Free chapter · Read without an account
Page 5
⚡️*GAMON JINI*⚡️
*NA FATIMA MOH'D GURIN*
*GUREENJO*
*E.W.F*
*PAID BOOK*
*FREE PAGE FIVE*
*TAURARI BIYU⭐️⭐️ DAGA TASKAR MARUBUTA BIYU✍️✍️*
*****
Har ya bud'i baki da niyyar amsawa hajiya yaya ne se ya fasa, waigowa yayi ga Amah yace
"Allah sarki, Allah ubangiji ya bata lafiya me yasa tun jiya d'in Abrar be sanar dani ba ai da da safen nan na tafi na dubo ta, d'a na kowa ne kuma musulmi d'an uwan musulmi ne kinga wani dalili ze sa in hanata zama gidana? Na san inda Allah ze jefa nawa tunda na haihu?"
Farin ciki ne ya cika zuciyar Amah wadda har yayi nasarar bayyanuwa saman fuskanta, ta kasa fasalta irin daad'in da taji sbd har ga Allah tausayi da kaunar Amatullah ya riga da ya tasirantu cikin rai da ruhinta, murmushi kayatacce tsohon ya saki ganin farin ciki kan fuskar matar tashi, Hajiya Yaya da ta had'e rai cike da takaici tace
"Amma dae Alhaji..." hannu ya d'aga mata yace
"Dakata Halimatu.! ina da yakinin Abrar baze ta'ba kawo abinda ze cutar damu ba, kai ko wani ne ya kawo se inda karfinshi ya kare wurin kare mu.. dan haka ki saurara min.."
Cike da takaici tace
"Au kenan yanzu da ni kake?"
'Dago ido yayi ya zuba mata kallon da yayi mata yasa ta fice fuu, d'age kafad'a yayi ya sani ita ma kuma ta sani ta sanadiyarta suka kusa rasa shi ba don kariyar ubangiji da kuma Abrar da Allah ya bashi ba da yanzu sede wani ba shi ba, yana godiya wa Allah da ya bashi d'a irin shi tabbas Abrar kyauta ne na mussaman a gareshi kuma za'babbe shi yasa ko da yaushe akan uzuri yake mishi sbd maganar Aure,sanin kuma waye Abrar yasa be yi yunkurin fitar da mace ya aura mishi ba dukda umarni kawai ze bashi ya cika.... maganar Amah ce ta dawo dashi daga duniyar tunani da ya tafi suka hau hira irin ta asalin masoya waenda tsufa ko girma be sa soyayyar da sukewa juna ta ragu ba sema karuwa da take a kullum...
*****
Cikin yanayin tafiyarshi ya d'auki doguwar varender d'in da zata sadashi da Amenity,kanshi kasa as usual bakinshi na motsi a hankali jin kaman ana kallonshi ne yasa ya d'ago a natse ya kalli gabanshi sau d'aya ya cigaba da tafiya,har ya d'an wuce da taku biyu chakk ya tsaya tare da waiwayowa...
"Brigadier General Muhammad Abrar Muhammad Magashi"
Matashin mutumin ya ambata wadda hakan ya tilastawa Abrar dakatawa tare da waiwayowa, a shekaru ze iya bashi shekaru uku zuwa hud'u, bayanshi sojoji ne guda biyu rike da bindigunsu cikin cikakken shiri sa'banin mutumin dake sanye da personal wear, kankance idanunshi yayi kan ya furta
"Wlh na tsaneka.."
'Dan wara idanu Abrar yayi yana d'age gira yace
"Na sani,sai me?"
"Nayi alkawari matukar ina numfashi a doron kasa se na kaskantar dakai mafi munin kaskantarwa,ba haka kake yawo ba kai wai me tausayin na kasa dashi? Muje zuwa.."
Baki ya ta'be tare da d'age kafad'a yace
"Wadda ya isa ya kuma yarda da kanshi shi ne ze iya yawo haka sa'banin matsoraci da ya riski matsayi ba tare da chanchanta ba,ka ta'ba ganin zaki ya tafi farauta a gayya? Ina so ka kwana da sanin cewa kai kai d'in nan colonel Nura bukar baka isa yiwa Muhammad Abrar muhammad magashi komai ba se abinda Allah ya hukunta. If you don't have any important thing to say fi amanillah"
Daga haka ya juya yayi tafiyarshi cikin kasaita da kuma isa wadda duk ya had'e su Amah d'iyar sarkin Gombe ce 'Lamido Muhammad' ce wadda ya ci sunan mahaifin nata kuma tsab ya gaje kasaitar da ita bata dashi sede jini duk inda aka ce jinin sarauta se kaga hakan a d'abi'ar mutum...
'Dakin ya tura ba tare da yayi magana ba da sauri Amatullah dake raku'be karshen gado ta d'ago kai idanunta jage jage da hawaye, ganinshi yasa tayi saurin dira ta nufoshi kan ta isa gareshi ya d'aga mata hannu sbd ya san haramcin ta'ba macen da ba tashi ba, a tausashe kaman yadda yake magana cikin rashin hayaniya yace
"Menene haka Amatullah? Taya zaki samu lafiya idan zaki kasance cikin damuwa? Me ke tsorata ki?"
Yayi maganan yana kallon jikinta tun kayan jiya ne, hindu dake gefe ya kalla sbd shirun da tayi bata ce komai ba se shesheka, amsa gaisuwar da tayi saurin rusuna ta mishi yayi ya d'aura da
"Ya akayi ne?"
A ladabce tace
"Likita ya ce in ta tashi ta ci abinci sossai ta samu ta sha malt sannan a tsaftace ta sede tunda ta tashi taki yarda in ta'bata yalla'bai abincin ma taki ta ci se kuka."
Hannun Amatullah d'in ya kama yana istigfari bakin gado ya ajiyeta shima ya zauna, hannu ya mikawa hindu alamun ta bashi plate d'in, mika mishi tayi ya fara d'iba a hankali yana bata se ta noke in ta kalli idanunshi taga ita yake kallo hannunshi kuma na makale a iska yana jiranta se ta bud'e baki ta kar'ba,seda ya tabbatar ta koshi yadda yake so kan ya bata malt d'in ta sha sossai ta mika mishi amsa yayi a tausashe yace
"Amatullah.! Duk wadda zaki gani a nan tare da ke makunsanci na ne bazasu ta'ba cutar dake ba, ki saki jikinki u r safe here kin ji ko?"
Kai ta gyad'a tana sake sunnewa yace
"In da gaske kin ji prove it... ki bi hindu ta taimaka miki tsabtace jikinki."
Hindu dake tsaye cike da alajabin dama Abrar na iya magana haka? Har kuma wai ya san sunanta? Ta de san duk sadda suke tare da Amah ko wani ya shiga shiru yake shiyasa ta yanke mishi hukunci kai tsaye ta lakaba mishi kurman Amah, tsawar da yayi ne yasa ta firgita a hasale yace
"U r very stupid,how dare you ina miki magana kin wani kura min ido kaman mayya?"
Cikin rawar jiki ta fara bashi hakuri ganin kaman har Amatullah d'in ma ta tsorata da tsawar yasa ya ja tsaki yana fiddo wayanshi dake ringing be kara bi ta kansu ba ya fara amasawa da kyar ran nan a chunkushe, Sun kusa mintuna talatin cikin bayin hindu na taimaka mata dayake Amah ta saka hindu d'in had'o duk abinda ya kamata da kayan sawar Humaida d'iyar Aunty amaryar Abbu da Amah ke riko duk kayan set d'in oriflame ne kaman yadda humaida bata iya anfani da ko wani product ba in ba nasu ba...
Bayan sun gama ta bata babbar towel ta d'aura karami kuma ta yafa a kai, duk abinda take yi tanayinshi ne a firgice a kuma tsorace duk hankalinta na kan Abrar, dukda Doctor ya bugawa hindu warning na kar ta yawaita kallonta in ba haka ba zata fara tsoronta hakan be sa ta kasa shagala daga kallon irin gashin da Allah ya baiwa Amatullah d'in ba, dukda ja ne irin asalin na fulani me yauki sede uban yawa wannan in ya samu gyara ba karamin kara kyau da tsawo ze yi ba... hindu bata ankare ba se had'a idanu sukayi da Amatullah wadda take jikinta ya hau tsuma, hindu ta ci gaba da kallonta tana shirin magana Amatullah ta tsala ihu a firgice tana rufe idanu, duhun da tayi arba dashi yasa tayi tunanin a ciki take wadda kuma ba'a son me irin ciwon ya ko kiyasta yana cikin duhu ne, wani irin ihu ta kuma saki tana me kara runtse idanun a gigice..
Itama hindun gabad'aya gigicewa tayi, turo kofar da akayi yasa ta maida kanta chan be kula hindun ba ya karasa yana cewa
"Amatullah... shhh..."
Fad'owa da tayi jikinshi ne yasa sauran maganan makalewa cikin hanzari ya marabceta ganin yadda duk jikinta ke karkarwa, janyeta yayi waje kan ya fara ambaton mata Allah, a hankali jikinta ke saki rawar na denawa, kan gadon ya mata masauki dukda ta kwanta sede ta rike hannunshi gam, karatu ya fara mata cikin suratul Ta-ha da daddad'ar muryarshi sak na sheikh Ali jabir Abdallah, idanunshi saman gashin kanta a haka bacci ya d'auketa se ajiyar zuciya take saukewa akai akai...
Seda ya tabbatar ta natsu kan ya d'ago zuwa ga hindu dake tsaye jiki a sanyaye a kuma tsorace yace mata
"Ki kula ki kuma kiyayi yawan kallonta..."
Dukda idanunshi ba ita suke kallo ba sede muryarshi ya tabbatar mata he is serious kuma umarni ne yake bata. A ladabce ta amsa, mikewa yayi ya fice za'a samu matsala a gidansu tabbas idan Amatullah ta koma, Hajiya babba ko hajiya Yaya babu me d'aga mata kafa ya sani sbd kuma ta hanyarshi da Amah ta zo gidan, be fata Amah ta riga ta sanar da Abbu maganan nan sbd a take ya da hi ya sauya shawarar kaita gidan Aunty mariya... da sauri ya d'aga waya ya latsa layin Amah d'in.
*****
"Wai ni Muhammad Magashi ke sokawa magana a fakaice... kuma a gaban wannan mayyar marar zuciyar, tabbas lokaci yayi da ya kamata in baje baabin cika cikan rashin darajata,daga kan Muhammad har Saude da yaransu d'aya bayan d'aya se sun yi nadamar sanina"
Hajiya Yaya ke maganar tana safa da marwa a cikin tamfatsetsen d'akinta, Nadra dake zaune gaban madubi tana d'aura d'an kwali tace
"Har kuma da Abbun? Me ya miki?"
Tace
"Har ni ze cewa na kawo abinda ze kasheshi ba don Allah ya bashi Abrar ba"
Da sauri Nadra ta d'ago tana kallon hajiya Yaya tunda abin nan ya faru Abbu be ta'ba fad'in komai ba kaman yadda be sauya daka yadda ya d'aukesu kaman'ya'yan cikinshi ba da sauri ta ce
"Sbd wa kika ce?"
Bayani ta mata na ta shiga ta samu Amah na korowa Abbu bayanin Abrar ya taimaki wata kuma ya taho da ita yarinyar da zatayi sa'ar humaida, da sauri ta mike tana kankance ido
"Wa ya baiwa wata damar ra'bar Abrar? Ta san kuwa abinda ta jefa kanta da rayuwarta? A cikin gidan nan kuma zata zauna... Kam bala'in chan"
Ta karasa da muryar lallai za'a tabka tsiya, hajiya Yaya tace
"Amma dae ba sonshi kike ba na gani.."
Murmushi tayi tace
"Bana son shi kam bana kaunar ganinshi sede ni na tanadarwa kaina shi sbd ni kawai aka halliceshi, zan aureshi sannan in tarwatsa rayuwar zaman lafiyarshi sena d'and'ana mishi azabar da ta fi ta mutuwa... bani da imani a fagen shi kaman yadda bazan saurarawa duk wata mace da zata ra'beshi ba ciki har da uwarshi.."
Muniba d'iyar Hajiya yaya er autarta da zatayi sa'a da Nadra d'in me shekaru 26 tace
"Me yasa kike zafafa kiyayya ne? Naga idan Auwal ne shine yayi abinda yasa Abrar harbeshi batare da option ba, ita kuwa Fadila da kanta ta kashe kanta me laifin Yayanmu anan?"
Gwa'be mata baki hajiya yaya tayi cike da masifa tace
"Ke Muniba ki fita idona in rufe, uban wa ya gayyaceki cikin maganar nan? Daga ke har Aisha dake bawa wanchan mayyar goyon baya alhali da cikina na haifeku se na ci muku mutunci, wlh ban ta'ba ganin marasa kishin uwarsu ba irinku, saura su biyar d'in kuma masu jin kaina duk sun yi aure sun tafi sun barni da marasa anfani... duk abinda kunnenki ze ji miki a d'akin nan idan kika kusakura na jishi a waje wlh ban yafe ba duniya da lahira kuma se kin biyani ruwan Nono na da kika sha... kaman yadda doka ta take a kanku fice ki ban wuri shashasha kawai."
A zuciye ta fice fuuu kaman iska se yaushe ne mahaifiyarsu zatayi hankali ta dena biyewa rud'in shedan akan Amah da bata ta'ba nufanta da sharri ba? Matar da tunda ta shigo gidan take girmamata a matsayin Yawuro(matar babban d'a ita ake cewa yawuro) sede ita Hajiya Yaya ta d'auki karan tsana ta d'aura mata fitinar yau daban na gobe daban, d'akin Aisha ta shige ta fad'a saman gado tana sakin kuka..
****
"Ban amince ba..."
Kai tsaye hajiya Babba ta amsa tana kallon Abbu da ya sadda kai yana fad'amata batun Amatullah...
Ta d'aura da
"Kai kam se na tashi tsaye kanka akan kokarin da nake in ba haka ba se Saude ta zamar da kai marar wayau da hankali, fisabilillahi ina aka ta'ba yin haka? Yanzu yadda duniya take ba'a kwancen nan ba tuzurun d'anka ya jaji'bo mana abinda ba shine ba? Wa ma ya sani ko dadiron shi c...."
A razane ya d'ago yana kallon mahaifiyar tashi dake shirin kiran d'anshi mazinaci ranshi na sosuwa, Amah da ta sanyo kai ta furta auzubillah wa iyazubillah,ubangijin talikai ka kare min yaro ka rabashi da duk wani kaidi na mutum da aljan... bata san a fili tayi maganar ba seda taga Abbu na kallonta gabad'aya ranshi a jagule a fuskanshi kad'ai zaka fahimci irin yadda ranshi yayi mugun'baci, tsaye hajiya Babba ta so yi sede kafa ya ki a haka ta fara salati tare da sanya kuka wai yau ita saude ke cewa shed'aniya a gaban d'anta ba matakin da ze iya d'auka wannan wani irin farraku ne...
Amah na shirin magana Abbu yace
"Je ki..."
Girgiza kai tayi a rud'e tace
"Kar ka min mummunar fahimta akan....."
A dake yace
"I said leave..!"
Fita tayi hawaye na silalo mata, itakam yaushe ne zata huta da fitinar gidan nan, tunda ya aureta kusan shekara arba'in da uku bata ta'ba hutawa da fitinar mutane biyun nan ba... karar wayanta ne yasa ta share hawayen fuskanta tare da picking ba tare da ta kalli wa ke kira ba tayi sallama
"Amah idan baki fad'awa Abb...." chakk ya tsaya da abinda yake son fad'i...
"Amah what is happening to you?"
Tambayar ta sakata jin zuciyarta ta karye ta tabbatar ta'batawa Muhammad rai sede d'a ya fi d'a ne ko kuwa uwa ta fi uwa ne? Wace uwa ce za'a jefi d'anta da wannan kalma ko da kuwa d'an d'in ba nagari bane tace bataji ba daad'i ba, Kuka ne ya so kwace mata karo da sukayi da Khalid yasa wayanta fad'uwa...
Da hanzari ya riketa ganin kaman kirjinta baya bugawa dae dae cikin sauri ya fiddo Ventolin dake ajihunshi wadda dama nemanta yake ya bata ya fara shaka mata, Yana cewa
"Innalillahi Amah, Amah me ya faru?"
Abrar da ya fara sauri be san ya had'a da gudu ba seda ya tsinci kanshi a mota cikin wani mummunan speed ya ja motar yana datse lip d'inshi na kasa idanunshi na sauya kala...
Kuuuuuuuuu karar da ya karad'e ilahirin wurin kenan kan......
****
*Ko kin shirya mallakar Wad'annan TAURARI Guda biyu😉 Da Naira Dari biyar kachal zaki mallaki gawurtattun littatafan nan guda biyu...
*GAMON JINI Na Fatima Muhammad Gureen (Gureenjo)*
*Da Kuma*
*SABABI Na Amina Ibrahim (Oum Ameer)*
*Akan Naira D'ari uku kuma zaki mallaki Guda d'aya cikin biyun, karku manta mun shirya tsab domin Nishad'antar daku, fad'akar daku da kuma Nishad'antar da ku masoya, Mallaki naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali er uwa👌*
Zaku iya biya ta account number kamar haka
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
Se a turo shedar biya ta wannan layin
***
Note: Banda Recharge card.
🖤Gureenjoh🖤