Free chapter · Read without an account
SHAFI NA TAKWAS
by Ummiaisha · FATY~ISLAM
©️ 2 WRITERS EMPIRE✍🏻✍🏻
*💜💜FATY ~ISLAM*💜💜
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
*8*
***Kamar kada ya fita haka yaji amma sai ya daure ya rufe idonsa ya fita, Islam ya jiyo tana ta dukan kofar ɗakinta tana dariya, a hankali ya tura ƙofar ya shiga tsayawa tayi tana kallonsa,
"mijina..... Mijina....." ta fada tana kallonsa sai kuma yaga tayi diff tasha kunu,
"a'a..... Ba mijina bane.... A'a...." ta fada cikin ɗaga murya fuskarta a daure babu shiri ya ja da baya ya fita ya rufo mata ƙofar, komawa tayi kan gadonta ta zauna tana cijar lips,
"ba mijina bane.... Wannan ba mijina bane" a haka bacci ya sake dauketa,
Shi kuwa bedroom dinsa ya koma ya zauna ya dafe kansa yana tunani, wai wannan masifar shi kuwa me ya aikata da ta sauko masa? "ya Allah me nayi ka sauko min da wannan masifa? Wallahi nidai ban so kaddarata tazo da haka ba akan aure Yadda nake tsananin bukatar aure amma shine da ya tashi zuwa zai zo min ta wannan mummunar hanyar? Akan me? Kai innalillahi, ya Allah ka kawo min ɗauki " ba dan tsananin gajiyar da yake tare da ita ba tabbas da bazai iya bacci ba a daren yau amma da yake ɓarawo ne shine ya sace shi ba tare da ya sani ba.
Washe gari har Ladidi tazo ta kawo musu abinci bai fito ba dan baima tashi da wuri ba, sai dai ya jiyo motsin ta tana gyara musu gidan, lukus yayi ya cigaba da kwanciyarsa har 11 sai lokacin ya fita ya karya sannan ya fita dan zuwa gaida su daddy,
Iya mommy ya samu kasancewar shi daddy baya nan ya fita, cikin karramawa mommy ta tareshi suka gaisa sai nan nan take dashi kamar zata goyashi,
"ya Islam din?"
"lafiya lau take mommy" ya fada kansa a ƙasa"
"to ai sai ka tashi ka koma da wuri saboda gudun kada ta nemeka baka kusa, ka san masu irin matsalarsu ba a yin nesa dasu dole sai an kula..."
"hakane mommy, bari na koma"
Tashi yayi ya fita ya bar mommy cikin farin ciki, part din su ya koma yana jin shifa gaba daya an takura shi saboda zama wuri daya yafi komai takura a gareshi, kenan haka kullum zai yi ta zama a gida? Zuciyar shi ce ta bashi amsa da ehh mana haka zaka yita zama tunda aikinka kenan, yanzun ma a falo yayi zamansa ya kunna kallo. Shi kansa bai san tsawon lokacin da ya diba ba dan nan nayi sallar azahar da la'asar sannan anan Ladidi tazo ta sameshi,
Ita dai Ladidi kawai kallonsa take acikin ranta tana tambayar kanta to menene dalilin da yasa ya auri Islam idan har ba zai bata farin cikin da iyayen ta suke bukata ba? Ita dai tunda aka daura auren nan bata ga abinda ya canja ba koda yake ya kamata a kara bashi lokaci dan ta yuyu yanzu da akwai abinda ke damunsa, yanzu ko kulashi bata yi ba ta wuce upstairs wurin Islam wacce ke zaune tsakiyar gadonta ta jajjera pillows kusa da ita tana wasan aure,
"kawayena..... Kawayena.... Zaku ga mijina? Kuna son ku ganshi? Bari in nuna muku shi...." daidai lokacin Ladidi ta shiga cikin dakin kuma bata katse ta ba sai ma samun wuri da tayi ta zauna tana kallonta cike da tausayawa, duk da mommy tace mata ta koma da wuri dan akwai aikin da zata yi mata amma sai ta kasa tafiyar kawai ta zauna tana kallon Islam kuma tana sauraren shirmen da take ta faman yi ita kadai,
"idan mijina zai zo ko.... Wannan zan saka" ta fada tana nuna kayan jikinta,
Ajiyar zuciya Ladidi ta sauke ta kamata tana cewa "to zo ki sake shiryawa ta yadda mijin naki zai zo ya ganki cikin kwalliya"
"mijina zai zo da gaske?"
"ehh zai zo"
Da murna tabi Ladidin tayi wanka ta zo ta sake wasu kayan duk da taimakon Ladidin, sai da Ladidi ta gama yi mata komai sannan ta tafi kuma har lokacin Khalifa yana kwance cikin falon yana kallo.
Har tsawon sati biyu babu abinda ya canja haka kuma babu wani abu da yake da niyyar canjawa na dangane da halayyar Khalifa akan Islam, su biyu suke rayuwa amma Islam ko ganinsa bata yi, a washe garin ranar da suka cika sati biyun da aure Ladidi ta samu mommy acikin falonta tace,
"mommy dan Allah ina so kiyi min izini kuma ki bani dama domin in koma sashen su Islam da zama gaba ɗaya...." shiru mommy tayi tana dan nazarin maganganun nata kafin tace,
"to ai Ladidi sai nake ganin kamar zaman naki atare dasu zai takura musu amma ya kika gani?"
"mommy zamana bazai takura musu ba insha Allah, saboda kinga koda shi Khalifan bukatar fita ta kamashi zai iya fita yaje ya dawo tunda ina tare da ita"
"hakane Ladidi amma ni ina ganin ba sai kin koma ba, wannan zuwan ma da kike yi akai akai ya wadatar tunda yanzu tayi aure to ya dace kema ki huta da wasu wahalhalun nata"
"to shikenan mommy na fahimta kuma insha Allah zanyi yadda kika ce"
"amma yaya kike ganin zaman nasu? Kin fahimci wani abu? Kin san nifa babban burinmu a yanzu nida yallabai bai wuce muga islam na laulayi ba..."
"eh to gaskiya mommy ban fahimci komai ba tunda kin san wannan sirrinsu ne bazai bari na fahimta ba shi Khalifan"
"eh to hakane, ubangiji Allah ya tausaya mana dai ya cika mana burinmu ya basu zuri'a ɗayyaba"
"amin mommy.... Bari naje na kai musu abincin tunda komai ya kammala".
Sati biyun da Khalifa yayi cikin gidan jinsa yake kamar a daure duk da ahakanma ya samu ya fiffita kusan sau biyu zuwa gidansu acewarsa kayansa yake daukowa, tsakaninsa da ashraf kuwa fada ne suketa yinsa saboda wai tunda ashraf yazo sau ɗaya bai dawo ba wannan dalilin yasa ashraf din yau shirya yi masa zuwan bazata,
Yana bedroom dinsa ya gama shakar baccinsa ya tashi yayi wanka yasa kananan kaya yayi salla yana idarwa ashraf ya kirashi yace gashi nan, downstairs ya koma dan tarar ashraf din,
Lokacin da ashraf zai shigo islam taga shigowarsa saboda lokacin tana gaban window tana lekawa ganinsa ya bude kofa zai shigo ai da gudu ta nufi downstairs tana murna,
"mijina yazo.... Dama na fada muku mijina zai zo..."
Ashraf yana shigowa itama tana saukowa nan ta kwasa a guje ta nufeshi cikin murna tana cewa "Yehhhhhh mijina yazo... Mijina yazo yehhhhhhhhh" rukunkumeshi tayi daidai lokacin itama Ladidi ta shigo, cikin sauri Ladidi taje ta ajiye kayan hannunta tazo ta kamata tana kokarin rabata da jikin ashraf wadda shima kokarin da yake ta yi kenan,
"Kinga mijin naki nan..... Ba wannan bane.... Gashi nan" Ladidi ta fada tana janta har zuwa gaban Khalifa wadda yayi tsaye ƙyam yana kallon ikon Allah,ai Ladidi na kai ta inda Khalifa yake ta daure fuska ta zazzaro idanuwanta waje,
"a'a..... Ba zai yuyu ba, ba wannan bane" ta fada cikin karaji tare da shako wuyansa, da kyar ya kwaci kansa tare da taimakon Ladidi, janye ta Ladidi tayi zuwa upstairs cike da mamaki dan bata taba ganin islam din tayi haka ko wani abu makamancinsa ba,
Shi kam Khalifa diff yayi yana shafa wuyansa inda islam ta shake shi yana jin wani irin zugi akan fatarsa kuma cike da damuwa ya kalli ashraf yace,
"Kaga irinta ko? Ka dai gani da idonka, a haka ake so inje in kusanci wannan yarinyar dan Allah?"
"calm down mana abokina, to ya zaka yi? A hakan dai zaka daure kayi duk wata mai yuyuwa har asamu abinda ake so"
"lallai saitin kanka ya kwance... Ba shakka baka da hankali ashraf .... Wai kai zato kake zan raɓi yarinyar nan har ta illatani? Tab"
Shiru suka yi dukkaninsu ashraf bai bashi amsa ba saboda fitowar Ladidi wacce tazo ta wuce su ta fita, sai bayan fitar ta sannan Khalifa yaci gaba da mitar shakar da islam tayi masa, har dare suka kai tare da ashraf yana mai sake kwantar masa da hankali amma gaba daya Khalifa ba jinsa yake yi ba dan ko sauraronsa bama ya yi a haka suka rabu,
Daren ranar daddy ya kalli mommy wacce tasha ado ta ci kwalliya sosai cikin wani jan leshi wanda yasha adon duwatsu sai tashin kamshi take yace mata,
"wai ni Hajjaju yaushe rabonki da ƴarki islam?"
Dariyar farin ciki tayi wacce ke dauke da fara'a ta dube shi tace,
"yallabai.... Ai tun ranar da aka daura mata aure"
"to bakya kewarta ne?"
"Haba yallabai ai kaima kasan ko ban fada maka ba ina cike da kewar islam, kawai dai babu yadda zanyi ne"
"to in dai hakane ya kamata ki tashi yanzu muje mu ganta dan nima din cike nake da kewarta mai tarin yawa, muje mu taya su hira mu ci abinci tare dasu muyi hira da su haka kuma mu kara musu kwarin gwiwa hakan zai sa su ji dadi...."
"hakane yallabai, hakika naji dadin wannan magana taka, bari na zo muje" ta fada tana gyara masa zaman wuyan farar jallabiyar dake sanye a jikinsa,ciki ta koma ta dauko mayafi babba ta rufe jikinta sannan suka fito, kafin su tafi sai da ta umarci Ladidi da cewa ta kawo musu dinner dinsu sashen islam dan yau a can zasu yi, shuru Ladidi tayi bayan fitarsu aranta tana addu'ar Allah yasa karsu mommy su je su ga ba daidai ba dan tabbas idan irin abinda take gani suma zasu gani to ta san dole ransu zai baci sannan zuciyar su zata ji babu dadi,
Suna tafe suna hira tamkar wasu saurayi da budurwa a haka suka karasa part dinsu Khalifa wanda ke can cikin bedroom dinsa yana kallo yayinda itama islam din ke cikin nata bedroom din tana wasan aure, wai biki ake yi itace amarya kuma ga jariri nan shima nata ne,
Sam ko da wasa bai ji zuwansu daddy ba dan ya kulle ko ina sannan ya kure TV, su dinma a falo suka bawa kansu masauki suka zauna nan daddy ya kalli mommy yace,
"Ranki ya dade kar muyi rashin hankali fa... Amma bari na kirashi a waya" daddy ya fada tare da kiran no din Khalifa,
"Assalamu alaikum daddy barka da dare"
"yawwa barka dai Khalifa ya gida ya Islam?"
"daddy gata tana nan lafiya"
"to muna downstairs muna jiranku nida mommy mun kawo muku ziyara"
"to daddy bari mu zo"
Zumbur ya tashi ya fita ya shiga dakin islam wacce ke rungume da tarin pillows a jikinta, yana shigowa ta dago ta kalleshi ta kwashe da dariya tace,
"mijina......"
Shima murmushin dole ya kakalo ya nufi bakin gadon, ai yana zuwa ta daure fuska kamar ba itace ta gama dariya yanzu yanzun nan ba ta harareshi tare da daka masa tsawa,
"a'a.... A'a..... Fice..... Ka fice...." ta fada cikin karaji tare da fara jifansa da pillows babu shiri ya fita yana faman waiwayenta, to shi yanzu yaya zai yi? Me zai je ya fadawa su mommy tunda yasan sun zo ne domin su ganta, tsaye yayi nan cikin corridor ya kasa gaba ya kasa baya........ ✍🏻
Ku shigo cikin daular mu domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku,
MASARAUTA tare da alƙalamin FATYMA XARAH
FATY ~ISLAM daga alƙalamin UMMI A'ISHA
Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira dubu ɗaya kacal, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no *** ko kuma recharge card na mtn ta wannan no *** da shaidar biya.
_*Ummi Shatu*_👌🏻