Free chapter · Read without an account
Chapter 15
✨ *ALLON* *ƘADDARA* ✨
*OUM FATIMA*
*Arewa* *Books@Oumfatima33*
***
*DASHEN ALLAH* *WRITERS* *ASSOCIATION*
*PAGE 15*
Gidansa ya nufa sabo da yana buƙatar wanka kafin ya koma can ɗin, yana zuwa samansa ya haura bai nemi komai ba sabo da yasan Kalisat bata nan. Kayan jikinsa ya cire a kasalance zuciyarsa ba daɗi, ga jimamin rashin ɗan uwansa da yake ciki, ga kuma wannan tashe-tashen hankalin da ke faruwa a cikin Gidansu. Wani irin nauyi yake ji a ƙirjinsa da wata lulluɓaɓɓiyar damuwa dake ƙoƙarin tasowa ta kassara natsuwa daƙwarin gwuiwarsa.
Toilet ya shiga ya tsaya ƙarƙashin shower ya sakarma kansa ruwa mai sanyi yana lumshe ido damuwar da yake ƙoƙarin binne wa na mamayesa tana bayyana rauninsa da ba wanda ya taɓa sani. Ya daɗe sosai kafin yayi wankan ya fito jikinsa sanye da bathrobe hannunsa riƙe da ƙaramin towel yana tsane sassalƙan baƙin gashin kansa na Fulanin Usul. Tsadaden body lotion ɗinsa ya jawo ya fara shafawa jikinsa cike da natsuwa da kasalar dake ɗawainiya dashi. Sosai Lion eyes ɗinsa sukayi laushi ga yunwar dake damunsa sakamakon duk yau bai saka wani abu a cikinsa ba.
Sumar kansa ya gyara ya taje da tsadaddun mayukan da suka lashe kuɗaɗe masu yawa sabo da baya ƙyashin kashe kuɗaɗe wajen siyen kayan amfaninsa. Ɗan gayu ne sosai da yasan kansa kuma abin ya haɗe da tsananin tsaftarsa, duk wani abin amfaninsa to luxury's ne baya mu'amala da ƙananan abubuwa, ba don fariya ba sai don Allah ya hore masa.
Miƙewa yayi ya nufi closet ɗinsa cikin taƙunsa na ginannun Mazan da suka san mutuncin ɗaha ƙarfe. Hasken da yaga wayar sa nayi ne ya gane kira ne ke shigowa, idonsa yakai kan Sunan. Alhaji Babba ke kiran don haka yabi kiran bayan ya katse, tambayarsa yayi jikin Hanan yake faɗa masa ya baro Asibitin yana gida amma yanzu zai fito "Ok to sai ka ƙaraso" ya faɗa yana katse kiran.
A shirye tsaf ya fito cikin ƙananun kayan kalvin Klein cotton wool Blend polo shirt and cotton Flex trouser. Turaren AZZARO ya fesa a jikinsa kafin ya aje ƙwalbar ya bar gaban mirror, wayarsa da key ɗin Mota ya ɗauka ya fice a gidan ba tare da ya nemi abinda zai ci ba ya nufi Gidansu.
Masallaci ya fara zuwa don gabatar da Sallar la'asar da lokancinta yayi, bayan an idar da Sallah tare suka fito dasu Baba Malam suka ƙara sa Gida. Bai tsaya a ƙofar Gida ba ciki ya shiga ya nufi ɓangaren Mahaifiyarsa, a cikin ɗakinta ya same ta ta gama Sallar la'asar tana lazumi. Zama yayi saman kujera ya fito da wayarsa yana dubawa har ta kammala ta juyo ta dubeshi "Har ka dawo daga Asibitn?, Yaya jikin nata?" Ta tambaye shi tana tsare sa da ido don ganin kamar da abinda ke damunsa.
"Eh gida na je daga Asibitn" ya bata amsa "kaci abinci kuwa?" Ta ƙara tambayarsa "A'a" ya bata amsa kansa a ƙasa.
Yunƙurawa tayi ta miƙa tana cewa "bari in sa Kalisat ta kawo maka abinci" bata jira amsarsa ba ta fice daga ɗakin, ɗakin Ruƙayya ta nufa ta taso Kalisat da taje can ta kwanta domin ta huta, tace "kije ki kaiwa Mijinki abinci yana ɗakina".
"To Hajiya" ta faɗa tana miƙewa ta fice a ɗakin. Kiching ta nufa ta haɗa masa abincin ta ɗauko ruwa ta kawo masa ta aje kafin ta koma ta haɗo masa Black tea ɗinsa ta kawo masa.
Zama tayi kusa dashi ta haɗa masa komai ta tura gabansa tace "Bismillah".
"Ɗagowa yayi yana kallon fuskarta cike da ganin girma da ƙimarta a zuciyarsa ya furta "Jazakillah" murmushi tayi masa kawai ya fara shan Black tea ɗinsa kafin yaci abincin kaɗan.
Bayan ya kammala ta kwashe komai kafin ta dawo ta zauna kusa da shi, gaisuwa ta ƙara yi masa da tambayarsa jikin Hanan yace mata "Alhamdulillah, yaya jikinki?, Kina jin wani abu yanzu?" Ya tambayeta cike da kulawa.
"Bana jin komai" ta amsa masa tana kwantar da kanta saman kafaɗunsa "I hope kinci abinci?".
"Yah naci"
"Ok" ya faɗa yana miƙewa yace "zan fita ki samu ki kwanta ki huta"
"Ok" ta faɗa tana kallon sa cike da soyayyar sa a zuciyarta "take care" ya faɗa yana ficewa daga ɗakin. Sashen Hajjo ya shiga ya gaisheta kafin ya fito ya nufi Asibiti.
Lokacin da ya shigo ɗakin ina kwance sai faman kuka nake wanda tunda na farka aikin kenan, Aunty Ade da Asiya sun yi rarrashin har sun gaji. Yanzu ma fama take dani akan in tashi inci abincin da ta haɗa min amma naƙiya "yauwa Jabeer gara da ka shigo kila kai ta ji maganar ka ta tashi taci wani abin" Aunty ta faɗa tana miƙewa ta fice daga ɗakin don amsa wayarta.
Itama Asiya mikewa tayi tace zata je gida ta dawo. Shiru na tsawon mintuna baka jin komai sai shesh-shekar kukana "tashi ki zauna" ya faɗa muryarsa ba alamar wasa.
Ban yi niyar tashi ba amma da ya zuba min azababbun idanunsa masu kwarjini dasa mutum ya shiga tai-tayinsa yasa ba shiri na miƙe na zauna ina ta sauke ajiyar zuciya.
Da kansa ya zuba abincin a plate ya matso da kujerarsa kusa da gadon ya miƙa mata "Hammah na..." Maƙalewa sauran magar tawa tayi sakamakon wani shegen kallo da ya watsa min. Duk tsaurin idonka da rashin kunya idan Hamma Jabeer ya zuba maka waɗannan idanuwan nasa sai ka rasa inda zaka sa ranka. Dole na fara cin abincin ba don ina jin daɗinsa ba.
Kaɗan naci na ture bai matsa min ba ya buɗe kwakin peak yoghourt ya bani yana tsare ni da kallo. Ba yadda na iya haka na fara sha, sai da nasha kusan rabi kafin na aje. Magungunan ya shiga ɓallowa yana ankare da yanda take taɓe baki sai ya ƙara haɗe rai. Kamar zan fasa kuka haka na amshi maganin na haɗiye da ƙyar ina yanutsa fuska kamar zasu dawo, allura naga yana haɗawa ba shiri na zuro ƙafafuna ƙasa na miƙe ina ƙoƙarin kwasawa da gudu in fice a ɗakin. Taku biyu nayi ya damƙo hannuna ya dawo dani ya zaunar, ai sai kawai na fashe da kuka da iya ƙarfina don a gaskiya na tsani abinda zai sa a huda min jiki na. Bana ƙaunar magani bare allura gashi kuma Allah ya yini ba mai cikakkar lafiya ba.
Ganin yanda take kuka da iya gaskiyarta yasa dariyar da ya jima bai yiba take ƙoƙarin bayyana a saman fuskarsa, amma ya danne ta ya barta iya ransa "marar kunyar ƙarya, duk tsiwar da tsaurin idonki kike yiwa allura wannan kukan, anji kunya Allah" ya faɗa ƙasa-ƙasa yana kamo hannunta ya saita allurar ya tsira kafin a hankali ya shiga juye mata ruwan yana kallon yanda ta ƙanƙame hannunsa ta rufe ido tana mimi da baki.
"Sai ki sake min hannu ko" ya faɗa yana hararata. Sakin sa nayi na matsa ina murguɗa bakina don sarai naji abinda ya faɗa dazu, ƙunƙuni nake a cikin raina ina rama maganar da ya faɗa min. Yana kallon bakinta na mimimi a ransa ya furta 'fitinanniyar yarinya kawai'.
Shigowar Aunty Ade yasa ya miƙe ya fice bayan ya faɗa mata da safe idan aka gama alluran da suka rage za'a sallame ni mu tafi gida.
Ko Office ɗinsa bai shigaba ya shige Motarsa ya nufi gida, dama sabo da ita kaɗai ya dawo Asibitin. Da dare ya ɗauki matarsa suka wuce gida a gajiye da kuma jimamin rashin da suka yi.
**** Washe gari aka sallame ni bayan ansha daga wurin yi min allura, don fir naƙi yarda Nurse ɗin da tazo dubani tayi min. Fama aka tayi dani har sai da yazo ya min da kuka da komai, don yau hada Allah ya isa nayi masa ko yaji ko bai jiba oho shi ya sani ba ruwan Hanan.
Mun koma gida akaci gaba da zaman makoki ni kuma naci gaba da shan magani a gida har aka yi kwana bakwai baƙi kowa ya koma saura mu ƴan gida kawai sai Fa'iza ƙanwar Momy da A'ishah matar Ya Nabeel da tayi wata irin rama a kwana bakwai ɗin nan tsabar damuwa da rashin cin abinci. Sosai ta shiga firgici da tashin hankalin mutuwar Mijinta don ba ƙaramin so take masa na, itama zuciyarta ta ƙara bushewa da tsanar Hanan sabo da ita da Momy da Mamynta duk sunce itace silar mutuwarsa.
Ranar kwana na takwas suka tardo mu har sashenmu suka yi mana cin mutunci Momy ta faɗi zafafan maganganu akai na ta kuma ce "Wallahi Harira tun da kuka yi sanadiyyar da na rasa ɗana keda matsiyaciyar ƴarki, to kema ba zan taɓa bari hankalinki ya kwanta ba, sai nasa kin yi da na sanin sanina a duniya, don sai na wulaƙanta rayuwar ƴar da kike taƙama da ita!".
"In sha Allah, Allah ba zai baki nasara ba Habiba, mugun nufinki a kanki zai ƙare!" Ammy ta maida mata martani a karon farko da na taɓa ganin Ammy ta tanka mata in tana rashin mutuncinta. "To shikenan zamu gani ta faɗa suna ficewa daga ɗakin.
Kuka na fashe da shi bayan sun fice na juyo na kalli Ammy da ranta yake a matuƙar ɓace don yau Habiba ta kai maƙurar haƙurinta. Sosai maganganun da ta faɗa suka tada mata hankali, sai dai kuma Allah ya fita, yana ji kuma yana gani. Kallonta nayi nace "Ammy wannan wace irin ƙiyayya ce haka Momy ke mana?, Don Allah Ammy yau ki faɗa min mai ke tsakanin ku da Momy?".
"In sha Allah Allah ba zai bata sa'ar cutar da muba, munfi ƙarfinta tunda mun riƙe Allah, duk kuma abin da kikaga ya same ki to rubutacciyar ƙaddararki ce, kuma yau in sha Allah zan baki labarin abinda ya faru a tsakaninmu...
*Kansa'u Bello*
( *Oum Fatima)*
***
Follow me on Arewa Books @Oumfatima33 for more pages