Free chapter · Read without an account
Chapter 2
*ZAWAJUL MUWADDA*
Daga alƙalamin
_Sarat Alƙasum (Mom Nusaiba)_
_(Labarin Sidra)_
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
Only N500
WhatsApp number +966577675904
*Shafi na* 2️⃣
Gudu suke amma gani yake kamar ba sa yin sauri, fuska ɗauke da damuwa ya kalli fuskarta da ta yi faca-faca da jini duk sai ya ji jikinsa yana ƙara mutuwa, sosai yake jinjina rashin mutumci irin na abokin nasa ya kaɗe yarinya amma ya ƙi a saka ta a motarsa a kaita asibiti, ɗan muskutawa ya yi ya zaro hankacip baƙi mai ɗan girma ya tallafo ta yana ƙoƙarin goge mata ya ji an riƙe hannunsa hannun ya bi da kallo cike da mamakin ɗansandan.
“Kar ka sa hannunka a wajen ciwon saboda za a bincika komai, ko kaine ka kaɗe ta?”
Girgiza kai ya yi cike da takaici taya duk jikinta ya ɓaci amma a hana shi goge mata fuska? Ɗaure fuska ya yi kamar wani boss ya dawo da kallon shi kanta ya shiga goge mata fuskar, ganin ya ƙi bin abin da ya ce mishi sai ya rabu da shi yana kallo ya goge mata jinin.
Suna isowa asibiti da kanshi ya fito da ita suka shiga ciki da sauri har yana haɗawa da gudu, kafin ya ƙaraso ciki nurses suka tare shi da gadon ɗaukar marassa lafiya suka amshe ta, bin bayan su ya yi har ɓangaren emergency suka shigar da ita cikin ɗakin, sai da wata nurse ta ce “Am yallaɓai ka yi haƙuri ka jira mu a nan ko ka samu waje ka zauna.”
Bai ce mata komai ba ya juya ya isa wajen da aka tanada domin masu jira ya zauna a hankali idanuwansa a kan ɗakin. Yana nan zaune abokinsa ya iso yana wani ciccin magani, zama ya yi cike da ɓacin rai ya ce “Amma dai kai David ba ka da hankali, yanzu a kan wannan ɗan abun ne ka sa za mu yi lattin zuwa waje mai muhimmanci? Ka tashi mu tafi zan ba wa 'yansanda kuɗi za su ji da komai, in ya so daga baya mun dawo.” Ya faɗa yana saka glass.
Mugun takacin shi ne ya rufe David ya miƙe tsaye ya kama hannunsa suka wuce, bai tsaya ko'ina da shi ba sai in da ya paka motarsa ya sake mishi hannun, huci mai zafi ya yi idanuwansa sun kada sun yi jajur saboda ɓacin ran da yake ciki ya nuna shi da hannu, so yake ya mishi magana amma ya kasa sai huci yake yana hura hanci sama.
Tsaki ya yi ya ce “Aikin banza ka fara halin naka ko? Kai ga ka shugaban masu tausayi na duniya, dalla can malam ka shiga mota mu wuce ka san dai jiran mu ake ko? In so samu ne ma ƙarfe 7:30 a ce mun je wajen nan.”
Sai da ya yi ajiyar zuciya ajere har sau uku sannan ya haɗiye yawu da kyar har yana haɗa wa da runtse ido, gyara tsayuwa ya yi sai a lokacin ya ji zai iya yin magana.
“My friend kana da problem babba ba ƙanƙane ba, ka buge yaro ka ji mishi ciwo amma ko a jikinka saboda ba ka da tausayi, ni babu in da zan je sai yarinyar nan ta farka mun kaita gidansu in yaso daga can sai mu wuce, in kayi wani abun kana ba ni mamaki Sayyid ba sai ka kira su ka faɗa musu mun samu accident a hanya ba su jira har mu gama mu je, idan kuma ba za ka tsaya ba ka tafi sai na hau motar haya na je.” Ya ƙarashe maganar yana juyawa zai koma ciki.
Da sauri Sayyid damƙo hannunsa ya juyo a fusace zai yi magana ya yi saurin faɗin “Okay naji mu je.”
Harara ya aika mishi sam ya tsani wannan ɗabi'ar ta abokinsa ta rashin tausayin talaka, shima a nashi ɓangaren haushi ya cika mishi zuciya a kan abin da David yake shirin aikatawa, duk ya ɓata mishi plan ɗinsa wanda ya kwashe lokaci mai tsawo yana jiran zuwan sa.
Duk abin da suka yi a gaban idon 'yansandan da suke tare da su, sosai suka y8 mamakin jiji da kan Sayyid.
Ana kiran sallar Isha'i aka buɗe ƙofar ya tashi tsaye yana jiran Doctor ta ƙaraso, tana isowa ta dube shi ta ce “Kaine Yayanta ko mahaifinta?”
Girgiza kai ya yi ya ce “Yayanta ne.”
“Okay to ka biyo ni office akwai abin da nake son faɗa maka game da ƙanwarka.”
Sayyid ya yi saurin faɗin “Kinga Doctor ba yayanta ba ne bige ta muka yi da mota shi ne muka kawo ta asibiti, bai ma taɓa ganin ta ba k...”
Kallon da ya auna mishi ne ya sa shi yin gum da bakinsa ƙarshe ya koma ya zauna ya ci gaba da latsa wayarsa.
Suna shiga sai da ta gama rubuta duk abin da take son rubutawa sannan ta ɗago ta kalle shi, shi kuwa duk ya tattara nutsuwarshi ya miƙa mata domin ya ƙagara ya ji a wani hali ɗiyar mutane take ciki.
“Mun tsayar da jinin ba ta bugu ba sosai sai dai abin da na gani bayan wannan ya matuƙar ba ni mamaki da al'ajabi.” Ta numfasa sannan ta ɗora, “Zuciyarta ce ta buga da ƙarfi sanadin tsoro mai tsanani da ya shige ta, shin ko za ka faɗa min kafin ta bugu ka ganta cikin firgici ne?”
Dogon numfasa ya ja sannan ya ce “Doctor a gaskiya ban san abin da ya faru da ita ba kafin ganin da na ta mata a sume, hasalima ban san abokina ya kaɗe ta ba saboda na saka eapis a kunne ina jin waƙa, da naji ya ja birki ya tsaya na ɗauka ko wani abu ne zai yi shi ya sa ban ɗago kai ba na ci gaba da abin da nake, sai da ga mutane na wuce na ɗago na ganshi a tsaye gaban mota na fito dan na ga me yake faruwa, shi ne na ganta kwance jini na zuba ta hanci da goshinta..” Nan dai ya sanar da ita har 'yansandan da suka biyo su.
Jinjina kai ta yi ta ce “To lalle muna buƙatar ganin iyayenta domin sanar da su abin da ke damun yarsu kar su rasa ta..”
“No problem ki sanar da ni.”
Ganin yadda ya canja fuska zuwa ta tausayi ya sa Doctor gyara zama ta cire medical glass ɗin da ke manne a idonta ta aje a gefe tare da haɗe hannayenta waje ɗaya tana murza su sannan ta ce “Wannan yarinyar da kake gani jininta ne ya hau sosai sakamakon zurfin tunanin da take, idan aka yi wasa za ta iya samun babbar matsala ya kamata a kula da rayuwarta, tana buƙatar hutu ba za mu ba ku sallama ba yau sai gobe zuwa da rana in mun ga yanayin jikin nata, sannan ga wannan a je a sayo waɗannan magungunan muna buƙatar su.” Ta miƙa mishi takardar ya amsa ya karanta ya gani, godiya ya mata sannan ya miƙe ya fita.
A bakin ƙofa suka haɗu da ɗansanda ya kalle shi da kyar sannan ya yi gaba shi ma ya mara mishi baya. Sai da ya sayo maganin ya kai musu sannan ya dawo wajen yansanda nan ya sanar da su abin da doctor ta faɗa mishi, babban cikin su ya gyada kai ya ce “Za a samu mutum ɗaya ya zauna har goben, sai dai ina son magana da ku duka biyun.”
Hannu ya zufa a aljihu ya zaro wayarsa ya ga kira sama da goma, tsaki ya ja ya nemo number Sayyid ya danna mishi kira, bayan ya ɗauka ya ce “Ka fito ana neman ka.”
Bai ce komai ba ya katse kiran ya fito daga mota ya nufo in da suke.
“Waye a cikin ku yake jan motar?”
Cike da gadara Sayyid ya nuna kanshi ya ce “Ni ne nan.”
“Ina kake kallo har ka bige yarinya?”
Haɗe fuska ya yi ya ce “Ita ta kawo kanta saboda tun daga nesa na dinga mata hon amma ta ƙi matsawa har na zo na bige ta, ta gode wa Allah ma da ba ta karye ba a ƙafa.”
Cike da mamaki ya sake jefo mishi wata tambayar, “Ya sunanka ?”
“Sunana Sayyid Alhaji Sabo.”
Waro ido ɗayan ya yi ya jinjina kai lalle dole ya musu gadara, kafin ma ya sake magana Sayyid ya fito da ɗaurin rafa guda uku ya miƙa musu ya ce “Ranka ya daɗe don Allah ku amshi wannan duk abin da aka buƙata a mata, goben za mu dawo saboda yanzu haka mahaifina sai kirana yake yana tambayar a ina muke, yau din nan ya dawo daga Dubai ina son na ganshi kafin nima jibi na wuce.”
Amsa ya yi hakan ya sa ya ji daɗi ya kama hannun David suka nufi mota dan kar ma ya ce wani abu, har ya tada motar ɗaya ya isa da sauri ya ce “Ba ku bayar da number ku ba.”
Number David Sayyid ya zano musu sannan ya ja motar suka tafi...
A can gidan su Sidra kuwa Inna ce zaune ta cika ta yi fam, gefe ɗaya Safwan ne zaune ya rafka tagumi yana kallon Suwaiba tana cin shinkafa da miya sai haɗiyar yawu yake cikinsa sai kuka yake. Harara Suwaiba ta aika mishi ta juya ta janyo takalmi ta wurga mishi ya same shi a fuska, da sauri ya dafe gefen fuskar yana shafawa ta jimƙi ƙasa ta watsa mishi, Inna ta kalle su ta ce “Ɗiyan mayya abincin ma ba za ka barta ta ci cikin salama ba sai ka ƙura mata wannan idanuwan naka irin na uwarka? To matsa ka ba ta guri kafin na tashi na wuce fushina a kanka.”
Tashi Safwan ya yi da kyar ya koma can gefe ji yake kamar ya warce abincin Suwaiba, rabon shi da abinci tun tuwon da aka ba su da suka dawo daga school. Ya kai hannu ya goge hawayen da suka zubo mishi murya na rawa ya ce “ Anty Suwaiba don Allah in zo ki dakeni ki ba ni shinkafar? Yunwa nake ji.”
Wani irin kallo ta jefa mishi wanda ya sa Safwan yin ƙasa da kai yana riƙe ciki, tsaki ta buga ta ce “Zo Wallahi sai na maka dundu sau biyar kafin na ba ka loma ɗaya, idan ka jure na maka guda goma zan ba ka duka abincin.” Ta faɗa tana hura hanci, shi kuwa saurin goge hawaye ya yi cikin jin daɗin za ta ba shi abinci a ransa ji yake indai za ta ba shi abincin to ta mishi dundu ashirin ma. Gaban ta ya matso Inna ta yi saurin ɗauke shinkafar ta ƙunduma mishi ashar ta ɗora da cewa “Kai ba ka isa ba fa ka ci shinkafar nan tun da ba malam ya saya ba, babu ko biyar ɗinsa a ciki.”
Amshewa Suwaiba ta yi tana dariya ta miƙa mishi jiki na rawa ya amsa, har zai kai loma ta riƙe mishi hannu ta ce “Ban dake ka ba shi ne za ka fara cin abincin.”
Tashi ya yi ya juya mata baya ya runtse ido yana jiran saukar duka, Suwaiba ta dunƙule hannu za ta zuba mishi ƴar karamar wayarta ta fara ringing, hakan ya sa ta miƙe ta ce “Kai ɗauke abincin ka cinye ba zan dake ka amma za ka je makota ka nemo mini ruwa zan yi wanka.”. Wani irin farin ciki ne ya ziyarci zuciyar Safwan ya tashi ya koma can bakin ƙofar ɗakinsu Inna sai harara take aika mishi, bai ma san tana yi ba burin shi ya ci abinci kafin 'yan rashin mutumcin Suwaiba su dawo ta ce ta fasa ba shi. Sai da ya cinye tas ya ɗauki kwanon ya kai wajen wanke-wanke ya aje sannan ya jiyo ya ce “Anty Suwaiba kawo abin da zan ɗauko miki ruwan.”
Riƙe ƙugu ta yi cike da masifa ta ce “Kai sai in daina ma na jibge ka kai makaho ne da ba ka san inda robar take ba.”
Haƙuri ya ba ta ya koma ya ɗauko roba ya fita da hanzari, a kofar gida ya tsaya ko zai ga Sidra ta dawo daga talla, ya fi minti uku a tsaye yana kallon hanya bai ga gillawar kowa ba sannan ya wuce ya shiga maƙota.
Da sallama ya shiga gidan suka amsa ya ce “Wai Anty Suwaiba ta ce a san mata ruwa za ta yi wanka.” Shuru ya ji ba su ba shi ba amsa hakan ya sa jikinsa ya yi sanyi murya na rawa ya “Don Allah karku hana ni Wallahi duka na za ta yi in ban kai mata ruwan ba.” Ya ƙarashe maganar yana sa musu kuka.
Matar gidan sanin halin Suwaiba da irin abin da take yi wa Safwan ya sa ta taso ta kama hannunshi, cikin tausayawa ta ce “Ka ga Safwan yi haƙuri ba za mu hana ka ba zo in zuba maka ka kai mata, amma ina Sidra ta barka ka fito da daren nan?”
Sunkuyar ya yi ya ce “Ta tafi talla har yanzu ba ta dawo ba.”
Zaro ido ta yi cike mamaki a ce yarinya kamar Sidra har kawowa yanzu tana waje gurin talla? Ba ta ce komai ba ta zuba mishi ruwan ya mata godiya ya tafi, ko da ya kai mata ruwan sai da ta zazzage shi ta uwa ta uba wai ya daɗe bai kawo mata ba ga shi saurayinta sai kiran ta yake, Inna ta sake yin kwafa a karo na barkatai ta ce “Na rantse yau Sidra in ta shiga gidan nan sai na mata dukan da za ta kasa motsawa, tana can yawon iskancin nata ta ƙi dawowa za ta zo ta sameni.”
Shi dai Safwan bakin ƙofar ɗakinsu ya koma ya zauna ya rafka tagumi..
_WASHEGARI_
Cikin takunsa na ƙasaita da iya gayu yake tafiya zuwa cikin asibitin, fuskarsa kamar kullum manne take da glass baƙi yayin da kunnensa yake da ƴar ƙaramar barima baƙa, sanye yake da t-shirt da gajeran wando iya gwiwa, gashin kansa baƙi sai shanin yake an maida ahi baya ya daure da wata kalar ribom mai mugun kyau sai wani daddan ƙamshi mai sanyin daɗi da yake fita daga jikinsa, dogo ne na gaban kwatance a cikin dogayen ma baƙi, fuskarsa ɗauke da kwantaccan saje wanda ya ƙawata fuskar haɗi da hancinsa dogo a miƙe sai dai yana da ɗan girma, idanuwansa 'yan matsakaita su ba ƙanana ba kuma ba manya sosai ba.
Tun da ya nufo ɗakin da aka sanar da shi tana ciki yake ji ihun wata murya, gaisawa suka yi da ɗansandan da ya kwana a nan ya nemi ya nuna mishi a wani take yana son ganin ta, da hannu ya nuna mishi ya sa kai ciki. Kunce ya samu ana yi da ita sai roko take a barta ta tafi gida, mamaki ya kama shi ya yi gyaran murya hakan ya sa duk suka juyo a tare, Sidra da ta rikice ganin mutum a tsaye sai ta ƙara firgicewa ta dirko daga kan gado ba ta damu ba ta yo kanshi, a gaban shi ta durƙusa ta fashe da kuka ta fara rokon shi. “Don Allah likita karka mini allura ku rabu da ni na tafi gida, Wallahi yau Inna kasheni za ta yi ban sayar da gyadar ba, ka ba ni kayana na tafi gida.”
Ganin ta rikice sai ya kalli Doctor ya ce “Doctor za ki ba ni dama na yi magana da ita?”
Jinjina kai ta yi suka bar musu ɗakin, bayan sun fita ya sunkuya ya kamo ta ya miƙar tsaye ta yi baya za ta faɗi ya yi saurin ruƙo ta, kan gado ya kaita shima ya zauna ya fuskance ta da kyau, gabaɗaya yarinyar ta tsaya mishi a rai tun da ya bar asibiti babj abin da zuciyarsa ke hasko mishi sai fuskarta, ya kasa baccin kirki saboda tunanin a wani hali take ciki, hannunsa ya sa cikin nata cikin nuna kulawa da kwantar da murya ya ce “ Baby girl comedown mana ni fa ba likita ba ne, ni ne na kawo ki asibiti da abokina ya bige ki jiya da mota.”
Zaro ido ta yi sai kawai ya ga ta ɗora hannu a ka ta fasa ihu ta zabura za ta tashi, da hanzari ya dawo da ita yana son yin magana amma ta birkice sai faɗi take “Waiyo Allah na shiga uku na lalace! Shi kenan mutuwa zan yi na bar ka ɗan'uwana.”
Rasa me zai mata ya yi ba yana son yi mata magana amma ta ƙi tsayawa ya ƙarasa mata bayani, yadda take sumbatu duk shi ya ƙara saka shi a kogin tunani, ganin fa za ta janyo nurses su shiga ya janyo ta suka faɗa gado cikin azama ya kai hannunsa ya rufe bakin tare da sa yatsarsa a baki ya ce “Shiii!”
Littafin na kuɗi ne only N500, my sister idan kin shirya me kike jira maza nemi number Maman Nusaiba domin biyan kuɗin karatunki. Whatsapp +966577675904
_Maman Nusaiba ce_