Free chapter · Read without an account

Chapter 19

by Kansa'u Bello · ALLON ƘADDARA

✨ *ALLON* *ƘADDARA* ✨





     *OUM FATIMA* 




 *DASHEN ALLAH* *WRITERS* *ASSOCIATION*






 *PAGE 19*




**** Washe gari kowa ya tashi da abinda ya kwanta da shi a cikin ransa. Bayan Harira ta gama duk wasu ayyuka da take taimakawa Mamansu da shi ta shirya ta nufi gidan su Habiba zuciyarta cike da fargabar yanda zasu ƙare.


Mamansu ta fara zuwa ta gaisar, lafiya lau ta amsa mata ba wani abu a fuskarta, tambayarta Habiba tayi tace mata "tana ɗakinsu" ta bata amsa taci gaba da abinda take yi, tashi tayi ta nufi ɗakin jiki ba ƙwari.


Sallama tayi har sai uku ba'a ambata ba, hakan yasa ta ɗaga labule ta shiga ciki. Zaune ta samu Habiba da ƙanwarta Sakina suna ƙaryawa "Ina ta sallama kuna jina kuka ƙyale Aminiya!" Harira ta faɗa fuskarta na nuna rashin jin daɗin abinda suka yi matan.


"Ba za'a amsa ɗin ba, ai ni bana amsa wayar munafukai maciya amana azzalumai irinki, bari kiji abinda baki sani ba shine, na tsaneki tsana mafi munin da ban taɓa yiwa wata halitta irinta ba, duk wanda yace zai shiga tsakanina da abinda nake so koda Sakina ce to kuwa mun ƙulla yakar juna ni da shi har abada!" Habiba ta faɗa cikin ɓacin rai.


Magan-ganun sun matuƙar yiwa Harira zafi a rai amma ta daure ta nufi Habiba tana ƙoƙarin taɓa ta "kar ki kuskura ki taɓa ni!" Habiba ta faɗa a tsawace.


"Bai kamata ki yanke irin wannan hukuncin a cikin fushi ba Aminiya, ya kamata ki tsaya ki sauraren ni ki..."


"Kada ki ƙara kira na Aminiyarki har abada na riga da na yanke ko wacce irin alaƙa tsakanina da ke!".


Bata haƙura ba ta ƙara matsawa zata yi magana sai jin saukar wani azababben mari taji ya sauka saman fuskarta, kafin ta dawo hayyacinta daga raɗaɗin marin taji an rufe ta da duka tako ina. Kamar sun samu jaka haka Habiba da Sakina suka yi mata dukan tsiya sai da Mamansu taji ihunta ta shigo ɗakin ta ƙwa wace ta a hannunsu ta rufe su da faɗa.


Haka ta tafi gida tana kuka hancinta na zubar da jini. Dai-dai kwanar da zata fita ta shiga layinsu suka haɗu da Sulaiman dake ƙoƙarin shigowa layin su Habiba da Motarsa. Gabansa yaji yayi mummunan faduwa ganinta a hargitse tana kuka ga jini na zuba a hancinta, da sauri ya tsaida Motar ya fito ya nufe ta yana tambayarta "lafiya na ganki a haka? Miye ya sameki? Jini fa kike zubarwa!" Ya ƙare maganar cikin tashin hankali yana ƙoƙarin riƙo hannunta.


Hannunta ta fizge cikin fushi tayi gaba zuciyarta na jin haushinsa "duk abinda ya faru ai kai ka jawo" ta faɗa tana fashewa da kuka. 


Bayanta yabi har zuwa ƙofar Gidan da ta shiga. Da gudu ta ƙara sa shiga gidan tana faɗa wa saman cinyar Mamansu ta fashe da kuka "Ke! Lafiya? Miye haka nake gani ni Salamatu?"Mamansu ta faɗa tana ɗagata.


Sai da tayi kuka sosai kafin ta faɗa mata duk abinda ya faru tun daga farko "gaskiya Habiba bata kyauta ba ai ba'a haka amma kiyi haƙuri ki tashi ki wanke fuskarki Ade ta raka ki kemis a duba ki, zan faɗa wa Babanku a san abin yi tunda ba'a san iya ina abin zai tsaya ba".


Sallama wani yaro yasa su ɗagowa suna kallon sa "wai ana sallama da mai gidan" yaro ya faɗa. Gabanta taji ya faɗi don tasan shine ya aiko "kace ya fita Kasuwa" Mamansu ta faɗa. Fita yaron yayi ya sanar masa ya ƙara maido shi yace yana neman izinin shigowa zaiyi magana da Mamansu.


Hijabi Maman ta saka tace ya shigo zuciyata cike da mamakin waye. Shigowa yayi da sallama aka yi masa iso a parlourn Babansu. Ruwa aka bawa Ade ta kai masa, gaishe sa tayi ya amsa da tambayarta sunanta ta faɗa masa ya ce "Yayarki fa?".


"Harira" ta bashi amsa ta juya ta fice ta barshi yana mai-maita sunan a zuciyarsa "Nice Name" ya faɗa yana lumshe ido.


Shigowar Mamansu yasa ya sauko ya duƙa har ƙasa ya gaishe ta, ta amsa masa da kulawa kafin ta tanmabaye shi abinda ya kawo shi. Bai ɓoye mata komai ba ya faɗa mata ya kuma ɗora da roƙon a taimake shi a bashi ita. Mama ta rasa mai zata ce masa sabo da girman al'amarin.


"In sha Allah za'a faɗawa Babansu idan ya dawo, ko mi kenan zaka ji" Mama ta faɗa masa. Godiya sosai yayi kafin ya nemi alfarmar su fito ya kai su Asibiti "Ba wani babban ciwo bane ƙanwarta zata rakata, an gode da kulawa" Mama ta faɗa kafin ta miƙe ta fice a parlourn.


Ba don yaso ba ya miƙe ya fice jikinsa a sanyaye. Gida ya nufa kai tsaye yaje ya samu Mamansa ya shaida mata akan ta fadawa Babansu aje a nema masa auren Harira. "Zan sanar da shi in sha Allah da ya dawo" godiya ya mata ya nufi ɗakinsa don yau baya jin zai fita wurin aiki.




**** Habiba kuwa sosai Mamansu tayi musu faɗa ta kuma sanar da Babansu da ya dawo, shima kiranta yayi ya mata faɗa sosai da nasiha, sai dai ba abinda ta ɗauka a abinda ya faɗa mata sai ma ƙarin tsanar Harira da taji, don haka ta koma ɗaki tasha kuka sosai kafin ta fara tunanin abin yi.


Babansu kuwa da kansa yaje Gidan Malam Musa ya bashi haƙuri akan abinda ya faru, nuna masa yayi ba komai yarinta ce ke damun Habiba sannan ya ɗora da faɗa masa zuwan Sulaiman Gidan da abinda ya kawo shi. Malam Umaru yayi murna sosai tunda shi da Harira da Habiba duk ɗaya ne a wurinsa, don haka bai ji komai ba sai ma yabin halayen Sulaiman da yake yi, ya kuma nuna masa ba matsala ɗan tsohon mai Gidansa ne, shi da kansa zai yi masa magana. A haka suka rabu cikin farin ciki.


A can Gidan su Habiba kuwa da Malam Musa ya sanar dasu yanda suka yi da Malam Umaru sosai Mamansu da Ade ke murnar abin alkairin da ya samu Harira, inda ita kuma ta kasa gane a wane hali take ciki akan al'amarin.



***** Kamar yanda Maman Sulaiman tayi masa alƙawari ta samu Babansu ta sanar da shi, sosai yayi murna tunda dama abinda yake jira kenan don haka yasa ta kirawo masa shi ya tambaye shi su waye iyayen yarinyar "Eh to Ƴar Aminin Malam Umaru ce Baba" Sulaiman ya faɗa yana sadda kai "Masha Allah Malam Musa kenan, ai abin yazo da suƙi na sanshi Mutumen kirki ne, ai lokacin da yazo garinnan a wurina ya fara sayen kaya sa" daɗi sosai ya kama Sulaiman jin abubuwan na zuwa masa cikin sauƙi.


"Kaje zan nemi Malam Umaru sai muje muyi magana da shi Malam Musa ɗin".


"Na gode Baba, Allah ya ƙara girma" ya faɗa yana tashi ya fita a ɗakin "Ja'iri da ana ta fama da shi ya fitar da Mata ya ƙiya amma dake yanzu lokancin yazo kinga da kansa yazo yake neman aje a nema masa aure".


"Abin da nake faɗa maka kenan dama Malam" Maman su ta faɗa. Hira sukaci gaba dayi kan yadda bikin zai kasance, kasancewar auren Babban ɗansu da suke ji dashi zasu yi.




**** Kamar yanda Allaji Wada (Babansu Sulaiman) ya faɗa da kansa ya kira Malam Umaru yayi masa maganar, anan yake ce masa eh dama shima zai neme shi akan maganar yanzu sai yasa rana a faɗa wa shi Malam Musa "Ai ba wani ɓata lokaci za'ayi ba inaga zuwa jibi Asabar zamu iya zuwa".


"To Allah ya nuna mana, in sha Allah zan faɗa masa shima sai a shirya"


"To Madallah" Alhaji Wada ya faɗa yana kashe wayar.


Malam Umaru da kansa ya ƙara komawa Gidan Abokinsa ya shaida masa zuwan su Alhaji Wada ranar Asabar "To! To!! Madallah, in sha Allah zan kira Yaya Sani sai yazo ayi komai da shi". Malam Musa ya faɗa "To hakanma yayi Allah ya nuna mana" cewar Malam Umaru.


"Ameen" Malam Musa ya faɗa kafin sukaci gaba da hirar Kasuwancinsu.


Bayan Malam Musa ya koma gida ya sanar da Mamansu yanda suka yi, yace mata "ki kirawo min ita Harira ya kamata aji ta bakinta" kiranta Mamansu tayi tazo ta zauna tana gaishe da iyayenta. "Akan maganar yaron nan ne, zasu zo a tsaida rana shin kina son sa?" Shiru tayi sai da ya ƙara tambayarta kafin tace "Baba Habiba ke son sa fa".


"Tambayar ki nayi kina son sa?" Shiru tayi ta kasa cewa komai, "tashi kije" ya faɗa da sauri kuwa ta miƙe ta shige ɗakinsu tana kukan da bata san dalilinsa ba.


"Allah ya raba ki da wannan halin Yaya" ƙanwarta Ade ta faɗa cikin takaicin Yayar tata.



Malam Musa a ranar ya kira Yayansa a waya ya sanar da shi abinda ke faruwa, yace masa yana tafe in sha Allah.


Iyayen Sulaiman sunzo a ranar da suka faɗa, Malam Musa da Malam Umaru tare da Malam Sani da wasu daga cikin maƙota suka tarbesu aka amshi alawa da goro aka tsaida biki wata biyu kafin suka tafi cike da farin ciki.



**** Duk wannan bidirin da ake Habiba bata sani ba tana can suna ƙulla yanda zasu liƙawa Harira wani sharrin da zai sa ko wani saurayi ma bazai ƙara kallonta da sunan so ba, bama Sulaiman ba sai dai Hausawa suka ce wai kana naka Allah na nasa.


Suna zaune a parlourn Mamansu Babansu ya shigo da goro da alawayaba Mamansu ya shaida mata an tsaida ranar auren Harira da Sulaiman wata biyu. "Allah yasa alkairi" Mamansu ta faɗa tana ajiye laidar alawar. Ihu Habiba ta saki kafin ta faɗi sumammiya, da gudu Sakina taje ta ɗauko ruwa aka yayyafa mata ta farka a ficgice tana fashewa da matsanancin kuka da faɗar munanan magan-ganu akan Harira da ɗaukar alwashi iri-iri tama manta a gaban Babansu take sai da ya daka mata tsawa kafin ta dawo hayyacinta.


"Ashe baki da hankali ban sani ba Habiba? Kece kike faɗar irin wannan munanan kalaman akan ƴar uwarki? To bari kiji daga yau na sake jin wannan maganar dai na mugun saɓa maki, har yaushe kika zama sakarai da zaki rasa hankaliiakan namiji? To daga nan na kashe wannan maganar har abada in kika ƙara tadata ban yafe maki ba kiji abinda nace? Cikin matsanancin kuka take gyaɗa kai.


Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ɗora da mata nasiha da rarrashi ya ɗora da cewa "Da ace Sulaiman da kansa ya ganki yace yana so zan yi farin ciki da hakan sabo da mutum ne mai nagarta, amma ba ke yake ra'ayi ba ƴat uwarki ya zaɓa kuma dake da ita duk ɗaya ne a wurina, sabo da haka ki manta da shi ki fitar da wani Mijin a cikin Manema ki na gama magana". Ya faɗa yana miƙewa ya bar ɗakin.


Kuka sosai Habiba tayi Mamansu da Sakina na rarrashinta kafin ta haƙura tayi tayi shiru "Tabbas rasa wanda kake so akwai matuƙar ciwo amma sai dai idan kayi haƙirinka barwa Allah lamuranka to sai ya musanya maka da abinda yafi alkairi" Mamansu ta faɗa mata cikin son kwantar mata da hankali.


Bata ƙara tada maganar ba ko sake neman Sulaiman kamar yanda Babansu ya faɗa sabo da basa tsallake maganarsa, amma daga lokacin ta ƙara ƙullatar Harira a zuciyarta da tsana mafi muni a rayuwarta ta kuma yanke ko wace irin alaƙa da ita, tace ko a lahira bata fatan su haɗa hanya sabo da Habiba Mace ce mai tsananin riƙo da taurin zuciyar da bata manta bashin gaba.


Duk yanda Harira taso ta fahimtar da ita cewa ba laifin ta bane taƙi bata damar hakan, haka aka yi bikin Harira da Sulaiman aka kaita ƙaton gidanta mijinta yaci gaba da kula da ita cikin tsananin kulawa da soyayya mai tsayawa a rai.


A wurin ɗaurin auren Harira Abba Mukhtar ya abokin Sukaiman yaga Habiba ta fito daga gidansu zata bar Unguwar don ji take zuciyarta kamar zata ƙone ƙurmus da baƙin ciki....





Oum Fatima ce

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.