Free chapter 路 Read without an account
LIKE, COMMENT AND SHARE
by UMAIMAH ADO GAYA 路 KUKAN KURCIYA masu iya magana suka ce jawabi ne, kuma gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah, labari ne da ke 茩unshe da gwagwarmaya, soyayya, cin amana, rudin she蓷an da dai sauran su , ku dai ku biyo ni umaimah ado gaya don jin me ya 茩unsa?
KUKAN KURCIYA
BY OUM AHMAD
UMAIMAH ADO GAYA
( MRS.NAZEE)
page 08
KARKASHIN JAGORANCIN
馃挭馃摎馃摎
*TASKIRA WRITER'S ASSOCIATION*
{T.W.A}
****
_Marubuta masu aiki da zallar fasaha da hikima rubutu baiwa ce ga wanda Allah ya bawa ita. da hikimar mu muke Alfahari_
*A茩alaminmu 拼ancinmu馃挭*
bismillahirrahmanirrahim
Shiru Ammi tai tana bin su da kallo bayan ta gama sauraren khadija da ta samu kwarin gwiwar gaya mata binda ya faru dan ita nafeesat ba abinda take har lokacin sai kuka,
Nisaw Ammi tai cikin muryar karaya ta fara fadin "Yanzu kuna nufin mutunci da daraja da tarbiyyar da nai tsawan shekaru ina ginawa ce wani can ya wargaza a cikin mintuna kalilan?
Yanzu ke nafeesat duk tattali da kare martabar ki da nai ta kokari dare da rana kika bari rudin duniya da shedan ya sanya kika zubar?
Ko kunsan cewar duk daren duniya bana iya barci cikin kwanciyar hankali saboda fargaba da tunanin ganin na aurar da ku na kai ku gidan mazajen ku cikin mutunci da daraja?
Kin bani mamaki nafeesat kuma kin bani kunya, nan ni da mahaifin ku da yayyin ku muka zaunar daku ke da yan uwanki mataa muka sanar daku duk wadda tasan tana bukatar aure ta sanar da mu ko ta tsaida mijin aure, lmrah da aisah suka gabatar da mazajen aure su da suke kannen bayan ku amma ku kuka zabi karatu ke da khadija shine yanzu zaki biyewa saurayi ku gama lalacewar ku a titi har ya fasa auren ki sannan yanzu rana atsaka ki sanar dani cewar ya miki fya蓷e bayan na kama na kama ki ciki sannan gani malohuwa na yarda?"
Kara karfin kukan ta nafeesat tai tare da rike kafafun Ammi cikin gunjin kuka take fadin "kiyi hakuri Ammi na tuba nabi Allah na biki, amma wallahi ban taba sakaci da tarbiyyar ki gare ni ba wallahi amma bada san raina hakan ya faru ba,"
Fincike kafarta Ammi tai da hanzari cikin tsananin fushi ta furta " ki tashi ki ban guri nafeesat!" Kara yunkurin riko kafar Ammi ta sake yi cikin gigita da tashin hankali take fadin " ki yi hakuri ammi amma bazan iya jure fushin ki ba , nasan wannan yana daga cikin kaddarata kuma idan nai hakuri na jure komai zai wuce amma idan na bari kikai fishi da ni wannan kam ganganci ne kuma na tabbata rayuwata lalacewa zatai,
Cikin kuka itama khadija ta riko ammi tana bata hakuri kamar dai yadda mafeesat ke yi, sun kai ruwa rana sosai kafin ammi ta sauko ta hakura, sai dai cikin zuciyarta ta tsinewa akram yafi cikin carbi,
Mikewa tai ba tare da tace dasu kala ba ta shige daki, kai da kawowa kawai take don ta rasa ta hanyar da zata sanar da Abba, don shi mutum ne mai matukar tsauri akan yaransa, kullum idan ka zauna dashi bashi da magana face ta Allah ya sa ya aurar da y'ayan sa cikin mutunci don yace da albishir dinda manzo ( s.a.w) yaiwa masu y'aya mata,
Abin haushin ma shine har da guzurin ciki "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un," ta furta tare da zama bakin gado tana dafe kai,
Bangaren nafeesat kam da kyar khadija ta lallashe ta suka shiga daki don yanzu ba maganar zuwa wani asibiti,
Kamar wasa daga bayyanar ciki sai laulayi ya sako nafeesat a gaba, wani irin laulayi mai tsanani, don ko abinda take farawa dashi da safe shine mugun amai kmar yan hanjin ta zasu fito kafin kuma kace me? Zazzabi mai zafi zai rufe ta, ba zai sauka ba sai azahar kuma sai lokacin zata samu ta danci wani abun tai sallah sannan ta kwanta ba zata farka ba sai la'asar shima da wani aman sai dai ba zazzabi idan tai sallah sai kuma a nemo mata ruwan zartsi shi zata karasa yinin baci na sha sai na ruwan zartsi,
Lokaci 蓷aya tabi ta rame ta dawo 茩ashi d rai sai wani uban 蓷ashewa da tai , sosai Ammi da khadija suke kula d ita don ita kanta ammi tausayin ta take ganin irin wahalar da take sha ,
Abba kam ya baiwa kowa mamaki don bayan dawowar shi daga tafiyar da yai ya tarar da halin da ake ciki da 茩yar Ammi ta iya sanar masa, amma ga mamakinta cewa yai kawai Allah ya kyauta kuma ko daga baya bai kara tada maganar ba, hasalima d kansa ya dauke ta y kaita asibiti, inda liktan yai ta fadan rashin kawo ta akan lokaci,
Ga jinin ta ya hau, ga ba ruwa a jikinta haka nan ba ishasshen jini a jikinta, shi dai abba hakuri kawai ya bada, nan take akai emergency da ita aka fara bata taimakon gaggawa, sai da tai sati sannan aka sallame ta da tarin dokoki,
Gaba daya gidan har yayyin su maza abba ya kira meeting , sai da kowa ya hallara sannan ya sanar da yayyin ta abinda ake ciki kasancewar basu sani ba sannan ya dora da fadin duk wanda yai mata koda kallan banza ne shi da su saboda ko cikin 拼a拼an sa nafeesat ta dabance a cikin su , ya tabbata tana sane baza ta rushe rayuwar ta a lokaci guda ba,
Sosai yai musu nasiha da jan hankali kana itama nafeesat yai mata nata , hakan yasa tundaga ranar ake rigerigen faranta mata, sam bazaka ganta ita kadai ba in har ba bacci take ba, yayyin ta kam idan zasu dawo daga aiki sun ringa kira suna jin me take so me za'a kawo mata haka ma abba, a haka har ta shiga watan haihuwa,
Kasancewar duk dangi da yan uwa sun san ammi na da ciki kamar yadda suka fada ya sanya basu da fargaba kuma da yake idan akai baki wuni take a dagi har sai an tafi haka idan na kwana ne hakan yasa ba wanda yasan abinda ke faruwa,
Cikin ikon Allah nafeesat ta haifo yaranta twins mace da namiji masu tsananin kama da ita sai dan abinda ba'a rasa ba a ranar kam ammi,abba, nafeesat da khadija sun sha kuka ba tare da dayan su yasan wani yayi ba sai nafeesat ce kowa yaga nata,
Kasancewar lafiya ta sauka ya sanya tana haifar su aka gyara su , a take ammi ta sanya likita yai mata allurar da ruwan nono zai zo dan acewar ta ita zata shayar dasu,
Sosai twins sukai farin jini don duk wanda ya gansu sai yaji kaunar su haka nan duk wanda ya gansu sai yace wannan ai nafeesat kika haifawa yaran nan don kamar su daya yanzu da tai aure ai cewa za'ai na tane, wasu ma cewa suke ai wannan idan nafeesat ta fita dasu cewa za'ai yaranta ne,su dai kawai sai dai su yi murmushi a haka har akai suna kowa ya watse,
After one year,
Sai da nafeesat tai shekara guda a gida sannan aka samar mata admission a buk ta fara karantar medicine kafin daga karshe babban yayan su dake aiki a london ya dauke ta ta koma can da karatun har ta kammala ta dora da gynaecologist, sai da ta zama consultant sannan ta fara aiki a can kafin su tattaro su dawo nigeria gaba daya wanda dawowarta ya dawo mata da tsohon miki, wannan kenan
Back to story