se rawar kai take lokacin da aka sanar da ita deal ɗin ta, sabida dama irin yaran ƙauyennan ne masu rawar kan tsiya da son abin duniya.
Se da suka gama tsara komi sannan Nucy ta tafi tabarsu, Nucy dakanta takai yarinyar akai mata wankin kai da na jiki aka wanke duk wani loko da saƙo na jikinta, dan a yanda Nafisa ta faɗa matuƙar jikinta da ƙazanta Haidar ba zai taɓa yarda da ƙudurinsu ba.
Tunda ya dawo gidan yaga tana ta wani faran faran dashi kaman ba ita bace yau wajen sati ke fishi dashi, hakan yasa yake ta lallaɓa abarsa dan gudun abinda zai sa ta sake fishin dashi. Bayan ya ci abinci har yayi shirin bacci ya haye kan gado ya manne a jikinta sabida yanda yai kewarta se kawai ta zame jikinta ta zauna.
"Kaifa Haidar na fuskanci wasu lokutan tunaninka guduwa yakeyi, sam ka kasa gane damuwa ta, naje asibiti an tabbatar min bazan iya haihuwa ba sabida magungunan hana ɗaukan ciki da nai tasha, gashi lokacin da mummy ta bamu sai daɗa tafiya yake", ta numfasa sannan ta cigaba
"Gaskiya Haidar wannan shi yasa na samo yarinya ƙarama wadda zata iya haihuwa sabida kayi mata ciki ta haihu, in yaso sai mu sallameta mu riƙe ɗan mu ko 'yarmu. Kaga daganan mun huta da fishin Mommy".
Jin zancen yayi wani iri a kansa, kaman ya suyi mata ciki ta haihu kuma yarinya, me Nafisa take nufi da hakan? Bai kai ga gama gane bayanin nata ba ta miƙe
"Kaga Haidar ba dole idan bazaka iya ba shikkenan, amma kasani our relationship will be ended with this matter, yes! I mean we will be separated and divorced".
Miƙewa shima yayi a zafafe ya riƙo ta da sauri " why are you behaving this way dearest ni nace miki bazanyi bane? Kawai dai ina jin zafin kasancewa da wata bake ba and kuma kinsan yanda nake ƙyamatar zina, so why not na auri yarinyar after then in ta haihu na sake ta ko ya kikai suggesting?"
Aliyu ya ƙarashe yana kallonta da fatan furicin sa bai sata fishi ba. Da masifar gaske ta hayayyaƙo masa kaman ta cinye shi" Who stand for you Haidar har kana da gut ɗin da zaka iya cewa zaka min kishiya, yaushe kayi baki yaushe har ka kai nan? ". Tsabar masifa na cinta kaman idanunta zasu zubo. Sai kuma ta tuna an ce mata matuƙar tana son nasara se ta bishi a hankali if not zata ɓata komi, tuno hakan ne yasa ta kalleshi tana rausayar dakai tare da riƙe hannayensa tace, "Haba one love kadena hasala ni, duk abinnan da nakeyi fa kishinka ne ya jawo, sabida kai naƙi yarda na haihu domin na baka lokacina da cikakkiyar kulawa, tunani na idan muka ƙara girma se mu fara haihuwa, yanzu kuma kaji abinda likitoci suka gano shan magani yamin illa, ga mummy ta uzzura. Haidar ya kamata ka tausaya min ai, kaifa kana gani za'a iya raba mu kuma kaje ka haihu da wata matar dan naga take taken Mummy kenan" ta ƙarshe tana matso hawayen munafurci.
Rungumota yayi jikinsa ya fara lallashinta. "Kiyi haƙuri one love ki kuma dena wannan zancen rabamun in ba so kike raina ya riƙa ɓaci ba, haihuwa kuma duk yanda kika tsara na amince ki kwantar da hankalinki".
Farin ciki ne ya cika ta fal, da kanta ta gyarashi yai waka duk yanda yaso yaɗanji ɗuminta ta hanashi a cewarta kar ya zubar da sperm cells ɗin a banza ayi asarar su. Har ɗakin ta rakashi yayi kicin-kicin yana kallon budurwar ta fito ta jawo musu ƙofa...
Karku manta wannan shine last free page, Duk mai buƙatan cigaba da karatun littafin should contact ***, ko kuma ku cigaba da bibiyar shadina Meryermerh@arewabooks. Kar ku bari a baku labari
This is the end of our free pages follow more updates, ina maraba da ku masoya.