Free chapter · Read without an account
3.
by BIL-SAN · LATYFA IMAM
3
LATYFAH IMAM
NANA DISO
Jiƙinta ne yafara rawa taƙe hawayen dataƙe rikewa ya fara bin ƙumatunta duk yadda ake muzantata yaune ranar dataji tafi kowacce rana muzanta, elephant? Takara maimaitawa aciƙin ranta, mijinta na halal shine ke jifanta da wannan maganar? Yanajin kunyar nunata? Sauƙar maganarsa yasata ƙara dagowa tana zuba musu ido " hy fatty kinzo ƙanmu ƙin tsaya or are you part of us?" Cikin zafi zafi Abdul yace " is she your girlfriend ko wife ne? " dariya matashin yayi yanafaɗin so kakeyi ta zaune ni kokuma kanaso ta ƙaryani after all ma dai babu laifi tanada 8 figure but matsalar she is ugly yafaɗa batare da damuwa ba." Dariya abdul yayi yana cigaba da danna wayarsa. Wata aciƙinsu ce tace " Yanzu wannan sai a aureta ko?" Wani nazir ne yace " Ai sai da gida da mota." Abdul ya karasa da faɗin gida da motarma ai sai tsoho yanadashi." Sosai hawaye ke bin fuskarta kallonsu tayi tace " Alhamdulilahi yaa Allah tunda baku kuka halicci ƙanku ba kuma bazaku iya canza koda danyatsanku ba kokuma kuna canza halitta ne? Idan kunayi sai ku faɗamin tafada tanayin gaba, bakaramar tafiya tasha ba ƙamin ma ta isa titi dakyar tasamu mai napep ya maidata gida ko data isa tundaga falo tafara wulli da jaƙarta tana saƙin wani zafaffen kuka tare da fara fasa duk wasu glass dake ƙan tebur dinta wayyo Allah na wannan wacce irin kaddara ce? Mijina fa ta ambata tana kara saƙin wani sabon kukan.
Sosai sukaci suka sha daga nan kuma kowannen su yashige motarsa yabar gurin ragewa yayi daga Adam sai Abdul. Aboki yafada yana dariya kasa kasa nasan fa matarkace wannan garin yaya kaje ka dakko wannan buhu mai kafafuwan? Gata Black and after all ugly dubeka fa beautiful handsome man cikakken namiji ga kudi ga ilimi uwa uba ga kyau, and ka kare da wannan ugly woman din? Nifa lokacin danasanka ko black girl bakaso.
Wani ƙallo yayiwa aboƙin nasa kamin yace " banda zabi ne da inada zabi ƙasan babu tayarda zan aure wannan ugly din and black yafaɗa yana jan tsaki." Dadi Adam yaƙaraji cikin ransa dan bashida burin da yahuce yaga aboƙin nasa ciƙin baƙin ciki dan haka sai yace " haba abokina sai kace wata macce da zaka yarda ayimaka auren dole?." " I have no right ince masa no, no way ban isaba kafi kowa sanin wanene dady ... " hmm gaskiya bakada m ko kadan! Zama zakayi da wannan maman? Tabbijan aikam zamuyita making fun of you class naka zai sauka fa, babban yaro mai ji ajika irinka ai sai dai ka auri balarabiya wallahi dan ko bafulata banga wacce zataƙaika kyau. zama zakayi Kai bari in gayamaka you have to change duka zagi and no food for her kafitar da komai na abinci let her start eating vegetables only da kafafunta zata fita." Cikin saƙin fuskar da rabon da yayi yamanta yace " Are you serious?" Dariya Adam yayi yanajin wani sanyi aransa saboda yadda abokin nasa ya dauki shawarar tasa yasa indai yabi wannan shawarar to dole mahaifinsa zai tsine masa ne babu wani kwana kwana ma and zai janye duk wani tallafi nasa. Murmushi yayi yace abokina ba'ayiwa mata sanya fa idan takama ka kai babies dinka gidan yafaɗa yana dariya.
Duk yadda takejin yunwa haka ta haķura da abincin ta kwanta baccin ma gagararta yayi juyi kawai takeyi tana tuna baya, yadda matar mahaifinta ke yawan gayamata ba babu mai aurenta dan gaskiya dan batada komai da namiji yakeso, a hankali ta furta to dagaske take? Wata zuciyar tata ce tace mata yes bagashi ba mijin naki yana wulakantaki har cikin abokanansa yana kunyar nunaki, Ya Allah ta furta wani hawayen yana zuba a fuskarta.
****
Nana mahaifinta ya ambata yana ajiye wayar daƙe hannunsa, Naam abiey shine abunda tafaɗa tana murmushi. Yaushe kuka koma yimun haka? Sai yayanku yakira yace kina buƙatar mota, me yasamu taki dana canza miki tazama tsohuwar yayine Yafada yana mai kara kallon diyar tasa. " kayi hakuri abiey kyauta nakeson nayi da'ita shiyasa amma tawa babu abunda tayi." Murmushi yayi yace "shine kuma baza'a a gayamin ni nasiya nasamu lada ba? " Murmushi tayi tace " tace abiy naga hidindimu sunyi maka yawane shiyasa ta ambata tana boye fuskarta. Dariya yayi yana miƙewa yace akan mota shine hidindumu sukayimun yawa? Gobe da safe zanta iso sai ayi kyauta lafiya." Mikewa tayi ta nufi mahaifin nata tana mada godiya sannan tafita, ko data isa sashinsu mahaifiyarta ke zaune tana harhada mayafan datasiya." Ummy tafada tana rungumeta . Wai danAllah sai ƙin karyani ne? Ke bakya girma ne? Menene yasakaki farin ciki uwar tafada tana waiwayowa." " ummy yasiyawa latyfah imam mota. " murmushi ummy tayi tace " ƙinsan inada niyar hakan kika rigani, Allah yabiyasa yakara masa budi wannan amintaka taku ubangiji yasa har cikin aljannah." Ameen ummyta bari naje na kwanta gobe akwai aiki.
*****
wani hadadɗen babban daƙine mai girma fitilu masu haske sunƙewaye ko'ina, dakin ɗauke da injinan motsa jiki, Tsaye yaƙe yana sauƙe numfashi alamu sun nuna bai daɗe da gama motsa jiƙin nasa ba, yaaAllah yafurta yana goge gumin dake tsatsafowa a jiƙinsa, karar sautin ringing din wayarsa ne ya cika gurin, a karo da farko da ya ɗan jiyo ya ƙalli inda wayar take sai ƙuma ya kawar da ƙansa yana mai kara duɓan ƙansa a mudubi, ƙallon kansa yayi a mudubi duk yadda yaƙai da rage sumar nan tashi sai ta fito, juyawa yayi inda wayarsa take ya ɗauka, cikin sallama ya amsa yana faɗin " bardu aini" ya ambata yana zama aƙan wata kujera. " Noor" tafaɗa kamar tayi kuka. "Uhm are you okay ?" " Wash Allah na mutuwa zanyi." Ƙalmar data ambata tasaƙashi saurin zabura yana mai miƙewa ya dauki car key dinsa yayi gaba, duk yadda ma'aikatan gurin ke gaisheshi bai ƙula su ba hanƙalinsa gaba daya yakoma ƙan matar tasa farinciƙin tasa data ƙirashi, yana shiga motar ya figetazcikin ikon Allah yaƙaraso gidan tana kwance jini har ya bata gurin? Tsayawa yaƙalleta ƙansa yana wani mugun sarawa, kayan training dinsa yacire yasaka jallabiya ya gyara mata gurin sannan yayi yunƙurin dauƙanta amma yaƙasa gashi da alamu suma tayi, innalilahi wainna illahirrajiun ya ambata yana saƙin sabon kukan da baisan rabonsa da yayi ba, haj hauwace tafito daga bangaren masu aiki da gudu ta kama masa ita akasaka amota, bakaramin gudu yayi a motar ba har suka isa asubutin ƙansa nasarawa ga kirjinsa dake faman bugawa aƙai akai, taimakon da likitoci sukafara bata yasata farfadowa amma bleeding din yaƙi yatsaya ga naƙuda taki tashi, ga jininta da ya hau. Likitane yafito hankalinsa atashe yace " Sir we are sorry dole sai munyi mata Cs and jinin yaƙi tsayawa kuma jininta ya hau, is between life ko mutuwa dole a dauki daya idan muka barta zata iya mutuwa har dan jiƙin nata dake nuna alamun wahala yanzu idan akayi Cs zasu iya rayuwa duk su biyun kuma zasu iya mutuwa dukansu and daya zai iya rayu, wannan kuma bamuda tabbaci akan kowanne. Tunda likita yafara maganar yaƙejin ƙansa sama sama dago idonsa da zaiyi yayi jajir jijiyoyin ƙansa sun bayyana ga wani dishi dishi da yaƙe gani zubewar dayayi yasa likita saurin nufosa yana kiran nurses, shima gado suka bashi suka saka masa ruwa tare da allurai, haj hauwa dake ta kuka jin halin da iyayen daƙin nata suke ciki, yanzu fa suka gama hira da Amina ko mintuna 50 ba'ayi ba har take cemata tayi mata alala anjima ta amsa mata, amma yanzu itace kwance halin rai ko mutuwa.
Doctor doctor wata nurse tafito tana faɗa shima cikin tashin hanƙali ya nufota yana binta zuwa daƙin haihuwar, yana kallon gadon amina tana jijjiga ga naƙuda datawo ranga ranga, ikon Allah duk suka tsaya gani kowannen su yakasa motsi sai da sukaji kuƙan jariri da ya ciƙa asubuti yasasu kara bata taimako amma ina gamawarta da sakanni Allah yaƙarbi abarsa, nurse din ce tace innalillahi wa'inna ilaihir raji'una doctor ta mutu, jiyowar da zaiyi numfashin jaririn yashiga sama sama nan suka fara kokarin saka masa na'urar numfashi amma ina kamin ma su dora Allah ya ƙarbi abunsa, nurse ce tasaka wani zafaffan kuka na tausayi tama kasa motsawa sautin kukanta daya cika asubutin yasaka haj hauwa itama fashewa da kuka dan ko ba'a faɗa ba tasan mutuwa akewa wannan shikenan innalillahi wa'inna ilaihir raji'una hannunta yana rawa sosai tashiga neman lambar ummy, dakyara ta'iya rike hannunta saboda yadda yake rawa kada wayar ta wadi, ummy na dauka tafashe mata da kuka dayasa hankalin ummy tashi tana faɗin haj hauwa lafiya?
Menene?
Wani abun yafaru?
"Anty ummy amina ta rasu yayanmu baisan kansa ba tafaɗa wayar tana waduwa kasa."
Ummy ce tamike daga kwanciyar da tayi wata sabuwar juwa tana kamata, wayarta ta dakko tana kokarin kiran abiey amma ta kasa, sarkewar da numfashinta yafarayine yasaata ajiye wayar tana kokarin fizgo numfashinta amma takasa, Nana dake kokarin shigowa daƙin nata karasowar da zatayi taji numfashin mahaifiyarta yana sarƙewa aguje taƙaraso tana kiran ummy, tana jijjigata ganin yadda take kakkafewa, saƙinta tayi taje ta dakko inhilarta tasakamata dakyar take ja kusan mintuna 40 kamin tadawo daidai tana ƙallon ummynta dake nuna mata ta dakko wayarta tayi, kira abiey kice amina ta rasu, kikira naseer yanzu ya nemana tafiya Canada...wani irin shock nana tashiga tana mai zubda hawayen da yataru a idonta....
Yadda yake riƙe da gawar yana shasheƙar kuka sai ka tausaya masa, bardu aini...matata.. aminata yazanyi rayuwa babuke amina...yadda likitan yarikoshi yasakashi kara fashewa da kuka...
****
Yau ƙanta ciwo yakeyi tunda tatashi idonta taƙara budewa yadda taga ana kwashe duƙa kayan abincin yadda yaran suke fita da buhun shikafa dasu taliya yasata nufarsu tana faɗin lapy? Wani mugun kallo Abdul.yayi mata yana nunata da hannu, " Ke ugly menene haka? Zaki tsayar dasu? Abinci ne ƙin dainaci anan gidan za'a kawomiki lettuces da vegetables..." mamakine yasata kara ware ido tana ƙallonsa ... " bangane ba..
MAGANIN GYARAN BREAST(NONO)
-NONON SANIYA
-GARIN CUKWI GWANGWANI 1
-GARIN ALKAMA RABIN GWNAGWANI
-GARIN AYA RABIN GWANGWANI
ZAKI HADE GARIN ALKAMA DA GARIN CUKWI DA GARIN AYA SAI KINA ZUBAWA ACIKIN NONO KINA SHA YANA GYARA BREAST SOSAI....
MORE COMMENT MORE POST..