Free chapter · Read without an account
011
*BAYA DA ƘURA.*
Fitattubiyar2025
©️Nana Haleema.
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11
*BOOK 1*
*Page 011*
Da safe kasancewar monday ce da wuri ya tashi ya shirya bai shiga wajan Mummy bama ya hau mota ya fita. Kai tsaye asibitin ya wuce sanin yana da appointment da wasu patients ɗin yana zuwa kuwa ya tarar da mutane da yawa suna jiran zuwan sa. Zaman sa babu jimawa ya fara duba mutane wasu ya basu magani wasu ya basu test, wsu a kawo masa kafin wani lokaci ya gama dasu sai ya shiga ɗakin da ya ajjiye Mama jiya.
Kallon ta yayi yana sake kallon bugawar zuciyar a na’ura sai kuma ya ɗauki abin gwada bugun zuciya dan so yake yaji da kansa ya auna bugun zuciyar ta ba laifi ta dawo daidai amma ba wani sosai ba, allura ya sake mata sannan ya fita zuwa inda Manal din take.
Tana zaune ta dafe kanta idanun ta biyu tana zubar da hawaye ya shiga da sallama ta ɗago ta kalle shi, yadda fuskar ta tayi ja abin ya bashi mamaki sosai tace, "ina kwana Dr, ya jikin Mama? Tun ɗazu nake so na ganta ance sai kazo dan Allah ka nuna min Mamana" tana faɗa tana hawaye.
Matuƙar tausayi ta bashi ya tausasa murya yace, "Maman ki tana nan lafiya."
"Ina so na ganta don Allah." Numfashi ya sauke a yanayin da maman ta take ciki bazai so ta ganta ba sai yace, "zaki ganta." Abinda yace kenan ya juya zai fita tace, "don Allah ka taimaka min naga Mama."
Baice komai ba ya fita dan bai san abinda zaice mata ba. Da nurses ya haɗu yana musu tambaya akan Manal yace, "an mata Fbs?."
"A'a ba'a yi ba." Da mamaki yace, "meyasa?." Wanda yake tambaya yayi shiru sai yayi tsaki ya koma inda Manal ya take yaga ta kwanta har lokacin kuka take.
Ganin yanayin ta sai yace, "zo." Abinda yace kenan a taƙaice ta kalle shi fuskar sa tana nan kamar kullum babu annuri ita kuma hakan ne yake bata tsoro dan kana ganin sa take wanda bashi da mutunci. A tsorace ta tashi zaune ganin zai fita sai itama ta tashi tsaye kanta na ciwo sosai amma saboda kar ciwon ya hana ta ganin Mama sai ta biyo shi duk da jiri take ji sosai. Ɗakin da ya shiga ta shiga itama ta hango Mama a kwance an saka mata ruwa ga oxgen a hancin ta da wani abu a yatsan hannun ta.
Da sauri ta ƙarasa wajan Mama tana kallon ta tana hawaye amma bata ce komai ba ta riƙe hannun Maman amma ta kasa magana yadda kanta yake ciwo bata tunanin zata iya magana a wannan lokacin. Kallon ta kawai yake yi tausayin ta yake ji a ransa, yadda take yi ya tabbatar masa da tana qaunar Mamn ta sosai sai yake ji ko shine Mummy take wannan yanayin bai san ya zai yi ba.
"Muje ko?." Jin abinda yace bata yi musu ba ta saki hannu Mama ta fito yana binta a baya har ta koma ɗakin da take ta zauna, shima bai fita ba ya duba gefe ya sauke ɗaukar glucometer ya sake auna sugar ta har lokacin bai yi yadda ake so ba ya kalle ta har lokacin tsayan ta yana hannun sa yace, "kin ci abinci?." Kai ya girgiza alamun A'a yace, "ina ƴa uwan ki?." Murya a shake tace, "basu zo ba."
Kai ya girgiza ya saki hannun ta ya fita. Tana nan zaune ba jimawa sai ga nurse mace da abinci ta shigo dashi tace, "Sannu, ga abinci Dr yace a kawo miki." Ajjiyewa tayi abincin a pack anyi selling ɗin sa da cleamfim. Kai kawai Manal ta ɗaga amma baza ta iya ci ba nurse ɗin ta fita.
Tana kwace ta sake gwada kiran Baba amma har lokacin wayar a kashe, take ta ajjiye wayar tana juya kanta har ta kawo bata gani ma sosai komai guda biyu yake ganin sa. Bebi koda ya koma office aiki kawai yake na ganin marasa lafiya dan yasan Huzaifa da Hamza suna babban asibiti sai azahar zasu je. Abubuwa sun masa yawa yana nan yana can duk da akwai taimakon nurses ga kuma sauran likitocin da suke aiki tare.
Glucometer ya koma ɗakin Manal dan ya ɗauka ya gwadawa wata mara lafiya nata jinin ya ganta kamar a sume take. Da hanzari ƙarasa inda take yaga idom ta kulle. Hannun sa ya kai wuyan ta yaji zafi sosai yace, "Subahanallahi." Abincin ya kalla yaga da alama ba'a ci bama, da gaggawa ya fara taimaka mata saboda yanayin jikin yayi weak sosai kuma ya tabbatar sugar tane yayi ƙasa da yawa.
Ganin ya saita komai sai ya fita ya kira nurse ɗin da ya tura ta bata abinci ta shiga office ɗin da sallama kafin tayi magana yace, "aikin nurse ne kula da mara lafiya ko ba aikin sa bane?." Jin hakan sai tayi shiru tasan tayi wani abun yace, "na baki abinci ki kaiwa patient sai ki ajjiye baza ki tabbatar taci ba? Wanne irin aiki ku ke yi wannan? Kin manta duk wata kulawa ta mara lafiya a kan ku take?, meyasa baku san aikin ku bane wani lokacin?."
"I'm sorry Sir!."
"Sorry for what? Sorry for your mistake?." Shiru tayi bata amsa ba daman in aka taɓo shi yan faɗa baya tsayawa. Shigowa office ɗin akayi Huzaifa ya kalli nurse ɗim da take tsaye ya kalli Bebi kafin yayi magana a Bebi yace, "In baku canja ba gabaɗayan ku zan ajjiye ma ɗauki wasu, wannan ai shirme ne da rashin hankali. Ku shiga medication baza ku yiwa patient fbs ba kawai sai bashi magan kun san diabities patient ne?.” Shiru bata ce komai ba yayi tsaki yace, “out!." Ta juya ya fita jiki a sanyaye.
Huzaifa yace, "laifin ta sake yi?." Tsaki yayi kawai baice komai ba kafin ga kalle shi yace, "har ka gama da can?."
Zama Huzaifa yayi yace, "A'a, nazo nan ne naga jikin Manal then na koma. Hankalina yana nan gabaɗaya." Wani irin kallo Bebi yayi masa har sai da Huzaifa yace, "wannan kallon da kake min na meye?." Bebi ya ɗage gira yace, "saboda ita ka baro wanda suke jiran ka kazo nan?."
"Yes, but I will go back now."
"What kind of relationship do you have with her?. Wacece ita ɗin ka?."
Huzaifa yayi murmushi yac, "nothing is going on between us, i simply adore her." Bebi ya jingina a jikin kujerar yana kallon sa yace, "ƙarya ka ke, akwai wani abun a ranka akan ta.”
Huzaifa yayi murmushi yace, "babu komai a tsakanin mu ina mata kallo kamar ƙanwata ne, mun saba da ita sosai tunda ni suke gani duk sanda suka je asibiti. Tana kula da Mama ta sosai shiyasa nake mata kallon kamar ƙanwata. Baka ji itama Yaya take cemin?.” Bebi yace, "hmmm! kai dai ka sani." Huzaifa yace, "na shiga ɗakin sai naga itace kawai a kwance, any problems?."
Bebi yace, "jiya an samu problem akanMaman ta, a yanzu ma Maman ta tana kwance babu lafiya sosai. Itama ƙanwar taka blood sugar ɗin ta is very hypo, shine dalilin faɗan da kaji ina yiwa wannan yarinyar."
Huzaifa yace, “mostly daman ita blood sugar ɗin ta bai cika zama so hyper ba gaskiya, yana tafiya daidai tana ƙoƙari wajan kiyayewa that’s why ban ɗorata akan magani ba, iya diet ɗin is okay dan bai fi sau biyu naga sugar ta yayi high ba, shima tace min cake taci.”
“Okay” abinda Bebi ya faɗa kenan dan shi bai ga amfanin bashi wannan labarin ba.
Huzaifa yace, "kuma har yanzu babu wanda yazo daga gidan su?."
"Ni zaka tambaya ko kai zan tambaya? Ƙanwar ka ko ƙanwata?.”
“Kai ma ƙanwar kace tunda kana da kamar ta.” Bebi ya yi shiru baice komai ba, Huzaifa ya girgiza kai shima baice komai ba kafin Bebi ya tashi ya fita shima ya biyo bayan sa.
Hanyar ɗakin sukayi a tare suka hango Surayya a tsaye a wajan ganin Huzaifa sai ta ƙaraso wajan su tace, "ina kwana?." Huzaifa ya amsa dan suna yawan zuwa asibiti da ita da Manal tace, "Dan Allah milky beauty ma bata da lafiya? Naga banga Mama ba kuma naga itama an saka mata ruwa." Huzaifa yace, "wacece Milky Beauty?."
"Manal nake nufi." Huzaifa yace, "eh, kin san tna da ciwon sugar ko?."
"Eh na sani."
"Shine yayi ƙasa, in ta farka ki tabbatar kin bata abinci taci." Surayya tace, "to, Maman fa ya jikin ta?."
Huzaifa ya kalli Inda Bebi yake yaga baya wajan ya kalle ta yace, "da sauƙi, kar ki damu zata dawo daidai." Kai kawai Surayya ta ɗaga ta shiga inda Manal take, gani tayi ta bud'e ido sai ta koma ta fita dan ta faɗawa Huzaifa amma baya wajan sai Bebi.
"Likita ta farka." Jin haka sai ya juyo ganin fuskar sa sai taji wani iri domin baiyi kama da mai mutunci ba gabaɗaya. Baice komai ba ya wuce zuwa ɗakin ya kalli Manal da take kwance idanun ta a buɗe ya kalli ita Surayya ɗin yace, "abinci zaki bata taci." Zatayi magana yace, "kar ki damu ki bata ko wanne ma.”
"Amma Milky bata cin abinci in bata sha tea ba, in taci bata sha ba amai take yi. Gashi ban zo da ruwan zafi ba." Ya kalle ta jin tana kiran ta da wani suna wai milky, shi baya son iyayi a rayuwar sa yafi son mace sak komai za’a yi ayi shi kai tsaye, yayi tsaki ya nuna mata inda kettle take baice komai ba kawai ya fita.
Da kallo ta bishi kafin ta ɗauke ido Huzaifa ya shigo yace, "ta farka?."
"Eh ta farka, na faɗawa wannan likitan wanda na ganku ɗazu." Baice komai ba yaje inda Manal ɗin take ya kalli Surayya tace, "abinci zaki bata taci, in da dama a bata ko wanne ma."
"Na faɗawa wancan likitan bata cin abinci sai ta sha tea wallahi, amma sai yayi tsaki yana nuna min can wajan kuma ban gane ne yake nufi ba. Ka fishi mutunci walalhi."
Huzaifa yayi murmushi yace, "kar ki damu yana nufin ga abin dafa ruwan zafi nan, ina da tea leave da sugar a office zan aiko a kawo miki sai ki haɗa mata tasha, amma sugar din kaɗan zaki saka mata ba mai yawa ba. Amfanin sa dan ya farfaɗo da blood sugar ɗin ta da ya sauka sosai.”
Surayya ta amsa ya fita yana darıya, wato in baka san Bebi ba nan take zaka tabbatar da bashi da kirki da fuskar sa batayi kama da ta masu kirki ba ko kusa. Amma da ka san waye shi kun saba a nan zaka tabbatar da kirki ma a wajan sa ya samu mafaka, musamman ma ace ke mace ce, Allah ya saka masa tausayin mace da kishin ta.
Mubeena a safiyar suna cikin makarantar Yusuf mai tama sule ta ƙofar nasarawa, fitowar su daga class kenan Bily ta kalle ta tayi dariya tace, "ke dai Mubeena wani lokacin kin yi asara wallahi, an kore ki daga school amma baki daina zuwa kina zaman lectures na banza da wofi ba." Mubeena tayi dariya tace, "zaman gidan mu ne bana so ke kin sani, kuma ni ko Manal bata san an kore ni ba."
Bily tace, "wataran zata sani ai." Waya ta ɗauka tana dannawa Bily tace, "dawa kike magana ne kina tafiya?."
"Baby ne, zai aiko a ɗauke ni kin san yau zai canja min waya." Bily da mamaki tace, "ke wai baza ki hankali dashi ba? Ke kika faɗa min kallon da yake miki da yadda ya riƙe ki bakya jin tsoro ne wai ke?. Kuma in ya canja miki waya ki cewa Mama waye ya baki?. Ni wallahi duk ya sire min.”
"Meye na tsoron? Falaqi da nasi kawai zan karanta ta zama makami akan ko wanne shege, dan ya riƙe ni wannan kin san normal ne ai ba wani abun bane, kawai na tsorata ne kasancewar hakan shine na farko amma bayan nan ai bai min komai ba ko?."
Bilkisu tace, "ki dai yi a hankali wallahi, domin somi somin hauka zubar da yawu." Mubeena tace, "kar ki yi min baki, aurena zaiyi in sha Alalh." Bily tace, "Allah yasa, zan fi kowa murna indai da gaske auren naki zaiyi. Yauwa yanzu mu je mu duba Mama daga nan sai mu wuce gida" ta faɗa a lokacin da suke zuwa wajan motar Bily.
Mubeena tace, "ai ni ba bin ki zan yi ba, na faɗa miki zai aiko a ɗauke ni, ke kije kawai ai na baki address ɗin wajan." Bily da mamaki tace, "kee Mubeena kiji tsoron Allah, yanzu baza ki koma wajan Mama ba?."
Mubeena tace, "to naje nayi me dan Allah? Naje jiya ban samu ta ganni ba to me zan koma nayi?, in naje bama ba lafiya zan bata ba kuma Manal zata yi mata komai." Girgiza kai Bily tayi tace, "lallai rashin jin ki ya wuce inda nake tunani, ni na wuce" ta faɗa tana shiga mota taja motar ta barta a wajan. ba jimawa aka zo da ƙatuwar mota aka ɗauke ta suka bar cikin makarantar.
Suna cikin tafiya drivern ya kalle ta ta madubi yace, "ranki ya daɗe akwai saƙon da Alhaji ya bayar yace na baki" ya faɗa yana nuna mata wata leda a kusa da ita. Ledar ta ɗauka ta buɗe, kwalin iPhone ne a ciki da hanzari ta buɗe taga wayar sabuwa dal a ciki, ta duba takardar jiki taga an rubuta iPhone 16 pro max. Farin ciki taji yana mamaye mata zuciya ta cigaba da juya wayar bayan ta kunna tana ji kamar tayi ihu saboda murna.
Wayar tace tayi ƙara ganin Babyn tane sai ta ɗauka cikin yanga da shagwaba tace, "Baby!." Daga can ɓangaren yace, "Babyna, an baki saƙon ki?."
"An bani Baby, na gode sosai."
"Kar ki damu Baby, kin cancanci fiye da hakan a wajan. Anjima kaɗan jirgina zai tashi zuwa lagos ina so na ganki." Mubeena tace, "to ai kaine baka zo ɗaukana ba."
"Ina da baƙi ne Baby, amma yanzu in kina so ya kawo ki nan inda nake daga nan sai ku wuce gida, minti biyu kawai ganin ki zanyi ki koma."
Mubeena tace, "Kar Mummy tayi min faɗa fa Baby."
"Baza tayi miki faɗa ba, baza ki jima ba ai."
"To gamu nan."
"Thanks you Baby, sai kun zo" ya faɗa tana yanke wayar ta faɗawa driver suka wuce gidan alhaji Mu'azzam.
Har gidan aka shiga da ita a motar ya fito aka nuna mata inda zata bi ta shiga cikin gidan ta same shi a zaune akan kujera yana danna waya ganin t sai ya miƙe cikin nuna farin ciki yace, "Welcome my Baby."
Murmushi yayi ganin harda buɗe mata hannu alamun runguma sai ta basar ta nuna kamar ba gani ba yayi murmushi yace, "Zauna Baby, ya school?."
"Alhamdulillah." Kallon ido cikin ido yake mata yace, "a kawo miki ruwa?." Kai ta girgiza alamun A'a kafin tace, "Ashe ma baka shirya tafiyar ba kasa nazo" ta faɗa da shagwaɓa wacce ta shige shi lokaci ɗaya ya kwance ya kasa gane kansa. Daƙyar ya danne abinda yake ji yace, "Yanzu zan fita ke kawai na tsara na hani."
Bata ce komai ba y sake cewa, "Dama zaki raka ni da nayi farin ciki." Murmushi kawai tayi bata ce komai ba ta miƙe tace, "zan koma gida Baby, sai ka dawo a kawo min tsarabar lagos." Ya miƙe tsaye yace, "kar ki damu, in ma lagos ɗin kike so a ɗauko miki zan kawo miki" ya faɗa yana matsowa kusa da ita kafin yace, "in na tafi zanyi kwana biyu ban ganki ba, baby please ki bani hug guda ɗaya wanda zan tuna dashi in bana nan." Jin abinda yace sai ta kalle shi kamar wani yaro har marairaicewa yake sai tayi murmushi dan wallahi dariya yake bata tace, "A'a ni dai."
"Yanzu bazan samu ba kenan? Ni ki bani dama to." Ƙafa take bugawa cikin son sake burge shi tace, "A'a nidai." Hakan da tayi bai san lokacin da ya jawo ta jikin sa ya rungume ba yana furta, "ina sonki Baby." Sacanni bai wuce goma ba ta janye jikin ta tana turo masa baki gaba wanda yake jin wani abun na fizagar sa akan bakin tace, "to zan tafi." Cikin taushin murya yace, "bana so ki tafi, ki tsaya a nan kin ji baby" ya faɗa yana riƙe hannun ta.
Bata ƙwace hannun ba tace, "A'a ni dai yafiya zanyi." Ya sauke numfashi yace, "shikenan Baby tunda bakya son kasancewa dani." Bata ce komai ba bai saki hannun ta ba ya ɗauki wayar sa yana dannawa da hannu ɗaya kafin ya kalle ta yace, "na tura miki kuɗin shan ice cream." Murmushi tayi tace, "thanks you Baby."
"I love you Baby."
"I love you so much" ta faɗa da wata murya mai ɗaukar hankali.
Ɗakyar yake iya riƙe kansa, amma ji yake kamar ya fizgo ta ya kama bakin ta ya tsotse shi ya haɗe kirjin sa da mata yana jin buguwar zuciyar shine abinda yake buƙata a wannan lokacin, amma baya son yi mata shigar sauri dan sabuwa ce shiyasa yake bin ta a hankali, ya san lagon mata irin ta sababbi. Har ƙofar falon ya tako ta kafin ya koma ciki ta shiga mota su ɗauki hanyar gidan su Bily.
Shima gidan ya shirya ya bari ya tafi gidan sa ya ajjiye motar sa ya shiga ɓangaren sa kai tsaye. Mama daman jiran zuwan sa take tunda ta san yana garin, tana ganin ya dawo ta nufi ɓangaren nasa ta same shi a tsaye a falon yana amsa waya yana murmushi a lokacin da yake cewa, "zanyi kewar ki sosai Baby, kamar na fasa tafiyar nan." Taji abinda yake cewa sai bata nuna ta ji ba ta shiga da sallama ya amsa yana yanke wayar bai kalle ta ba tace, "sannu d zuwa." Sai da ya kalle ta sannan ya cigaba da abinda yake yi yace, "Yauwa."
Mama tace, "ina so zanje na gaida Hajiya an jima." Fuskar sa a ɗaure matuƙa yace, "sai kin dawo." Ta juya zata tafi yace, "zanyi yafiya zuwa lagos yau, ki faɗawa ƴar uwar ki." Mama ta kalle shi tace, "ai mu ko yaushe a baka nan muke ɗaukar ka a gidan nan, ko baka faɗa mana ba, hakan ba sabon abu bane a wajan mu Alhaji."
Kallon ta yayi kamar zai magana sai ya fasa tayi dariyar takaici tace, "Su baby sune suke ganin ka ko yaushe, amma matan gidan ka sune basa ganin ka sai lokacin da ka so, sai lokacin da su Baby suka sallame ka ka ke zuwar mana." Ya kalle ta yace, "me kike nufi?." Kai tsaye tace, "ƴan matan ka nake nufi, sune suke ganin ka ko yaushe available amma matan ka na gida ko yaushe baka nan a wajan su, Allah ya kiyaye hanya. Sannan ina yawan faɗa maka ka dinga sara kana duban bakin gatari, kar ka bar baya da ƙura” tana faɗa ta fice ya bita da kallo sai ya share dan kar maganar tayi tasiri a zuciyar sa. Abinda yazo ɗauka kawai ya ɗauka ya fito y sake gida mota driver ya ja suka fita.
Zuwa yamma Manal taji faɗin jikin ta sosai, wanka take so tayi ya canja kaya gashi Surayya ta tafi. Tashi tayi ta fita zuwa ɗakin da Mama take tana kallo duk da bata ganin ta a wajan ta kallon ɗakin ma kawai hankalin ta kwanciya yake yi. Tana zaune tayi tagumi tana hawaye Bebi ya fito daga ɗakin ya kalle ta dan bata ji fitowar sa ba.
Wucewa sa ta gani ta gaban ta ta kalle shi taga dai shine sai taji tsoron tambayar sa halin da Mama take ciki dan babu wannan fuskar a tare dashi. Miƙewa tayi kawai tabi bayan sa duk da bata jin dadi amma haka ta tashi ta bishi zuwa office ɗin da ya shiga, ƙwanƙwasawa tayi ya amsa daga ciki ta shiga da sallama ta same shi a tsaye shan ruwa, ya kalle ta ta kalle shi ya sauke jarkar ruwan daga bakin sa ya amsa sallamar sannan tace, "Likita don Allah ya jikin Mamana?."
Kallon ya yayi yaga kamar jiri take a tsayen sai yace, "zauna" ya faɗa yana nuna mata wajan zama ta zauna ya ajjiye ruwan ya ƙarasa inda take ya zauna akan kujerar da yake zama ko yaushe yace, "jikin ta da sauƙi zata samu lafiya." Ta goge idanun ta tace, "yaushe zata tashi?."
"Nan kusa!" Ya bata amsa a taƙaice.
Kafin tayi magana yace, "meye sunan ki?." Murya na rawa tace, "Manal."
Ya maimaita sunan a zuciyar sa kafin yace, "Ina Baban ku?."
"Baya nan yayi tafiya ina ta kiran wayar sa a kashe take."
"Baki da Yaya namiji?." Ta girgiza kai tace, "bani dashi, sai dai ɗan Baban mu kuma baya ƙasar nan yna Qatar.”
Yayi shiru kafin yace, "yaushe Mama ku ta samu ciwon rashin gani?." Manal tace, "ba'a fi shekara uku ba, kuma da tana gani da rana da daddare ne ganin yake raguwa sosai."
Ya girgiza kai kafin yace, "zuciyar fa?."
"Ta riga samun zuciya akan idanun, ciwon baiyi yawa bane sai yanzu." Ya girgiza kai cikin gamsuwa yace, "zata samu lafiya in sha Allah. Kar ki damu, kwantar da hankalin ki.”
"Allah yasa" ta faɗa a raunane hawaye na zubo mata. Sosai yaji ta burge shi da alama tana son Mama ta sosai, shi kuma duk wanda yasan darajar iyayen sa yana samun matsayi babba a wajan sa yace, "zaki din shan wannan magani kema shine zai dinga daidaita sugar jikin ki, but na iya lokaci kawai ba ko yaushe ba” ya faɗa yana tura mata maganin gaban ta yace, "ki buɗe yanzu ki sha kafin ki tashi."
Da to ta amsa ta buɗe maganin ta riƙe a hannu tana kallon inda taga yasha ruwa, tana niyar tashi ya dakatar da ita ya ɗauko mata ya ajjiye tayi murmushi tace, "Na gode." Maganin ta sha ya kalle ta yace, "zaki iya tafiya."
Manal tace, "don Allah zan iya zuwa gida na dawo? Har na dawo Mama bata farka ba?." Ya ɗaga mata kai ta tashi ta fita ya sauke numfashi yayi shiru cikin tunani. ganin macen da yayi a motar mahaifin sa yana sake dawo masa cikin zuciyar sa da idanun sa.
Manal daga nan ɗakin da take kwance ya koma ta saka takalmi ta fito zuwa bakin titi. Titin kamar anyi shara babu abin hawa ko kaɗan shiru, kasancewar asibitin a cikin gra ne ba’a samun mota sosai a hanyar sai kayi sa’a. Tana nan tsaye sai taji tsayuwar baza ta yu ba sai ya zauna akan wani ƙaramin dutse da yake gefen wajan.
Wanda ya kai ta wajan Alhaji Mu'azzam ta gani gaban ta yayi mugun faɗuwa ta tashi tsaye tana kallon sa, ganin kamar ita yake nufowa tana ja da baya bata san ta shiga kan titi ba ga mota ta tawo sai jin ta tayi a ƙasa tayi ƙara.