Free chapter · Read without an account

9

by Ameera Adam · SHU'UMAR MASARAUTA 2

*SHU'UMAR MASARAUTA*

          *BOOK 2*


      ©AMEERA ADAM


 *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

  (_Home of qualities and trusted writers of the nation_)


Tsokaci: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a wata kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.

  

 SHAFI NA TARA


  A karo na biyu hayaniya ta sake ɓarkewa a cikin kotun jin furucin da Yarima Ramadan ya yi, a wannan lokacin ma Mai shari'ar ce ta buga teburin gabanta nan take shiru ya ratsa. Barister Fahima ta saki murmushi haɗe da miƙewa tsaye ta ce.


 "Yarima Ramadan, Idan har kana ganin ɓata wa kotu lokaci ne me ya sa bayan ka kashe shi ba ka miƙa kanka a gaban hukuma ba? Me ya sa ba ka dubi yawan iyalan marigayinsa ba? Saboda kawai son zuciyarka ka hallaka shi..." Cikin hanzari Mubarak ya miƙe ya ce.


 "Objection my lord! Ya mai shari'a ina neman alfarmar da a gargaɗi lauyar masu ƙara, da ta daina yunƙurin cusa wa wanda ake zargi tsauraran kalamai a cikin bakinsa. Tun da har kawo yanzu zarginsa ake yi!" Mubarak ya ƙarasa maganar cikin girmamawa.


 "Barister Fahima a kiyaye." Alƙaliyar ta furta.


 "Za a kiyaye ya mai shari'a." Barister Fahima ta yi maganar tana sake fuskantar Yarima Ramadan.


 "Bayan kisan da ka yi wa marigayi Sarki Kamalu, sai kuma aka samu dogarinsa kace-kace da miyagun raunika a jikinsa. Shin me za ka ce a game da wannan Yarima?" 

Wani baƙin ciki ya mamaye Ramadan, zuciya ta ciwo shi har wuya. Rintse idonsa ya yi yana jin yawun bakinsa yana yi masa ɗaci, bai tanka mata ba. Kuma ta lura ba shi da niyyar tanka mata, don haka ta juya wurin Mai shari'a ta ce.


 "Koda ba mu baje kolin hujjojin da muke da su ba ya mai shari'a, alamomin rashin gaskiya da laifin kisan da ake zarginsa sun bayyana ƙarara a gaban kowa. Ya mai shari'a ina fatan kotu za ta yi duba na tsanaki, da kyawawan hujjojin da za mu gabatar mata ta yankewa Yarima hukunci daidai da laifin da ya aikata. Na gode." Barister Fahima ta yi maganar cikin girmamawa sannan ta zauna.


 "Ko lauyan wanda ake ƙara yana da abin cewa?" Alƙaliyar ta tambaya tana gyara zaman gilashin idonta.


"Mai girma mai shari'a ina roƙon wannan kotu mai adalci da bibiyar koken marasa gata, da ta ba ni dama zuwa zama na gaba, domin mu gabatarwa da kotu hujjojin da za su gansar da ita cewar Yarima ba shi ya kashe marigayyi Sarki Kamalu ba. Ina kuma sake roƙon mai girma mai shari'a da ta bayar da Yarima Ramadan a hannun beli." Alƙaliyar na gama jin kalaman Mubarak ta ce, "Kotu za ta ɗaga zaman wannan shari'ar har zuwa goma ga watan janairun shekarar dubu biyu da goma sha biyar (10/01/20215) kuma a wannan zaman kotu tana buƙatar kowanne ɓangare ya gabatar da hujjojin kariya, bayan haka kuma kotu ba za ta bayar da Yarima a matsayin beli ba. Za a cigaba da killace shi har zuwa zama na gaba." Tana gama maganar ta buga teburin gabatan sau uku, ba a ɗauki lokaci ba jami'an gidan yari suka saka Yarima a gaba, Fulani Kubra ban da kuka babu abin da take yi.


 Tun ranar da abin ya faru da Yarima bacci ya ƙaurace masa, idan kuwa ya ɗauke shi sai dai ɓarawo. Don haka ya dage da nafilolin dare da rana, yana kai kokensa wurin Ubangiji. Watarana yana zaune da daddare a ɗakin da aka rufe shi, duhu ne da ɗakin sai hasken farin wata da ya mamaye harabar wurin. Yana zaune bayan ya idar da sallah yana addu'a, ya ji motsin daga can nesa da shi. Da sauri ya waiga duk da idanunsa ba gani suke ba, amma ga mamakinsa sai ya hango ta tana tunkaro shi, ta jikin ƙarfen ƙofar ta ratso ta shigo ta tsaya a gabansa.


  "Zan fitar da kai daga ƙangin da kake ciki idan har za ka ba ni jini a masarautarku!" 

Ya ji ta furta masa tana zuba masa idanu. Duk da ya ga baƙon al'amari a tattare da ita, hakan bai sai ya razana ko ya firgice ba, ya miƙe tsaye ya fara tunkararta bakinsa ɗauke da addu'a yana shirin yin magana ya ji ta zabga ihu ta fita da gudu. Shiru Yarima ya yi yana nazari don tun bayan tafiyarta sai ya ji idanunsa sun shafe ba ya iya ganin komai, ya kai hannu ya tattaɓa jikinsa yana mamakin hallitar da take buɗe masa idanu har makantarsa ta kau.


 "Wace ce ita?" 


Ya tambayi kansa cikin mamaki, sannu a hankali mafarkin da ya yi na baya ya shiga dawo masa. Ganin tunane-tunane na neman yi masa yawa ya sa ya fara biya karatun Alƙur'ani, a haka har bacci ya yi awon gaba da shi.

           ***


 A fusace Shugaba ya tunkaro ta cikin matsanancin ɓacin rai, sai ya zo gabanta ya damƙi hannunta da ƙarfi har sai da ta saki ƙasa. Cikin azaba Rawiya ta furta.


  "Don Allah Shugaba ka yi mini rai..."


 Tun ba ta gama magana ba ya katse ta cikin tsawa.

  "Kada ki sake kiran sunan Allah a wurin nan, domin nan matattarar shaiɗanu ce." 

Da sauri Rawiya ta gyaɗa kai, Shugaba ya cigaba da cewa.


 "Ɗan ƙanƙanin aiki kin kasa zartarwa da ƙungiya shi, kin yi wa ƙungiya asara mai girma dole sai kin bayar da rayuka biyu." 

A hargitse Rawiya ta ɗago ta dube shi, tana shirin yin magana ta ji ya ci gaba da cewa.


 "Mahaifinki ya ƙi zuwa yau don kada ya fanshe ki to kuwa dole ki sadaukar mana da rayuka biyu." 

Shugaba ya ƙarasa maganar yana nuna jikin bangon kogon ƙungiya.


 "A cikin waɗannan mutanen su waye kika fi so kika fi ƙauna har a cikin zuciyarki."

Ya furta yana nuna mata jikin bangon da ke ɗauke da hotunan makusantanta. Mahaifiyarta, ƙanwarta, kakanninta na wurin mahaifinta da 'wasu tsirarun 'yan uwan mahaifi da mahaifiyarta waɗanda suka fi shaƙuwa.


 "Wannan zaɓin na ki dole ne, idan kuma ba haka ba ƙungiya za ta zaɓi duk wanda ya yi mata."

Bakin Rawiya yana rawa ta ce, "A ɗauki Kakana da ƙanin mahaifiyata."


 Rawiya na gama magana ta ga Shugaba ya watsa musu jini a fuska, ta durƙushe a wurin ta rushe a matsanancin kuka. A sanyaye ta bi hanyar da ta shigo ta koma gida, duk kiran da Shugaba yake yi mata ko waigensa ba ta yi ba. Shigarta gida ya yi daidai da fitowar Daddy a gaggauce, domin wani irin hatsabibi bacci ne ya yi awon gaba da shi. Ganin yanayin sanyin jikin da Rawiya ta shiga gida da shi ya sa shi shan jinin jikinsa. Ya bi ta ɗakin da sauri amma kafin ya ƙarasa ta rufe ƙofar. Wayarsa ce ta fara ringing da kamar ba zai ɗauka ba, sai kuma ya ciro ya duba. Lambar Maleek ya ci karo da ita, gabansa ya buga da ƙarfi don dare ya yi sosai kusan ƙarfe ɗaya da rabi na dare.


 Tamkar zakaran da ya bi ta mayanka haka Papa ya ɗaga wayar jiki a sanyaye.


 "Maleek!"


"Yaya jikin Baba ne ya yi tsanani " 

Maleek ya furzo kalamansa cikin matsanancin tashin hankali. Dam! Ƙirjin Papa ya buga, lokaci ɗaya jikinsa ya fara karkarwa. Murya na rawa ya ce.

 

 "Maza ku kai shi asibiti gani nan yanzu zan zo!" 


 Daga haka Papa ya kashe wayarsa, ya fara zirga-zirga abin duniya goma da ashirin ya haɗe masa. Rawiya da ke tsaye a bakin ƙofa jin wayar da Papa ya yi ya sa ta fashe da kuka, ta rasa wanne irin sabon al'amari ne da yake faruwa da ita. Ba ta san mutanen ba, amma haka kawai ta ji ba ta iya yi musu musu a kan duk abin da suka umarce ta. Har yanzu ta gagara gano lokacin da suka yi wa rayuwarta ƙawance, ƙawancen da ke tsoma rayuwarta a kunci da tashin hankali. Tun da tana ji tana gani ta salwantar da rayuwar kakanta da ba ƙanin mahaifiyarta.


 A gaggauce ya koma ya samu Mami da ke bacci ya tashe ta, a nan yake sanar da ita abin da yake faruwa. Hankalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba, domin duk lokacin da jikin Baba ya yi tsanani ji take tamkar mahaifinta, saboda Baba ba a surika ya ɗauke ta ba. Ya ɗauke ta tamkar 'yar cikinsa duba da irin soyayyar da yake nuna mata, hijabinta ta saka ta rufawa Papa baya ya shiga motarsa yana yi wa Mai gadi horn. Nan take ya buɗe masa suka fita da gudu hankali a tashe.


 Fitar su Papa babu jimawa agogon ƙungiya ya kaɗa wa Rawiya, tana ji sai dai ta yi kamar ba ta ji ba. Ta jima a zaune a haka tun agogon yana kaɗawa har ya daina, daga can kusurwar bango ta hango Shugaba da tawagarsa sun ɓullo, kowannensu sanye da jajayen doguwar riga mai baƙar hula. Shugaba ya ƙarasa gabanta ya miƙa mata doguwar riga irin ta jikinsu ya ce.


 "Ki saka wannan rigar domin halartar zuƙe jinin kakanki da ƙanin mahaifiyarki, kina da zaɓi biyu daga wurin ƙungiya." 

Shugaba ya yi maganar yana tsugunnawa a saitin Rawiya, Rawiya ta kawar da kanta gefe ganin ta yi tozali da mummunar fuskarsa. Ga wani irin wani mai haɗe da ƙarni yana dukan hancinta, ta ji ya yi gyaran murya ya ce.


 "Idan har ba ki da ƙarfin zuciyar da za ki bi mu, mu jagoranci zuƙe jininsu. Za ki ba mu jinin mahaifiyarki, shi zai baye gurbin zuwanki. Ko kuma ki yi tarayya da baƙin gunkin ƙungiya." A razane Rawiya ta dube shi, Shugaba ya saki murmushi, munin fuskarsa ya sake bayyana. Babu yadda Rawiya ta iya hakan ta ta karɓi doguwar riga ta shiga banɗakin ɗakinta ta sauya kayanta ta fito, domin duka zaɓin da Shugaba ya ba ta ba mai yuwuwa ba ne a wurinta.


          ***

  Jin furucin Malam ya sa Zayyan ya lumshe ido haɗe da sauke ajiyar zuciya ya ce.


 "In Shaa Allahu babu abin da zai faru malam sai alkairi, haka kawai nake ji a jikina wannan macijin yana cikin uƙuba wacce take da alaƙa da baƙin ƙullin sihiri. Taimakonsa zai iya zama silar fitarsa daga ƙangin rayuwa." 


  A daidai lokacin Malam ya ƙarasa kusa da shi, ya ƙura masa ido yana kallo. Wani tunani ne ya faɗo masa, haka kawai ya ji tausayin Zayyan ya kama shi. Ya dafa kafaɗarsa ya ce.


 "Shi ya sa a duk cikin 'ya'yana nake alfahari da kai Zayyan, ina ji a jikina za ka kasance ɗaya daga cikin zaratan jaruman da Musulunci da dauniya za ta yi alfahari da su." Sosai Zayyan ya ji daɗin yabon da mahaifinsa ya yi masa, ya faɗaɗa fara'arsa ya ce.


 "Duk ɗan da ya samu mahaifi kamarka ya gama dacewa duniya da Lahira Malam." 


 Daga haka ya tunkari macijin bakinsa ɗauke da addu'o'i, wani iri ya fara ji tamkar ana mayar da shi baya. Juwa-juwa ta fara fisgarsa a haka ya ƙarasa gabansa, ya yi A'uzubi kalimatullahit tamma min sharri ma kalak, da A'uzubillahi minasshaiɗanir rajim. Tare da waɗansu addu'o'in kariya, iya ƙarfinsa ya tattara ya ɗauke dutsen, sai dai tun kafin ya ƙarasa sauke dutsen sai dutsen ya yi wani irin wurgi da shi can gefe. Da sauri Malam Bukar ya yi kansa yana yi masa sannu cike da tsananin mamaki, dafa bayansa Zayyan ya yi da yake jin zafin buguwar. A hankali Malam Bukar ya riƙo hannunsa, tashin da suka yi suka ga wannan macijin ya miƙe tsaye a a bayansu, tsawon macijin ya kai har saman manyan bishiyoyin da ke wurin. Idan ba gizo idonsu yake yi musu ba, sai su ce sam ba haka girman macijin yake ba.


 Gaban Malam Bukar da Zayyana ya buga, suka ja baya suna addu'a haɗe da ɗaga kai domin gano ƙarshen macijin. Suna cikin wannan yanayin suka ga macijin ya sunkuyo da kansa ƙasa, ya fara ƙanƙancewa yana yin girgiza suka ga wani dattijo tsugunne a gabansu. Razani, firgici da tashin hankali ne suka mamaye duniyarsu a daidai wannan lokacin, Malam ya rungume Zayyan jiki na rawa ya ce, "Zayyanu ka ga abin da na gani kuwa?" 

 

Ganin hankalin mahaifinsa ya kai ƙololuwar tashi ya sa ya rungume shi sosai yana tofa masa Ayatul kursiyyu.


 "Assalamu... alai... kum!" 

 Suka riski muryar dattijon ya yi musu sallama a wahalce.


"Wa alaikassalam!"

    Zayyan ya amsa masa, sai a lokacin Malam ya ɗan saki jikinsa.


 "Don Allah ku ba ni ruwa na sha, amma ba ruwan ƙoramar can ba." 

Dattijon ya furta yana sauke numfashi da ƙyar.


 Malam ne ya sauko da ƙatuwar jakar goyonsa, ya ciro waɗansu manyan gorar ruwa ya miƙa masa. Dattijon yana karɓa ya kafa kai ya shanye ruwan cikin jin ƙishirwa. Jingina ya yi da wata bishiyar tsamiya yana mayar da numfashi, daga Malam har Zayyan suka zuba masa ido suna kallo.


 "Don Allah ka da ku ji tsorona, ni ma musulmi kamar ku. Sai dai ni ba jinsin bil'adam ba ne. Sunana Dattijo Maharaz, na samu kaina a wannan ƙungurmin dajin sanadiyyar mummunan sihirin da aka haɗa baki da wani makusancina aka yi mini shi."


            ***    

  Bamaguje yana tafiya Umaima ta fito daga maɓoyar da Boka Jassu ya yi mata, ta saki murmushin farinciki sannan ta ce.


 "Ya kai babban Boka, ina mai yi maka albishir da matuƙar Bamaguje ya mutu a daren yau sai na sadaukar maka da ilahirin jikina!" 


 Boka Jassu ya tashi daga kan kujerarsa, ya ƙarasa gaban Umaima ya fara shafa gashin kanta cike da sha'awa ya ce.

   "Idan har tunaninki yana ba ki Bamaguje ba zai mutu a daren yau ba kin yi kuskure Umaima, na rantse da kaifin tsafin da nake tunkaho da shi. Matuƙar Bamaguje bai mutu a yau ba sai na sare kaina zuwa wayewar gari, haka wannan tsohon munafikin da ke taimakon masarautar Huddam! A daren yau wanda na ba wa aikinsa zai zartar da shi, don ma yana da shegen taurin kan tsiya da ƙarfin addu'a da hallaka shi zan yi." 

  Lokaci ɗaya Umaima ta haɗe fuska cikin ɓacin rai ta ce.


 "Kana nufin Maharaz ya fi ƙarfinka Boka Jassu? Kada ka manta na faɗa maka Maharaz shi ne mutumin da ya bankaɗa mini labulen sirrina, idan ina ƙaunar mutuwata ina ƙaunar Maharaz. Ka taimaka mini ka halaka shi cikin gaggawa." 

Boka Jassu ya yi shiru har sai da Umaima ta gama sannan ya ce.


 "Idan kin san mutuwar tsaye, shi ne abin da zan yi wa wancan la'anannan tsohon. Zai kai shi ƙasurgumin daji mai ban tsoro wanda babu wani bil'adam ko aljan da zai shiga cikinsa, ballanta ya kai masa ɗauki. Zan shafe idanun jinsi da zuri'arsa daga kan dajin don ma kada su yi yunƙurin gano wurin da yake har su kawo masa agaji. Surar da zan mayar da shi kuwa, zai yi wuya bil'adama ya kusance shi ballanta ya iya taimaka masa."

  A fili Umaima ta sauka jiyar zuciya ta ce.


 "Da dama-dama kibiya a cikin ido, amma ba haka aka so ba wai ƙanin miji ya fi mijin kyau." 

  Umaima ta yi magana tana shigewa cikin ɗakin tsafin Boka Jassu.

  Tun a wannan lokacin Boka Jassu ya fara gudanar da aiki a kan Bamaguje, sai da ta ga ya kusa kammalawa sannan ta fice ta nufi kogon tsafin Bamaguje.


  Bamaguje tun da ya tafi haka kawai yake jin jikinsa a sanyaye, yana zuwa kogon tsafinsa ya ga kogon ya yi ƙurmus kamar wanda aka yi wa gorin gobara, duka kayan tsafinsa ya ƙone kamar gawayi. Ƙirjinsa ya buga da ƙarfi, ya shiga yunƙurin aiwatar da tsafi domin ya haske cikin kogon dutsen amma abin ya gagara. Jingina ya yi da bango hawaye na zuba daga idanunsa.


   "Tabbas na yi kuskure da na aminta da babban maƙiyina a baya, har na sakar masa ragamar rayuwata, kaicon rayuwata da halin da na tsinci kogon tsafina a ciki."

Bamaguje yana gama magana ya ji jikinsa ya ɗauki wani irin zafi tamkar ana ɓararraka namansa a ruwan dalma, tun yana tsaye har ƙarfinsa ya fara ɗaukewa ya durƙushe a ƙasa. Sama-sama yake sauke numfashi yana kwance ya hango wani haske mai haɗe harshen wuta ya tunkaro shi, daga cikin haske ya hango ta tana tafe hannunta riƙe da murtukeken baƙin kare tana janye da igiyar wuyansa. Ƙirjin Bamaguje ya buga, jiki na karkarwa ya nuna ta da yatsa zai yi magana ya ji Umaima ta ce.


   "Ka jima da yin sake ɗan zaki ya girma Bamaguje! Na jima ina fakonka har zuwa yau da za ka baƙunci ajalinka. A kan ƙwayar idonka zan saki ɗana Basiru, da ka mayar surar kare ya cinye namanka, wannan shi ne hukuncin zalincin da aka aikata masa."

 Bamaguje ya numfasa da ƙyar ya ce. "Umaima kada ki yarda da daɗin bakin Boka Jassu, domin maci amana ne. Yadda ya munafurce ni kema a sannu zai halakar da ke." Tari ne ya turnuƙe shi, yana yi yana aman jini, sai da ya gama sannan ya ɗora da cewa.


 "Dalilin da ya sa na mayar da ɗanki kare, na yi bincike shi ne zai zama ajalinki duk daren daɗewa. Umaima ina ƙaunarki a matsayinki na 'yata, ba don ke jinina ba ce da tuni na jima da halaka ki bisa abubuwan da kika aikata..." 


 "Tun da kai ka yi jinkirin halaka ni, ga shi ai ni zan halaka ka Bamaguje." 

Umaima ta yi maganar cike da izgilanci.

"Ke uwa ce Umaima, ki rubuta ki ajiye duk daren daɗewa za ki ɗanɗana zafin dafin da ke zuciyata. Duk lalacewar mahaifi ko mahaifiya ba zai ta taɓa hallaka ɗanta ko ta nakasa shi ba, amma ɗa ko 'ya suna iya butulcewa soyayyar da suke yi musu. Umaima koda bayan raina, akwai ranar da duniya za ta koyar da ke darasin da zai kai ki ga lulluɓa bargon nadama." 

   Jin haka ya sa Umaima ta saki tsaki, Bamaguje ya girgiza kai yana jin ɗacin cin amanar da Umaima ta yi masa ya ce.

  "Duk tashe da ƙaurin sunan da za ki yi Umaima ba za ki kai koda farcen ƙafar Bamaguje ba, na yi shaharar da har a shafe duniya ba za a taɓa mantawa da kundin tarina ba. Ko kallona kika yi Umaima zan zame miki izina, yau a ce mai wannan furucin shi ne Bamaguje. Bamagujen da yake tarwatsa soyayyar uwa da ɗa, ya tarwatsa soyayyar miji da mata. Bamagujen da bai ɗauki kisa da zalinci a bakin komai ba, Bamagujen da yake tatse jaririn da ya faɗo daga cikin mahaifa. Bamagujen da ya ke bin gawa har cikin kabari ya cusa mata annoba, Bamagujen da yake binne mutane suna rayayyu, bayan sun ruɓe ya kwashi ƙashin jikinsu ya yi sihiri da shi. Bamagujen da ba zai lissafa adadin mutanen da ya kashe ko ya haukata ba, Bamaguje da bai ɗauki zina a bakin komai ba, Bamagujen da ya taka fadar baƙaƙen aljanu har ya cimma sarkin lokacin da yaƙi. Bamagujen da yake ba wa hatsabiban mutane da aljanu umarni jikinsu na karkarwa su bi, Umaima duk tsagerancinki ba za ki kama ƙafata ba, don haka ga fili nan ga doki sukuwa ya rage miki." 

  Bamaguje ya ƙarasa maganar jikinsa yana karkarwa, Umaima ta dube shi a yatsine ta tofa masa yawu a saman cikinsa. Lokaci ɗaya wuta ta kama kayan cikinsa, Bamaguje ya saki kururuwa da ƙarajin azaba har sai da kogon tsafin ya yi girgiza. Ta saki murmushin farinciki ta kalli Basiru da ke cikin surar kare ta tasa ƙeyarsa zuwa kan Bamaguje. Kamar mayunwacin zakin da ya shekara da yunwa, haka Basiru ya dinga yagar naman jikin Bamaguje. Duk inda ya zuba fiƙoƙinsa sai Bamaguje ya ƙwalla ƙara da kururuwar neman ɗauki, sai da Basiru ya ci kusan rabin jikin Bamaguje sannan Umaima ta dakatar da shi, ta koma saitin kan Bamaguje da yake numfashi da ƙyar, sai dai da alama ba ya cikin hayyacinsa. Ta ciro wani farin ƙyalle ta tura hannunta cikin ƙwayar idonsa ta ƙwaƙwalo duka ƙwayar idon biyu, sannan ta sake mayar da Basiru ya cigaba da cin namansa a haka har numfashin Bamaguje ya ɗauke rai ya yi halinsa.



🥹🥹🥹🥹 Duk da Bamaguje bai da hali na fa ji mutuwarsa wollah.


***

Ummou Aslam Bint Adam🌚

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.