Free chapter 路 Read without an account

09

by Fareeda Aliyu 路 Ba Ni Da Masaniyya

Gaisuwa ta Musamman

Nauwara Muhammad Indabawa

Uwar Ammar da Mahmud

Our one and only Adda

Bafullatana mai canza side saboda naman akuya 馃槅

************


Ni'ima da 茩yar ta iya rufe bakin sannan ta 茩ara bu蓷e shi ta ce "Zara? Are you okay? Like okay okay? Hajjo taya ni duba ta mana." Ta 茩arasa maganar ta girgiza ni tare da le茩en fuskata.

Na 茩wace jikina na ce "Ku fa ba ku iya cin ribar zance ba. Ku 蓷an tsaya ku ga abin da zai faru mana kafin ku tara mana mutane da wannan 蓷aga muryar da Ni'ima take yi. Hold my hand, Abdullahi. Please."

Kallo 蓷aya za ka yi masa kasan shi ma mamakin yake yi, amma da yake shi namiji ne sai ya basar ya ri茩e hannun nawa a yanayi irin na masu musabaha. Na 蓷an yi jim ina nazarin wane sa茩o hannun nawa zai isar min. Lokacin da nake shirin bu蓷a baki na ce ya isa haka nan sai idona ya fa蓷a kan Nabila budurwar Abdullahin, tsaye take daf da mu tana huci. Na san me tunaninta yake fa蓷a mata domin ni ma master ce a wannan fagen kishin da insecurity.

Cikin dakiya na ce "Abdullahi, ya isa haka. Nagode sosai." Yana sakin hannun nawa na juya sosai na fuskanci Nabilar na ce "So sorry, i was experimenting something ne. Da da akwai wani namiji a wurin nan da ba shi ba, da ba zan gwada da shi ba. It's not what you think."

Ta 蓷an yi jim tana kallonmu kafin ya ja ta suka yi gefe. Ban san me ya fa蓷a mata ba, amma daga murmushinta nasan we are in the clear. Ya rakata ta tafi kafin ya sake dawowa wurinmu.

Tun kafin ya dawo su Hajjo suka dame ni da nacin sai na fa蓷a masu mene ne ma'anar abin da nayi 蓷azu. Tun da na ce su jira ya dawo don yana ha茩茩i ya san me yasa na yi abin da na yi 蓷in, ban 茩ara tanka maganarsu ba.

Bayan dawowarsa ne na fara magana da cewa "Wani abu ya ba ni mamaki. 茒azun Abdulrashid ne ya ri茩e min babban yatsan nan, kawai sai na ji kamar wuta ce ta ta蓳a ni. Na yi wannan gwajin ne don na tabbatar da wani abu, amma wannan ri茩on na Abdullahi ba shi da maraba da yanda nake ji idan ke Hajjo ko Ni'ima kun ri茩e ni. (Na harari Ni'ima) Kar ki sake ki tambaye ni me ya kawo hakan tsakanina da Abdulrashid 蓷in, don ba fuska na bayar ba. Atoh!"

Ni'ima ta fara dariya don kuwa tuni bakinta ya fara 茩ai茩ayi. Hajjo kuma ta ce "Kuma lafiyarsa 茩alau Abdulrashid 蓷in?"

"Garas yake. Shi wannan idan ba shi da lafiya akwai wanda ya kai shi langa蓳ewa ne? Cha蓳!"

Abdullahi ya ce "Ina tunanin gaskiya babu so ko ka蓷an tsakaninki da shi."

Ni'ima cikin sauri ta ce "Ko kuma aljanu gare ki ba."

Na juyo na 茩ara hararar ta tare da jan 蓷an 茩aramin tsaki na ce "Wani sa'in kanki yana motsi, aljanun 茩aniya? Ke kika sa min su?"

Su Hajjo suka kwashe da dariya har taba cewa "Yanzu dai kina nufin ba hankali Ni'ima ta cika ba kenan." A haka muka rufe maganar muka koma wata maganar daban har zuwa lokacin da Malam Habu ya zo 蓷aukata. 


Da daddare sai ga Yaya Bello da Anti Hajiyayye sun biyo ta gida, wai daga gidan za su je siyayya ne. Tun da suka zo kam 蓷iyarsu Ikram tana hannuna na hana kowa 蓷aukarta. Yawan dariyarta ya sa ni ma nake ta yi kamar mahaukaciya sabon kamu.

Minal dama tuntuni take son zuwa siyan kayan gyaran gashi, don tun shekaran jiya Alhajinmu ya sallameta. Jin tace za ta bi su, sai ni ma na 茩i zaman gidan na bi su. In dai yawo ne, ai da蓷i gare shi.

Ni dama idan dai za a ambaci kwalliya to tabbas ba ni a wurin. Ha蓷ina da kayan kwalliya powder ce, ita ma don ba na son fuskata ta yi mai茩o ne sai kuma man le蓳e, shi 蓷in ma don gujewa bushewar la蓳蓳an. Sai dai idan an zo ajin gyaran fata ina 'yar gaba gaba, ba ka raba ni da mayuka, sabulai, oils na gyaran fata amma ba na bilicin ba. Sannan ina da matu茩ar juriya wurin bautawa fata. Kullum kuma a cikin gwajin sabbin abubuwan kula da fatar nake ko da kuwa a ce na abinci ne.

Sai 茩arfe goman dare suka dawo da mu gida, suka wuce abinsu ba tare da sun sake shiga gidan ba. A falonsu Umma muka yada zango don nuna mata abin da aka siyo. Umma ta ce "Oh ni Minal, dama gashin nan naki zai tausaya maki ya fito ko don irin bautar da kike yi masa. Kalli na Zara da take ko'in'kula da nata har ma ya fi naki tsayi."

Ta zum蓳ura baki ta ce "To ai ita dama can haka nata yake. Abin ma bai san ina zai je ba, ayi ta wula茩anta shi yana nacewa." Ai kuwa mu duka muka kwashe da dariya.

Da sati ya zagayo, ranar Litinin muka sake yi da su Ni'ima za mu ha蓷u a makaranta domin biyan ku蓷in registration a bankin cikin makaranta. Na fi minti talatin ina jiransu amma ko mai kama da su ban gani ba. A fusace na dokawa Hajjo waya domin jin ina suka tsaya suka shanyani haka. Kuma 蓷aga wayarta ne ya sa nasan ashe a newsite suka za mu ha蓷u. Ita ma yanzu take tahowa tana wurin 茩ofar famfo, na fito bakin gate sai mu ha蓷u mu rankaya. Sai ma da ta 蓷an jirani tunda da 茩afa nake fitowa daga cikin makarantar.

Muna takawa domin 茩arasawa bankin da Ni'ima ke jiranmu watau Fidelity. Muna dariyar wani abu da muka hanga ni da Hajjo muna kuma 茩o茩arin tsallaka titi zuwa 蓷aya hannun. Gaba蓷aya hankalina na tattara shi akan hannun da ababen hawa ke tafiya a 蓳angaren da nake, kula ganin an samu sarari sai muka tafi da sauri domin tsallakawan... Ni da ban san ya ya aka yi ba, na dai ji an buge ni da 茩arfi sai kuma haske kala kala da idanuwa suka nuna min kafin na dawo nutsuwata na gan ni nayi zaman 'yan bori bisa kwalta. Sai kuma a lokacin ne na gane wani mai mashin ne da ya biyo hannun da ba na shi ba ya kwashe ni na fa蓷i. Gaba蓷aya hankalin 蓷aliban da ke wurin ya dawo kanmu. Zuciyata ba abin da take yi sama da tafasa.

Hajjo ta yo baya da sauri don har taje tsakiyar titin, sannan ta fara 茩o茩arin mi茩ar da ni tsaye amma na 茩i ba ta damar hakan. Tun daga nesa nake jiyo kwakwazon Ni'ima da alama nutsuwarta tayi mata nisa kamar koyaushe.

Wanda ya bugenin ne ya 茩araso yana cewa "Don Allah ki yi ha茩uri. Ku taimaka ku 蓷aga ta mu mi茩a ta clinic (babu nisa sosai da wurin da nake a lokacin)." Sai da na bari ya matso kusa da wurin da hannuna zai iya kai wa gare shi sannan na shammaci kowa na wurin na wanke shi da mari.

Marin a bazata ya je masa don haka a gigice a mi茩e tsaya daga 蓷an dur茩uson da yayi da fari lokacin da yake min magana, hannunsa dafe da kumcinsa yana min kallon mamaki.

A daidai lokacin na samu na mi茩e tsaye ina gyara mazaunin jakata a yayinda da idanuwa suka kafe a fuskarsa na ce "Amma ka cika 蓷an rainin hankali wallahi! Na farko, ka bi hannu ba naka ba. Idan mu ba mu lura da kai ba ai kai kana ganinmu don me yasa ba za ka dakata ba? Marin da nayi maka kuwa, na takaicin cewa duk yawan ababen hawan da ke cikin gari ba wanda ya ta蓳a ni bare har ya buge ni sai a cikin makaranta? 茒an gaba da rainin wayo kawai. Mtswwww!"

Na juya gaba-ga蓷i zan yi tafiyata, sai na ji yayi kukan kura wai zai kawo min bugu. Mazan da ke wurin suka tare shi ana ba shi bakin wai ya yi ha茩uri ba a fa蓷a da mata.

Na 茩an茩ance idanuwana na ce "Hmm! Wallahi idan ka yi kuskuren 蓷ora hannunka a jikina za ka sha mamaki. Wayyo Allah! Da alama tsautsayi ne yake jan ka zuwa gare ni yau 蓷in nan. Wallahi ka yi wa Allah godiya da iya mari ka蓷ai na yi na ha茩ura. Mts!" Na juya na tafi sakamakon jawo ni da su Hajjo suke yi.

Ni'ima ta ce "Al-masifatu! 'Yar bala'i! Tsautsayi ya jawo shi ya ta蓳a ki. Dama Hajjo ce da babu wanda zai san me ya faru ma."

Na 蓷ago kai na kalleta na ce "Na yi masifar tsanar rainin hankali! Kuma ni 蓷in ma da a ce akan hannunsa ne ya buge ni saboda nawa kuskuren da babu wanda zai ji mu. Babban takaicina bai wuce na yanda mashin bai buge ni a wajen makaranta ba wai sai anan! Kyanta a ce na ba shi marin fin sau 蓷aya wallahi. Jaki kawai."

Hajjo ta ce "Da蓷ina da ke Zara mita. Abin nan ya wuce a ha茩ura hakan nan."

Kafin yamma kuwa jikina har ya fara ciwo da alama buguwar nan ba da wasa na yi ta ba. Umma dai ta ba ni magani na sha bayan na gasa jikina da kyau.

**********


Birthday 蓷in Minal ya zagayo. Na san ba wata kyauta da za a ba ta a burgeta sama da wani man gashi da take ta nema amma ba ta samu ba. Ni kuma an tabbatar min zan iya samun shi a Wellcare. Don haka shi na sa a raina zan nemo mata.

Lokacin da na tashi zuwa Wellcare 蓷in sai aka samu akasi Malam Habu yayi niss ba zai yiyu na jira shi ya zo kai ni ba, kuma ba zai yiyu na gota yau ban siya ba.

Da yamma li茩is ma hau keke Napep na tafi can. Hoton man na cikin wayata don haka na bu蓷e shi ina tafiya a hankali ta 蓳angaren mayuka ina dubawa.

Har na gota, sai na ga kaman na hango shi ta gefen idona don haka ban lura da irin saurin da na yo baya don 蓷aukar shi ba, har sai da na ji na buge mutum da 茩arfi ta bayana. Kuma garin yayi regaining balance 蓷insa sai ya saki kayan hannunsa suka tarwatse a wajen. A tsorace na juyo domin ba da ha茩uri da neman afuwa, na fara magana "Don Allah yi ha茩uri...." Irin kallon da yake mani ne ya sanya maganar tawa ta katse. 茦wara ne. Matashin saurayi ne tsaye gaba na yana yin min kallon sama da 茩asa. A take wani haushi ya kamani. Don shi 茩wara ne sai yake yi min kallon banza? Sai ka ce ba cin arziki suka zo garinmu ba. Mts! Na fasa bayar da ha茩urin, don haka sai na harare shi na fisgi man tare da tafiya 蓷ayan 蓳angaren ina laluben abin da nake bu茩ata kamar babu abinda ya faru balle ya dame ni.

Har na gama siyayya na fito waje ban 茩ara ganinsa ba. Wayar Hajjo da ta shigo ne ta dakatar da ni a bakin 茩ofa.

Ta ce "Zara ke kam ban ga amfanin wayarki ba. Tun 蓷azun nake pinging 蓷in ki amma kin kasa gani balle ki amsa ni."

"Yi ha茩uri Madam, ina Wellcare ne yanzu, hankalina ba ya kan wayar. Ta samu ne?"

"Dallah. Sunan handle 蓷inki na twitter za ki fa蓷a min sharp sharp, Abdul (茩aninta) ya bu蓷e min ni ma."

Na 茩yal茩yale da dariya na ce "Ji Hajjo, sai ka ce tashin duniya? Saurin me kike yi ne? Ba dai sunana na twitter kike so ba?" Na fa蓷a mata sannan na fito domin samun abin hawa zuwa gida. Magriba ta wuce na san za mu yi ta Umma. Yau nasan sai an kira ni mai kunnen 茩ashi har babu adadi.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.