Free chapter · Read without an account

05

by Salma Ahmad Isah · KAWA ZUCI

*KAWA ZUCI*



*©SALMA AHMAD ISAH*


*05*


*No. 32 Rue de I’Abreuvoir, 278, Paris, France.*


*09:01 na safiya.*


HAMMAD POV.


Gida ne da ya ƙunshi ɗakunan bacci guda biyar, uku daga ciki na ɗauke da bathrooms, sannan akwai living rooms guda biyu, a cikin ko wanni living room akwai fire place, saboda yanda weather'r sanyi ta zama jiki a garin na Paris. Akwai private garden a gidan wanda yake da outdoor a dining area. Akwai kitchen dai-dai misali, wadda yake haɗe da living room ɗin dake ƙasa, sannan akwai wani sitting area da yake saman gidan, wadda idan kana wurin kai tsaye za ka iya ganin Eiffel Tower. Daga ƙasa kuma akwai babban compound da ya ƙunshi parking lot.


A cikin babban bedroom ɗinsa yake kwance saman wani gado mai kyau, yanda ya nutse cikin ɗumi da laushin gadon yasa a kallon farko ba za ka ce akwai mutum a kan gadon ba, kukan dokin da yake ji ne ya yi nasarar farkar da shi daga bacci, maimakon ya tashi sai ya miƙa hannunsa ya ɗauki wani pillow ya toshe kunnuwansa da shi, kuma hakan bai sa ya daina jin kukan dokinn ba, ya san gardamar dokin nasa, yanzu haka masu kula da shi sun kasa control ɗinsa, shi yasa yake ta jin hayaniyarsu a waje.


Ba dan baccin ya isheshi ba haka ya tashi zaune yana shafa gajerun twist ɗin dake tsakiyar kansa, dan bayan gashin da akayi wa twist ɗin wanda yake a tsakiya ƙasa da kuma gefe da gefen kan nasa babu gashi an aske. Ƙafafunsa ya sauƙe ƙasa, saitin inda night slippers ɗinsa ke aje, sai da ya yi miƙa sannan ya tashi tsaye yana jan wani siririn tsaki, sanye yake da wasu sport wears masu kauri, saboda sanyin da ake a gari, bai fita daga ɗakin haka ba sai da ya ɗauki jacket ya ƙara a kai, sannan ya fito daga ɗakin. Sai da ya ratsa ta cikin ɗan ƙaramin corridor sannan ya shiga ƙaramin living room ɗin dake sama, wanda ya ƙunshi kofofin ɗakuna uku daga cikin biyar da suke gidan.


Daga falon ya buɗe wata ƙofa wadda take manne da stairs, ya sauƙa ƙasa inda babban living room ɗin gidan yake, shi kuma ƙofofi huɗu ne a cikinsa, ɗaya ɗakin Sarah ne, wato maid ɗin dake masa girki da kuma kula da gyaran gida, ɗaya ƙofar ta store ce, ɗayar kuma ta gym, kitchen kuma babu ƙofa, domin marabarsa da falon wata ‘yar gajerar katanga ce, sai kuma ɗaya ɓangaren da galss yake a tsakaninsu. Kai tsaye ya wuce kitchen, inda Sarah ke aikin haɗa abin kari, tana jin shigowarsa ta tsayar da abin da take ta juyo tana risinawa, cikin girmamawa ta masa barka da safiya.


“Me yake faruwa a waje ne?”


Ya cilla mata tambayar bayan ya amsa mata da ƙyar, fuskar nan kuwa a haɗe kamar hadarin dake gaf da sakin ruwa.


“Mik ne ya ƙwace Sir”


Kansa ya girgiza dan ya san hakan ne ke faruwa a wajen, a karo na biyu ya sake jan tsaki, sannan ya nufi outdoor dake cikin kitchen ya fita garden ta ƙofar. Tun daga inda yake ya hango mutum ukun da suke da alhakin kula da Mik ɗin wato dokinsa, suna ta famar ƙoƙarin riƙe dokin amma sun kasa, dan gardama ce da shi kamar uban gidansa, in ba shi ya masa magana ba a irin wannan yanayin da yake ciki ba ya jin maganar kowa.


“Me yake faruwa ne?”


Ya tambaya sanda ya isa wurin, sai da gaba ɗaya suka gaishe shi kafin ɗayan cikinsu ya amsa tambayar tasa.


“Tun jiya da likita ya zo duba shi ya ƙi cin abinci, yanzu kuma da na yi ƙoƙarin masa loma (A cusawa doki abinci a bakinsa ta karfi) sai ya birkice ya fara ƙoƙarin guduwa...”


Suna ba shi ba’asin yana nufar dokin dake ta huci yana buga kofatonsa a ƙasa, babu ko tsoron illar da farin ingarman dokin zai iya masa ya nufe shi.


“Hey! Hey! Kwantar da hankali Mik…”


Ya ƙarasa maganar tare da ɗora hannunsa a gefen wuyan dokin, a hankali ya soma shafa wuyan nasa yana kallonsa da ƙananun idanuwansa. Tun dokin na huci har ya dawo dai-dai, a hankali ya kama wuyan dokin ya haye kansa.


“Bravo good boy”


Ya fada yana shafa kansa.


“Ku je ku ci gaba da aiki Machelle”


Cewarsa ga masu aikin, suka amsa masa sannan suka bar wurin, Ya daɗe zaune kan dokin yana zagayawa a cikin wadataccen garden ɗin dake kewaye da gidan, har sai da ya gaji dan kansa ya sauƙa, sannan ya ƙira mai kula da shi yace ya maida shi wurin da ake killace shi. Shi kuma ya koma cikin gidan, tsakanin shigarsa ɗakinsa da fara ringing ɗin wayarsa ba ace ga wanda ya riga wani ba.


Ko kallon wayar bai yi ba ya nufi jikin wani stand yana cire jacket ɗin da ya saka a saman sport wear'n dake jikinsa, ya rataye jacket ɗin a jiki, sannan ya dawo ya zauna bakin gadonsa, sai a lokacin ya kalli fuskar wayarsa dake ruri a karo na biyu. Hannu ya miƙa ya ɗauki wayar, duk da ya ga cewa Muhibba ce ke inviting ɗinsa voice call through WhatsApp hakan bai sa ya ɗaga kai tsaye ba. Kawai yana riƙe da wayar yana kallon sunan nata kamar mai ƙirga adadin harufan. 


A wannan karon bayan ƙiran ya katse ba ta sake ƙira ba sai ta tura masa da saƙo, ganin shigowar saƙon yasa ya shiga inbox ɗinta. 'Ya Hammad ka ɗaga wayata, wani abu zan faɗa maka game da ciwon Ya Maryam..' shi ne abin da ta rubuto masa, fuskarsa ya haɗe yana tunani kan me take so ta gaya masa game da Maryam? Tunowa da cewar Maryam ɗin ba ta da lafiya ya ba shi damar ɗaga ƙiran nata da ya sake shigowa wayar tasa.


Ya kara wayar a kunnensa bayan ya ɗaga, amma sai ya yi shiru ba tare da yace komai ba.


"Ya Hammad ka san me ya faru yau?"


Muhibba ta fara faɗi, domin ta san in ba ita ta yi magana ba sarkin jin kan da wuya ya fara magantuwa. Hanmad ya tsinkayi tashin hankali a cikin muryarta, dan haka kai tsaye yace.


"Cut the carp! Ta fi zuwa ga gundarin magana"


Muryar nan a dake, babu sautin nishaɗi cikinta ko wani abu mai kama da walwala.


"Jiya Ya Sa'ad ya kai Ya Maryam asibiti wurin likitan ƙwaƙwalwa..."


"What the hell? Uban waye ya ba shi wannan damar?"


Ya katseta tun kafin ta ƙarasa, tuni wani baƙin abu ya soma tasowa daga ƙirjinsa zuwa maƙogwaronsa na ɓacin rai.


"Ubanmu mana? Ka san dai ba zai yi hakan ba tare da izinin Takawa ba..."


"Me likitan yace?"


"Ya ce akwai alamun taɓin hankali tattare da ita, Wallahi ba ka ga halin da ta shiga ba sanda ta ji wannan batun..."


"Shi kansa Sa'ad ɗin ai ba hankali ne da shi ba, da dan har ya ɗauketa ya kaita wurin wani mahaukacin da shi ma bai san kansa ba, ya shatci magana ya gaya muku za ku yarda! Babu gwaji babu komai? Saboda su suka fi kowa hauka?"


Ita dai Muhibba shiru kawai ta yi tana jin wani abu kamar nadamar gaya masa na kamata, dan yanda ya kafa masifa a cikin wayar kai kace Sa'ad ɗin ne a gabansa, duk da faɗa ko cacar baki ba ta taɓa haɗasu ba, magana ma wannan ba ta haɗasu, sai su haɗu a wuri su baje ba tare da wani ya kalli wani ba, duk yadda Takawa da Galadima suka so haɗa kan bayin Allahn nan sun ƙi haɗuwa har yau har gobe.


"Yanzu ni dai ba gaya maka na yi dan ka rufeni da faɗa ba, na gaya maka ne domin a samu mafita"


Muhibba da tsawar da yake mata ke naiman kurmanta mata kunne ta gaya yayin da yake tsaka da balbala bala'in nasa da ya saba. Shiru ya yi yana huci kamar macijin dake gaf da kai sara, ya rintse ƙananun idanuwansa yana murza goshinsa, can kuma ya buɗe idonsa yana sauƙe numfashi da ƙyar, kamar wanda ya kinkimi buhun hatsi.


"Nan da next week nake sa ran zan ɗauki hutun ƙarshen shekara, kuma Nigeria zan zo, idan na zo zan naimi izini a wurin Takawa na taho nan da ita, domin ƙwararrun likitoci su dubata a gano a inahin abin da yake damunta, likitocin Nigeria ub*n me suka sani..."


(In ji Hammad🤥, ba cewar Candy ba ce)


"To Ya Hammad, Allah yasa dai su yarda"


"Suka yarda aka kaita wurin wani mahaukaci ma..."


Ya ƙarashe da tsaki, bai ko bari sun yi sallama ba ya katse ƙiran, gaba ɗaya wannan batun ya dagula masa mood ɗinsa. A ɗaya ɓangaren bayan ya katse ƙiran Muhibba ta sauƙe wayar tata tana binta da harara kamar da aka ce mata ga Hammad ɗin nan, ko da yake in aka ce shi ɗin ne ma ba ta isa haɗa ido da shi da garaje ba, domin bakin rijiya ba wurin wasan yaro ba ne. Sa'ad ne ke sakar musu fuska ita da Aysher, shi yasa suka bi suka raina shi, saboda shi ke musu wasa, amma Hammad ko kallo ba su ishe shi ba ballantana ya musu wasa. A fili ta ja tsaki tana faɗin.


"Masifaffe!"


*Kauyen Yarimaru, Gembu, Mambilla, Taraba state.*


Wasu magidanta ne guda biyu durƙushe a ƙasa, kowanne cikin su biyun ya haɗe hannayensa suna kuka cikin naiman yafiya suke kallon wani mutum dake zaune kan kujera, duk yawan shekarunsu da idan aka haɗa da nasa za su iya haifar ɗa kamarsa, roƙonsu suke cikin naiman sassauci. Tun da ya zauna a kan wannan kujerar tasa ta gado bai ko motsa ba ballantana ya basu damar sa ran yana jinsu ko kuma zai iya yafe musu kamar yanda suke rokon yafiyar tasa. Ɗan ƙaramin littafin “Hisnul Muslim” ne riƙe a hannunsa, a hankali fatar bakinsa ke motsawa yana bin harufan larabcin dake rubece a cikin littafin ɗaya bayan ɗaya yana karantawa hankalinsa kwance, kamar ba shi ne yasa a hukunta magidantan da za su iya haifarsa ba, kuma hukunci mafi ƙasƙanci, domin ƙananun yara ya sa suka zanesu da bulali kamar a makaranta.


“... Mun haɗaka da Allah GURU ka mana rai, ka ƙyalemu haka, Wallahi ba za mu sake kai ƙararka wurin ‘yan-sanda ba!”



Ɗaya daga cikinsu ya faɗi yana kuka wiwi kamar ƙaramin yaro, dan ba ƙarya sun doku kamar jakuna masu taurin kai. Sai a lokacin da ya yi maganar Guru ya samu damar janye idonsa daga kan littafin hannunsa ya ɗorasu a kansu su biyun dake durƙushe gabansa jikinsu yana kyarmar tsoro, littafin ya rufe yana taɓe bakinsa.


“Wa ya gaya muku cewar za ku ci gaba da rayuwa bayan yau? Ai sai kuna raye za ku kai ƙarar tawa ko Tijjani?”


Ya ƙarashe da tambaya yana kallon wanda ya yi wancan furucin, jin batun za a kashesu ya ƙara rikitar da su, dan haka suka ƙara ƙaimi wurin roƙonsa kan ya yafe musu, hayaniyar da suke naiman tada masa da rana tsaka yasa ya toshe kunnensa da hannu ɗaya, sannan ya ɗaga kai ya kalli yaransa wanda kallo ɗaya ka musu za ka musu kuɗin goro ka kirasu da ‘yan daba. Da ido kawai ya yi wa ɗaya daga cikinsu alama, shi kuma ya kalli ƙananan matasan da da wuya za ka samu wanda ya haura shekaru 20 a cikinsu, cike da iko yace.


“Ku ɗaukesu daga nan”


Haka yaran suka kamasu suka ɗaukesu daga wurin, su kuma ba su fasa magiya da naiman a yafe musu ba, duk kuwa da su aka yi wa laifi.


“Me kake so a musu Oga?”


Yaron nasa da alamu suka nuna cewa shi ne na hannun dama ya tambaya yana sunkuyawa a saitin da yake, ajiyar zuciyar kwanciyar hankali ya yi, sannan ya ɗora ƙafarsa ɗaya kan daya, ya buɗe littafin alamun zai ci gaba da karatun da yake.


“Ku kullesu na tsawon kwana uku, bayan ruwa ban yarda a basu komai ba, kwanakin nan ba na jin son a kashe rai, dan haka kawai a sake su bayan kwana ukun, ko ba komai zuwa lokacin na san jikin ta ƙaura yay la’asar”


Maganar ta fito cikin salihin amon muryarsa na masu imani a baka, a zuci kuwa ƙannen shaiɗan. Shi fa har yanzu an rasa a wani state za a aje shi, shin ɗan daba ne ko ko bawan Allah mai imani? Tun da Guru yake a duniya bai taɓa shan ko da sigari ba ballantana aje kan sauran kayan maye, ammam kuma a gaba ɗaya yankin duk wani mai safarar kayan maye to a bayansa yake, babu kalar kayan ta'addacin da ba ya kawowa yankin. Haka kawai idan ta raya masa zai sa a ɗauko matasan cikin gari ya basu kayan maye su sha, da haka da haka har ya janyesu su koma yi masa aiki, irin hakan ce ta haɗosu da ɗan Tijjani.


Lokacin da Tijjani ya samu labarin ɗansa ya fara shaye-shaye tare da tallafawar Guru bai yi ƙasa a gwiwa ba wurin kai ƙararsa ofishin ‘yan-sandan cikin garin Gembu. Aka zo aka kama shi aka tafi da shi can, sai dai kafin su dawo cikin Ƙauyen Yarimaru har Guru ɗin da aka kama domin fuskantar hukunci ya rigasu dawowa, a’a ƙarshe ma a ƙofar gidan Tijjanin suka same shi zaune, har yana tambayarsu sai yanzu suka samu ƙarasowa?


Ba Tijjani da Halliru ne kaɗai suka taɓa shigar da ƙara a kan Guru ba, jama’a da dama sun yi hakan, sai dai ko an kama shi ba ya daɗewa zai fito, saboda yana da ɗaurin gindi a wurin ‘yan siyasar yankin. Ganin cewa doka ba za ta yi aikinta a kan Gurun ba yasa jama’a suka fidda rai a kan lamarin, suka naɗe hannayensu suka koma gefe suka zubawa sarautar Allah ido. Idan ka ga Guru a zahiri za ka iya rantsuwa da sarkin da ya hallici kowa da komai kan bai san yanda ake mugunta ba, kana ganinsa ka ga mutum mai cike da kamala da kuma nutsuwa. Amma a cikin zuciyarsa ban da tarin mugunta da ƙeta babu komai, idan yace zai rantse kan bai taɓa kisa ba za a yarda, domin shi kansa ya san bai taɓa kashe wata rai da hannunsa ba, sai dai yasa yaransa su kashe.


Rayukan da suka salwanta dalilinsa ba su da adadi, goyon bayan ‘yan siyasa da ya samu shi ne ya ba shi ƙwarin gwiwar cin karansa babu babbaka, domin duk aikin da suke so a musu tabbas zai saka ayi, saboda shi ba zai yi da kansa ba, to hakan yasa su ma suka ɗaure masa gindi yake ta’addacinsa yanda ya so, duk da abin na damun jama’ar gari da dama, babu wanda ya isa ya yi magana a kai, saboda in ka ce ƙala to za ka yi ta ranka. A kaf duniya mutum ɗaya ne ke iya takawa Guru birki, kuma shi ne tsohon malaminsa Malam Yakubu.



*Kauyen Kinkin, yankin kabilar Hadzabe, kusa da tafkin Eyasi, arewacin Tanzania, Africa.*


AKIRA POV.


Cikin dajin da ya cika da dogayen ciyayi, akwai wata ƙatuwar bishiyar kuka, wadda aka fafake cikinta ya zamto kamar kogo. Sa’ilin da hasken rana ya ɗaga ya haske ƙofar kogon bishiyar, kai tsaye a kan idonta ya sauƙa ba tare da ɓata lokaci ba ta farka, ta tashi zaune tana hamma, a lokaci guda kuma cikinta ya soma ƙugin yunwa, saurin sauƙe hannayenta da ta ɗaga sama domin yin miƙa ta yi tare da dafewa cikinta dake kiran ciroma-ciroma. Fuska ta yamutsa sannan ta miƙe tsaye, wannan T-shirt ɗin da ta zama kamar tare aka kawosu duniya ce a jikinta, asalin kalar rigar orange ne, amma saboda ba ta samun gatan wanki ballantana ta samu ‘yar uwarta da za a saka yayin da take hutawa yasa ta koɗe ta koma wata kala da ba ta da suna. Bayan T-shirt ɗin babu komai a jikinta sai zanin da suka zaba ɗaurawa bisa kafaɗunsu, sai kuma tarin sarƙoƙin dake wuyanta, da waɗan da ke ƙugunta har da na kai wanda aka haɗa da guntun didigaggen gashin kanta.


A daddafe ta samu ta fice daga cikin kogon, sai ta tsaya a bakin kogon bishiyar dafe da cikinta tana kallon hasken rana da ya ɗaga sosai, duk da tana jin yunwa yanzu ba ta isa ta shiga cikin gari ba. Domin sarkin ƙauyen nasu da kansa ya haramta mata kwana a cikin garin duk ranar asabat, kuma idan garin ranar Lahadi ya waye ba ta da ikon shiga cikin garin sai rana ta tsaya a tsakiya, wato wajejan karfe sha biyu na rana, a cewarsu hakan zai nisantasu daga fushin abar bautarsu. 


Bayan da ta zo duniya mahaifiyarta ta mutu, a ranar kuma jaruman ƙabilar tasu suka tafi wani daji dake kusa da su farauta, kaɗan daga cikinsu ne suka dawo, sauran duk sun yi asarar rayukansu a can, ciki kuwa har da mahaifinsu. Kuma a washe garin ranar aka kaita gaban abar bauta domin raɗa mata suna, a yadda al’adar garin take, za a aje jaririyar da ake son sanya mata suna a gaban abar bautar, sannan malamin ɗakin bautar zai zauna da yashi a gabansa ya yi rubuce-rubece na taurarin haihuwar yarinyar, bayan haka za a tsaya a ga ikon abar bauta, domin ita da kanta za ta zana sunan da ya dace da yarinyar a kan yashin nan da aka rubuta taurarin haihuwarta.


Sai dai ita Akira nata sunan ya zo da tangarɗa, a’a maimakon ma su ga suna sai suka ga an rubuta tsinuwa, to daga nan ne fa abin ya samo asali, sai aka zauna aka fara bincika yarinya, tun da ake haihuwa a ƙabilar Hadza ba a taɓa haihuwar yarinyar da ta kai Akira baƙi ba, baƙa ce ƙirin babu ko da ɗison fari a kan fatarta, sannan ba a taɓa haihuwar jaririyar da idonta yake wata kala ba sai ita, su dai sun saba ganin ƙwayoyin idon jama’arsu a matsayin baƙaƙe ko kuma brown, amma ita nata idon kalar na mage ne. gaba ɗaya sai aka tattara hujojjin hallitar da yarinyar ta zo da su, da kuma abubuwan da suka faru ranar da aka haifeta, sai suka fitar da hukunci kan tabbas wannan yarinya da aka haifa musu ba komai bace face tsiniwar abar bautarsu a kansu. A wancan lokacin sun so kasheta, Amma Nikamba yayanta shi ne yace a ba shi ƙanwarsa, kada su kashe masa ita domin a yanzu bayan ita ba shi da kowa, tun da iyayensu sun mutu. Da ƙyar da fama suka yarda suka ba shi jaririyar, shi da kansa ya saka mata sunan AKIRA wanda a yaren Hadzane AKIRA na nufin (haske). 


Tun a wancan lokacin wannan dokar ta hana Akira kwana a cikin ƙauyen duk ranar asabat ta soma. Domin ranar Asabat rana ce wadda suke gudanar da sha’anin bautarsu a cikinta. Hakan yasa ba su bari ta zauna musu a gari gudun jawo masifa. Har kwanan gobe jama’ar ƙauyen ba su ɗauketa a matsayin ɗaya daga cikinsu ba, kawai dai tana rayuwa a cikinsu ne, amma ko da yaushe fatansu shi ne ganin barinta duniya, har yanzu ko wani iftila’i da zai faɗo musu za su danganta shi da ita ne, tun ba ta da wayo har ta zo ta san me hakan ke nufi, tun tana jin zafin abin har ya zame mata jiki.


Wani daddaɗan kukan tsuntsu ne ya karaɗe wurin da take, hakan yasa ta miƙe tsaye baki buɗe tana dariya, kanta ta ɗaga sama tana naimansa a kan bishiyar kukar, tana ganinsa ta ƙara tintsirewa da dariya, tsuntsun ya saki kukansa mai daɗin sauraro, ita ma sai ta ci gaba da kallonsa tana tsuke bakinta, kafin a hankali bakinta ya fara fitar da wani sauti da ya yi kama da na tsuntsun, idan ya yi ita ma sai ta yi, sai kuma ta yi dariya, ba tsuntsun kaɗai ba, a wannan wurin da take kwana ta saba da dabbobi da dama, wani lokacin ko ba ranar asabat ba ta kan zo ta kwana, kwanan wurin ma ya fi mata daɗi, tun da cikin ƙauyen ba daɗinsa take ji ba. Tun tana jiran zuwan Nikamba ɗauke da abin da za ta karya har ta fidda rai, ta ma yi fushi da shi, dan ita ba haka suka saba ba, duk sanda za ta kwana a cikin dajin sassafe zai zo ya kawo mata abinci ta ci, amman yau ga shi har ranar na shirin zuwa tsakiya bai zo ba.


Cikin jin haushin biris da ɗan uwan nata ya yi da ita ta nufi cikin dajin, ƙafarta ko takalmi babu, tana tafe tana wata waƙa cikin yaren nasu na Hadzane. Duk in da za ta ga wata dabba babba ko ƙarama to za ta tsaya, sai ta gama shaɗancin kuma sai ta ci gaba da tafiya, da haka har ta iso wurin da wasu ciyayi suke, tsugunnawa ta yi ta kama ƙasan ciyayin ta soma tsigosu daga cikin ƙasa, idan ta ciro kuma sai ta cire jijiyar ciyawar, ta cillar da ganyen, domin ya zama mara amfani a ganinta. Sai da ta ciro wanda ta san zai isheta, kafin ta tare jijiyoyin tsirran da ta cire, ta kama wata bishiya dake wurin ta hau, ta zauna tana kallon dangin jakin daji (Zebra) suna shan ruwa a wani ruwa mai gudana kusa da inda take, zamanta ta kuma gyarawa za ta fara cin jijiyar ciyayin da ta ciro a ƙasa ta ji Nikamba na ƙiran sunanta.


“Akira!”


Banza ta masa ta fara cusawa a bakinta tana taunawa da ƙyar, dan da can ma idan ba ta samu abin ci ba su take zuwa ta ci, ba ita kaɗai ba, hatta jama’ar ƙauyen nasu na cin jijiyar tsirran.


“Akira bu ta shay” (Akira sauƙo)


Cewar Nikamba sanda ya iso jikin bishiyar da take kai, kanta ta sauƙe ƙasa ta kalle shi ta tsakiyar ƙafafunta, ta haɗe rai tana kumbura bakinta, irin abin da ta saba ke nan idan ranta ya ɓaci.


“Bikakke buta shay” (Ba zan sauko ba)


“Bu ta shay ji bu” (Ki sauko na ce)


Sai ta girgiza masa kai, ganin da gaske ba za ta sauƙo ɗin ba yasa ya kama stem ɗin bishiyar da take zaune a kai, kawai ya soma jijjigawa. Ihu ta ƙwala tare da sakin abin da ke hannunta ta rungume bishiyar daga sama tana kuka.


“Nikamba ka bari! Zan sauƙo, zan sauko”


Ta faɗa muryarta na shaida tsoron da take ciki, Nikamba ya tsaya kamar yadda ta buƙata.


“Taho”


Ya ɗaga hannayensa sama ya miƙa mata, ta kalle shi wasu guntayen hawaye kwance a kuncinta, a hankali ta kama ta sauko, ya riƙota ya ƙarasa sauƙo da ita.


“Yunwa kike ji?”


Ita ce tambaya ta farko da ya fara mata bayan ta sauƙo.


“A’a”


Ta ba shi amsa har yanzu da guntun jin haushinsa a muryarta, dariya kawai ya yi, dan yasan ƙarya take.


“Da gaske ba kya jin yunwa?”


“Eh...”


Ba ta gama amsawa ba cikin ta ya yi wani uban ƙugi, ta yi sauri ta dafe shi kumbura bakinta, Nikamba ko dariya kawai ta ba shi.


“Ga abincinki nan, sai da na tsaya na dafa miki shi, shi yasa na makara”


Ya ƙara she yana miƙa mata wani abu mai kamar kwano, wanda aka yi shi da duma, Akira ta karɓa ta buɗe, take ta washe baki ganin kayan cikin dabba a dafe, bayan ruwa da gishiri babu komai a cikin girkin.


“Zauna ki ci... idan kin gama za mu je kogi”


Ta gyaɗa kai tana zaunawa a ƙasa, sannan ta fara ci a da sauri-sauri, duk kuwa da zafin da yake da shi.

____________


_Wannan Guru ɗin, ya zo da nasa sabon salon gadarar, bari mu zuba ido mu sha kallo, domin har yanzu ba mu je ko ina ba…_


_Sannan kar a manta da KAWA ZUCI paid book ne_


#SalmaAhmadIsah

#MiniCandy

#Bahadejiya

#KawaZuci

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.