Free chapter · Read without an account

10

by Salma Ahmad Isah · KAWA ZUCI

*KAWA ZUCI*


*©SALMA AHMAD ISAH*


*10*


*PSG (Paris Saint-Germain) Training Center, Camp des Loges, Paris.*


HAMMAD POV.


Gaba daya ‘yan wasan club ɗin ne ke training a cikin ƙaton training ground ɗin dake centern, duk sun bazu a ko ina suna atisaye bisa jagorancin Coauch ɗinsu. Tsaye yake a cikin filin, sanye cikin baƙin jogger trouser da farar jersy irin wadda ke jikin sauran abokan wasan nasa. Sai woollen hat dake kansa ya naɗa scarf a wuyansa, saboda sanyin da ake a gari, shi da abokinsa Henri BB suke nasu training ɗin.


Da ƙarfi Henri ya buga ƙwallon da suke passing da ita, tana isowa inda yake ya tareta da ƙafarsa ta hagu, ya ɗora ƙafarsa ta dama a kan ball ɗin, ya yi knee block ya sakata a tsakiyar kafafunsa biyu, sannan ya yi slap ya haɗa da Rocket launch ta hanyar ɗagota da ƙafarsa ya cafeta da hannunsa ya cilla sama, kafin ta faɗo ƙasa ya sa ƙafarsa ta hagu ya bugata da ƙarfi, bisa tsammanin za ta isa ga BB, sanya hakan a cikin tunaninsa yasa dawowar ball ɗin ya zo masa a bazata, dan bai ankara ba sai da ta dawo ta daki ƙirjinsa da mugun ƙarfin da saida ya faɗi ƙasa. Faruwar lamarin tasa hankalin kowa ya dawo kansu, Hammad bai damu da ya kalli waye ke da wannan aikin ba, dan ya san duk cikin club ɗinsu mutum ɗaya ne zai aikata hakan.


Nicolas Wande! Kuma yana ɗaga kansa suka yi ido huɗu da shi, tsaye yake a kansa yana murmushi, shi dai a duniya ya rasa abin da ya tarewa bawan Allahn nan, amma haka kawai ba ya sonsa, tun sanda ya fara bugawa PSG ƙwallo har zuwa yanzu da ya shafe shekaru uku a Paris ba su taɓa dai-daitawa da Nicolas ba, tun abin na iya tsakaninsu har ta kai ga kowa ya fara fahimtar hakan. Shi dai Hammad bai ga dalilin da zai sa Nicolas ya tsane shi ba, dan ya san idan ɗaukaka ce Nicolas ya fi shi, tun da shi ne Captain ɗinsu, a cikin club ɗin ma mutum nawa ne suka fi shi suna? Amma cikinsu babu wanda ya tsokale masa ido sai Wakili. Da farko ya alaƙanta hakan da kasancewarsa sabo a cikinsu, amma daga baya ya sauya tunani, yanzu tunani yake kamar suna samun saɓani saboda shi baƙin fata ne, kuma ɗan Africa, sannan musulmi. Rai ya haɗe sanda Nicolas ɗin ya tsugunna yana miƙa masa hannunsa alamun ya kama zai miƙar da shi. Henri ya kama kafaɗunsa ya miƙar da shi.


“Ba ka ji ciwo ba ko Wakili?”


Ya girgiza kansa yana kallon Coauch ɗinsu dake musu magana.


“Me ya faru ne?”


“Ina gwada kaifin tunanin ɗan wasanmu ne?”


Nicolas ya yi caraf ya amshe yana murmushi.


“To da kyau yara! Maza a ci gaba”


Nicolas ya sake kallon Hammad har yanzu yana wannan murmushin.


“Ba ka da kula Wakili! Yana da kyau ka ƙara kula! Hmm?”


Ya ƙare da tambaya yana miƙa hannunsa zai taɓa kafaɗarsa Hammad ya kauce. Nicolas ya dunƙule hannunsa da ya miƙa yana wani murmushin, sannan ya barsu nan tsaye shi da BB.


“Ba ka ji rauni ba ko Wakili?”


BB ya sake tambaya yana duba hannunsa da ya rike.


“Ban ji rauni ba”


“Sannu”



ZAHRA POV.


Adai-daita sahun da suka hau tun daga Yalwawa ya taka birki a kofar wani gida mai kyau dake cikin unguwar Mobile Base. Ita da kawarta Saddiqa dake cikin napep ɗin suka fito a tare, Saddiqa ce ta sallame shi, sai da mai napep ɗin ya tafi sannan suka fuskanci gidan da aka sauƙesu a gabansa.


“Kamar nan ne gidan ko?”


Saddiqa ta tambayeta tana leƙe-leƙe a ƙofar gidan, wai ko za ta ji hayaniya a ciki.


“Wannan gidan bai yi kama da gidan da ake taron suna ba Saddiqa”


“Haka ne, to ya za mu yi ke nan?”


“Bari na ƙira Zainab ɗin, sai mu ji”


A cikin jakar hannunta ta fito da wayarta ƙirar Tecno Smart5, lambar ƙawarsu Zainab da ta gayyacesu zuwa taron sunan yayarta da ake a yau ta lalubo, sannan ta aika mata kira.


“Har kun zo ne?”


Da ƙyar Zahra ta tsinkayi muryar Zainab ɗin a cikin tarin hayaniyar bikin suna, kuma jin hakan ya ƙara tabbatar mata da cewa gidan da suke tsaye a gabansa yanzu ba shi ne gidan yayar Zainab ɗin ba.


“Eh mun iso unguwar, napep ya sauƙemu a ƙofar wani gida mai farin fenti”


Ta bata amsa da ɗan karfi, dan ita kanta tana jin hayaniyar sosai, ballantana kuma ita Zainab ɗin dake cikin hayaniyar.


“Na gane gidan, ku tsaya a nan bari na sa a muku iso”


“Wa za ki turo?”


“Ku dai ku jira mana, waye zai saceku da girmanku?”


Zahra ta yi murmushi.


“To muna jira”


“Me tace?”


Saddiqa ta yi saurin tambaya sanda ta sauke wayar daga kunnenta.


“Ta ce mu tsaya a nan za ta turo wani ya mana iso zuwa gidan”


“Wallahi da ma kin ce ba ki yarda ba, sarai kin san halin Zee da shiririta, yanzu haka sai ta mance da lamarinmu”


Zahra ta kuma yin murmushi tana girgiza kai, sannan ta samu wani dakali ta zauna.


“In ban yarda ba me kike so na ce mata?... tana cikin hidimar suna dole a mata uziri”


Ita dai Saddiqa abin bai mata ba, dan haka ba ta sake cewa komai ba ta zauna kusa da Zahran, suka shiga hirar form ɗin naiman gurin karatu a poly Dutse da Zahra ta cike. Sai da suka kwashe kusan minti goma suna zaune a wurin, tun Saddiqa na haƙuri har ta fara ƙorafi, tsaki ko ta yi ya fi cikin kwando.


“Dan Allah Zahra sake ƙiranta, wallahi yanzu haka ta manta da lamarinmu”


Cewar Saddiqa da ta ɓata rai.


“To miye abin ɓacin rai? Cool off bari na sake ƙiranta”


Ta ɗauki wayarta da zummar sake aikawa Zee ɗin ƙira dai-dai da fakawar wata mota a inda suke. Sai da suka ƙarewa motar kallo kafin Saddiqa ta kalli Zahra.


“Ko dai su suka zo ɗaukan namu?”


Kafin Zahra ta bata amsar tambayar da ba ta sani ba, aka sauƙe glass ɗin gaba na motar da ya kasance baƙi, wasu samari biyu suka bayyana a cikin motar, ɗaya a mazaunin direba ɗaya kuma a na me zaman banza. Wanda ke mazaunin me zaman banzan tun da suka sauƙe glass ɗin yake jifansu da murmushi…


“Wacece Zahra a cikinku?”



SA’AD POV.


Kasancewar ya ga babu wani sarki sai Allah yasa ya fara shirye-shiryen komawarsa zuwa Abuja. Ranar talata ya yanke shawarar kaiwa abokinsa Mubarak ziyara, abokinsa ne tun na tasowa kuma har kwanan gobe suna nan tare. Tun da ya zo garin sau ɗaya suka haɗu, ga shi nan da kwana biyu yake son komawa Abuja. Motar Aysher ya ara, duk da sharuɗan da aka dinga kafa masa a kan motar bai fasa ɗaukan motar ba, ba wata tafiya mai tsayi ya yi ba sai ga shi a unguwar su Mubarak ɗin.


Yana isa gidansu ya aje motar da ya zo da ita a harabar gidan, sannan ya fito ya nufi part ɗin Mubarak kansa tsaye, tun da gidan ba baƙonsa ba ne. A ɗaki ya samu Mubarak ɗin zaune yana amsa wayar da kana ji za ka san cewa waya ce da ta shafi wurin aikinsa. Ba tare da yace masa komai ba ya nufi gadonsa ya zauna yana cire safar ƙafarsa, zuwansa ya sa Mubarak gajarce wayar da yake domin ya fuskanci abokinsa.


“Ai na ɗauka har ka tafi ba za mu sake haɗuwa ba”


Mubarak ɗin ya fara da wannan bayan ya sauƙa a layi, ba tare da Sa’ad ya kalle shi ba ya miƙa hannu ya buɗe side drawer ya fara laluben shisha.


“Kai ma ka san babu yadda za ai na tafi ba tare da na zo na maka sallama ba”


“Sallama? Ba ka na da sauran sati ɗaya ba?”


“Mts manta kawai, Takawa ne ya rage mini kwanakin hutun”


Mubarak ya yi ‘yar gajerar dariya.


“Dai-dai ke nan, ai Wallahi Sa'ad da ace kai da Hammad ragon uba kuka samu sai abin da hali ya yi, dan duk watsewa za ku yi, to da Allah ya so ku da rahama sai ya haɗaku da jajirtaccen uba, wanda zai yi maganin iskancinku ba tare da rai ya ɓaci ba!”


Sa’ad bai tanka masa ba ya ci gaba da lalube.


“Wai binciken me kake mini ne? ko ka bani ajiya?”


“Shisha nake nema”


“Ina taka?”


“Tawa ba caji ka gaya mini inda take please”


“Babu”


Wani irin kallo Sa’ad ya masa na ka raina mini wayo.


“Babu?”


“To tun da ba ka yarda ba ka ci gaba da dubawa in za ka samu”


A mamakance Sa’ad ya dawo kusa da shi ya zauna yana ƙare masa kallo.


“Me yasa ka daina sha?”


“Budurwata ce ta nuna cewa ba ta so, shi yasa na wastar da ita”


Wata irin dariya ta shaƙiyyanci Sa’ad ya saki.


“Miye abin dariya a ciki? Kai ma wata rana za ka daina”


“Na daina? In your dreams Man!”


Mubarak ya taɓe bakinsa alamun kai ka sani, Shi dai Sa’ad ya kasa yarda da abin da Mubarak ɗin yace masa, dan ya san halin Mubarak sarai idan ya saba da abu duk nacin mutum bai isa ya raba shi da shi ba, to ya za ayi ace wata budurwa ta sauya shi, ai abin ya wuce tunani.


“Taron me ake a cikin gidan ne?”


Ya tambaya ganin warmers da container na abinci a ɗakin.


“Hauwa (yayarsa) ce ta haihu, kuma yau suna”


Sa’ad ya jinjina kai yana buɗe wata container da ya ɗauka, wanda ke ɗauke da cake ya ɗauka me isarsa ya dawo ya zauna ya fara ci.


“So ya aikin naka yake tafiya?”


Mubarak dake latsa wayarsa ya cilla masa tambayar.


“Ba daɗi Mubarak… Wallahi kwata-kwata aikin jarida ba nawa ba ne, ba ƙaddarata ba ce, amma ƙarfi da yaji Takawa ya cuso mini shi cikin tsarikana, kuma babu yanda na iya dole na karɓa… Duk wayewar garin duniya idan ina workout a unguwar da ya kama mini haya sai na wuce ta Kofar Wakili Motors, kullum ganin wurin ƙara saka mini son aiki a wurin yake, kullum zan wuce sai na yi addu’a Allah ya cika mini burina na zama Manager'n kamfanin nan, har na fara tunanin da gan-gan aka kama mini gida a unguwar nan, dan kawai na riƙa kallonsa yana mini ƙwalele”


Mubarak ya yi dariya.


“Sa’ad! Takawa ya yi iya abin da zai iya a kanka, ya baka dama mai kyau wadda idan ka damata za ka mallaki abin da kake buri, kai ne ka sa wasa da shiririta a lamuranka!”


“To wai ni dan Allah me yasa ba za a bani aikin nan ba? Tun da akwai damar hakan, kawai so ake sai na wahala”


Mubarak ya girgiza kansa.


“Manufar Takawa a kanka ba ta shan wahala ba ce, so yake ka san zafin naiman kuɗi da kanka, ka san wahalar dake tattare da samun halal kafin ya baka ragamar wahalarsa ta tsawon shekaru, Wallahi da ace ni ne a matsayinsa zan yi same thing, domin babu yanda za ai na ɗauki ragamar kamfani guda na bawa wanda bai san zafin naiman kuɗi ba”


Sa’ad ya yi shiru, dan ba shi da ta cewa kuma. Wayarsa da ta soma ruri ya kai hannu ya ɗauka, ganin sunan ɗaya daga cikin ‘yan matansa yasa ya aje cake ɗin dake hannunsa ya ɗaga wayar tare da karawa a kunnensa.


“Hello Baby”


Mubarak ya kalle shi, shi kam yana mamakin adadin Babies ɗin da Sa’ad yake da su, ‘yan matan Sa’ad sun fi a ƙirga, ga shi da farin jini kamar aljanna, da wuya yace yana son budurwa ta ƙi amince masa, wata ƙila dan yana da kyau ne, wata ƙila kuma dan yanda yake kashewa ‘yan mata kuɗi ne, amma shi dai Mubarak zai iya rantsewa kan duk cikin tarin ‘yan matan nan babu wadda Sa’ad ke wa son gaskiya.


“Ok nawa ne?”


Ya tambaya kana ya yi shiru yana sauraron bayanin da ake daga ɗayan bangaren.


“Dubu casa’in da biyar ai ba yawa, ki turo mini account details naki, insha Allah yanzu zan saka miki su”


Ya sake yin shiru yana murmushi, kafin ya ce Bye tare da sauƙe wayar, yana ɗagowa suka haɗa ido da Mubarak.


“Ita dubu casa’in da biyar ɗin ta miye?”


“Anko”


Ya ba shi amsa kai tsaye yana latsa wayarsa.


“Naira dubu ɗari ba dubu biyar za ka bawa budurwa saboda anko kawai?”


Ya jinjina masa kai hankali kwance.


“Dubu ɗari ma zan tura mata, wata kila daga wannan ita ma ta ci rabonta”


Jin hakan yasa Mubarak ya yi murmushi yana ɗaukan cup ɗin da ya zuba kunu a ciki.


“Rabuwa za ayi da ita ke nan?”


“Sai ka tambaya ma? Yarinyar ta fiya roƙo, ni kuma ba na son hakan”


Mubarak ya sake sakin wani murmushin.


“Dan Allah Sa’ad yaushe za ka yi wa kanka karatun ta nutsu ka daina wannan albozarancin da kuɗi, ka daina kula ‘yan mata barkatai”


Sai ya aje wayarsa bayan ya yi transfer na kuɗaɗen da ya ambata.


“Wallahi komai lokaci ne Mubarak, ni kaina na san tara waɗannan ‘yan matan ba rayuwata bace, kawai dai har yanzu ban samu wadda zuciyata ta kwanta a kanta ba ne, amma ka san an ce mai naima ba zai rasa ba, wata ƙila mu dace a nan gaba”


Ƙofar ɗakin da aka ƙwanƙwasa ne ya katse hirar tasu, Mubarak ya tashi ya buɗe kofar.


“Mummy?”


Ya faɗa ganin mahaifiyarsu tsaye a bakin kofar.


“Na’am, kai da waye a ciki ne?”


Ƙofar ya wangale mata ta ga Sa’ad dake zaune yana cin cake, shi ma kuma ganinta yasa ya miƙe yana gaisheta.


“lafiya ƙalau Sa’ad, ya wurin Ammin taka?”


“Tana nan lafiya”


“To in ka koma ka ce ina gaisheta”


“Insha Allah za ta ji”


Mummyn Mubarak ta kalli ɗanta.


“An rasa wanda zai kai kajin can, idan babu inda za ka fita ka zo ka kai musu”


“Ah ba inda zan je, bari na kai musu kawai”


“To suna kitchen, bari na saka Taladi ta kawo maka su”


“To Mummy”


Sai da ta juya sannan shi ma ya dawo ɗakin, ya shiga naiman key'n motarsa.


“Ina kuma za ka je?”


“Gidan Hauwa, wai kaji ne ba a kai musu ba”


Mubarak ya amsa masa sanda ya samo key'n.


“To mu je tare”


“OK”…


----------------------

_Me kuke ganin zai faru a wannan tafiyar?_


#SalmaAhmadIsah

#MiniCandy

#Bahadejia

#KawaZuci

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.