Free chapter 路 Read without an account

Page 02

by Nanameera 路 IMARA

*IMARA 馃拫馃拫*



*漏 AMEENA I IBRAHIM*


*Nanameera 鉁嶏笍*




*Page 2*



"A'a Ameer dan Allah ka rufamin asiri wlh zuciyata zata iya tarwatsewa idan har ka cigaba da yimin irin wadannan abubuwa..." Cak maganar tata ta tsaya ganin hawaye na sintiri kan fuskarsa baki bu蓷e Imara tashiga kallonsa sai kuma tashiga girgiza kanta hawaye na bin kuncinta, Ameer bai sake cewa komai ba ya mi茩e tsaye yana ri茩e da sandarsa ya fice daga 蓷akin hannayenta biyu ta 蓷ora aka ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi wace irin masifa ce haka?. A hankali ta tashi daga kan gadon tana tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a jiki ta fice daga bedroom 蓷in nata, tafiya take tana le茩e-le茩e amma babu wanda taci karo dashi har ta 茩araso wajen swimming pool 蓷in haskene a wajen tamkar rana a hankali ta 茩arasa wajen kujerar daya saba zama saidai kuma babu shi babu alamunsa ba 茩aramin mamaki hakan ya bawa Imara ba above 5mins tana tsaye gaban kujerar kafin tabar wajen cikeda zulumi kai tsaye kuma bedroom 蓷insa ta nufa tana zuwa ta tura 茩ofar a hankali gabanta na fa蓷uwa saidai ga mamakinta nanma baya nan da alama ma kwata-kwata bai shigo 蓷akin ba, jingina tayi da jikin 茩ofar tana tunanin inda Maheer ya tafi da wannan tsohon daren ganin lokaci na shigewa yasa tabar 蓷akin ta koma nata kwanciya tayi ta lulla蓳a da duvet saidai bacci ya gagari idanunta tana nan kwance har ta jiyo kamilalliyar muryarsa yana kiran sallar farko hakan yasa kawai ta tashi ta shiga toilet dan 蓷auro alwala.






*6:45am*


A harabar fadar motarsa tayi parking ya fito yana sanye da wasu English wears ya 蓷ora p-cap akansa yana tafe ana gaisheshi wani ya amsa wani kuma ya 蓷aga musu hannu har ya shigo cikin fadar zaune ya sameta tana sanye da wata t-shirt milk colour sai wani mini skirt data sanya irin mai kama jikin nan tana operating system 蓷in dake gabanta kallo 蓷aya ya yi mata ya 蓷auke kai



"Barka Akii"



Sautin muryarta ta daki kunnensa lokacin da yake shirin hayewa sama 蓷an juyowa ya yi ya kalleta sai kuma ya saki fuskarsa ya ce" saukar yaushe Joda?" rufe system 蓷in tayi ta tashi tana tafiya cikin isa ta 茩araso gabansa a jikin handle 蓷in benen ta 蓷ora kanta tana kallonsa ta ce" jiya nazo nd kuma ban ganka ba sai yanzu fatan kana lpy" jinjina kansa ya yi ya ce" ina klao y mutanen Turkey 蓷in" murmushi tayi wanda ya fito da zallar kyanta ta ce" suna jiran ranar komawarka" samun kansa ya yi da yin dariya ya shafa kansa ya ce" yep lemme take shower zamu yi magana" okay ta ce sannan ya juya yabar wajen, da idanu Joda ta bisa har ya kammala hawa stairs 蓷in sannan tabar wajen tana zuwa ta 蓷auki system 蓷inta zata bar wajen



"Joda!"



Batareda ta juyo ba ta tsaya ya 茩araso inda take yana murmushi ya ce" ni Meyasa baki kulani" 蓷ago daradaran idanunta tayi ta watsa masa sai kuma ta ce"kana lpy" bata jira amsar dazai bata ba tabar wajen, kwafa Dameer ya yi ya zauna kan kujera ya yi crossing legs 蓷insa cikeda annashuwa yake fa蓷in



"Karki damu yarinya soon zanyi gyara komai zan tabbatar da cewa Udaid ta dawo 茩ar茩ashin ikona!".




Tura 茩ofar bedroom 蓷in ya yi ya hangota zaune kan stool tana 茩o茩arin gyara gashin kanta ta蓳e baki ya yi sannan 茩araso gabanta yana kallon fuskarta ta jikin mirror 蓷in gabanta ya ce"idan kin gama akwai kaya a bedroom an ajiye miki kije ki 蓷auka su zaki saka" yana fa蓷in hakan ya juya zai tafi



"Wait!"



Cak ya tsaya ya juyo yana kallonta ya ce"akwai wani abun ne?" Tasowa tayi tana kallonsa ta ce"inada kayan da zan saka anan beside ma kuma ina kaje da daddare banganka ba" wani banzan kallo Maheer ya watsa mata baice komai ba kuma ya yi ficewarsa. Da idanu Imara ta bishi sai kuma takoma ta cigaba da abinda take, fitowa tayi cikin wata doguwar riga milk colour ga gyara gashinta rabi ya sauka gadon bayanta rabi kuma yana ta gefen kafa蓷arta a main parlor na fadar tasamu duk family 蓷in kowa yana harkar gabansa cikin sanyin jiki ta 茩araso tana zuwa ta tsuguna gaban Shamma


"Barka da safiya"


Shafa kanta Shamma tayi tana murmushi ta ce"how was ur night?" kanta a 茩asa tana wasada fingers 蓷inta ta ce"Alhamdulillah" jinjina kai Shamma tayi sannan ta 蓷aga idanunta tana kallonsa sanye yake da wasu suit black colour gashin kansa ya sha gyara ya yi wani irin sihirtaccen kyau da hannu tayi masa alama da yazo ya 茩araso yana zuwa ya zauna gefenta ya 蓷ora kansa gefen kafa蓷arta tana sauke ajiyar zuciya shafa kansa tayi cikin taushin murya ta ce" Maheer what's wrong with you?" shiru ya yi bai ce komai ba sai ajiyar zuciya da yake saukewa a jere a jere, fitowa ya yi cikin hanzari yana gyara ma蓳allin hannunsa murmushi Immi tayi ta ce"magaji ka fito?" gya蓷a mata kai ya yi ya ce"Eh Immi zani Company ne, Sabahul khair Shamma" ya fa蓷a yana kallonta jinjina masa kai tayi fuskarta 蓷auke da murmushi kamar koda yaushe ta ce"ka tashi lpy Dameer?" "Alhamdulillah" ya bata amsa yana 茩o茩arin fita daga fadar, da idanu Immi ta bishi sai kuma ta tashi tabi bayansa.




*** Tsaye yake gaban motarsa hannayensa na蓷e cikin aljihu ya zuba mata ido yana kallonta, "baka jina ne Dameer?" 蓷an mirmushin gefen baki yayi sai kuma ya ce"nafa蓷a miki ki bar komai a hannuna Immi zan kula da komai amma sai kina neman dagulan lissafi" 蓷an juyawa tayi tana kallon ma'aikatan da suke ta kai komo a compound 蓷in sai kuma ta jawo gefen rigarsa tana kallonsa cikin ido ta ce"kai baka gane abinda nake nuna maka idan har bamuyi komai a yanzu ba zamu fa蓷a cikin danasani Udaid zata kwace daga hannunmu" hannunsa ya sanya ya hargitsa gashin kansa wanda yake a gyara sai kuma ya furzar da wani zazzafan numfashi ya ce"shikenan naji na kuma san abinda zanyi da fari dole mu janye wannan yarinyar dan ita ce babbar matsalarmu a halin yanzu" "nasani kuma ina goyan bayanka duk abinda zaka aikata dan ganin ka kwaci abinda yake mallakinka" jinjina mata kai ya yi sannan ya juya ya shige mota yayi mata key not too long ya bar fadar. Tunda ta shiga kitchen 蓷in take kai komo tama rasa abinda zatayi jingina tayi da jikin carbinet tana sanya 蓷an yatsanta 蓷aya a baki tana tsotsa kamar yanda tasaba, shigowa yayi yana kallonta bai ce mata komai ba ya kama hannunta suka bar kitchen 蓷in 蓷an ta蓳e baki Joda tayi tana gyara zaman Bluetooth 蓷in dake kunneta a hankali ta ajiye cup 蓷in hannunta ta fita, kai tsaye 蓷akinta tashiga tana zuwa ta zauna gefen royal bed 蓷inta ta jawo wayarta ta shiga danna wasu nambobi tana jin wayar ta fara ringing ta tashi ta shige toilet ta rufe 茩ofar



"Akwai bu茩atar ka dawo Al-Udaid Damisa abubuwa na gab da lalacewa a tanan Al-Udaid na bu茩atar magaji!" Joda ta fa蓷a cikin tsantsar nutsuwa da kwantar da murya shiru taji yayi kuma daman tanada tabbacin bazai magana ba tana ji ya katse kiran. Jingina tayi da jikin bango tana sauke ajiyar zuciya.






*** Kallonsa take da manyan idanunta wanda sukayi jajur dasu sun kumbura ganin yanda ta zuba masa idanu ya sanya ya matso kusada ita hannunsa ya sanya ya dungure mata kai tayi saurin dafe kanta hawaye na biyo kuncinta hannunsa ya sanya ya kama ha蓳arta yana kallon fuskarta ya ce"idan ina miki magana kina kafeni da idanu ranki zai dinga 蓳aci" turo baki tayi tana 茩o茩arin kwace fuskarta ta ce" daman akwai watarana wacce raina yake ba a 蓳ace ba a gidan nan?" Baki bu蓷e Maheer ke kallonta sai kuma ya yi kwafa ya janyo rigar dake ma茩ale jikin hanger ya wulla mata ya ce"yanzu ba sai anjima ba ki sanyata ki fito karki bari nadawo kiranki"



"Amma..." Maganar ta tsaya cak ganin ya rufo mata 茩ofar bathroom 蓷in wasu zazzafan hawaye suka fara sintiri kan fuskarta a hankali ta sulale a 茩asa gefen sink ta ha蓷e gwuiwarta tana rushewa da wani kuka mai cin rai kwata-kwata lamarin Maheer ya fara 蓷aga mata hankali nema yake ya tarwatsa zuciyarta kullum tunaninta 蓷aya wacece KATALINA? Meyasa Maheer ya za蓳i ya mayar da ita KATALINA?!.




Tana fitowa ta ganshi tsaye hannayensa zube cikin aljihu da alama waya yake hakan yasa taja ta tsaya a wajen saida ya kammala sannan ya kalleta ya 蓷an ta蓳e baki ya ce" ki saki jikinki ki daina wannan abun da kike ki sani ke yanzu matsayin Gimbiyar Udaid kike dole ki koyi komai kuma ki ganeshi kamar yanda nafa蓷a miki zan mayar dake Katalina to bazan sare ba har sai naga kin zama kamar tan saboda haka ki shirya!" Da idanu kawai Imara ke binsa sai kuma ta bu蓷e bakinta wanda takejin ya yi mata nauyi ta ce"dan Allah zan iya tambayarka abu guda 蓷aya?" yana kallon wani wajen daban ya ce"tambayi" "Meyasa ka aureni? Kuma wacece KATALINA?" Kallonta ya yi sai kuma ya yi murmushi ya ce" idan lokacin ki sani ya yi xaki sani" kafin tayi magana taga ya juya ya bar wajen hakan yasa ta bisa da kallo sai kuma ta juya da niyyar tafiya.



"So kike kisan wacece KATALINA?"


Cak! Imara ta tsaya tana tunanin muryar dan bata ta蓳a jin mai irinta cikin fadar ba cikin takunta na isa ta 茩araso gabanta tana sanye da riga da wando as usual ta raba gashinta gida biyu rabi ya zuba bayanta rabi kuma gefen kafa蓷arta da idanu Imara ta bita kallo irin na mamaki kyakkyawace irin ajin farko 蓷in nan tanada manyan idanu masu 蓷aukan hankali, cikin sanyin murya Imara ta ce"Eh inaso nasani inason sanin dalilin daya sanya Maheer ya aureni meyasa kuma yakeson mayar dani wata daban kuma..."



"Hyyyy what's wrong with you?, Kina ta magana baki gajiya I'm just asked u a single question amma kina neman fasamin kai da hayaniya kinsan matsayinki a gidan nan kuwa? kinsan me zama matar Maheer yake nufi? Stupid!" Da idanu Imara tashiga bin Joda har ta 蓳acewa ganinta


"Ko wace ita take yiwa mutane masifa ohho!" Imara ta fa蓷a tana yin gaba abinta.




*** Tunda ya shiga yake zagaye office 蓷in yana girgiza kai tamkar wani mahaukaci kallonsa Ahlan ya yi sai kuma ya ce" wannan fa duk ba mafita bace Dameer idan har kanason ganin ka kwaci Udaid dolene ka saita zuciyarka ka rage fushinka" kallonsa Dameer ya yi da idanunsa wanda suka sauya launi sai ya ce"me zanyi Ahlan? Akanme za'a dinga bawa Maheer abu ni ana banza dani? Maheer ya yimin abubuwa dayawa yasha hanani samun abu shiyasa this time around billah sai naga bayansa yanda ko babu ran Ameer ni ne Magaji!" Dafashi Ahlan ya yi ya ce"kayi komai abokina ka tsaya tsayin daka ka kwatarwa kanka yanci kaima 蓷an Ameer ne saboda haka kanada kowace dama tazama shugaban Udaid".




Shamma na zaune kan 蓷aya daga cikin kujerun dake zagaye da fadar ta 蓷ora 茩afa 蓷aya kan 蓷aya wanda ke nuni da irin tata isar fitowa Immi tayi tana kallonta kamar zata shige sai kuma ta ce"Barka da hutawa Shamma" jingina mata kai tayi ta ce" ykk?" Yanda ta bata amsa ba 茩aramin 茩ona mata rai ya yi ba amma kawai ta dake ta juya ta fice daga fadar ta蓳e baki Shamma tayi tana cigaba da kallonta, da gudu Joda ta fito tana zuwa ta zauna gefen Ameer tana dariya ta ce"Ameer dan Allah kalli kaga" kar蓳ar system 蓷in tata ya yi sai kuma ya kalleta ya yi murmushi ya ce"yanzu kinyi farin ciki?" gya蓷a masa kai tayi tana murmushinta mai kyau dafa kanta ya yi ya ce"Allah ya sanya albarka" "Ameen ya rabbi Shukran Ameer" jan kumatunta ya yi ya ce"haza wajib" tashi tayi ta shige ciki da idanu Shamma ta bita sai kuma ta girgiza kai shi kansa Ameer bai ji da蓷i yanda ta rasheta ba amma ya ya zai yi haka 茩addara ta za蓳ar musu.




Zaune take gefen swimming pool 蓷in ta zubawa ruwan idanu yanayin yana tuna mata da wasu shekaru da suka shu蓷e cikin rayuwarta lokuta wanda bazata manta dasu ba duk da batada wayo amma hakan bai hanata kasa tuna wani abu daga ciki ba duk da bata ganin fuskarsa amma tana jin bugun zuciyarta na sauyawa a duk Lokacin da taga surarsa. Tsugune take bakin Kogin tana 茩o茩arin 蓷iban ruwa tanajin sanda yazo ya tsaya a bayanta hakan yasa ta mi茩e tana kallon fuskarsa da take a rufe ta ce" yauma ka sake zuwa ko?, wai ya sunanka?" da idanu kawai taga yana binta hakan yasa ta tura baki gaba tana harararsa ta ce"wannan kaman kurma baya magana, kai kana jina? Yayane sunanka?" Shiru nan ma taji ya yi mata ta galla masa harara ta 蓷ora tulunta aka tashige ta gefensa saida tayi nisa sannan ta tsaya ita ka蓷ai take cewa" to kodai nayi masa turanci inaga baya jin Hausa" da wannan tunanin ta koma inda yake tsaye har sannan tana kallonsa ta ce" kai what's ur name? Kanajin turanci? Ni sunana Imara gurin granny na nazo wannan 茩auyen kai ya sunanka? ko kai bature ne? nima mama ta ce inada kyau kai kaga kyan?" Ganin har sannan bai ce mata komai ba kuma bai bu蓷e fuskarsa ba ya sanya ta ha蓷e rai tana 茩o茩arin fashewa da kuka ta sanya hannunta a baki cikeda shagwa蓳a take cewa"sai kai ta tsaiwa nonse kawai ni babu ruwana ma dakai aljani kawai".




"Keeee!"


A 蓷an firgice ta 蓷ago idanunta sai kuma ta sunkuyar da kanta "what are you thinking?" Girgiza masa kai tayi tana 茩o茩arin tashi tsaye cikin rawar murya ta ce"bab.bb.bakomai" ta蓳e baki ya yi ya ce"koma mene bai dameni ba kije Ameer na kiranki" dafe 茩irjinta tayi tana gwalalo ido ta ce" Ameer kuma ni?" Da mamaki yake kallonta ya ce"akwai matsala ne? ya ce kin masa laifi to kije yanzu ba sai anjima ba ki kuma shirya gobe zaki fara zuwa school karki manta da sunanki KATALINA!" Cikeda tsiwa ta ce" nifa wlh sunana IMARA!" ha蓳arta ya kama yana mata wani banzan kallo ya ce" ba ro茩onki nake ba idan har kinajin zaki iya to gobe idan kin fita daga Udaid kice sunanki IMARA a sannan zaki gane kuskurenki sannan zan nuna miki wane Maheer!" yana gama fa蓷in hakan ya juya ya bar wajen yana wuci. Dafe kanta tayi tana sakin kuka ta ce"nashiga ukuna Allah ka taimakeni bazan iya ba" tafa蓷a tana fashewa da wani sabon kukan.




*** Around 10pm tana tsaye jikin mirror tana gyara kanta ya turo kofar ya shigo batasan sanda ta saki comb 蓷in hannunta ba tana girgiza kanta a hankali yake tafe cikin nutsuwa ya 茩araso gabanta ja da baya tafara bakinta na rawa ta kasa magana


"Lolo narh"



Ameer ya furta cikin wani iriyar murya mai rauni gaba 蓷aya ya rame kamar bashi ba manya-manyan idanunsa sun janye ka蓷an kuma sun sauya launi daga farare zuwa ja damuwa tagama bayyana akan fuskarsa, tsayawa yayi ya zuba mata idanu yana kallonta 茩asa tayi da nata idanun wanda hawaye ya gama cikashi cikin sanyin murya take cewa" dan darajar Annabi Ameer kayi ha茩uri kabar wannan tunanin a cikin ranka wlh nasan shai蓷an ne kayi ya茩i dashi kamar yanda kake fa蓷a a masallaci ka taimaki rayuwata kada ka jefani halin da bazan iya ba ka taimaka Ameer" tafa蓷a tana ha蓷e hannayenta waje 蓷aya alamar ro茩o, numfasawa ya yi cikin taushin murya yake cewa"Lolo nafi kowa son na ganki cikin farin ciki nafi kowa damuwa dake a cikin fadar nan wlh nafi kowa sonki nine na dace dake ba Maheer ba ki taimaka ki fahimci Ameer 蓷inki zan shiga wani hali idan har kika cigaba da watsar da bu茩atata koda yaushe zuciyata zafi takemin inaji kamar zan mutu dan Allah Lolo ki taimaki Ameer" girgiza kanta tayi tana 茩unshe bakinta gudun kada kukanta ya fito ta ce" inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun Auzubillahi minna shai蓷anin rajeem astgfirullah ya Allah dan Allah Ameer kadaina fa蓷ar wannan maganar wlh zuciyata zata buga nashiga uku ni IMARA!" Shiru Ameer ya yi ya zuba mata ido yana kallon yanda take kuka kamar ranta zai fita above 5mins sannan ya yi murmushi yana kallonta ya ce"kina iya kirana da duk sunan da kikaso Lolo naji nine shai蓷ani amma inason ki sani bazan ta蓳a iya daina sonki ba IMARA koda kuwa a ce soyayyarki zatayi ajalina Ni Fahad ke nakeso kuma zan cigaba da sonki har zuwa 茩arshen numfashina a duniya nasan koda bana raye watarana zaki so ni" banda kuka babu abinda IMARA keyi gaba 蓷aya ta birkita kanta tashi ya yi yana dogara sandarsa ya yi waje daidai nan Maheer ya shigo 蓷akin da sauri ta juya masa baya ta goge hawayen fuskarta sannan ta juyo tana cigaba da taje kanta



"Lafiyarki?"


Girgiza masa kai tayi tana 茩o茩arin 蓳oye hawayen dake shirin sauka kan fuskarta 蓷aga kafa蓷arsa ya yi irin i don't care 蓷in nan ya ce" anyway ga kayana an kawo maki ki tabbata gobe kin shirya kamar yanda na nuna miki kafin ki fito" yana gama fa蓷in hakan ya bar 蓷akin da idanu Imara ta bishi zuciyarta na mata suya wane irin miji ne Maheer????.



Tana gama gyara kanta ta 蓷auki wata sleeping dress ma 蓷an kauri ta sanya a jikinta ta ha蓷e gashinta waje guda ta 蓷aure gudun kar ya dameta ta shafa turare sannan ta 蓷auki wata hula ta rufe gashin kanta, agogon gefenta ta kalla taga kusan 11pm hakan yasa kawai ta fice daga 蓷akin kai tsaye kuma apartment 蓷in Maheer ta nufa tana zuwa without knocking ta tura 茩ofar 蓷akin turus tayi tana kallonsu ganin yanda take zaune ta 蓷ora kanta akan cinyarsa tana masa hira sai dariya yake yana ganinta ya ha蓷e rai Joda ta mi茩e tsaye tana kallonta sai kuma ta ta蓳e baki ta kalleshi ta ce"saida safe Akii" mi茩ewa tsaye ya yi shima ya sumbaci goshinta ya ce"laylatan sa'eedan" murmushi tayi sannan ta ratsa ta gefen Imara ta fita, Maheer bai sake kallon inda take ba ya shige toilet jiki a sanyaye ta 茩arasa gefen gadon ta zauna lokaci 蓷aya hawaye ya kawo kan fuskarta. Kusan 30mins kafin ya fito sanye da bathrobe sai 蓷an 茩aramin towel yana goge gashin kansa tana kallonsa har ya kammala duk abinda yake ya shirya cikin pyjamas maroon colour wanda sukayi masa kyau cikin takunsa na isa ya 茩araso gefen gadon ya zauna yana kallonta ya ce" keeee!" 蓷ago idanunta tayi ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kanta tana wasada fingers 蓷inta. "Me kike anan?" Cikin sanyin jiki ta ce" ni tsoro nakeji bazan iya kwana ni ka蓷ai ba anan zan kwana" a fusace ya juyo yana kallonta ya ce".




*Nanameera#*

*Fashion gurl 馃グ#*

*IMARA 馃拫#*

*LOLO#*

*Writer 鉁嶏笍#*



Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.