Free chapter · Read without an account
16
A ɗan tsukun nan, yawan kallon status ɗin Sardauna sun tabbatar min ya bar ƙasar nan zuwa Misra kamar yanda ya ba ni labari kafin tafiyar tasa amma ko da wasa ban ce masa ya ya hanya ba, saboda lokacin da shi ma zai tafi bai sanar min ya tafi ɗin ba. Na zuba masa ido kawai. Kuma sai na ga bai fi sati ɗaya ba ya dawo, to babu mamaki shirye-shiryen tafiyar ne ya kai shi can kafin ya tafi gabaɗaya. Ni share junan da muka yi ma daɗi yake yi min, ko banza na fara dawowa asalin kaina mai jinjinawa da kuma bin tarbiyyar da aka yi min daga gida.
Ranar wata Juma'a muna tare da Yaya Muna, mijinta sai kuma Yaya Lawal (ɗan gidan Baba mijin Gwaggo), ita Yaya Muna daga wurin aiki ta taho gida duka a main falon gidanmu. Umma ba ta dawo daga wurin aiki ba da alama kuma ta biya wani wurin ne. Ka na doso ɓangaren za ka fara jiyo muryoyinsu suna ta surutu har da musu, don dama in dai Yaya Lawal da Yaya Muna suna wuri dole sai ka gane da shegen musunsu, yanzu kuma zaman mijinta a wurin sai suka tarar wa Yaya Lawal. Ni dai ina gefe na zama 'yar kallo don babu wanda zan shigarwa sai ma dariya da abin nasu yake ba ni.
Kiran da ya shigo wayata ne ya tilasta min barin kallonsu. Sunan Sardauna na gani bisa allon wayata, a take kuma gabana ya faɗi a hankali na ce me wannan yake nema kuma? A sanyaye na ɗaga wayar tare da sallama. Ko da ya amsa sallamar sai duka muka yi shiru, kafin daga bisani ya ce "Ke da su waye haka?" Na san muryoyinsu Yaya ne ya ɗauki hankalinsa.
"Ina gida, ni da su Yaya ne. Ka dawo lafiya?"
Ya amsa "Ban sani ba. Ai kina kallona ko a dawo lafiya kika gaza faɗa min. Ki riƙe ka dawo lafiyarki, ranar da kike son tambaya ta sai ki kira ni don kanki ki tambaya."
Na ɗan yi ƙasa da muryata saboda su yaya da suke wurin na ce "Daga tambaya sai faɗa? Allah ya huci zuciyarka."
"Ba wani Allah ya huci zuciyana, ai kina sane kike yin duk abin da kike yi."
Na amsa "Hmmm"
Ya ɗora da "Ina hanyar Kano daga Taraba gobe idan Allah ya kai mu. Saura ki ƙi ganina domin ƙarfin zuwana ke ce."
Bana son yin doguwar magana kar a gane wace irin waya nake yi kuma ban isa na tashi daga wajen na je amsa waya ba, don ina tashi daga Yaya Lawal har Yaya Muna hankalinsu zai dawo kaina, sai ka ji an fara binciken wace irin waya ce ba za'a iya amsawa a gabansu ba? Sai dai idan mutum ba ya da gaskiya. Ko a gaban Umma ne dole ba za ka tashi ba, kuma ba ka faɗa a wayar cewa kana gabanta ba, yanzu sai cibi ya zama ƙari. Don haka bakina alaikum na ce "Allah ya kai mu."
Washegari tun da safe nake tararrabin haɗuwarmu, nayi ta jin kamar na ba shi uzurin da zai hana haɗuwarmu amma sai na kasa kwata-kwata. Wuraren la'asar sai ga wayar shi wai ya iso Kano, a ina zai zo ya ɗaukeni? Sai da na gama shiryawa sannan na yi masa text akan mu haɗu a shatale-talen dangi. Umma kam biki da su Ni'ima na ce mata za mu je, sanin da nayi Minal na da lectures 4-6 ranar Asabar ɗin shine a gaban Umma na ce ko za ta zo mu je tare? Kowa ya san mayyar son zuwa biki ce, kuma na san lectures ɗin ne kaɗai zai hanata zuwa don malamin nasu tsauri gare shi, ba a yin wasa da attendance ɗinsa.
Ya daɗe yana jirana kafin na ƙaraso. Ina isowa kuma ya fara mitar shi fa yunwa yake ji, kawai sai na ji nauyinsa ya kama ni sosai da sosai don babu abin da na riƙo masa. A gidan abinci muka tsaya ya siya tare da lemo sannan muka wuce otel ɗin da ya sauka. Oh ni ɗiyar babanmu! Yau ga Zara a hotel! Sai ɓoye fuskata nake yi kar na ci karo da idon sani, jikina sai rawa yake yi.
Yayi mitar shariyar da nayi masa ni kuma na kare kaina da cewa tun da bai sani a ciki sabgarsa ba, shine ai na koma gefe na zauna a matsayina.
Ya tsura min ido kamar me neman amsa a fuskata lokacin da ya ce "To me yasa ba ki son zuwa Kaduna?"
Sai na fara dariya don na tuna abin da ya faru da ya tsoratar da ni. Na ce "Hmmm! Ashe ban ba ka labari abin da ya faru ba ko? Ni da alamomin masu ciki ya same ni? Na rikice na tsorata har da su alƙawarin ba zan ƙara zuwa Kaduna ba."
Ya jingina da kujera yana kallona ya ce "Ciki? To me ya sa ba ki faɗa min ba?"
"Chaɓ! Ai ba zan iya maganar ba ne da kowa a lokacin. Tsoron da nake ji ma har da kar nayi maganar abin ya zama gaskiya ne."
Ya fara dariya ya ce "Matsoraciya kawai. Kin san hakan ya taɓa faruwa da ni ina ABU Zaria? Wata yarinya ce muka ɗan yi flinging tare sannan trust me ko zangon ƙarshe ba mu taɓa kaiwa ba, amma ta zo tace min ba ta ga period ɗinta ba. Forget say i be guy! Wallahi na tsorata ba kaɗan ba. Abokaina ne suka cece ni, suka ce a tafi asibiti kawai amma ta dinga yi mana yawo da hankali har da muka fuskanci duk bula ce abin."
Ni ma na fara dariya na ce "Shi ne kake ce min matsoraciya? Bayan alamu sun nuna daga ni har kai matsoratan ne."
Cikin dariya ya ɗan kwanto kusa da ni yanda zai yi magana a hankali kuma na ji ya ce "Da fa yanzu ina da baby tare da ke ko?"
Da sauri na daki gefen kafaɗar shi ina faɗin "Bari faɗin zance irin wannan mana, kar ka ja ya zama da gaske."
Ya ce "Gaskiya tsoronki yayi yawa! Ban da abinki ma me ya faru a tsakaninmu da har za ki samu ciki? Ko kin manta ne? Babu fa."
Na amsa "Ni ma abin da ya hanani haukacewa ta sosai kenan. Na ce to sai idan sha nayi. Na tsorata gaskiya duk da cewa dama na kan ɗan yi pseudo-pregnancy symptoms kafin period ɗina ya zo ko kuma idan ina cikin yi."
"Pseudo-pregnancy kuma?"
"Eh. Tun da ba cikin gaske ba ne kawai alamomi ne irin na masu ciki. Ina zama bloated watau cikina ya kumburo kamar me ƙaramin ciki. Tashin zuciya. Amai. Kumburin kafa da fuska da ire-irensu."
Na kasance tare da shi har wurin ƙarfe taran dare na dake faɗan Umma. Tunda na ji shiru ba ta kira wayata ba har yanzu na san ta ɗauka tuni na dawo ina ɗakina.
A ɗan sahu na dawo gida don ba ni da buƙatar ya maido ni gida, ba yanda ban yi da shi akan kar ya biya min kuɗin keke Napep ba bayan ya rako ni amma ya ƙi sai da ya biya. Lokacin da nake ƙoƙarin shiga adaidata sahun kuma ya tsayar da ni ya rage murya sosai ya ce "Idan kin ga zai sace ki ki yi min waya."
Ina dariya na ce "Ashe zan kama babu kenan. Kai da ba wani sanin Kano kayi ba? Tsaf za ka ɓata kai ma fa." Muka yi sallama na tafi bayan zuciyata ta sake ɗaukar hotonsa da kwantacciyar suma mai danshi.
Ina shigowa gidan muka ci karo da Umma tana fitowa daga kicin, gabana ya faɗi daram! Cikin hanzari na ɓoye hannuna a baya mai ɗauke da purse ɗina. Ta tsaya tana kallona tare da tambayar daga ina nake? A take na zuƙo ƙarya na ce "Tun ɗazu ina ƙofar gida" ma'anar maganar tawa tana nufin ina zance ne a ƙofar gida. Ta girgiza kai kawai ta wuce ɓangarensu. A hankali na saki ajiyar zuciyar tsallake rijiya da baya na wuce sashenmu.
Minal ce ke faɗa min tun magriba ta tambayeta ko na dawo, ita ce tace mata na dawo har na yi sallah, na fita waje ne an aiko kirana. Ƙaryarmu ta zo ɗaya kenan. Shi yasa ashe na ga Umma nan da nan ta yarda da maganata ta wuce duk da dama ba za ta taɓa zargina da aikata kwatankwacin abin da nayi ɗin ba bare shi kan shi.
Tun tafiyar Ahmad na wannan karon sai na tsinci kaina da kewar shi, abin da bai taɓa faruwa a tsakaninmu ba. Har yanzu yanayin hirata da shi bai sauya ba, ko da wasa ba ma maganar wani abin da ya wanzu tsakanina da shi bare na ji tsoron ajiye wayata ko kuma na tsinci kaina da goge hirarrakinmu. Wannan na ɗaya daga cikin halayensa da nake so.
Ta ɓangaren makaranta ma komai daidai yake tafiya, kuma har yau Allah bai sa mun ci karo da carry over ba. Har yanzu na kasa tsayawa na yi saurayi, ba kuma don na rasa masu cewa suna son nawa ba ne. Kawai kowa ƙarfi da yaji ya zama bature, idan ka dage ba za ka basu damar taɓa ka ba sai ka ga sun fara janye jikinsu daga gareka zuwa ga waɗanda za su basu. Ni kuma hakan ƙona min rai yake yi. Idan kana so na yanzu sai dai mu yi soyayya babu taɓe-taɓe. Idan kuma hakan bai yi maka ba to sai dai kowa ya kama gabansa.
Hajjo ta tafi bautar ƙasa, Ni'ima kuma har an kawo kuɗin aurenta. Maa shaa Allah.
***********
Ranar Asabar ina gida don lokacin mun kammala jarabawa sai ga Ni'ima ta biyo min za mu gidan yayarta a Alu Avenue. Muna kan layin shiga gidan wayata ta ɗau ƙara, Abdulrashid ne. Na taɓe baki na ce yau an tuno ni kenan.
Daga wayar yayi daidai da isar mu ƙofar gidan yayar Ni'ima ɗin. Bai jira nayi magana ba na ji ya ce "Ina zuwa haka? Yanzun nan kika wuce mu ni da abokina Faruk."
"Ai na isa wurin da zani ɗin ma." Na amsa masa.
"Bari na ƙaraso na ganki mana."
"Ba yanzu ba don Allah. Ɗan bari mu fara shiga mu gaishe da mutanen gidan da muka zo wurinsu tukunna."
Mun shiga gidan muka iske su a tsattsaye a harabar gidan cikin shirin fita, amma yayar Ni'ima tace mu je mu zauna falo ba daɗewa za su yi ba, gaisuwa za su je.
Ina idar da sallar azahar sai ga wayarsa ta sake shigowa don haka sai na ce ya ƙaraso bayan na faɗa masa lambar gidan.
A wani sitting-room can gefen ainihin ginin gidan Ni'ima ta sauke shi, a can masu gidan suke sauke baƙi maza da ba 'yan gida ba.
Ya sa ni a gaba yana ta min ƙorafin yanzu na daina son shi, na canza masa gabaɗaya har ya fara karya min zuciya ina jin ban kyauta ba, ina laifin wanda ya ce yana sonka? Ganin na rusuna sai yayi amfani da damar ya rungumo ni jikinsa. Na fara kiciniyar ƙwace kaina amma sai magiya yake yi min wai taimaka mashi zan yi.
Wani mashahurin ɓacin rai ya dirar min da har ya sa zuciya ta fara tafasa! Watau a wurinsa wannan shi ne so kenan. Ba ni da wani amfani gare shi idan ba ta wannan hanyar ba. Watau a baya don a sarari muke haɗuwa shi ya sa bai taɓa kamanta wa har zuwa wannan ɓigiren ba kenan. Na sani sarai a baki yana taɓa irin maganganun nan amma na ɗauka iyakarsa kenan.
Da naga ƙarfin da nake sa wa ba zai kwace ni ba, sai na cije na daure na danne ɓacin raina na ce "Ɗan sake ni mu yi maganar sosai to." Da ƙyar na samu ya sake ni.
A take na koma bakin ƙofa na tsaya tare da cewa "Wannan abun da kake buƙata, ni ba ni da buƙatar shi. Sannan a zahirin gaskiya kasan hakan bai cancanta ba ko? Kama daga al'ada har zuwa addin...."
Ya yi saurin katse ni "Na sani. Na sani Zara. Don Allah ki yi haƙuri. Yes. Duk abin da kika faɗa gaskiya ne amma ki bar ni na yi wasa da ke kaɗan. Kin ga tunda muke ban taɓa roƙon ki game da haka ba, kuma roƙo mai yawa irin wannan. Wallahi a matse nake. Don Ya Rasulullah ki taimaka."
Maganar da yayi gabaɗaya ji nake yi kamar ya ɗauko tafasasshen ruwan zafi ya sheƙa min. Zuciyata yanzu kam ta wuce tafasa ina ga zaɓalɓala take yi. Gayen nan yayi matuƙar raina min wayo wallahi. A take na ɗaure fuskata na ce "A'a wallahi. Wannan abun ba mai yiyuwa ba ne! Ka zo ka tafi mu ma yanzun nan za mu kama hanya."
Duk wata magiya da daɗin baki irin na shi ya ƙi tasiri akaina, a ranar kam ni kaina na san taurin kaina ya tashi don ko kalmomin da yake magana da su bana ji balle su yi min tasiri. A haka muka rabu, ni raina na min zafi shi kuma ba ni da tabbacin me yake ji, shi ya sani.
Ni'ima tunda na shigo ciki ta lura da yanayina, ta sa ni a gaba tana tambayata me ya faru nake cikin tsananin ɓacin rai har haka? Tsaki na yi nace "Ni da wannan Abdulrashid ɗin ne mana."
"Me ya haɗa ku?"
"Mtsww! Rabu da shi kawai. Can da yawarsa!"