Free chapter · Read without an account

46

by Kansa'u Bello · ALLON ƘADDARA

✨✨✨✨✨✨✨✨  

 _*ALLON ƘADDARA*_

        _*By*_

   *_OUM FATIMA_* 

_*(Hakimar D. A. W. A)*_

✨✨✨✨✨✨✨✨ 


     _*DASHEN🌲ALLAH*_ 

_*WRITER'S📚ASSOCIATION*_


            _*TEAM*_

_*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*_





 *PAGE 46* 


_*بسم الله الر حمن الر حيم*_




*OUM FATIMA DATS* *SERVICES*



INA KUKE MA'ABOTA AMFANI DA DATA MAZA KU GSRZAYO GA DAMA TA SAMU, OUM FATIMA TA SHIRYA TSAF DOMIN SAYAR MUKU DA KO WANE IRIN NETWORK AKAN FSRASHI MAI SAUƘI.



GA TARIN KAMAR HAKA



MTN


500 MB ₦170


1GB ₦300 


2GB 600


3GB ₦ 850


5GB ₦ 1400


10GB ₦ 2850



 *AIRTEL*



500MB ₦170


1GB ₦ 300 


2GB ₦ 650



3GB ₦ 950


5GB ₦ 1460


10GB ₦ 2840



 *GLO*


500MB ₦ 170


1GB ₦ 320


2GB ₦ 600


3GB ₦ 900


5GB ₦ 1450


10GB ₦ 2840



 *9 mobile*


500BM ₦ 1400


1GB ₦ 300


2GB ₦ 450


3GB ₦ 650


5GB ₦ 950


10GB ₦ 1900


Sai kun zo



**** Bayan mun yiwa amarya sallama mun fito sabo da Hammah daya kirani akan na fito mu wuce, su Anisa ma fitowa suka yi za'a mayar dasu Gida. Muna fitowa ne take dawowa Gidan, ganin Mutane na fitowa daga part ɗin dake kusa da nata ne yasa ta tsayawa tambayar "Su waye ku, me kuke min a Gida?". Ta faɗa tana yatsuna cike da rainin hankali.


"Kan uban can anzo wurin". Na faɗa sabo da na daɗe ina son Allah ya haɗani da Matar nan in koya mata hankali ko don magan-ganun rainin wayon data riƙa faɗa lokacin da Mijinta ya nemi aurena don haka na matsa kusa da ita nace "Wacece ke? Don da buƙatar in tabbatar kafin na baki amsa". Na faɗa cike da gadara ina binta da wulaƙantaccen kallo.


Cikin ƙufula da abinda nayi mata itama tace "Nice nan Matar Gidan kuma mai iko da Gidan dabo da haka ku gaggauta sanar dani abinda ya kawo ku cikin Gidana!". Ta ƙarasa a tsawace da ɓacin rai.


Nunata na shiga yi ina ƙyalƙala dariyar rainin hankali mai cusawa mutum haushi, ai kuwa ta shaƙa don take ta fara masifa tana kumfar baki. Sai da na tabbatar ta shaƙa yanda nake so kafin na fara magana "Wai Matar Gida a hakan? Ni gaskiya banga Matar Gida a nan ba sai ballagaza sha-sha-sha mara sanin ciwon kanta, abinda ya kawo mu kuwa shine amarya muka kawowa Alhaji Bilal, eh mar'atusssaliha ta shigo da ƙafar dama In sha Allah nan da wata tara zamu dawo shagalin suna". Na ƙara sa cike da tura mata baƙin ciki.


Kukan kura tayi zata nufo ni ni kuma na gyara tsayuwa ina son ganin ƙarshen haukarta naji anja hannuna baya cikin zafin nama, ɗagowa nayi don ganin waye muka haɗa ido da Hammah da naga ransa a ɓace amma muna haɗa ido na shagwaɓe fuska yayi min alamar kar nayi rigima muje Gida.


Juyawa nayi na watsawa Aliya kallon gargaɗi yayinda take ta hauka tana fizga daga hannun Mijinta da yazo ya kamata ya nufi sashinta da ita tana ta ɗura manyan zagi tana kuka sai kace mahaukaciya.


Hamma Jabeer da Anisa ta kira a waya ta faɗa masa abinda ke faruwa ne suka shigo tare da Alhaji Bilal ɗin, har su Anisa ya ɗauka muka fara aje su kafin muka wuce Gida ina ta cika ina batsewa da ba'a barni na sassaɓawa Matar cen kamanni ba. Kallonta yake yana mamakin rigimarta, yanzu da aka barta sai ta daki Matar mutane a cikin Gidanta. "Allah ya shirya ki my rigimammiya". Ya faɗa ganin yanda take ta turo baki gaba. Ai kuwa bakin na taɓe na fara masa rigima, rarrashina yayi har muka ƙarasa.


Da yake mun tsaya a hanya ya mana take away shi yasa muna zuwa wanka muka fara yi muka shirya kafin mukayi zaman cin abinci. Sai da muka gama ya shiga min nasiha cikin hikima akan kar na ƙara kulata ko mun haɗu, alƙawari na masa akan zanyi yanda yace amma idan ta taƙaleni ba zan ƙyaleta ba. "Soffy nah!" Ya furta cikin wani irin voice.


"Na'am Hammanah". Nima na faɗa a hankali.


"Karki kulata kin ji ko".


"To Hammah". Na faɗa ina ɗora kaina saman kafaɗarsa. 


"Yauwa yarinyar kirki Allah ya maki albarka".


"Ameen" na faɗa cikin jin daɗin albarkarkar da ya saka min. Tattare komai nayi na mayar nayi brush na kulle ɗakina na nufi nasa don nima yanzu na saba kwanciya a jikinsa.


Ina zuwa na samu ya gama shirinsa hannu ya miƙo min na miƙa masa ya janyoni ya rungume daga haka muka yi barcinmi cikin natsuwa.





****** Rikici sosai aka kwasa tsakanin Aliya da Alhaji Bilal don da bakinsa ya shaida mata cewar aure ya ƙara kuma mutu ka raba idan zata kwantar da hankalinta ta kwantar, idan kuma taga haukarta zata canza wani abu to Bismillah.


Kwalarsa taci ta shiga zaginsa tana faɗin "Wallahi ƙarya kake Bilal baka isaba wallahi sai ka saketa yanzun nan ma kuwa ko kuma in kasheta kaima in kasheka kowa ya huta!". Ta faɗa cikin tsananin ɓacin rai har tana jijjiga.


"Sakeni!" Ya faɗa a matuƙar tsawacen da bai taɓa mata ba don gab take da ƙure haƙurinsa.


"Ba zan sake ka ba munafuki algungumi, ni zaka munafunta kaje kayi aure ban sani ba azzalumi mug..." Tas-tas saukar zafafan maruka saman fuskarta yasa ta kasa ƙara sa faɗar abinda tayi niya ta sakar masa riga ba shiri ta dafe fuska tana kururuwa tamkar ƴar bori.


"Naga alama haukarki bai san ido ba, ni zaki riƙa fadawa irin waɗannan magan-ganun sha-sha-sha da bata san ciwon kanta ba!". Ya faɗa a fuface ya fice daga ɗakin. Ihu ta saki tabi bayansa yasa key ta waje ya rufeta tana ta dukan ƙofa tana kuka da zaginsa.


Ɗakin yaransa ya shiga ya samu suna ta kuka don duk abinda ya faru suna ji musamman babbar, lallashinsu yayi suka yi shiru ya kaisu sukaci abinci ya tsaya suka yi shirin barci suka kwanta bayan yayi musu addu'a ya rufe musu ɗaki kafin ya fita ya rufe part ɗin yabi ta kofar da zata kaisa nasa part ɗin ya shiga shirin zuwa wurin amarya da ya san tana can ita kaɗai.


Shiryawa yayi cikin dogayen kayan barci masu kyau da tsada ya yi amfani da turarukansa masu daɗi, sai da ya gama kimtsawa ya tabbatar komai yayi masa yanda yake so kafin ya ɗauki laidojin da ya shigo dasu ɗazu ya rufi part ɗin nata.


Ƙarfe 10:00pm lokacin da ya shiga don haka ta gaji da jira har tayi barci cikin tsoro don duk abinda ya faru tana ji don haka a tsorace take kar ta shigo ta kasheta kamar yanda tayi iƙrari, da yake a tsorace take shiyasa barcinma cikin tsoro tayi sa. Tana jin ƙaran buɗe ƙofa ta zabura ta miƙe zaune tana salati.


"Ki natsu nine". Ya furta lokacin da yake ƙarasowa kusa da ita, zamanta ta gyara tana rufe fuskarta da mayafin lafayar dake jikinta. Ƙarasowa yayi ya zauna kusa da ita. "Amarya bakya laifi". Ya faɗa yana leƙa fuskarta.


Murmushi tayi tana ƙara ɓoye fuskata, abinci ya gabatar mata sukayi sallah kamar yanda Addini ya koyar yayi mata tambayoyi game da Addini, haka suka raya darensu cike da farin ciki.



★★★



Ya ta kama Friday da wuri Hammah zai dawo sabo da shirin zuwa Masallaci, da wuri nima na kammala aikina nayi wanka nayi kwalliyata cikin Kuwait Abaya na fito tamkar jinin Larabawa. Hotuna nayi masu kyau na zauna a parlour muna chatting da amarya Samha ina tsokanarta da "Amaryar Alhaji Bilal da girman kujerarki". Na faɗa ina murmushi.


"Ke kuma amaryar Doctor Hamma Jabeer ya taki girman kujerar zata kasance?". Ta faɗa daga ɗayan ɓangaren. Fari nayi da manyan idanuna nace "Tawa ta musamman ce sabo da Hammmanah na musamman ne". Na faɗa cike da nishaɗi.


"Shegiya ƙawata an kurɓi so a kofin lu'u lu'u an faɗa laga-laga, da kikace bakya son sa". Samha ta faɗa cike da shaƙiyanci. Ido na kuma juyawa nace "Ke maganar tsohon zance kike ai yanzu an shiga new sation, ke kin san Hammanah abin so ne ga ko wace Mace sai dai ba wacce zata samu ba". Na faɗa ina juya ido.


Dariya Samha tasa tace "Baki da dama ƙawata Allah ya ƙara danƙon ƙauna".


"Ameen" na faɗa ina ƙoƙarin sake magana aka buɗe ƙofar parlourn, ganin Hammah ɗauke da Little yasa nayi mata sallama na aje wayar na kwasa da gudu na nufe su. Duka na haɗa na rungumesu ina dariya.


Tunda ta ɗebo da gudun nan ya tsaya ya zuba mata ido yana kallon yanda take ta fara'a, wani sanyi yaji a ransa don ba abinda yake son gani a fuskarta irin farin ciki da murmushi. Allah da ya halicce shi ya halicci zuciyarsa shi kaɗai yasan irin son da yake yiwa wannan halittar.


"Wayyo! Hammah ashe zaka kawo min ita ne shi yasa jiya nayi mafarkinta". Na faɗa cike da farin ciki ina amsarta, yarinya ta girma tayi ɓul-ɓul abinta Masha Allah.


"Hi Habebty ga Mamanki ". Na faɗa ina ɗagata sama, kamar taji mai na faɗa ta ƙyalkyale da dariya. Nima dariya na saka muka tayi shi kuma ya zuba mana ido yana kallonmu fuskarsa ɗauke da murmushi.


Wani irin farin ciki yake ratsa zuciyarsa 'Allah Sarki Kalisat shi yasa ta zaɓeki ta maki kyautar ta sabo da ta san cewa zaki ƙaunaceta, Allah ya jaddada rahama a gareki'. Ya faɗa cikin zuciyarsa.


"Shikenan bari in koma ni tunda baza'a kulani ba". Ya faɗa cikin ɓata fuska kamar zai yi kuka.


"Sorry Hammah nayi matuƙar kewarta ne Hammah, muje kayi wanka your food is ready".


Sama muka hau na shiga ɗakinsa na haɗa masa ruwan wanka ni kuma na wuce da Little ɗakina na mata wanka na shiryata cikin sababbin kayan da ya shigo mata da su.


Tsaf na shiryata tana ta ƙamshi abinta na haɗa mata abincinta na bata. Fitowa yayi cikin shirin tafiya Masallaci yayi kyau sosai cikin wani tsadadden farin yadi ɗinkin shakwara da jamfa.


"Hammah kayi kyau sosai" .


"Kin fi kyau yin kyau Sofy ".


"Your food is ready". 


"Lokaci ya ƙure sai na dawo".


"Allah ya tsare min kai Hammanah". Na faɗa ina sake masa kyakykyawan murmushi.


"Ameen ya Allah". Ya faɗa cikin jin daɗin addu'ar da tayi masa da kuma nata data kirasa da shi.




Assalamu alaikum barkammu da wannan lokacin ina mai baku haƙuin jina shiru da kuka yi sakamakon rashin lafiyar da nayi fama dashi, ina matuaƙar gidiya da addu'oinku a gareni Allah ya saka da alkairi ya bar zumunci. Kuyi haƙuri da wannan naso yafi haka amma na kasa.



Oum Fatima

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.