Free chapter · Read without an account

10

by Rahinat Hussein (R.Hussain) · LUBE (BODARA)


________Humaira ce kwance a kan Italian bed ɗinta, tana waya cikin nutsuwa da alama wayar Mai mahimmanci ce " Eh Umma har yanzu ban gama warware gajiyata ba ne, kin ga garin kuwa, Allah ba ƙaramin ƙoƙari na yi ba seven mouth fa is not easy Umma" Daga can side ɗin Umma ta ce"ke dai Allah ya taimakeki da kika dawo, ga su Faiza nan za su zo su, sai ki ba su sak'on" Humaira ta ce"ok to shikenan sai sun zo" da haka suka suka yi Sallama.



Gyara kwanciya ta yi da niyar yin bacci kafin Bilki ta kawo Affan, knocking door ta ji cikin gajiyawa ta ce" yesss" Kulu ce ta shigo ta ce" Hajiya kin yi baƙi ne a ƙasa" kallon agogon da ke bedside drawer ta yi sha ɗaya saura ta ce" su waye da sassafen nan?" Kulu ta ce" uhm to na dai gane ɗayar wannan ɗin nan ce wacce take zuwa ƴar Sokoto" Firdausi Sokoto ki ke nufi" da sauri ta tashi, Kulu ta juya, gyara fuskarta Humaira ta yi ta sa kaya sannan ta fito.


Wasu jiga-jigan Mata ne a zaune kowacce ta haɗa uwar ƙiba sun sha kwalliya, cikin sakin fuska Humaira ta sauko" a'a'a'ah yau a gari inji maƙi baƙo Firdausi Sokoto" Humaira ta faɗa ta na zama suna tafawa.


Da dariya Matar ta ce" wallahi Allah ya yi yau dai gani a Kano" Bilki da ke goye da Affan ta shigo ta na ajiye musu drinks " kar dai ki ce min Affan ne ke bacci?" Humaira ta ce" shi ne dai,ga shi nan daman baki taɓa ganinsa physically ba" ke!!! Sauko shi na ganshi" Matar ta faɗa tana mamakin girman da Affan ya yi.


Ɗayar wacce ba ta da magana sosai ta ce"ma sha Allah ya yi wayau" nan suka shiga hira, Firdausi ta shiga fito mata da kayan gyara, tana tsula uban kuɗi.Wani ƙulli ta ɗauko wanda akayi rubutu a jiki ga uban guard lock ta ce" Kinga wannan wallahi dar ne, ƙaidarsa baa bawa mai kishiya dan idan kika yi amfani da shi, ayyah Hajiya kin gama kama shi, ko uwarsa ba zai yi wa biyayyar da zai miki ba, inda kika san Raƙumi da akala haka zai zame miki" Humaira ta ce" oh Firdausi akwai zuzuta abu ke kam, ni da ma mijin baya gari wana amfani zai mini yanzu" Firdausi ta ce" aikuwa ina baki shawara ki siya ki ajiye ko shekara zai yi babu abinda yake, daga Singapore yake, wani babban malami ne ya ke haɗa shi, kinsan turawa dai yanda suke iya kama aljani su sa shi a kwalba ma,ke wannan maganin ƙarshe ne" Humaira ta ce" to nawa kuma dan gaskiya da alama zai yi aiki" Firdausi Sokoto ta ce" babu tsada dan ƙanin kyauta ne dubu ɗari da Hamsin ne kacal' Humaira ta zaro idanu ta ce"ɗari da Hamsi gaskiya a yanzu ba ni da ita,idan na samu na yi miki magana a kawo min" Alawiyya ta ce"aa fa ƙawata muddin kika bar wannan magani wallahi kin yi asara,kin ganni nan mu huɗu ne a wajen mijina, tunda na yi amfani da shi, sai abinda na ce a gidan nan,ni ban zaci ma zaki ga yawan kuɗin ba,yo Allah na tuba kwana nawa ne kin mayar da dubunsu" take Humaira ta karɓi shawara,ɗan kuɗin da take sarving a account ɗin ta, ta yi musu transfer dubu ɗari da Hamsin, suka tashi suka tafi.

Ɓoye maganin ta yi, ƙannenta suka shigo, kowacce mayafi a gefen kafaɗa su uku suka nufi parlour'n gidan.


Safiya ce ta fara ƙure home theater volume, waƙar film ɗin nan na Happy new year ta cike parlour'n.Sannan suka zauna,Khadija ta nufi kitchen ta ɗebo musu lemuka da Rufaida ta dawo,while Fauza ta shiga ciki dan kiran Humaira.


"Aunty!!! Humaira ta fito tana faɗin" iye kaga ƴan ukun Mama sai yanzu?" Fauza ta ce" wallahi wani mai adaidaita sahu ne ya ɓata mana lokaci, ina my Insaaf?" parlor'n suka koma ta ce" tana school ya Mama" suka ce lafiya ƙalau.

Nan suka baje suka dinga shagali suka ɓata ko ina da ciye-ciye sune wainar fulawa su ne indomie su ne awaran dankali sune pepper chicken sune pepper fish, haka suka yi kaca-kaca da kitchen suka zuba a cooler zaa tafi wa da Mama.

Humaira ta ba su dubu hamsin ta ce su kaiwa Mama, Faiza ta juya kuɗin ta kuma juyawa ta ce" yanzu aunty ko 100k ba ki samo ba a tafiyar da kuka yi, wai sunan kina auren mai kuɗi" Humaira ta ce"zanci kutumar ubanki, an gaya miki kuɗin sato shi nake yi, ba ni idan ba za ku kai ba" a hand bag ɗinta ta saka ta ce" a'a me ya yi zafi Allah ya baki haƙuri" Khadija mu je" Humaira ta ce"mu je in sa a mayar da ku gida. Audu driver ta kira da gudu ya ƙaraso yana faɗin" gani Hajiya" 

Humaira ta ce" ka mayarda sisters ɗina gida" angama Hajiya" ya faɗa ya na nufar mota.


Ɗaya daga cikin motocin da ke wajen ya buɗe yana faɗin bisimillah, duk suka shiga Fauza ce ta zauna a gaba, driver ya shiga maigadi ya buɗe gate suka fita, yana musu a sauka lafiya.


Jinsu suke kamar ƴaƴan wani shege a gari ganinsu a motar alfarma, har ƙofar gida ya ajiye su, suka fito ɗauke da cooler da flask suka nufi cikin gida.

Umma da tasan yau akwai bushasha bata ɗora komai ba, kuɗin suka bata ita ma ta ce" amma Humaira anyi banza ɗan wannan kuɗin ta baku, ba ni waya in ci ubanta wajen wata goma amma dubu hamsin" Safiyya ta ce"hahhh kai Mama kika sani ko adashi ta yi" cikin izgilanci, duk suka fashe da dariya. Ta ce" uhm yaran nan Allah ya shirye ku,ai dan ku nake ta wannan fafutukar,idan aurenku ya tashi ido zaa zuba min" duba abincin da suka zo da shi tayi take ta ce a ɗauko mata kwano.


Tamkar mayunwata haka suka hau cin nama da kifi suna korawa da lemon fenta da coke, hirar gidan Humairan suke kowacce tana faɗar albarkacin bakinta.

Yayan su ne ya shigo, da gani yunwa ta ci ta cinye ya zauna ya na faɗin' Allah ya kawo mana sauƙi a wannan rayuwa" Mama ta ce"amin Amir ya kasuwar?" ya ce"yanda na je haka na dawo,ana ta ciki waye zai sayi wasu kayan jarirai mtsww" Abincin aka zuba masa, sai ya washe baki yana faɗin "ta dawo kenan wai rabon dana ci nama tun ranar ɗaurin auren Yusuf wata kusan huɗu kenan yanzu" Hahhh kai Amir naga ranar da za ka daina wannan wautar sai ka ce tambayarka akayi" ƙannen nasa ma suka sa dariya.Ranar dai an tauna ƙashi a gidansu Humaira.




********


Gidan Baba danƙam da ƙawayen Lube, ta sa su gaba tana sanar da su ta kusa aure, sanye take da zanin atamfa coffe, da rigar atamfa green da ɗankwalinta tayi furu-furu dan yau jikinta baiga ruwa ba.

Marawiyya ta ce" dan Allah da gaske aure za ki yi Lube?" Lube ta yi fari da idanu ta ce" ko shakka babu yarinya" 

Kai amma naji daɗi alkur'an za'a ci uwar sabada waye angon?" Lube ta saki murmushi ta ce"ke dallacan Lado ne nima zan zama matar Malam hahhh" duk kansu suka kama baki cike da al'ajabi "Ladoooo!!!! Lube ta ce"eh ai Baba ma ta tafi gidansu a sanya rana" Mara da ta fita hankali ta ce"ku alkur'an ƙarya ne take muku wai wani Lado, wannan mai girman kan tsiya mtsss" kafin ta dire tsakin Lube ta bige bakin.


"Munafuka algunguma watukun baƙinciki kike min zan yi aure ko" Mara ta ce"wa zan yi wa Baƙinciki Ladon mtsww daga ke har shi baku ishe ni kallo ba, shawara ta gare ki shine ki rage tusar nan taki mai ɗoyin bala'i kar ki kumbura masa ciki, ni bazan yi faɗa da ke ba,dan Innata ta faɗamin ko ke wace ce" yaran ɗakin da suke ta hau faɗin" kaiii alkur'an Lube amarya kar ki yarda sai ta faɗa miki wace ce ke ɗin aka ce" Lube da take ganin hassada da baƙinciki ne kawai Mara ke yi mata ta ce" meye ya wuce ace uwata mayya ce, kafin su faɗa dubunsu sun faɗa dan haka ko a jikina aheee" ƙarshe dai abin ne ya koma kan mara, suka dinga yanka mata ba'a har sai da tayi kuka.



Muryar Baba ta jiyo tana mita akan cin mutuncin da aka yi mata ga kuma Adama da ta ke son hura wuta ga ƴaƴanta.

"Baba ansa ranar?" ce war Lube da zumuɗi, Baba ta girgiza kai cikin tausayi ta ce"kayya ashe yaron ba shi da kirki ba ki ji zagin da suka ƙare min ba shi da uwarsa ke har malam Liman ɗin ashe Malum-malum ne duk bula ce" 

Ƙawayen Lube da ita duk sai suka zagaye Baba Delu dan jin ƙarin bayani, tas ta labarta musu komai har da kukanta, ran Lube ya yi masifar ɓaci take tsanar Lado ta mamaye ranta, cikin baƙinciki ta ɗaga yatsa sama ta ce" kamar ni Lube Lado zai wulaƙanta to alkur'anin Allah sai na auri miji ɗan zinare da lu'u-lu'u kuma ɗan sarkin makka wanda ya fi shi karatu" sai hawaye ya zubo mata masu ɗumi.


Cikin so da tausayi su Mara suka dafata kowa zuciya babu daɗi.

"ki yi haƙuri Lube in sha Allahu sai kin sami mijin da ya fi shi" Baba Delu ta ce"yanzu bayan shi akwai wani da kike so?" Lube ta girgiza kai" take Mara ta ce"akwai Ɗanliti mijin Uwangale yana sonta" da murna Baba Delu ta ce" Ɗanliti dai wanda na sani?" Mara ta ce" eh shi dai, a dandali yake gayamin yana son Lube, sai ya yi ta yi mana siyayya,amma ya ce kar na faɗa sai ya turo manya an ba shi izini" 

Wata guɗa Baba Delu ta rangaɗa na farinciki.

"Allah na gode maka da ka sharen kuka na, Mara tun yaushe akai haka ba ki sanar da ni ba" ta yi dariya tana faɗin" ai ya ce kar na faɗa,kullum sai ya ba ni goma ko ashirin ma.


Lube da bata san duk abinda Ɗanliti yake akanta yake ba sai yanzu.Baba ta ce" Lube kina son Ɗanliti?" Cikin yarinta da rashin sanin me ye so ɗin ta ɗaga kai alamar eh.Yeeehhhh duk suka sa ihu su Mara da Marawiyya dan burinsu kawai a sha biki.Lube kuma burinta ta yi aure a siyamata alkaki da nakiya ta yi ta ci,a siya mata robobin ɗibo ruwa iri ɗaya yau ta fita da wannan kala gobe wannan.



Sun daɗe suna ta budirinsu, sannan kowacce ta tafi gidansu.

Washe gari Baba ta sanarwa da ƴaƴanta to akwai Ɗanliti, yanda akai ta faɗa musu,Ali wanda yake ganin rashin dacewar a nemo Ɗanliti da maganar ya ce"ku gafarce ni Baba,da ni da Lube duk mallakinku ne,amma dan Allah da abar maganar auren nan yanzu zuwa nan gaba" 

Gaba ɗaya suka rufeshi da faɗa" sannu ubanmu na ce sannu Malam Habibu watukun mu ba mu iya hukunci ba sai kai ko, wai kai nan kana zaga duniya ko,to auren za mu yi mata,naga ɗan bantan uban da zai hana" ta ƙare tana nishi.

Baba Sa'idu ya ce" ka ba ni mamaki Ali watukun ka nuna mana ba mu isa muyi ikon da ƴarka ba ko" nan Ali ya dinga bada haƙuri,ya na ta danasanin maganar da ya furta.


Lube da take laɓe tana jin abinda ake faɗa akanta sai murna take za ta yi aure,sai da ta ji Baba Lawan zai neme Ɗanliti hankalinta ya kwanta.


Musamman Baba Lawan ya nemi Ɗanliti,cikin biyayya da ƙanƙan da kai.Lawan ya ce" na tasoka rana tsaka" Ɗanliti ya ce"aa babu komai Baba Allah dai tasa lafiya" Lawan ya ce"lafiya lau magana ce muke ji a wajen yara game da kai da Lubabatu" take Ɗanliti ya cika murna ya kuma ƙanƙantar da kai ya ce"bashakka anyi haka Baba,amma ban fara magana da ita ba ne sai na zo na nemi izini" sosai Lawan ya ƙara yabawa da hankalin Ɗanliti.Take Baba Lawan ya ba shi izinin zuwa su gana da Lube sannan ya turo manya.


Murna kamar zata kar Ɗanliti, yana tafe yana dariya da nishaɗi, babu abinda yake hange irin abinda zai samu a jikin Lube.Shagon Zayyad ya nufa dan yi masa kyakkywan albishi tarar da shagon a rufe ya yi, ya wuce hayin diga gidansu.



Iyayensa ya faɗawa zaa je nema masa aure, sun yi murna sosai dan gadon gidansu ne yawan aure-aure.


Tunda ya koma gida yake ta zumuɗi, Uwangale sai kallonsa take gajiya ta yi ta ce"megida wai me muka samu ne kake ta wannan ɓarin jiki haka?" Ɗanliti da ya ke ta goge kaushi ya kalleta kallon sorry'nki ɗin nan ya ce" taɗi zan je, ki shirya karɓar ƙanwa kwanan nan" dariya Uwangale ta yi ta ce" wai taɗi to sai ka dawo" ya juyo sosai ya ce" ba fa da wasa nake miki ba, alkur'an aure zan ƙara Uwangale" wani hantsilowa ta yi daga kan turmin da ke girke a tsakar gidan sai ta miƙe tsaye idanunta suka fiffito waje, ta ce" idan ka isa ka ƙara aure wutar Allah ta ci ni za ka wa kihiya" ta nufo shi gadan-gadan cikin gushewar hankali......





******

Gida ne mai tsananin tsaho a ɗunƙule yake shi kaɗai tal a tsakiyar daji, ko tsutsu sai a wuni bai gifta ba, wata ƙofa ce ƴar ƙarama gajeriya a jikin gidan da alama nan ne ƙofar shiga. Wasu samudawan ƙarti ne ke kai kawo a gidan babu ɗigon imani a idonsu.

Wani ɗakine cike da yara ƙanana sai kuka suke suna zazzaune anyi musu aski kannan ƙwal, duk kaninsu tsirara suke, an kullesu.Wani rami ne daga tsakiyar gidan kamar rijiya, ƙofa ce ta shiga gidan ƙasa, wanda anan ne ƴan Cultism ɗin suke tsafe-tsafensu da sassan jikin ɗan Adam.


Daga can ciki wasu ɗakuna ne ajere sun fi guda ashirin, tankar cell, Mahaukata mata ne a ciki gaba ɗayansu ba su haura shekara ashirin ba wasu da tsohon ciki suna zaune, wasu na ta surutai wasu ba um-ba um-um........



Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.