Free chapter · Read without an account
04
*KAWA ZUCI*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*04*
*Unguwar Yalwawa, Dutse, Jigawa state, Nigeria.*
ZAHRA POV.
“Ruwaida wai har yanzu Zahra ba ta tashi ba?”
Cewar Mama sanda ta fito daga ɗakinta ta duba tsakar gidan ba ta ga Zahran ba, bayan Adali da dake cin abinci, da Saama dake wanki sai Ruwaida da ita ma ke cin nata abincin safen, ta san dai a lokaci irin wannan Zahra ba ta zaman ɗaki, dole ka sameta zaune a tsakar gida tana wani aiki.
“Mama ba ta daɗe da kwantawa ba ai… Jiya ba ta kwanta da wuri ba”
Ruwaida ta bawa Mama amsar.
“Ai na san ba za ta hutar da kanta ba har sai ta gama wannan azababben rubutun nata”
Cewar Mama tana taɓe baki, ta ja kujera ‘yar tsugunno ta zauna kusa da Ruwaida, yayin da take kallon Saama da Adali dake hirar satar da aka yi lokacin zanga-zanga.
“… Shi fa Abba Jaalo ya saci buhun taki ya fi goma, ya je ya taresu a ɗakinsa, yana jiran lafawar ƙura ya je ya siyarsu”
“To ai shi tasa satar ƙarama ya yi, ka san Habibu na gidan Malam Adamu? Allah ne kaɗai ya san adadin abin da ya kwasa na ganima, shi kuma Khabiru shi ne ya cinnawa wannan motar wuta ta sakateriya!”
“Hmm! Ai yanzu gwamna ya bada umarnin ayi bincike a kamo duk wanda aka kama da kayan gwamnati, ko waɗan da suka lalata kayan gwamnati”
Mama ta basu ɗan kaɗan daga abin da ta saurara a labarai.
“Ai Wallahi Mama duk abin da za su yi ba su isa sun kama kowa ba, domin wasu ma sun yi hijara sun koma Haɗejia, wasu kuma Kano”
Faɗin Saama.
“Yo a Haɗejian ma tsira suka yi? Can ɗin ma kamen ake… Shi yasa ranar da aka yi tashin hankalin nan na ce ku kula, kar ku taɓa kayan wani ballantana na gwamnati”
“Ai Mama wannan zanga-zangar ba ta kawo ci gaban komai ba face ci baya, har yanzu wasu masu shagunan ba su kai ga fara buɗewa ba, an tafka asarar rai da ta dukiya, ga yanda abincin nan ke hawa, abin dai sai dai kawai mu ce Allah ya mana magani”
Cewar Adali da ya gama cin abincinsa, Mama da Saama da a lokacin ya miƙe tsaye yana shanya kayan da wanke a igiya suka amsa da amin.
“Wai da ma har yanzu Zahra ba ta gama rubutun nan ba”
“Ina fa? Ta dai kusa gamawar, ina jin bai fi izu ɗaya ya rage mata ba”
“To ya kamata ta maida hankali dai”
“Ruwaida wai ba za ki hanzarta ki gama cin abincin nan ki tafi makaranta ba? Ko yau ɗin ma ba ki da niyyar zuwa?”
Adali ya tambayi Ruwaida da tun d'azu ta kasa gama cin abincin dake gabanta saboda kawai yau ma ba ta son zuwa makaranta, shi yasa ta ƙi ta gama da wuri, ta yanda za ta makara sai tace ba za ta je ba saboda kar a mata dukan makara, ta san Saama zai goyi bayanta a kan hakan, shi yasa ma ta yanke wannan shawarar, amma dai yanzu tun da Zazzaɓi sarkin duka ya yi magana ta san cewa shirin nata ya wargaje, dan in ba ta yi wasa ba sai ya sakata kuka kafin ya tisa ƙeyarta a gaba zuwa makarantar.
“Ai gara ka tambayeta, dan jiya ma haka yarinyar nan ta yi ƙirmisisi ta ƙi zuwa makaranta saboda iskanci”
Kamar Ruwaida za ta yi kuka haka ta kalli Mama, cikin sigar Mama ki rufa mini asiri, abin da take gudun ya faru dai sai da ya faru, Adali ya sakata a gaba yana mata faɗa, faɗan da da kanta take cewa da ace Malam na raye ba su isa sun mata ba. Ta san Mama ba ta mata gatan autanci, mahaifinsu Malam shi ne ke shagwaɓata, tun bayan mutuwarsa kuma ta rasa mai shagwaɓata, sai Saamari, shi ma ba kullum, dan ko yanzu da ake mata faɗan bai saka baki ba, tunowa da mahaifinsu da ta yi yasa ta fara hawayen kewarsa. Ba ta tanka ba har Adali ya gama banbamin faɗan nasa, sannan ta tashi ta bar sauran abincin nata da take jin ya fita ranta. Ta kai sauran ta aje a rumfar da suke girki a gidan, ta dawo ta saka hijabinta ta tafi makarantar duk jikinta a sanyaye.
“Allah sarki Ruwaida, Adali ka riƙa binta a hankali, Malam ne ya sangartata haka dole ba za ta dawo yanda muke so tashi ɗaya ba sai a hankali”
Cewar Saama cikin tausayawa halin da ƙanwar tasu ke ciki.
“A’a fa Saama, rashin jin Ruwaida ya fara yawa, dole a rija taka mata birki”
Mama ta ba shi amsa. Kafin wani cikinsu kuma ya sake cewa komai aka rangaɗa sallama a soron gidan, suka amsa su duka dai-dai da lokacin da wata farar mata ta shigo gidan, riƙe take da wata yarinya wadda kammninsu suka nuna cewa yarinyar ‘yarta ce. Yanda yarinyar da aka shigo da ita take rusa kuka yasa dukansu suke binsu da kallo ɗauke da tambaya ɗaya a ransu ta me yake faruwa.
“Laraba lafiya?”
Mama ta tambaya sanda ta nufi matar tana bin ‘yar tata da kallo.
“Ina fa Lafiya Abu? Ruwan zafi ne ya ƙona Mannira!”
Ta faɗa tana yaye hannun rigar yarinyar, gurin da ruwan zafin ya zubo mata ya yi jawur, abinka da farin mutum, kuma wurin ya fara alamun tashi.
“Subhannalahi… Adali zo ka zuba mata ruwa a wurin”
Faɗin Mama da ta kama hannun yarinyar tana dubawa, Adali da Mama ta umarce shi ya nufi randar dake tsakar gidan, ya saka kofi ya ɗebo ruwa a ciki, sannan ya dawo wurin da suke tsaye ya kama hannun yarinyar ya zuba mata a wajen.
“Sannu Mannira”
Ya mata sannu bayan ya zuba mata ruwan, Mannira ta jinjina kai tana sharar hawaye, Saama ya shimfiɗa musu tabarma, Mama ta zaunar da Mannira Laraba ta zauna kusa da ita suna ta jera mata sannu, a lokacin kuma Zahra da kukan Mannira ya tasheta ta fito daga ɗakinsu tana hamma, dan ba laifi yau tana jin bacci sosai.
“Insha Allah ba zai tashi ba tun da har an zuba miki ruwan nan, Saama ka ɗauko roba ka zuba musu ruwan su tafi da shi ana zuba mata a kan ƙunan insha Allah ba zai tashi ba”
“To Abu, mun gode sosai”
Laraba ta godewa Mama.
“Ah haba ai ba komai Laraba, wannan abu ne da Malam ya bar musu gadonsa, kuma ya zama dole garesu su taimakawa al’ummar annabi da baiwar da Allah ya wadatasu da ita domin gode masa”
“Haka ne”
“Ina kwana Maman Mannira”
Zahra ta gaisheta tana zama kusa da su, murmushi kwance kan fuskar Laraba ta amsa, kamar ba ita ce ta shigo hankali tashe ba.
“Mama ni zan fita”
Cewar Adali yana saka takalmansa.
“To a dawo lafiya, Allah ya tsare ya bada sa’a”
“Amin… Zahra zo”
Ya ƙarashe da ƙiran Zahra tare da nufar hanyar soro, Zahra ta bi shi a baya, a soron gidan nasu inda ɗakinsu yake shi da Saamari ya tsaya, ita ma tsayawar ta yi domin jin abin da zai ce mata.
“Kina da indigene ko?”
Ita ce tambayar da ya fara cilla mata, ta yi saurin gyaɗa masa kai.
“Zamanki hakan nan ba ya min daɗi, dan haka zan naima miki gurin karatu a Poly Dutse...”
Cikin wani abu da ya ɗara murna Zahra ta ɗago kai ta kalli yayan nata, bakinta kawai take motsawa tana son cewa wani abu, amma ta kasa, sai dimples ɗinta na ko wani ɓangare dake motsawa tare da motsin bakin nata, domin duk yadda za ta motsa bakinta to sai sun loɓa.
“Na-na gode sosai Ya Adali, Allah ya ƙara buɗi”
Wani gajeren murmushi ya mata, dan shi ba mutum ne me fara’a ba.
“Ba komai Zahra, ki je ki haɗo min indigene ɗin naki da certificate ɗinki na makaranta da kuma result na WAEC ɗinki”
Ta jinjina masa kai, ya nufi ƙofar fita tana masa addu’ar Allah ya dawo da shi lafiya, ta dawo gida tana jin kamar ta tashi sama dan farin ciki. Za ta iya cewa bayan rasuwar mahaifinsu ba ta taɓa samun wani giɓi a rayuwarta ba, kuma duk da Allah ya ɗauki ran mahaifinsu lokacin tana kan tasowa ya bar mata ‘yan uwa guda biyu da suke kula da ita tamkar mahaifin nata.
Rayuwarta na tafiya a kan dogon miƙaƙƙen layin da bai karkace ba tun daga farkonsa har zuwa inda take a yau, ba ta san ƙarshen layi ba, domin komai zai iya faruwa da ɗan adam a lokacin da bai yi tsammani ba, ita dai har zuwa yanzu da take numfashi a duniya bata taɓa haɗuwa da wani abu da ya girmi ta ɗauke shi ba, kullum cikin fatan kasancewarta a hakan take… ba tare da sanin tarin abubuwan da suke tunkaro rayuwar tata ba, domin taƙi kaɗan ne ya rage tsakaninta da ƙaddarar rayuwarta.
Asalin mahaifinsu Malam Rabi’u Sharif mutumin wani ƙauye ne da yake Yobe, wai shi Tulotulo, babban malamin addini ne kuma sharifi wanda ya yi gado tun daga kakkaninsa, yawon kasuwanci ne ya kawo shi Jigawa, har ya haɗu da matarsa Abu, ‘yar asalin garin Haɗejia. Bayan sun yi aure suka koma garin Dutse da zama, inda ya kafa makarantar gargari. Malam Rabi’u ya tara almajirai bila adadin, domin a unguwar da ya zauna babu wanda bai san makarantar Malam Rabi’u Sharifi ba.
Ana kawo masa almajirai daga jahohi da-ban-da-ban na sassan Nigeria, Adali shi ne ɗansu na farko, me biye masa kuma Saamari, sai Zahra da auta Ruwaida. Duka cikin yaran Malam Rabi’u babu wanda bai taso da baiwa irin ta mahaifinsu ba, wuta ba ta ƙonasu, kuma sukan bada maganin ƙunan wuta, ko ruwan randar gidansu suka ɗiba suka zubawa mutumin da ya ƙone to da yardar Allah wurin ba zai tashi ba.
Hatta Ruwaida ƙarama dake da shekaru goma sha uku ta sauƙe al’kur’ani mai girma, ballantana kuma manyan, shi Adali sau biyu yana rubuta al-kur’ani da ka. Allah ya musu ilimi kamar zuban ruwan sama, abin da ya kawo wargajewar makarantar Malam Rabi’u ita ce rasuwarsa, bayan rasuwarsa gaba ɗaya almajiran makarantar suka kama gabansu. Sannan ‘ya’yansa suka ci gaba da kula da gidan, duk da ba wani kuɗi suke samu ba ba su yarda ƙannensu su yi rashin wani abu da bai fi ƙarfinsu ba. Shi Adali shago ne da shi a kasuwa na siyar da yadika, yayin da Saamari yake aiki a wani gidan shinkafa, duk da sun rasa mahaifinsu ba su daina bada taimakon maganin ƙuna da addu’o’I ba idan mutane sun zo da buƙata, hakan yasa ma ake ƙiran gidan nasu da gidan Sharifai.
*Masarautar Dutse*
SA’AD POV.
Gyaran muryar Galadima Khabir, babban ɗan Takawa kuma ɗan fari a wurin Adda ne ta fara musu iso a falo na biyu dake turakar Adda. Shi ya fara wucewa, sanda bayi da hadiman sashin Adda da suka zube a ƙasa suke ta kwasar gaisuwa suna ta ƙirari. Sa’ad na biye da shi a baya har zuwa cikin falon, Galadima ya zauna a kan sofa, yayin da Sa’ad ya zauna a saman carfet kusa da ƙafafunsa.
Jim kaɗan Adda ta shigo falon da suke, cikin girmamawa kowannensu ya gaisheta, ta zauna tana binsu da kallo, domin ta san da batun da suka zo da shi, saboda tun da Sa’ad da Maryam suka dawo daga asibitin da ya kaita bai zo ya ce musu ga takamemen abin da ya faru ba, ita kanta Maryam ɗin da Adda ta tambayeta cewa ta yi ba ta san me likitan ya gayawa Sa’ad ba.
“Adda! Sa’ad ya gaya mini komai game da abin da likitan da ya duba Maryam ya gaya masa, ba ni kaɗai ba, hatta Takawa ya san da batun, domin a gabansa Sa’ad ya faɗi komai… Nauyin maganar yasa Sa’ad ya kasa furta miki ita kai tsaye, ya fara sanar da mu domin mu mu sanar da ke”
Adda ta kalli Sa’ad da yake kallon wasu vase da aka jera kan kykkyawan center table da aka aje a tsakiyar falon, don shi ba ma su yake kallo ba, amma kuma a jikinsa yake jin kallon da Adda ke binsa da shi, sanin halin da za ta iya shiga yasa ya kasa gaya mata da kansa, duk rashin hankalinsa ya kan iya fahimtar halin da za ta shiga idan har ta ji batun cewa ‘yarta ta kamu da ciwon hauka, shi yasa ya zage ya fara faɗawa Takawa da Galadima, in ya so a cikin su biyun a samu wani ya tunkari Adda da ita kanta Maryam da wannan batun.
“Me likitan yace yana damunta?”
Adda ta tambaya cikin ƙarfin halin son danne abin da zuciyarta ke raya mata, yo me ma zai kasance yana damun ‘yar tata? Bayan ta san wurin irin likitan da aka kaita ya dubata, ai da ace lafiya ƙalau take tashin farko kawai za a gaya musu cewar ƙwaƙwalwarta lafiya take, amma tun da aka fara mata wannan kewaye-kewayen ta san cewa abin da ake zargi ne ya tabbata. Galadima ya yi gyaran murya tare da zamowa daga kan kujerar da yake kaɗan yana tattara hankalinsa gaba ɗaya kan kalaman da suke hanƙoron fitowa daga bakinsa.
“Abin da likitan da ya duba Maryam jiya yace shi ne… akwai alamu na ƙwaƙwalwar Maryam ta taɓu, duk da bai ba da tabbacin hakan ba, yace zai iya kasancewa aikin jinnu ko asiri, amma a nasu ɓangaren za a iya danganta ciwon na Maryam da hauka!”
Maraym da Muhibba dake tsaye a can cikin corridor ta inda Galadima, Sa’ad ko Adda ba za su iya ganinsu ba ta yi baya-baya tana jin hajijiya na naiman kayar da ita, Muhibba ta miƙa hannunta za ta riƙota ta kauce hawaye na zubo mata, sannan ta fara ja da baya tana yin hanyar da ɗakinta yake, cike da tausayawa Muhibba ta ƙira sunanta ita ma nata hawayen na zubowa na tausayin ‘yar uwarta.
“Ya Maryam!”
Ba ta amsa ba ballantana ta tsaya, tana shiga ɗakinta ta kulle ƙofar, sannan ta ɗauki wayarta ta naimo lambar Sadiq mijinta ta aika masa ƙira, sai da ta jera masa ƙira uku ba a ɗauka ba. Zama ta yi a bakin gadonta tana fashewa da kuka.
“Dan Allah ka ɗaga wayana Sadiq”
Ta faɗa hawaye na zubo mata kamar da aka tanadesu dan wannan ranar kawai, sai a karo na biyar ta ci sa’a ya ɗaga wayar, ba su ko gaisa ba ya birkice yana tambayar abin da yake damunta, jin tana kuka.
“Maryam me ya faru? Ko jikin naki ne? Hammad ba ya nan ballantana na ce shi ya ɓata miki rai… me aka miki?”
Kanta ta girgiza tana jan numfashi kamar za ta shiɗe dan kuka, akwai matuƙar tashin hankali a cikin lamari irin nata, a ganinta wannan ƙaddarar ta mata nauyin da ba za ta iya ɗauka ba, ta manta da Allah ba ya taɓa ɗorawa rai abin da ba za ta iya ba, kuma abin da ba ta sani ba shi ne, ƙaddararta na ɗaya daga cikin ƙaddarori mafiya sauƙin cinyewa a duniya, domin akwai waɗan da suka fi nata wahala da nauyin ɗauka.
“Sadiq! Sadiq me ya sa ba ɗaga ƙirana ba”
Ta daure ta faɗa da ƙyar tana shafa wuyanta.
“Sanda kika ƙira wayar tana hannun Bahijja (Abokiyar zamanta) ban san me ya sa da ta ga ƙiran naki ta ƙi ɗagawa ba, faɗa mini abin da yake damunki”
Silalewa ƙasa ta yi tana riƙe kanta da hannunta ɗaya, ɗayan hannun nata kuma riƙe da wayarta tana kuka sosai.
“Jiya mun je asibiti ni da Ya Sa’ad, mun… Mun je wurin likitan ƙwaƙwalwa, ya zaunar da ni ya min tambayoyi game da cutar da take damuna, bayan ya gama yace… wai yace…”
“Me yace? Kar ki tabbatar min da abin da nake hasashe yanzu haka?”
Cikin ƙunar rai ta jinjin kai tana toshe bakinta.
“Sadiq wai yace akwai alamun taɓin hankali a tattare da ni!”
Don't forget to follow my account
----------------
#SalmaAhmadIsah
#Candy
#Bahadejia
#KawaZuci