Free chapter · Read without an account

SHAFI NA TARA

by Ummiaisha · FATY~ISLAM

©️ 2 WRITER'S EMPIRE ✍🏻✍🏻





   💜💜 *FATY ~ISLAM*💜💜




    *NA*


*UMMI A'ISHA*




*9*




***A hankali yaje ya lekata bayan ya tura ƙofar dakin nata, hangota yayi tana tattare pillows din da ta jefeshi dasu tana cewa,



"shhhhhh.... Ƙawayena kar ku yi kuka.... Yi hakuri.... Yi hakuri zan gyara komai...... To muje mu kwanta, dare yayi ko...." ta fada cikin alamar lallabawa tare da kwantar da su a gefenta tana murmushi duk yana kallonta, mintuna kadan yaga kamar tayi baccin gaske hakan yasa ya shiga cikin dakin gaba daya yana tafiya cikin sanɗa, leka fuskarta yayi nan yaga ai kuwa da gaske baccin tayi, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juya ya fita a hankali, ƙasa ya sauka inda su daddy ke zaune suna zaman jiransu shida mommy, cike da alamun jin kunya yaje ya tsugunna gabansu,


"daddy sannunku da zuwa.... Ina yininku"


"lafiya lau Khalifa, ya aka ji da kokari?" mommy ta bukata itama nata kan a ƙasa amma sai dai duk da haka tana kallonsa,


"lafiya lau"


"to ina ita uwar tawa? Naga ka sauko kai daya" daddy ya fada cikin fara'a,


"wallahi daddy bacci tayi, inata son mu sauko tare amma taki saboda baccin da yaketa rinjayar ta..."


"ikon Allah, wato har yanzu islam tana nan da wannan saurin baccin nata kenan.... To amma ta ci abinci ne?" mommy ta bukata bayan ta tsaida kallonta kan Khalifa,


"ehh to shine nima dama damuwar, amma ta ci dazu tare da Ladidi...."


"to shikenan in dai taci ai babu damuwa muma sai mu tashi mu koma, dama mun zo muku dinner ne to amma tunda ita har tayi bacci gara mu tafi..."


"hakane amma ni dai zan leka in ganta dan wallahi ina son ganinta yallabai...." mommy ta fada tare da mikewa tsaye, nan Khalifa ya wuce gaba mommy na biye da shi a baya amma shi daddy yana zaune inda yake bai tashi ba,


Har cikin dakin mommy tana biye da shi a baya, suna zuwa mommy ta ganta kwance kamar yadda ta saba," Allah sarki Islam ubangiji Allah ya shiga cikin lamarinki ya baki lafiya..." mommy ta fada cikin ranta tare da shafa kanta, buɗe idonta tayi ta kalli mommy a hankali ta furta "mommy.... Mommy"


"na'am Islam..."


"mommy kince ba zaki tafi ki barni ba...."


"Islam ban tafi na barki ba, koda yaushe ina nan tare dake.... Ba zan taba yin nisa dake ba...." idanuwanta ne suka sauka kan Khalifa wanda ke tsaye gefe guda yana kallon su, wani irin kukan kura tayi ta kai masa cafka mommy tayi saurin riketa cike da mamaki,


" fita.... Fita.... " ta fada cikin tsawa, juyawa yayi ya fita a ransa yana jan tsaki kafin daga bisani yayi magana acikin zuciyar sa, "gashi nan dai kun gani da idonku, amma da ahaka kuke ce min kuna so ta haihu, ta yaya?" downstairs ya koma wurin daddy wanda ke zaune kamar yadda suka tafi suka barshi sai dai yanzu waya yake yi da amininsa wato Alhajin Allah sannan cikin farin ciki da ɗoki yake sanar dashi yana gidan ƴarsa Islam yaje kai musu ziyara shi da Hajjaju, zama Khalifa yayi a kasa kan carpet yana sauraron tattaunawar daddy din da abokin sa wanda hakan ya sake bashi karin haske sosai kan soyayyar da su daddy din ke yima islam.


Bayan fitar Khalifa mommy rike dukka hannun islam tayi tana kallonta ranta a bace,


"islam menene haka? Yaushe kika fara duka ban sani ba? Ai ko kina duka to bai dace ki doki har mijin ki ba wadda ya rufa miki asiri ya taimaka miki ya aureki.... Ba a dukan miji kinji? Wannan mijinki ne ki so shi ki kaunace shi sannan ki bishi sau da ƙafa.... " mommy din ta fada hawaye na ciko idonta saboda ta san islam din bata da cikakken tunani bare hankalin da zata fahimci duk waɗannan bayanan da take yimata,


" yanzu ki kwanta ki yi baccinki kafin ya shigo.... "


Kwantar da ita mommy din tayi bayan ta taimaka mata ta sauya kayan jikinta zuwa wata farar doguwar rigar bacci, fita mommy tayi ta koma kasa inda su daddy ke hira domin ya gama wayar da yake yi yanzu kuma ya koma hira da Khalifa duk da har yanzu ba wai Khalifa din ya sake dashi bane,


"Yallabai zamu iya tafiya, amma Khalifa ina mai sake baka hakuri kan islam, dama sai anyi hakuri da ita saboda yadda kaga take a burkice sai hakuri fa, sannan sai ka kula da ita sosai saboda a koda yaushe akwai abinda tunaninta ke bata wanda ita kuma gani take yi kamar daidai ne, sai an hada da hakuri da kuma kulawa "


Sake sunkuyar da kai Khalifa yayi ya ce" babu komai mommy insha Allah babu wata matsala "


" Allah yayi albarka, Allah yayi albarka " daddy ya fada cikin farin ciki, duk da basu samu zama da islam ba anan suka yi dinner din tare da Khalifa kafin suka yi masa sallama suka tafi,


Bedroom din islam yaje ya buɗe a hankali bayan yayi shirin bacci nan ya ganta sanye da hadaddiyar rigar baccin da mommy ta saka mata ai take yaji wani abu yana fusgarsa mai kama da mayen ƙarfe wadda har yaji ya fara shawara da zuciyarsa akan yaje ko kar yaje, tuno irin shakar da tayi masa yayi nan take ya ja baya ya tsaya can nesa yana kallonta, duk wani tunani nasa ya tafi baya jin komai sai tsananin bukatarta, jiki a sabule ya fita daga cikin dakin saboda baya son ta tashi ko ta farka ta ganshi ta burkice,


Bathroom ya sake komawa ya sakarwa kansa ruwa kafin ya fito ya zauna zuciyarsa na ta radadi shi dai gaskiya ana daukar hakkinsa sosai ba kadan ba, yarinyar nan ita ba lafiyayayya ba amma an tashi an manna masa ita sannan sai a rinka tsokanarsa? Wannan abun da ake yi masa bai da maraba da tsokana, so yake ya kira ashraf amma yasan wani takaici da bakin cikin zai kara masa, da kyar yasa mu yayi bacci a wannan dare. Washe gari bai yi wa kowa sallama ba ya fita ya tafi gidansu dan yana son ya samu zama da umma haka kuma yana son ya dauko wasu daga cikin kayansa wanda bai taho dasu ba,


"umma ni dai albarkarki da yardarki kawai nake nema, idan har kin amince min zan samo matar aure in kara aure...."


"ikon Allah.... Khalifa wai kanka ɗaya kuwa? Ka kuwa san abinda kake fada?"


"umma wallahi ina sane, ba zan iya cigaba da zama da islam ita kadai ba gaskiya saboda da ita da babu kusan duk daya ne, ita ba hankali ba bare tunani ta yaya zan bari rayuwata ta kare a haka?"


"Khalifa.... Ka san me nake so da kai? Kabi komai a hankali kuma a sannu, komai Kaga ya faru da bawa to akwai hikimar hakan, gaggawa ba abu ne mai kyau ba, komai acikin sauki ake binsa sai ka ga an kai ga nasara, maganar kara aure gaskiya koda zaka kara tofa ba yanzu ba, suma wadannan mutanen ya dace muyi musu adalci, sannan ina son karka manta yarjejeniya kuka yi dasu zasu biya ka zaka auri ƴarsu dan haka ina so ka zama mai kiyaye alkawari "


Shiru yayi yana sauraren umma wadda gaba daya ya kasa gane inda ta dosa to ko itama ba zata amince masa ya kara auren ba? Suna gama tattaunawa ya bude dakinsa na da ya shiga yayi kwanciyar sa bayan yace mata bari ya debo kayansa amma shiru shuru bai fito ba, kyale shi tayi a ranta tana cewa yayi dai ya gama.


A hankali islam ke saukowa daga kan steps din upstairs tana kallon ko ina alamar bata gane gidanba, babu kowa a falon dan haka ta wuce hanyar dining area tana zuwa ta tsaya tana kallon yadda aka kawata wurin aka shiryashi, dariya tayi ita kadai tace,


"abinci? Oh bari in zo in dafawa kawayena abinci, kowa zai ci abinci" hanyar kitchen tabi ta shiga tana girgiza alamar murna, komai gashi nan a shirye sai dai babu abinda aka taba amfani dashi amma an ajiye komai a position dinsa, drawers din sama ta bude babu komai sai tukwane haka ma na kasa dan babu kayan abinci aciki gaba daya sai ko kayan tea sai coffee, ruwa ta zuba cikin tukunya ta dora ta kunna sucket nan aka yi rashin sa'a yana jone da electric stove take ya kama aiki, haka take ta yawonta acikin kitchen din tana surutu ita ɗaya har ruwan ya tafasa ya fara ƙonewa daga karshe ya kafe tukunyar ta fara kamawa nan hayaƙi ya soma tashi kamar an hada wutar kara,


Masu gadi ne suka hango part din su islam kamar ba ƙalau ba dan haka sune suka kai ɗauki kuma suka kashe komai bayan sun gama suka tafi da islam din part din mommy dan dai tari take tana numfashi sama sama,


Ran mommy idan yayi dubu ranar sai da ya ɓaci saboda jin abinda ya faru to shi Khalifa ina ya tafi yabarta har hakan ta faru? Me hakan yake nufi? To ko dai wannan yaron ba zai iya wannan aikin da suka bashi ba amma yayi kwance kwance ya karba? Mommy ba tace komai ba ta rike ƴarta domin ita tana son ta koma aya take,


Khalifa yana can gida bai san abinda yake faruwa ba dan yasamu ashraf suna ta shan hira bai sake waiwayar gida ba sai magrib, lokacin da ya koma tun a bakin gate ya fara samun labarin abinda ya faru domin masu tsaron gidan suna ta jajanta masa, part dinsu ya fara zuwa ya duba kitchen din nan ya ganshi yayi bakikkirin a takaice dai arziki aka auna ba dan haka ba da tuni yanzu wani labarin ake yi daban ba wannan ba, jiki a sanyaye ya fito ya shiga part din mommy, ita da Ladidi ya samu suna hada hadar haɗawa bakin da daddy zai yi anjima kayan motsa baki dan mommy da kanta take gyaran fruits tana yanyankasu yayin da ita kuma Ladidi ke dafa farfesun kayan ciki,


"barka da yamma mommy"


"barka kadai" ta fada fuskarta a daure,


"mommy ashe bayan na fita abinda ya faru kenan?"


Wani kallo mommy ta watsa masa kafin cikin fada ta fara cewa "duk abin da ya faru sakacinka ne, mu da yake ba muyi sakaci da duk wani abu da ya shafeta ba ai Kaga hakan bata taba faruwa ba, na fuskanci tun tafiya bata yi nisa ba kamar ba zaka iya sauke nauyin da ka dauka ba Khalifa, in banda haka ya za ayi ace ka fita kabar Islam ko ka shiga bedroom kayi kwanciyarka kabarta ita kadai tana sha'aninta alhali kasan irin lalurar dake tattare da ita, to gaskiya muyi ta a bayyane idan har ba zaka iya ba to babu lallai kuma babu dole, kofa a bude take amma babu dalilin da zamu daukoka mu baka yarmu mu rinka biyanka dan ka zauna da ita sannan ka lura da ita amma ka rinka wulakanta mana ita ba zai yuyu ba.... " kai daga ganin yadda mommy take magana ka san ranta a ɓace yake, sunkuyar da kansa yayi kafin yace,


" mommy kiyi hakuri wallahi nima fitar da nayi ba haka kawai bane, wasu kayana naje gida daukowa amma insha Allah hakan bazata sake faruwa ba "


" koma menene Khalifa ya dace ka san duk wata bukata tamu a wurinka sannan ka yi duk iya kokarinka wurin samar da abinda ya kamata, mu bama neman komai daga gareka face ka kula mana da ita ka nuna mata dukkanin soyayya that's all"


"kiyi hakuri mommy insha Allah zan yi yadda kika ce"


"to Allah ya yarda, Kaga ko mahaifinta ban sanarwa ba saboda na san ranshi zai ɓaci domin bai hada komai da son da yake yi wa islam ba dan haka sai ka kiyaye"


"insha Allah mommy"


Anan yayi sallar magriba da ishah sannan mommy tasa Ladidi ta sauko masa da islam suka nufi sashenshu ransa fal tunani iri iri......... ✍🏻






Ku shigo cikin daular mu domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku, 


MASARAUTA tare da alƙalamin FATYMA XARAH 


FATY ~ISLAM daga alƙalamin UMMI A'ISHA 



 Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira dubu ɗaya kacal, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no *** ko kuma recharge card na mtn ta wannan no *** da shaidar biya.




*_Ummi Shatu_*👌🏻

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.