Free chapter · Read without an account
KUSANCI PAGE 10
KUSANCI
NA
HAJ HABIBA ABUBAKAR IMAM
(Mrs Aliyu mayere)
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
..........page 10
Sajeeda bata wani bata lokaci ba, wajen wanka da shiryawa. Daga bisani ta fito da sauri zuciyarta cike da addu'ar Allah yasa Bakil bai riga ya tafi ba, hakan yasa ba ta fara zuwa sasan mahaifanta ba, sai ta wuce sasan Dada domin tasan bazai wuce dakin Dada ba, don tasan nan kadai ne zai iya zama ya bata lokaci.
Duk uban saurin da take yi ƙafa na hadewa, tana kusa shiga dakin Dada sai kawai ta rage sauri, ta shiga tafiya a hankali cikin yanga, ta shiga falon tana sallama.
Dada ta amsa lokaci daya ta na kallonta, ita kuma tana waige waige a falon da addu'ar ganin Bakil, cikin rashin karfin guiwa ta zauna akan kujera, Dada ta kara dubanta tace, "sajeeda me yasa ke kin cika sa abu a rai ne , ba ki da sauki, ga mitar abu da rashin hakuri, wannan halin baki tun kina yarinya shine yake wahalar da ke, yanzu ma kuma idan kika yi wasa shine zai hanaki zaman lafiya a gidan mijinki", sajeeda ta ɗan turo baki tace "To ni yanzu kuma Dada me nayi, aure ne Kun riga Kun mara masa baya ya yi, tunda kun fi son sa da kowa, to ba shikenan ba".
Ta sakar mata harara tace "Me ki kayi?, Don meye yasa baki bi mijinki kun koma ba, zaman me zaki cigaba da yi anan, kuma da kike maganar mun goya masa ba, umarnin Allah ne zamu hana shi yi , mu din banza dole yadda yake son ya kara aure mu amince masa, kamar yadda mu ma ya amince mana wajen yarda da aurenki ". Sajeeda ta dubeta a gaggauce tace "Don ku ya aure ni dama ba don yana so na ba?", Da sauri Dada ta juya maganar, tace "komai son da muke ya aure ki idan baya sonki ya za'ayi ya aure ki," za tayi magana ta daga mata hannu "kin gani sajeeda ki bar maganar nan kawai, tunda dai Bakil ya riga ya riga ya tafi sai kiyi ta zama , ki jira har zuwa ranar da zai dawo, ke kika sani". Gaban sajeeda ya fadi har cikin ranta ba ta so ya tafi ya barta ba, ta so ta bi shi, duk da dai ita tayi ma kanta gashi nan kilu ya ja bau.
Ta tashi kamar wacce kwai ya fashewa a ciki ta fice ba tare da ta kara magana ba. Hankali tashe ta shiga falon Haj Aseeya ta zube akan kujera tana aikin kuka, Haj Aseeya ta fito da sauri daga uwar daki ta zauna daf da sajeeda tana tambayar ta cike da tashin hankali, "Menene ? Meya faru kike wannan kukan?, Ina Bakil ɗin". Ta dago kai hawaye sharkaf a fuskarta tace "yaya Bakil ya tafi Umma", da karfi tace "Ya tafi ya barki?", Tace "eh", nan ta shiga fada "Don me zai tafi ya barki , me yake nufi, nifa bazan dauki wannan wulakancin ba, babu yadda za'a yi na yarda a dinga wulakanta min ya", sajeeda ta ɗan tsagaita da kuka tace "yace na zo mu tafi, don nace bazani ba, shine yaƙi lallashina kawai ya yi tafiyarsa ya barni". Haj Aseeya ta tsaya tana kallonta galala kamar ta na mamakinta tace "Don me tun farko baki amince ki bishi ba, kinsan Allah sajeeda idan baki natsu ba zaki zo kiyi danasani, kinsan dai Bakil shine rufin asirinki kuma rufin asirin mu, wannan yaƙin babu wata riba da zaki ci idan aka cigaba da tafiya a haka ".
Sajeeda ta tashi ta zauna sosai ta tsaida hawayenta ta zuba ma Haj Aseeya idanu, ganin ta tattara nutsuwarta a wajenta yasa ta cigaba da cewa " Duk gidan nan babu wanda zai goya mana baya Bakil ya fasa kara auren nan, Haj Hadeeza ce kawai nake tunani, itama a yanzu na fahimci babu abinda zata iya yi mana tunda mijinta bazai goya mata bayan yin hakan ba, saboda haka komai a yanzu ya rage namu, shi kuma yaƙi ɗan zamba ne, don haka dole ki natsu kisan abinda kike ciki, tunda dai na yi Miki alkawarin ba ki ba zama da kishiya to ki sa min ido kawai, don na gaya Miki yadda ban zauna da kishiya ba kema ba zaki zauna da kishiya ba, kuma kamar yadda yayarki Hindatu taki zama da kishiya haka kema". Wata irin nutsuwa ta cigaba da shiga jikin sajeeda, son mahaifiyarta da kaunarta ya kara kama zuciyarta.
Ta kara Matso ta sosai tace " Ke kadaice nake samun kwanciyar hankali a wajen ki, Nagode umma, tabbas idan kika yi min wannan kin gama min komai, domin bana son wata ta shiga tsakanina da yaya Bakil ". Tace "ki kwantar da hankalinki, komai zai tafi yadda muke so.......?.
Sallamar Haj Hadeeza ya katse musu maganar da suke yi, duk kansu su kayi shuru, ayayinda Haj Aseeya ta shiga fara'a tana faɗin, " yanzu fa nake cewa bari na tashi na shiga sasanki, ta lalubi kujera ta zauna tana cewa "Ai gani na riga ki ", sajeeda ta yi saurin sakkowa daga kan kujera ta gaida Haj Hadeeza, cike da so da kulawa ta amsa, lokaci daya tace "sajeeda, ban jidadin yadda kika ƙi bin mijinki ba, saboda bana son ki ba wata damar kwace Miki miji, hakuri zakiyi don ni kaina bana son auren nan, na kuma gaya masa bana so , ba ni kuma da wata suruka bayan ke", Haj Aseeya ta amshe "Abinda nake ta gaya mata kenan, babu yadda za muyi tunda abinda Bakil yake so ne dole mu so", tana maganar ne cike da munafurci da kissa, Haj Hadeeza ta tabe baki tace "komai son abinda yake so ɗin ni bazan so ta ba, har abada ina kuma addu'ar Allah yasa komai ya watse tun kafin akai ga yin auren, don babu hannuna aciki", Haj Aseeya cikin gwanewa a iya waje da kisisina tace "A'a Haj ki daina fadan haka, dama dai ke kadaice zaki iya hana faruwar hakan, amma tunda naga har an kawo wannan gabar ba kiyi komai ba, nasan kema abin yafi karfinki ne, shi yasa nace mata ta yi hakuri kawai ta rungumi ƙaddara tunda dama dai kece gatanta ", nan da nan kan Haj Hadeeza ya kara girma ta ji wani girman kai yana kara shigarta, cewar itace gatan sajeeda ba karamin dad'i ta ji ba, itama Haj Aseeya tasan hakan take son ji shi yasa take amfani da irin wadannan kalaman tana kara saye zuciyar ta da su.
Haj Hadeeza ta ɗora hannunta a saman kan sajeeda tace"sanin hakan yasa bazan taba barin a zalunceki ba , ko Bakil ne bai isa ya zalunce ki ba balle wata, saboda haka ki kwantar da hankalinki ko Kinga banyi nasarar hana wannan auren ba, to yarinyar ba zata taba samun jindadin zama da dana ba, don zan tsaneta fiye da komai har sai tayi nadamar auren ɗana". Dadi ya kara lullube sajeeda ta dago tace "Nagode Mama Allah ya saka da alheri", ta girgiza kai tace "kada ki damu sajeeda a tsaye nake akan matsalar ki sai inda karfina ya kare". Haj Aseeya tace "Nagode da irin kaunar da kike nuna ma sajeeda Nagode".
Tace " sajeeda ai yata ce, ko ba Bakil take aure ba, na rantse Miki sai inda karfina ya kare akan lamarinta, balle da na take aure, don haka bazan taɓa yarda a tauye ta ba". Sajeeda ta kara marairaicewa , ita ma Haj Aseeya sai kara girmama Haj Hadeeza take yi tare da nuna tana da muhimmanci a rayuwar sajeeda, hakan ya ƙara ma Haj Hadeeza tsanar jawaheer gami da tsanar aurenta.
Ta kuma tabbatar ma da sajeeda duk ranar da take son komawa dakin mijinta to ta gaya mata, zata kira Bakil tasa ya zo ya dauke ta. Bayan ta gama lallashin sajeeda ta tattara ta koma sasanta.
Haj Aseeya ta dubi sajeeda cikin murmushi tace " kin gani ko, in dai Haj Hadeeza tana bayanki baki da wata matsala, tunda Bakil ya na gudun bacin ranta", a karo na farko ta ɗan yi murmushi tace "Umma na gani , na kuma jidadin maganar da tayi sosai , a karo na farko kuma kenan da naji na fara samun nutsuwa". Haj Aseeya ta gyara zamanta tace "hmmm muje dai zuwa, ina da kuduri me yawa a cikin aurenki da Bakil kuma ina da yakinin zan samu cikar burina". Sajeeda ta dubeta sosai tace "umma wane irin kuduri gareki?", Dariya kawai tayi me cike da alamun mugunta da wani boyayyen mugun abu acikin ranta, sannan tace "zaki sani amma ba yanzu ba", ta gyada kai tana cigaba da kallon mahaifiyarta, Haj Aseeya tace "yanzu dai abinda nake so ki kwantar da hankalinki, kinsan gidan nan cike yake da yan bakin ciki da hassada irin su Bintu da Naja, waɗan da basu da buri a duniya da ya wuce su ga kin samu matsala da Bakil ko don su kya yi hakuri kada su ga kasawar ki su yi dariya, duk da nasan ko yanzu suna can suna yin dariya don Bakil zai yi Miki kishiya". Sajeeda ta yamutsa fuska tace "Ta Allah ba tasu ba, murnar banza su ke yi tun da dai ko da zai min kishiyar ba korata ya yi ba, ni naga damar tahowa gida", Haj Aseeya tace "Ai ba zasu gane hakan ba, yanzu karya da gaskiya su zaki ji acikin bakinsu".
Shigowar Alh saluhu Malami yasa duk sukayi shuru. Ko zama baiyi ba ya dubi sajeeda rai a bace yace "Don me baki bi Bakil kun tafi gida ba, ko kuwa kin zaɓi zama a gidan ne saboda sakarci da shirme irin naki", Haj Aseeya ta dube shi fuska a turbune tace "Duk meye nayin wannan lissafin, tana da yadda zatayi ne tunda shi ya zaɓi ya tafi ya barta, to me kuma zatayi ?". Ya girgiza kai yace "ki daina kokarin goya mata baya, domin ba Bakil bane yaƙi tafiya da ita , itace bata ga damar binsa ba, ai Dada ta sanar da ni komai", ta kara bata fuska tace "Eh, ai da yake dan gaban goshin ku ne, baya laifi don haka duk abinda ya fada da shi za kuyi aiki ". Juyawa ya yi ya kalli sajeeda sosai sannan yace "ke je kiyi tunani, ananne zaki gane babu wani rufin asiri a gareki da ya wuce ki zauna dakin mijinki, ina gaya Miki haka ne saboda nasan zafinki na kuma damu dake duk abinda ya sameki ni nasan ni ya samu, don haka ya rage ruwanki".
Bai kalli inda Haj Aseeya take ba bai kuma zauna ba, ya juya ya yi ficewarsa. Yana fita Haj Aseeya ta tabe baki tace "Abinda ya iya kenan, karayar arzikin sa ya haɗa masa harda karayar zuciya, bashi da tunanin komai sai tunanin da yan'uwansa suke so ya yi". Sajeeda ta gyara zamanta lokaci ɗaya suka cigaba da tattauna yadda zasu bulloma lamarin da ita da mahaifiyarta, wacce babu komai acikin zuciyarta sai tsatsa.
Shi kuwa Bakil tun komawarsa Kaduna, yake cikin farinciki ji yake kamar ya riga ya gama mallakar komai na rayuwa. Gidan su jawaheer ya tare da ya taso office nan yake wucewa ya je ya ci abinci ya koshi ya yi hira da jawaheer sai dare sannan yake yakicewa ya dawo gida. Kuma ko da wasa bai taɓa daga waya ya kira sajeeda ba balle ya ji halin da take ciki, itama kuma ta dake taki kiransa duk da abin ya na damunta.
Alh Nuraddeen canji ya sanar da Bakil cewa, magabatansa da zasu zo ranar Alhamis, su bari sai ranar asabar ko Lahadi shine yake gida. Hakan yasa Bakil ya kira Dada ya sanar da ita, ya kuma kira Alh Bello Malami ya sanar da shi.yana zaune a falon Haj Hadeeza suka yi wayar, yana aje wayar ta dube shi tace " Shi dai Bakil yana cikin jarabawa da wannan yarinya, zuwa nema masa auren ma sai anyi ta gutsuttsura magana, kawai suce ba zasu bashi yarinyar nan ba ai yafi da su dinga yin walagigi da shi", Alh Bello Malami ya juyo ya na kallonta yace "To bashi yace ya ji ya gani ba, don haka, haka zasu yi ta buga shi kamar kwallo, ni ban ma yarda da wai iyayen ta masu kuɗi ba ne kila ya dai faɗa ne saboda na daina zargin da nake yi, na cewa kudinsa kawai suke so su cigaba da ci bayan wanda suka ci a baya ". Haj Hadeeza ta tabe baki cikin rashin son faruwar auren tace "shi yasa auren nan sam bai kwanta min a rai ba hakanan bana son yarinyar duk da ba saninta nayi ba, idan kuma har tun lokacin da akace ya jira ta ya cigaba da hulda da ita ne to zuwa yanzu dai Allah kaɗai yasan irin arzikin da su kayi da shi, azzalumai kawai". Alh Bello Malami ya gyada kai gefe yace "Tunda ya matsa ya kuma dora ma kansa fitina, yana da sha'awar karama kansa wahala ai sai yaje ya yi ta kara auren, Allah ya kaimu ranar asabar din", ya mike ya nufi kofar fita ya na cewa "Bari naje wajen Dada muyi magana". Addu'a sosai Haj Hadeeza take yi a zuciyarta akan Allah kada ya tabbatar da auren Bakil da jawaheer.
Tun dawowar sajeeda gida, Anti Amarya ke matukar son ta shiga Maganar, duk da babu wanda ya sakata a cikin maganar sai mijinta Alh Bello Malami, shi ne ya sanar da ita dalilin dawowar sajeeda, da son kara auren da Bakil yake so ya yi, duk da ta fahimci Alh Bello Malami shima baya son kara auren nasa, wanda duk ba taga dalili ba, taso kwarai ta samu kebewa da Bakil suyi magana ta kuma bashi irin shawarar da zata ba dan cikinta, domin irin kallon da take ma Bakil kenan na dan da ta haifa. Domin har cikin zuciyarta tana yi ma Bakil irin son da take ma ƴaƴanta saboda shima tasan yana mutunta ta kamar mahaifiyarsa. Duk da tafi kowa sanin Haj Hadeeza bata son Bakil yana hulɗa da ita. Anti Amarya macece me sauƙin kai duk irin mugun zaman da matan gidan suke yi bata yi saboda tana da ilimin addini ga hakuri shi yasa kowa ke ci mata kashi aka.
Taso ta daure kada ta yi ma sajeeda magana kamar yadda Haj Bintu ta yi, domin ko da Anti Amarya ta gaya mata kudurinta na son yi ma sajeeda magana cewa tayi , duk abinda zai faru bakinta bazai taba budewa tayi magana ba balle harta ba da shawara, babu abinda ya dameta ko sakin sajeeda Bakil ya yi babu abinda zata ce da ya wuce Allah ya ƙara kwata kwata Anti Amarya bata jidadin maganar ba sai dai tasan ko zata yi mata nasiha ba zata saurare ta ba karshe ma su rabu baram baram. Don haka ta kyale ta, sai dai ita ta sha alwashin yin magana ko da ba za'a saurareta ba , don tasan abinda yafi komai sauki Kenan.
Sajeeda tana kan kujera zaune kan cinyarta dan wajen Hindatu ne da take goyi Waleed sunan mahaifinsu yaci saluhu. Hindatu kuma na zaune hannun kujera yau tun safe ta ke gidan, duk da babu wanda ta damu da taje ta gaida, hatta sasan Dada bata je ba. Tunda ta zo babu maganar da suke sai na auren da Bakil zai kara. Har yanzu fuskarta tamke take mafadaciya ce bata barin sai ta kwana, babu wanda take ragama. Hakan yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa kwata kwata basa shiri da mafiyawan yan'uwanta na gidan musamman Bakil, domin shi yana da dabi"ar rashin son fada hakan yasa duk mutumin da yake da faɗa yake kiyayarsa.
Hindatu ta kara gyara zamanta cike da fushi tace "in Banda wulakanci kwananku nawa ne da auren, shekara huɗu kacal, saboda ya ga Allah ya buda masa ya na da arziki shine zai nuna Miki iyakarki, daɗin dai abun tun kafin ya zama abinda ya zama yanzu kika aure shi, ko lefe dai baiyi Miki ba, kuma kada ya manta kafin ya ƙera wannan gidan da kuke ciki, ai a gidan haya ya fara a jeki , wane dare ne jemage bai gani ba, ai ni dama nasan zaki sha wahalar wannan miskilallen mutumin,".
Haj Aseeya ta tabe baki, tace "hmmm, har yanzu babu wanda ya gane kalata acikin gidan nan , iya wannan shekarun da muka kwashe tare babu wanda yasan wace irin bak'ar zuciya nake da ita, babu wanda yasan abun da zan iya akan tsare mutumcin ya'ya na, na rantse muku babu wanda ya isa ya wulakanta min ku ko ya hanaku kwanciyar hankali ban dauki mummunan mataki akansa ba", ta kara mimmike kafafuwanta, idanunta da fuskarta suna tabbatar da abinda bakin ta yake faɗa, duka su sajeeda ido suka sa mata suna kallon bakuwar fuskar da basu taba ganinta da ita ba.
Ta cigaba da cewa "Na kyale kowa ne ya gama taka irin tasa rawar, kafin na taka kalar tawa........?.
Sallamar Anti Amarya yasa Haj Aseeya ta hadiye sauran maganar da bata karasa fitowa daga bakinta ba, ta amsa sallamar can cikinta, tana kuma tsareta da wani kallo.
Bata damu da ganin hakan ba , ta lalubi kujera ta zauna, cike da fara'a ta dubi Hindatu tace "Hindatu ashe kina gidan", Hindatu bata tanka ba balle fa ta samu arzikin gaisuwa, duk da haka ba tayi fushi ba ta kai hannu zata ɗauki Waleed, ya make kafada dama bai yarda da mutane. Ta janye hannunta tana cewa "Har yanzu baka da yarda ko, idan ka fara tafiya aika dinga yarda da mutane". Babu dai wanda ya tanka mata duk ido suka zuba mata.
Harta fara tunanin ta hakura da maganar da ta zo da ita kawai ta tashi ta tafi, "lafiya ko?" Haj Aseeya ta jefo mata tambaya.
Ta ɗan muskuta tace cikin taushin murya, "Lafiya lau, dama kan zaman sajeeda a gida ne?"
Nan fa duk suka kara sa mata ido, har ta so ta muzanta, Haj Aseeya tace "uhum me ya faru da zaman sajeeda a gidan "Anti Amarya tace "a'a ba wani abu bane, kawai dai naga rashin dacewar hakan ne, don Bakil yace zai kara aure babu dalilin da za'a ce sajeeda tabar dakinta ta dawo gida ba, wannan abin da zai yi babu wanda zai iya hana shi saboda wani kusanci don kuwa Allah ne da kansa ya ba shi damar yin hakan , cikin suratul nisa'i Allah ya yi bayanin komai ya kuma bashi damar kara aure matukar zaiyi adalci, don haka kamata yayi tayi hakuri ta rungumi wannan ƙaddarar..... ?.
Da sauri Haj Aseeya ta dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu duk idanunta sun canja.
Ku dakace ni
Daga taskar ✍️
Yar gidan imam.