Free chapter 路 Read without an account
Chapter 19 , 20
by Ikilima Adam 路 RAMIN KARYA
馃崅馃崅_*RAMIN K'ARYA*_ 馃崅馃崅
NA
IKILIMA ADAM
*( Kyauta daga Allah)*
Marubuciyar da ta nishandantar daku a littafanta kamar haka:
Kai ka jawa kanka
Kanwata
Rai daya ( Jan zaki)
Rudani
Makauniyar shari'a
And now
Ramin karya yan karin magana suka ce kurarre ne , mu je zuwa.
Da sunan Allah mai Rahma mai jin kai .
Page daya ya rage na daina postin a public sai yan special group kadai ne zasu ci gaba da bibiya.
Baki makara ba kina iya payment akan wannan acct din 9069080725 ikilima Adam Opay.
Domin Karin bayani *** kada ku manta Ramin karya yana dauke da darussa da ta inda bakwa tunani .
SHAFI NA SHA TARA
Kana ya dan juyo yana fuskantar ta . Murya cikin amo da tsawa ya ce '
" Akul dinki kika kara danganta cikin jikinki da Maryam dita , wallahi kinyi kadan ki sanya sunan abar sona da wannan kazamin cikin ki " ya fada yana mai buga sitiyarin motar yana fesar da zazzafan numfashi. Duk inda tsoro yake ya gama bayyana a fuskar Lailat dan ji take kamar duka ze aika mata , hakan ya sanya ta fara dan dan jan jikinta gefe daya , ta gefen idanu yake kallonta , idanunsa sun kada jajir lokaci daya , dakyar da kokari ya kunna wutar motar yana mai hangen su Jidda gilashin motar , ganin yanda suke a tsorace suma. Tunda ya dau hanya babu mai yiwa wani magana , sauran motar dake biye dasu mamaki ne ya cika su matuka , ganin yanda yake tuki kamar ze tashi sama. Ya sanya kowa yasha jinin jikinsa a motar. Lailat ga mamakinta kofar Gidan iyayenta yayi parking . Sai da magoya bayansa suka iso kana ya sauko daga motar yana mai budewa su Jidda motar , fita suka yi , suna rarraba idanu akan unguwar da suka zo , Lailat cikin hanzari ta shige Gidan nasu , ganin ta shige ne ya sanya shi , kallon su Jidda.
" Mu je ku gaida mamar Maryam " ya fada yana mai yin gaba. Take masa baya suka yi dan basu isa suyi masa musu ba. Suna shiga cikin Gidan a conpund din Gidan suka hango Lailat na kuka , mamarta sai tambaya take ta kasa mata bayani.
Takun tafiyar su Jidda ne ya sanya Lailat hadiye kukanta , tana mai kallonsu a wulakance.
" Me kuke nema Gidan mu " ta fada tana kallon Jidda.
" Ni nace su zo su gaida Umma" Prince ya bata amsa a takaice.
" Maraba sannunku da zuwa Maryam , wash Allah yi hakuri Jidda zan fadi" ta fadi tana mai basu wuri da su zauna saman tabarma. Zama suka yi dan tsayuwa ba dabi'arsu bace .
" Ina kwana" suka hada baki wajen gaishe da Umma.
" Lafiya lau amare , kai Adamu ai sai kace mun zaka kawo su da yanzu , na shirya musu wani abu" ta fada tana kwalawa yarinyar dake hannunta.
" Halima kawo ruwa , da lemu" ta fada cikin zakewa
" Karki damu akan hanya muke. Amma zan bar lailat ta wuni sai dare ta dawo Gida , ina kwana Umma ya gida ya hakuri da rayuwa " ya fada cikin girmamawa. Duk sanda ta gama Adamu ko Jidda ji hakan na mugun tuna mata da wani abun .
" Lafiya lau nake , naga amarya sak margayiya , dan Allah ka rike min ita da amana " ta fada cikin sanyi. Lailat a rikice take kallon mamarta. Karkada kai take yi tana nazartan kalaman Umma . Maganar Adamu ne ya dawo da hankalinta kusa jin yana fadin.
" In Sha Allah, zamu tafi " .
"Ya ankawo ruwa baku sha, don Allah ku sha , Jidda na tausaya muku da gobarar da ta sami iyeyenku" ta jefo maganar daga sama. Jidda dago kai tayi suna hada idanu ta mama, wani irin rass gabanta ya buga, haka ita ma mama.
" In Sha Allah zan kawo su. Su wuni". Ya fada tare da kama hanyar fita.
Mama tashi tayi tana mai kama hannun Jidda cikin nata , tana matsewa cikin nata , kana ta furta .
" Allah ya kai ku lafiya , na gode matuka da ziyara , Adamu na ji dadi " ta fada tare da masu rakiya sai da ta ga sun fice kana ta dawo Gidan jiki a sanyaye .
" Wallahi Mama kin bani mamaki" cewar Lailat tana zubar da hawaye.
" Me ya faru Lailat kike wannan danyen furucin " .
" Mama ashe baki kaunata ,kin fi son bare a kaina. Da cikin ki fa kika haifeni" ta fada tana zubar da hawaye.
Shafata Mama tayi cikin sanyin jiki da kulawa ta ce.
" Haba Lailat ance ka so naka duniya taki shi. In kaki naka duniya ta soka , suma yaya ne fa , kina son na mata mugun adua ne gaban mijinta ".
" Eh haka nake so " ta fada murya na tashi. Ta kara da fadin " ai ba dole sai kinyi hakan ba sai ki bar abun a cikin ki , karara kin siya min raini a wajensu , haba Mama !!! " .
Mama kallonta take tare da zama saman tabarma .
" Lailat baki ga tana kama da margayya ba. Yanayin maganar su daya komi banda yanayin tafiyar su " ta fada a raunace .
" Ai kama da wane bata wane " kawai bana so!! Bana so!! ki daina wani hulda dasu , kuma abba ya dawo daga Masar zan fada masa , ko ma na sanar masa a waya " ta fada cikin takaici.
Mama kuwa ranta ya soma baci dan sai lallaba Lailat take kamar tana cewa ci gaba.
" Duk abunda kike so kiyi Lailat daman tun farko bakya jin maganata " ta fada tare da tashi ta bar mata wurin.
Lailat kuwa wayarta ta dauko ta dannawa Maimuna kira.
Dagacen bangaren.
" Uwargida ran gida , sai yau ake jin ki " ta fada cikin zolaya.
Sheshekar kukan Lailat ne ya sanya Maimunat kauda wasan gefe.
" Lafiya kuwa " ta fada cike da damuwa.
" Maimuna ko nawa ne zan kashe in har za'a iya kashe min Mama " ta fada zuciya a dake.
Zumbur Maimunat ta tashi daga zaune da take .
Baki na rawa ta ce ." pls Dan sake maimaitawa ".
" Kin ji komai , bana son wasa serieu nake " .
" Lailatu baki da hankali ne , Mama fa uwarki ce , dan kin kashe Maryam kina tunanin yin haka akan Mama dawa kike son ki zauna , wannan aiki sai Nura yafi karfina " ta fada cikin tsananin tsoro."
" Don Allah karki bari maganar nan ta fita , sannan zan kira Nura , anjima zan miki bayanin komi" ta fada ba ta jira amsar Maimunat ba ta katse wayar.
Bangaren Maimunat safa da marwa take yi cikin dakin yatsarta daya a baki , kalaman Lailat ne je yawo kwanyar kanta.
_________________
Prince Adamsy yana zagawa ma'aikanta sa na Shinkafa , magoya bayansa na bayansa yana bi yana kallon yanda inji ke aikin shinkafa suna zubawa a buhuna . Hannun ya saka ya debo shinkafar ganin ingancinsa ya sanya shi maidawa , yana mai tambayarsu ko akwai abunda ake bukata. Manager ne ya tabbatar masa babu komai da suke bukata . Hakan ya sanya ya taka har zuwa office dinsa , dan a sati sau daya yake zuwa. Sosai ya jama'a dake son ganinsa suka cika room dinsa ana jirar isowarsa. PA ne ya kai file din kowa cikin office dinsa . Domin samun ganin kowani bako dake zaman jiran ganawa dashi.
" Yana zama office dinsa ya ji takanas gabansa na tsananta bugawa da karfi. Dakin ne ya mamaye da duhu tare da wani irin iska mai karfi kai kace a waje yake . Adu'oi ne yake karantowa yana mai yi muryansa na tashi , ya dade yana adua kana abun ya sassauta stil dai akwai iskan .
Cen daga sama ya ji muryan na tashi .
" Adamu !!! Adamu !!! ". Be amsa ba , sai da ya gyara zamansa yana karanto ayatul kursiyyu a sannu sannu ya daina jin komai tare da samun nutsuwa har ya sanya a fara shigo da masu jiransa.
______________
Nura zaune waya yake da Lailat , zaune yake gaban dodon tsafi , daga shi sai jan zani , babu riga .
" Dole ne a dauki mataki akan Mama fa. Wallahi abun yana yawa , kuma zuba idanu kiyi kallon yanda wasan ze fara a yau , maganar Mama me sauki ne , Jidda zata fara girban abunda ta shuka kuma zata mutu a tsaye " ya fada yana mai tabbatar mata .
" Har kasa na ji sanyi a raina wallahi " ta fada tana zaune cikin dakin gidan na su , jin kamar Mama na buga kofarta ya sanyata fadin.
" Zan kira ka , Mama na kira na " katse wayar tayi bata jira cewarsa ba.
Prince Adamsy cikin dauriya da kokari ya isa Gidan babban malamin addinin nan Wanda ya zo aikin da'awa garin cotonou sheik Isa Ali pantami.
Sheik Isa zama yayi suka yi kan diner table suna hira shi da prince Adamsy bayan sun gaisa cike da mutuntaka .
"Adamu naga ka rame , ko yanayin rayuwa ne " .
Hawayen da yake rikewa ne suka fara cika masa idanu .
" Ina cikin damuwa babba Wanda bansan ta inda zan fara ba".
Sheik dake kallonsa tasbihi na hannunsa , cikin kosawa ya ce " fadi babu abunda ya gagari Allah.
" Sheik ba zan boye maka ba , wannan zancen daga ni sai kai matata ce take shirin haifa min d......
0906980725
Taku har kullum kyauta Allah
馃崅馃崅_*RAMIN K'ARYA*_ 馃崅馃崅
NA
IKILIMA ADAM
*( Kyauta daga Allah)*
Marubuciyar da ta nishandantar daku a littafanta kamar haka:
Kai ka jawa kanka
Kanwata
Rai daya ( Jan zaki)
Rudani
Makauniyar shari'a
And now
Ramin karya yan karin magana suka ce kurarre ne , mu je zuwa.
Da sunan Allah mai Rahma mai jin kai .
Last free page , daga wannan na kare tura littafin Ramin karya a kowace group sai Vip .
Domin kasance a ciki ki min magana ta wannan ma maganar.
*** .
In kin tura kudin ki min screenshot zuwa ki tura evidence ga number dake sama.
9069080725 ikilima Adam Opay.
Kada ku bari a baku labari domin tafiyar ta musamnan ce .
SHAFI NA ASHIRIN
" Sheik ba zan daga ni sai kai matata ce take shirin haifa min dan dana ke kyautata zaton ba nawa bane , kuma banda bakin da zan iya kare kaina a Masarautar, dan akwai kyakyawan alaka tsakanin Sarki da Mahaifinta , kana iyayenta mutanen arziki , imagine yanda zasu kalli abun da wata fassara ta daban " sai ya fesar da numfashi kana ya kara da fadin.
" Yau ma sai da na kaita asibiti bisa ga Umarnin Sarki. Ban san yanda zan saba musa ba " yayi shiru yana kallon yanda Sheik ke rike da baki yana sauraronsa.
Murya cike da kamala sheik ya ce .
" Adamu , ina ce matarka ce , kuma kana kusantarta, me ye ze sanya kayi wanna tunanin " ya fada cikin mamaki.
" Ban taba mu'amala da ita ba " ya fada cikin dacin rai.
Kwalolo idanu Sheik yayi suna kallon juna na sakanni kafin ya samu damar dukar da kansa kasa.
" Adamu ka tafka babban kuskure taya zaka auri mace ka ajiyeta , kana kayi tunanin zata zauna haka nan ".
" Malam tun farko bana son auren nan , dole aka min " ya fada yana mai baiwa Sheik labari tiryan tiryan.
Sheik sosai ya shiga tashin hankali jin labarin da prince ya bashi .
Ya dade yana karkada kai yana mamakin tunda yake be taba jin makamancin hakan ba .
" Adamu na fahimceka , zauna dakyau muyi magana ta yanda in sha Allah muna kyautata zaton sauki na tafe". Samun wuri suka yi suna tattaunawa cikin gamsarwa.
Sai da aka kira Magrib kana suka tashi daga zaman nasu , zuwa massalaci , daga nan Adamsy ya yi hanyar Gidansa yana mai jin kamar ya dan rage damuwarsa yana jin kansa , kamar wanda aka dauke daga haske zuwa duhu.
_____________
Rayyah ta mayar da hankalinta a wayarta inda take chat da mutumin nan .
" Rayya me zaki yi da kudade bayan kudin da gidan ku suke dashi " ya fada yana shu'umin murmushi.
" Wallahi zanyi birthday ne , ka san ba kudi za'a bani ba. Dan Adamsy ya hana bikin birthday 馃巶 , kuma zance ya zauna " ta fada .
Reply ya mata in har kudi kike so , zan hadaki da mai gidana komai kike so zai baki hatta garin nan yana iya siyen rabinta " .
Gwalalo idanu tayi don ita mayyar kudi ce gaba da baya , barin ta ji manyan kudade .
" Pls ka hada mu mana , kaga in ya bani sai nayi shirya taro na " ta fada cikin shauki.
Daga bangarensa zaune yake yana kasaitaccen murmushi.
Keyboard wayarsa ya shiga dannawa , da yayi rubutu in bai dai-dai sai ya goge , a karshe ya rubuta.
" Okay ga numbersa nan , kice nina baki , kuma karki masa musu, duk abunda ya ce , sannan mata da yawa ya biya musu bukatan su.".
" Ni wallahi in har ze bani kudi ko meye ya sanyani zan yi banda kisan kai ".
Sosai ya dara kana ya rubuta .
" My love , ban so a ce na rasa kudin da zan baki ba , kawai Abba ne be tura min kudi ba inna ce ki jirani lokaci ze tafi , am sorry please kin ji baby na ".
" Karka damu in ya dawo, sai a fara zancen auren mu , ni fa na yarda da kai" .
Number da ya tura mata ne ta dauko tare da aika masa da sakon sallama.
________________
Lailatu ganin yau kwananta ne ya sanya ta , hanzarta shiga dakin nasa ta mike kafa a falon tana kallon Tv .
Shi kuwa yana dawowa ya iske Debora ta dawo , tana Bangaren Hajiya Babba , nan ya iske Jidda da Ummi har Abdullahi da yaran suna zaune .
Da sallama bakinsa ya shigo fuskarsa dauke da walwala dan tunda ya baro Malam ya ci shi da nutsuwa.
Cike da ladabi ya gaishe da Hajiya babba , yana mai amsa gaisuwar Ummi da Abdullahi.
" Barka da zuwa Shugaba na " cewar Deborah fuska cike da annuri.
" Yawwa da fatan kin iso lafiya , yaki ka baro su , ya su yan uwa " yana kallonta fuska sake.
Cike da zakuwa ta ce , Shugaba lafiya lau suke , sun ce a gaisheka " .
" Ma sha Allah " ya furta yana mai satar kallon Jidda da tayi kamar bata san da zuwansa ba , ganin tana kus_ kus suna magana da Ummi ne ya sanyashi fadin.
" Jidda " idanunsa na kan Hajiya babba.
Ita kuwa kallonsa take, cikin dauriya da ganin Hajiya n wajen sanya amsawa kasan makoshinta.
" Ki je dakin Hajiya zaki ga leda ka kan drowe dauko min " ya fada , stil baya ko kallon inda take. Kallon kallo sukewa juna ita da Ummi , kana suka hada ido da Deborah dake mata kallon rashin sani . Ummi ce ta mata idanu alamun ta tshi ta tafi. Tashi tayi tana tafiya kamar wacce bata so har ta shiga sashin . Ita kuwa Hajiya babba ganin ta shige ciki ya sanyata fadin.
" Gaskiya Jidda yarinya ce mai hankali ga nutsuwa da kamala , bata cika yawan magana ba , ga aiki sam Koda bayi sun je mta aiki tare da suke yi " ta fada tana mai jin dadin hakan.
Karkada kai yayi be ce uffan stil hankalinsa na kan Jidda da ta shiga daga ciki.
" Ina zuwa " ya furta yana mai nufar tsararren dakin Hajiya babba . Ita kuwa Jidda sai dube dube take bata ga ledar ba , juyowa tayi dan zuwa gaya masa bata gani ba , taga an bude kofar. Ganin ya shigo bakinsa dauke da sallama , ya sanya yin kasa da kanta bata amsa ba , " ban ga ledar ba " ta fada cikin dakiya.
Banza ya mata yana mai karasowa cikin dakin , gefensa ta raba zata fice , karo na farko da ya sanya hannunsa ya cafko ta , cikin rudu da rude take kallonsa tsoro da fargaba sun maye rashin sa .murya na rawa da kaduwa ta sake fadin" na ce ban gani ba " kamar me shirin kuka.
" Ba'a koya miki gaisuwa bane" ya furta .
Garin janyota ta sulale tana kokarin kaiwa kasa , azafafe yasa hannu domin tare ta , hakan ya janyo faduwar akanta , akan lallausan carpet din dakin mai dan karen kamshi . Jidda kuka ne ya zo mata ganin yanda kirjinsa ya mannu da nata da ta ji dan zafi .idanunsu tsarke cikin na juna . Kwayar idanunta yake kallo yanda ruwan hawaye suka cike su , lumshe idanunsa yayi yana jin wannan yanayin kamar tare da Maryam yake , wani irin kasala ne ya mamaye shi , dukan ila'ihirin jikinsa yayi sanyi.
" Wayyo?
! daga ni" ta furta cikin disashewar murya.
Ajiyar zuciya ya sauke ya tashi cike da jin kunya. Yana tashi ita ma ta tashi tana kakkabar jikinta kamar wacce ta fada cikin yashi. Kamar me dube_dube ya shiga duba drower din Hajiya babba , dama cen ba abunda ya ajiye tsabar son ya zo ya ja mata kunne ne .ganin har ta kai bakin kofa ya furta.
" In kin ganni cikin mutane ki ringa gaishe ni cike da girmamawa dan ni ba abokin wasanki bane" ya fada yana mai zama bakin gado. Ganin tana kokarin murda handle din kofar ya sanya shi fadin.
" Kika kuskura ko da wasa, na ji kina fadawa Ummi ,mun fadi sai na zama dodo na dode muku bakunan ku " ya furta yana dan hada rai. Jin in ta kara minti daya zata iya maida masa martani dan ita bata barin ta kwana haka take tin fil'azal , fita daga dakin tayi tare da nufar falon . Deborah kuwa kallonta take tana maganar zuci.
" Wannan Kuma wace ce ? naga ya bi ta sun dade cikin dakin , anty Lailat bata nan , na san da zata bi su taga me suke yi " rasa me bata amsa ya sanyata barin wannan tunanin.
Jidda sai raba idanu take tana neman Ummi , ganin bata nan ne ya sanyata fadin.
" Hajiya ina Ummi ta shiga " ta tambaya cikin bukatar hakan.
" Ai kun dade dakin ke da mijinki naki , ita ma nata mijin ya zo sun tafi sashin nasu , ina ga baku ga ledar bane ko , Dan ban san lokacin da ya ajiye ba".
Debora saida kanta ya buga jin wai Jidda matarsa ce , cikin hanzari ta tashi ta bar dakin ba tare da ta musu sallama ba , dan sosai take jin wani irin zafi a ranta. Hajiya basu kula da fitar ta ba , dan hira suke da bayi da ma'aikata. Da abokiyar shawarar Hajiya watau delu.
" Jidda kama yaran nan ki kai su dakin su , dan shi har yanzu yana cen yana neman abunda ban san ranar ganinsa ba".
Daga sama ta ji yana fadin.
" Ayya ashe ba adakin ki na ajiye ba , yana dakin margayya Maryam" ya fada yana sosa keya.
Delu dariya tayi tana fadin" Yawwa Babana ai na san mantuwa ne kayi shiyasa , sai ka kama mata ku kai yaran nan dakinsu" ta fada tana murmushin. Hajiya babba ma murmushi take tana mai jin son jikokinta .
Shi kam murmushi yake yana mai sosa keyarsa .
Sallama ya musu , kana ita ma Jidda ta ma Hajiya da Delu sallama . Kama hannun Hassana Jidda tayi , shi kuwa ya kama hannun Hussain. Tana gaba yana bin ta a baya , hakanan ta ji ajikinta yana kallonta . Waigowa tayi ta ga ita din yake kallon , hanzarta tafiyarta tayi dan ta tsani kallo kuma abunda ya faru ne ke yawo saman kwanyar kanta .
Lailat sanye cikin kayan barci ta fito jin ya dade be shigo ba , fitowa tayi tana sanye da hijab , hango su tayi shida Jidda sun kama hanyar dakin yara .
" Jar uban nan " ta furta tana mai jin wani irin azazaben kishi na dibanta.
Kokarin bin sahun su take , taci karo da Nura da shima kamar wajent ze je .
" Lafiya kuwa " ya furta yana kallon inda take kallo.
" Adamsy yau kwana na ne , tunda ya shigo be zo sashinsa ba , zaluncinsa ya fara isata fa , Nura zan iya kasheta wallahi" ta fada a harzuke .
" Haba Lailat kwantar da hankalinki , akan Jidda ki kwantar da hankalinki , mu je dakin ki naki kiga abunda ze faru a yanzu nan " ya fada , suna mai bin hanyar dakin Lailat din.
Koda shigarsu , wani roba ya dauko ya zuba ruwa a ciki. Saiga Jidda da Adamu sun bayyana a ciki.
Kallonta Lailat ganin , Jidda tana kokarin kwantar da yaran saman gado , shi kuwa yana musu adua yana shafe musu jiki.
" Ita kallon yanda wasan ze canza " cewar Nura yana dariya.
Zura idanu tayi ,ganin Nura ya jefa wani kwallo cikin ruwan Wanda ya sanya ruwan ya fatsama a kasa.
Ganin tayi Jidda dake kokarin daukan kofin ruwa , ta z.......
Duka duka anan na kawo karshen free page na wannan Littafin Ramin karya . Masu son cigaba dan bin littafin har karshensa , Kuna iya tuntuba ta akan wannan lambar.
***.
Naira dari biyar kacal zaki biya ga asusun banki na .
9069080725 ikilima Adam Opay.
Ki turo da shaida biya akan number dake sama.
Don Allah in kin san baki ahirya ba kada ki min magana , kuma in har kinsan kin siya ne dan ki fitar shi ma don Allah ki min magana na dawo miki da kudin ki. Kudin karatu kika biya bana mallakaba.
Taku har har kullum kyauta daga Allah