Free chapter · Read without an account

SHAFI NA BIYAR

by Ummiaisha · FATY~ISLAM

©️2 WRITERS EMPIRE ✍🏻✍🏻




💜💜 *FATY~ISLAM*💜💜



   *_NA_*


*_UMMI A'ISHA_*




*5*




***Daddy ya jima bai dago daga sujjadar da yayi ba wanda har sai da mommy ta kagu kuma ta kagara domin kwata kwata daddy bai sanar mata da maganar Khalifa ba wannan karon shiru yayi ya boye bai bayyana mata ba,


Lokacin da ya ɗago ta jima da kosawa, fuskarshi sharkaf da hawaye ya rungumeta yana kewaya falon da ita cike da farin ciki,


"Yallabai.... Ka fada min me yake faruwa? Rabon da inganka cikin irin wannan farin cikin tun kafin Islam ta zama haka.... Dan Allah ka sanar dani abinda yake faruwa"


"Hajjaju na ki shirya tarbar sirikinki gobe wato wanda zai auri Islam, dama nayi shiru ne ban fada miki ba saboda na gaji da fada miki abin dadi daga bisani bacin rai ya maye gurbinsa amma insha Allah wannan karon farin cikin zaki tayi...."


"yallabai ya yarda zai aure ta a haka? Shin ka fada masa halin da take ciki?" 


"Zai aureta Hajjaju, amma ban fada masa halin da take ciki ba yanzu but insha Allah am very sure babu abinda zai faru saboda tamkar contract na bashi tunda biyansa zan rinka yi...."


Share hawayenta itama tayi ta kalle shi," duk da haka ya dace ya sani amma sannu a hankali zai sani din.... "


" hakane, amma idan sun zo gobe zan fada musu babu wani taro da za ayi ko biki, iya daurin aure kadai za ayi zuwa sati mai zuwa insha Allah, sannan zan kira lawyer na barrister Haisam wanda agabansa za ayi komai haka kuma zai tsara komai a yi shi arubuce ta yadda duk zamu saka hannu... "


" masha Allah hakan yayi, Allah ya tabbatar mana da alkhairi "


Murna, farin ciki da kuma zumudi su ne suka taru suka hana su mommy bacci ayau, gari yana wayewa aka tashi da shirye shiryen tarbar manyan baki wato sirikai, girke girke da soye soye gami da hade hade aka yiyyi saboda su aka gyara ko ina, kowa Kaga na gidan cikin farin ciki yake ba wai iya su daddy ba har da sauran ma'aikatan gidan kowa ka kalli fuskarsa zaka ga annashuwa da madarar farin ciki tana zuba,


Driver abba ya tura aka kwaso gaba daya yan gidansu Khalifa wanda suma suka shirya kowa ya kure adaka, katuwar jeep din da aka je daukarsu kadai abar kallo ce domin motar daddy ce ta shiga taro, tare da ashraf suka taho gaba ɗaya nan suka ga gida kamar villa dan tsananin girma da kuma tsaruwa, irin ganin tarbar da suka samu abin ya burge kowa dake cikinsu saboda babu kyama babu gani gani musamman ma mommy da ta rungume umma kamar dama sun san juna ko kuma irin kawar nan tata daɗaɗɗiya,


A falon daddy duk aka zazzauna aka ci aka sha akayi ƙwarya ƙwaryar liyafa kowa cikin farin ciki tun daga yan gidansu Khalifa har su mommy,


"amm... Am dama Khalifa ne yace wai zai iya ganin koda hotonta?" ashraf ya fada kansa a kasa yana shafa keya,


"why not? Me zai hana, ga hotonta nan ko ina" daddy ya fada yana nuna musu da hannu inda hotunanta ke ajiye manya manya, kowa sai da ya jinjinawa irin kyawun surar da Allah yayi wa Islam wanda tamkar ita tayi kanta dan tsananin kyawu kai ka rantse da Allah jinin larabawa ce ko indiyawa, gashinta baki sidik har gaban goshinta,


Khalifa ji yayi kamar yayi suman zaune dan tsananin shauki da zumudi, take hankalinsa ya bar jikinsa ya zamto baya iya gane komai, dan har papers din da barrister ya bashi ya karanta yayi signing bai iya karantawa ba duk da cewa barrister Haisam nata sake jaddada masa ya karanta a nutse a fahimci komai, ai kawai saka hannu yayi ba tare da ya fahimta dinba,


"Alhamdulillah.... Kamar yadda na fada tun farko, Khalifa tunda ka yarda zaka auri Islam to lokaci yayi da zan cika dukkan alkawarirrikan da na daukar maka, amma da farko nima ina son in tunatar da kai wani abu, ina mutukar son ƴata saboda ita kadai Allah ya bani sannan bana hada son ta da komai shiyasa ba zan lamunci cin zarafi ko cin mutuncin ƴata ba, abinda nake bukata daga gareka kadai shine ka kular min da ita, ka bata farin ciki da soyayya, zan tanadar muku duk wani abun bukata wanda zaku bukata haka kuma zan rinka baka albashi duk karshen wata saboda bana son kayi nesa da ita, Islam tana bukatar tsantsar kulawa da tarairaya tare da soyayya, idan Allah ya kai mu ranar Juma'a za a daura muku aure kuma nine zan biya sadaki, haka bama bukatar komai daga gareka, zan sa a gyara muku part guda daya daga cikin parts din dake gidan nan, anan zaku zauna, yanzu insha Allah zan baka wasu kudade wanda zaka siyi duk abinda kake bukata wurin fitar biki, nagode madalla Allah yayi maka albarka kuma ya sakawa aurenku albarka.... "


Kowa yaji dadin wadannan kalaman na daddy wanda yayi su cikin nutsuwa da mutuntawa haka kuma sai da ya bawa kowa dubu dari dari acikinsu banda Khalifa wanda shi dubu dari biyar ya saka masa a account yace yaje yayi shirye shiryen biki daga nan suka yi sallama kowa zuciyarsa fes. 


Washe gari mommy ta tafi Dubai dan hadowa Islam lefe da sauran kayan furnitures wanda za a saka mata, wani babban part guda daddy yasa a sake gyara musu inda zasu zauna ita da Khalifa idan anyi bikin, ai Islam tunda ta farga mommy bata leko dakinta ba take kuka tana kiran "mommy.... Mommy" 


Sai da daddy ya bata lokaci wurin rarrashinta sannan ta hakura amma motsi kadan zata ambaci mommy, kwanan mommyn biyu ta dawo nan aka shirya mata part din nan aka gyara ko ina aka zuba kayan alatu komai golden color, 2 bedrooms ne kitchen da store da dining a kasa sai babban falo yayinda bedrooms din kuma ke upstairs, komai dai yaji masha Allah. Su Khalifa kam suma suna can yanata shirye shirye yayi dinkuna hadaddu masu tsada haka kuma ya siyo kananan kaya da sabbin inner wears sai takalma da turaruka kasancewar yana son kamshi sosai,


Daga aski wurin ashraf ya wuce nan ya sameshi a dakinsa yana typing a system dinsa, kallonsa ashraf yayi yai murmushi saboda ganin yanda kan Khalifa da gemun sa suka sha gyara,


"kaifa jikinka rawa yake ko, zaka je ka saka yar mutane a daki daga kai sai ita..."


"ban sani ba, wai kai me yake damunka ne"


"ai halinka na sani, abune da dama nemansa kake ido rufe sai gashi ka samu"


"ni wallahi ma abin ne yake bani mamaki kamar a mafarki wai nine zanyi aure nida ko nan da shekaru uku ban kawowa kaina aure ba"


"ehh to abin ai na Allah ne, kana naka yana nasa"


"nasan kuma shine gaskiya ba, Allah yasa mu dace, bari na karasa gida"


"alright sai ka fito"


Koda yaje gida samun umma yayi da dan uwanta wanda su ne zasu yi masa wakilci tare da kanin mahaifinsu baba Lawan, bai iya zama a wurin ba ya mike bayan sun gaisa dan a zahiri kunya yake ji idan yaji ana maganar auren nan nasa duk da ya jima da isa auren dan ko kannensa ma babu wanda bai isa aure ba acikinsu bare shi.


Kamar yadda al'ada take an san kowacce amarya ana yi mata gyaran jiki da su kunshi da kitso ko gyaran kai amma banda Islam domin ita babu wanda ya samu a ciki ko guda daya ita kuma mommy abinda yasa bata damu da sai anyi mata su kunshin ba gudun kada ta damalmalashi take kawai dai an ware mata kayanta masu kyau masu tsada wanda zata saka ranar daurin auren, bin kowa take da kallo dan ta kasa gane me yake faruwa a gidan nasu bare har ta fahimci wai itace za a yi wa aure, ko ranar daurin auren tana kwance da ta jiyo kide kiden maroka haka ta bazamo a guje ta sauko ƙasa daidai lokacin sukuma su Khalifa sun dawo daga daurin aure yasha farar shaddarsa da farin takalmi sai agogon silver yayi kyau sosai, ai su mommy na hangota da hanzarinsu suka zo suka kamata ita da Ladidi suka nufi sama da ita mommy tana ce mata,


"kefa amarya ce, aurenki aka daura yanzu ga angonki nan yazo...."


"amarya? Mommy amarya? Ango?" ta fada a sanyaye,shiryata su mommy suka yi aka saka mata farin less aka yi mata daurin dan kwali tasha turare,


Su dai su Khalifa gaba daya kansu a daure yake su mommy sun tafi sun barsu da tunani kala kala, to me yake faruwa? Shine tambayar da kowannensu ke yi acikin zuciyarsa, musamman ma irin yadda suka ga su mommy sun kamata suna janta zuwa upstairs,


"anya kuwa lafiya?" inji ashraf,


"me ka gani?" Khalifa shima ya bukata,


"to ai naga kamar amaryar ne ta sauko a guje kuma an zo ana kamata zuwa sama"


"malam babu wani abu, kabar maganar nan"


Shiru dukkaninsu suka yi suka cigaba da zaman jira saboda ga mai daukar hoto nan zai daddaukesu. 


A hankali suke saukowa daga upstairs din su mommy suna rirrike da hannayenta tasha kyau har ta gaji sai dariya take ita kadai, suna zuwa tsakiyar falon kasa inda su Khalifa suke tasha kunu tana bin su da kallo daya bayan daya, tafiya tayi da gudu zata rungume ashraf Ladidi tayi gaggawar rikota tana nuna mata Khalifa,


"Kinga mijin naki.... Ba wannan bane"


Tsayawa tayi cak tana kallon Khalifa kamar yadda shima ya tsaya yana kallonta kwakwalwarshi tana bashi duk yadda akayi tabbas kam wannan ba ƙalau ba akwai damuwa to amma yanzu menene abin yi tunda kaddara ta riga fata an riga da an daura musu aure.......✍🏻





Ku shigo cikin daular mu domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku, 


MASARAUTA tare da alƙalamin FATYMA XARAH 


FATY ~ISLAM daga alƙalamin UMMI A'ISHA 



 Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira dubu ɗaya kacal, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no *** ko kuma recharge card na mtn ta wannan no *** da shaidar biya.




*_Ummi Shatu_*👌🏻

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol