Free chapter · Read without an account

11

by Ramlat Abdulrahman Manga · SO da CIWO

*❤️‍🩹SO da CIWO❤️‍🩹*



®©Ramlat A Manga

  Mai_Dambu

Paid book 

*Assalamualaikum everyone yau mun zo muku da ingantattun maganin mata daga shahararriyar mai maganin nan De Majestic Aprodiasic best kayan mata ever, We have the best kayan mata 100 natural kada ki zama Bora a wurin namiji kada ki zama koma baya a wurin kishiyoyin zo ki gwada ki yadda babu wacce zata d'aga miki kafada macen da tasan ciwon kanta ita take gyara buje 😆🤣 anayi ana sha'anin arziki*


Muna d ingantatun kayan mata kamar hka:

Maganin sanyi 

Exclusive Tsumi 

Abulbulo 

Gumbar Madara 

Gumbar budurci 

Zumar budurci 

Zumar kacha kacha 

Royal Honey 

Zumar goran tula

Garin Emergency 

Garin kwatai 

Sallanta

Dan wata bakwai 

Spoil her HQ 

Back to virgin set 

Exclusive zuma

Tsumin Ayu 

Man Ayu 

Maniyin Ayu 

Zumar Ayu 

Gaban Ayu 

Kazar Mallaka 

Kazar sirri

Zabon Amare

Dan Shila 

Ciccibi 

Dambun nama

Man power 

Yajin Maza 

Men energy

  Gamu bukatar kayanmu su tuntubi wannan number *** we are the best among the other' 


11

"Bai da ce dake ba, don haka ba zaki auri Sharahbil ba." "Akan me? Ina ruwnaka da Ni? Ina ruwnaka da matsalata? Ina ruwanka da rayuwata?" Na fada da karfi ina kuka, make min kai yayi na kara fasa ihu Mama ta ce mishi. "Matsalata da kai saurin hannu." Cikin shashekar kuka na ce mishi. "Idan aka fasa auren Baffanmu ya kori Yaya zaka iya nima min wata Uwar? Zaka iya nima min madadin Yaya? Ko idan ya kore su dukkansu biyu zaka iya kula da ni ne babu su, idan kuka yi wani abu Yaya ta bar gidan nan, wallahi mutuwa zan yi domin Baffanmu ya ce sai ya saka kafar wando daya da ita." Yadda na fada ina kukan yasa ita kanta Yaya da tazo make ni ta gaji da rashin mutuncina, ta tsaya cak tana kallon Mama, tashi Mama tayi tana murmushi. "Duk Yaran dakin da na dakinki,duk kin rike baki tab'a raba su da jikinki da jininki ba, ita kuma tana kulafucinki, amma kike watsar da ita. Yanzu take bukatarki imma ki janyo haushin da take baki, imma muna ji muna gani mu rasata, kin san duk da sakarya ce tana son iyayenta abin da kika kasa fahimta kenan!" Fita suka yi Hamma Umar ya zauna kusa da ni domin tunda na ambato batun Baffanmu zai saka kafar wando daya da Yaya, jikinshi yayi sanyi.


Rigimar da ake a gidanmu ya fara damuna, domin sau biyu ana zaman meeting a kaina da sharahbil, na farko bashi hakuri da nayi n a daukar laifina na biyu bayan an gama wannan wani maganar ya kara fitowa, wannan lokaci abin ya fusata Mama domin kuwa maganar abin da ya faru lokacin Ina Asibiti aka turawa Mahaifiyar Sharahbil, sai da Baffanmu yayi barazanar sake su Mama da Yaya, don ya fahimci cewa bakinsu ɗaya, domin cewa yayi su fita su bar gidan, ko ya saka kafar wando daya da su, ni dai wannan kalmar tana min ciwo, aka yi ta bashi hakuri amma Baffanmu ya fusata abin haɗin baki daga Mama har Yaya hade kayansu suke ta yi, na fito na same shi a har lokacin fada yake yi. "Baffanmu!" "Na'am Rahmatullah!" "Idan Mama da Yaya suka bar gidan nan, zuwa nan da minti talatin in sha Allah zaku yi zaman jana'izata ne, na gaji na ce zan auri Sharahbil me yasa basu huta ba? Shi kenan!" Na juya na koma daki, kallon fan din dakina nayi na kashe na nufi closed dina, na bude tare da wargaza duk abinda yake ciki na ciro wani igiyar kayana. " Are you attempt suicide Rahmah?" Muryan Baffanmu ya ratsa dodon kunne na. Juyawa nayi ina kallonshi kaina a sunkuye hawaye na zuba daga idanuna. "Ya dace ki min haka Maamah?" Muryan Yaya ya ratsa tsakaninmu, "Maamah me muka miki mai zafi da zaki dauki rayuwarki?" Inji Mama da take kuka. "No wannan ba Maamah ta bace something happened with you Maamah talk to me Maamah m, waye yake baki umarnin kashe kanki ba kanki daya ba!" Fadawa jikin Baffanmu nayi ina sauke ajiyar zuciya da shakuraren kukan da nake yi. "I'm sorry Baffanmu, ba zan kara ba kada ka kore su Please Baffanmu ko mahaukaci ka bani idan su Yaya zasu zauna nima zan zauna da shi, I'm sorry Baffanmu su Mama basu tab'a cewa na rabu da sharahbil ba, baffanmu ka ji tausayina bani da kawaye sama da Mama da Yaya, bani da kowa da na taso na gani sama da Yaya da Mama, Baffanmu kada ka dauki laifin da ba naso ba ka daura musu, Please i need then!" Rufe ni yayi da babban riga yana shafa kaina ya ce. "Maamah ke albarka ce da rahama, taya xan kasa amsar rokonki? Na hakura!" Juyawa yayi ya kalli Mama ya ce mata. "Hassanah kira min Abdulkarim ya duba min ita." "Tow Alhaji!" "Where is your phone?" Yaya ta tambaye ni, rintsa idanuna nayi jikina yana rawa, na d'ago kai na kalle shi babu wasa a fuskarta. "Yayana kiyi hakuri wayar tana hannun Heemah?" "How long?" "Kifa kaina nayi a jikin Baffanmu naki magana." "Please Abidah ki kyaleta!" Fita tayi daga dakin ta nufi gidansu Heemah, suna parlourn suna ta dariya,ta same su tare da kawayenta. Ganin Yaya ta san halin Yaya bata wasa kai yaran gidan da manya da Yara kowa shakkar Yaya yake, ita ko wasar jika da kaka bata yi. "The phone!" Ta mika mata hannu, ba musu ta nufi dakinta. Itama Yaya a sassarfa ta bita bata san yaya ta shigo ba, cikin fada ta kira Maamah "Ni wannan shegiyar yarinyar zata hada da Uwarta?" Ta baya Yaya ta kwashe da da mari sai da ta zube a kasa. A razane ta kwalla kara, Yaya ta mika mata hannu ta mika mata wayar. "Don na kyale Rahmah tayi yadda take does mean na ce useless child irinki su yi control din ta, i will make sure da na raba wanan yarda da tayi miki, na kara ganinki ko na ji zuwanki wurin Maamah sai na saka an rufe Uwarki yadda zaki gane baki da wayo hakkin Maamah da kike dauka Allah sai ya sata mata, sannan nasarar Maamah da kike hangowa kike bakin cikin ki taka wurin In sha Allah, matuƙar Ina raye ba zan tab'a evil child like you su kusanci shadow din Maamah ba, keep your mind Maamah tayi nasara an gama domin ina gayawa Allah kuka na!" Daga haka ta fita, a bakin kofar suka hadu da Zaituna wato Aunty ita kanta tsoron Yaya take ji, kaf danginsu kowa yana shakkar Yaya, yanzu zata ci Uban kowa ta kwana lafiya, Yaya ita da mijin Addah Ma'u ya ishe ta da fitina, wanke kafa tayi ta nufi gidan Uwarshi wato Addah Mairoh, a gabanta taci Ubanshi ta kuma rantse sai ya biya rashin mutunci da yake idan yana wasa ne ya zuba idanun, tana barin wurin ta kira inda yake aiki domin familyn Yero sannannun mutane ne, haka yasa akan lokaci kafin ta isa gida an dakatar da shi a aikinshi, sannan wannan abin da ya faru ba bakantawa Alhaji Umar Datti rai, wato shi Abidah zata nunawa tana da arziki, kuma ai idan da Adalci case din naan anyi shi ba sau daya ba ba sau biyu ba, kullum cikin goyan bayan Yasir domin Yasir baya laifi saboda shine jikanshi na fari, sai gashi cikin ikon Allah, hukuncin da Yaya ta yanke aka dakatar da shi na tsawon wata uku, albashinsa ya tsaya cak, an rufe account dinsa ma an hana shi cire kudin ma, ai bai san lokacin da ya haukace tare da nufar Gidan Alhaji Umar Datti, yayi ta rokon ya kira Yaya ya bada hakuri duk abinda yake faruwa laifinsa ne, ba na Ma'u ba, dakyar Yaya ta saurare su tare da sharadi me karfi bata hana shi yayi auren shi ba, amma ya sake ya cutar da Asma'u zai gani a ƙwaryan cin tuwonshi, da yake warning din ya shiga jikinshi sai gashi tuni ya hau hanya dodar, daga nan duk wani case na Yaran gidan da na dakinta da dakin Mama, tana tsaye a kai haka yasa kowa yake zaune lafiya, sannan ko matsalar Abdulhameed da Shamshiya bata sani ba, da tuni ya zama tarihi.


  Tunda ya shigo dakin Mama ta same ni ina shan ta cilla min wayar ta fita zauna ta min nasiha da yasa nayi ta kuka, sannan ta ce min. "Ina ɗaya wayar?" "Yana kasar pillowna!" Fita tayi sai gata da wayar ta mika min wayar tana kallona fuskarta kamar hadari, saboda hadewa da tayi har wani jajjajan b'acin rai nake hangowa yasa jikina ya fara rawa, ban shirya na bude mata, fita tayi ban san me take nufi ba, tabbas na ji muryanta a fisace sama da kullum. Can naji Muryan Baffa Junaid yana ta bata hakuri, wanda na fahimci si ta kira. "Kamar Raheemah zata na gayawa Maamah maganar da yayi mata har tana kiranta masifa ce a rayuwar Ahalin Alhaji? Wallahi sai na shigar da Zaituna kotu a shiga tsakanin Raheemah da Maamah tunda bata da mutunci da take cewa Maamah ta kashe kanta wato da ta shafaffiya da mai zata kashe min y'a zan kira Abdulkarim ya zama shaida tunda shine lauyar kowa." Tunda ta fadi haka da wasu zantuttuka na fahimci Yaya so take ta raba ni da Heemah, kuma ban ga laifinta ba, ban san me yasa Heemah ta sauya ba duk da tun muna Yara take min haka, amma yanxu takai ta kawo kowa yana jin zafin abinda take min. Koda Baffanmu ya dawo ya ji abin da ya faru ya shiru yayi yana faɗin, lamarin ya fi karfinsa tunda har Raheemah tana faɗin kwanciyar hankalin zuriarmu shine na kashe kaina kowa zai yi farin ciki bayan an yi jimamin kwana biyu na rashina, Baffa Haruna ya kadu jin wannan furucin kamar umarni take bani na kashe kaina. Abin ya tashi hankalin Dattijo domin har gida yazo ya samu Aunty yayi mata rashin mutunci. Sai a lokacin ta farga da abin da ya faru tabbas ta fadawa Raheemah yadda Maamah take jin maganarta idan har ta ce mata ta kashe kanta zata yi, shine ita da yake mahaukaciya ce ta gwada haka. Ranar sai da ta yiwa Raheemah mugun duka, domin su take ta janyo mata masifa ana zaman lafiya. Ta kalleta cikin d'acin rai ta ce mata. "Kina tsammanin albashin Ubanki ne yake rike damu? Shegiya me kama da mayu, da nasan kanki babu kome da na kashe ki kafin ki saka min bakin ciki, albarkacin Maamah kike ci don ubanki shegiya wacce bata iya takunta ba, kika sake wani abu ya same ta sai na kashe ki da hannuna jaka wacce bata da wani abin alfahari sai dakikanci." Tana huci ta shure ta cikin hargagi ta ce mata. "Idan Ubanki yazo ki san yadda zaki kare kanki domin ba zan iya tsaya miki ba." Kiri-kiri Aunty ya juya mata baya, kamar tayi hauka haka Raheemah take ji.


  Da karfe tara Baffa Haruna ya shigo gidanmu, yayi ta bawa Baffanmu hakuri. Yana kuka domin shi kuma nashi jarabawar jinya da Matarshi tare da yarsa, Baffanmu ya kalle shi yayi murmushi. "Ko da wasa kada ka dauki damuwar Mata ka daura akanka, wannan shirme na dauke shi, Matanmu da Yaranmu ba zasu raba mana zumunci da kanmu ba, sai dai ina son na ji Raheemah me kike so Rahmah ta daina yi miki kamar akwai abin da take yi da yake miki zafi?" Da kunya ta ce ita mijin da Rahmah zata aura take so, don haka ta girgiza kai tana faɗin. "Babu kome Baffanmu, sharrin shaidan ne kawai." 


  Sai da Baffanmu ya kira ni ya haɗa mu yayi mana nasiha, tare da fada sosai kada wani ya cutar da wani idan yaji labarin zai saka kafar wando daya da mutum. Bayan mun tashi muka fito na wuce abuna domin Yaya ta min kashedin na rabu da Raheemah. "Twins!" Tsayawa nayi ina kallonta. "Kiyi hakuri bana nufin haka don Allah kada ki kullace ni." Murmushi nayi na ce mata. "Ya wuce ai!" Tun daga lokacin muka dawo sai dai ban yarda mun kara fada ba,.ko na shiga bangarensu kamar da. Amma har yau idan aka min abu xan raba biyu na tura mata Uwani ta kai mata rabi, Yaya da Mama kamar su kashe ni don takaici haka suka zuba min idanun tunda Baffanmu ya ce baya son tashin tashina.


***

 South Africa 

Dubai Mansion Houses.

Abhu Zar.

   Kwance yake idanunshi a rufe, wayar shi ce tayi ƙara. Ya bude golden eyes dinsa ya zubawa wayar idanun, kafin ya dauka. Lusmhe oil eyes din yayi domin har wani maiko maiko kwayar idanun da suka kasance zaiba yayi ya buɗe shi akan wayar. Tashi yayi a hankali kamar wanda kwai ya fashe mishi a cikinsa ya zauna shiru yana me sake bin wayar da idanun akaro na uku, kafin ya saka hannunshi a samar wayar ya tab'a alamar amsa kiran.."Abhu gani kofar gidanka!" Shiru yayi yana jin ta kamar ba zai yi magana ba, kafin ya kara amsa wayar ya ce mata. "Ok Ummina!" Zura kafarshi yayi kasa ya shuri takalmin dakin ya mike, yana jin kamar jiri-jiri yake ji, dafe kanshi yayi yana son tuna abin da ya faru daren jiya. A hankali yake takawa kamar yana yawo a gajimare. Har ya isa entry door na gidan ya bude kofar yana kallon Umminsa. Ajiyar zuciya ta sauke tana mishi wani irin kallo me tattare da b'acin rai. "Ina ka je jiya?" Ta tambaye shi bayan ta shiga cikin gidan. "Ina tare da Jacob!" Kallonshi tayi ta mika mishi wayarta. "Ummina ban san kome ba, kin san bana son hayaniya, ki yarda da ni ba zan tab'a kaucewa tarbiyyarki ba!" Ajiyar zuciya ta sauke a karo na biyu ta ce mishi. "Ka ji tsoron Allah kamar yana ganinka, shi wannan jin dadin rayuwar da kake gani me wucewa ne, jiya aka turo min sai da asuba na bude Dad dinka ya hana Ni doka maka sammako!" Yake yayi ya zauna yana kallon basket din da aka shigo da shi. "Sannu Ummina!" Amsar abincin tayi ta fara zuba mishi, tana faɗin. "Sam ban ji dadin video nan ba!" Shi kan bai da ta cewa domin tun da aka sallame shi asibiti kusan kwananki biyu da yayi a gidanta kamar ta mai da shi cikinta, sam bai da ikon motsi zata fara tambayar shi yana bukatar wani abu ne. Zai ce mata a'a har ya samu ya dawo gidanshi.


  Nasiha take mishi domin kuwa babu gatan da zata mishi da ya wuce, ya bar duniya lafiya idan ya sake wani abu ya hada shi da duniya tow bata da amana. Tana gamawa zaman ganin lafiyarshi tayi sallama ta bar gidan, ko minti goma batayi da barin gidan sai ga Professor AbdulGaffar AR, ya zo da abokanshi. Sai da ya mishi mitan abin da aka turo musu jiya, kafin ya ce mishi. "Ka san shi ai?" "Eh Da!" Ya fada yana mika mishi ruwa sannan ya kara zubawa Bakon ya ce mishi. "Wannan shine Mr Thomas daga London!" Gyada kai yayi yana kallon Dad dinsa. "Akwai wani zane da kayi a studio dinka gidajen tarihin London sun tabbatar da yayi kama da tarihin ƙasar." Lumshe idanu yayi a nutse ya kalli Mr Thomas kafin ya bude yana me yake. "Ba zan sayar mishi ba!" "Why?" Numfashi ya sauke yana kallon kofar studio din kafin ya mike ya je ya dauko zanen, mikewa Baturen yayi yana faɗin. "Shi ne!" Ajiyewa Abhu yayi ya kalli Baturen ya ce mishi. "Ba zan sayar ba!" "Akan me Abhu Zar?" "Kawai bana da niyya ne!" Haka yake da takaici, babu ruwanshi idan ya ce a'a ne, "Allah ya shirya ka son." Ya Professor ya fada yana yiwa Mr Thomas bayani. Take ya shiga mishi bayani an bashi dillancin ya nimo zanen ahincinsa yana jikin zanen, kirmisis Abhu ya ki amincewa. Bayan Dad ya raka Mr Thomas ya dawo ya samu ya saka zanen a gaba yana kallon yadda zanen yake.

"Me yasa ka ki sayarwa?" "Kawai ban yi niyya ba ne." "Amma kada ka sake min haka!" "Tow na ji dad!" Takowa yayi yana kallon zanen da kyau yana faɗin. "Zanen nan yana da bala'in kyau, na mishi bayani yaki fahimta. Amma sai ka ji kunyata ka ce nayi magana." Murmushi yayi yana faɗin. "Dad karya haramun ne a Muslunci, sannan idan na ce na sayar daga baya naki sunana munafiki. Kayi hakuri ka dauka ka sayar mishi don kanka amma Dad wannan zanen daga zuciya ta nayi shi, bai zama dole na sake yin irinsa ba." "A'a ka barshi zai amfane ka don nasan a dalilin mace kayi shi ka bar shi." Shiru yayi kafin ya juya yana kallon Dad dinsa, abin da ya faru jiya yana dawo mishi daki-daki, "innalillahi wainnalihir rajou!" Ya furta yana rike kanshi. "Me ya faru?" Da dan sauri ya haura sama, wayarshi ya dauka ya kunna wayar ya shiga bincike, tabbas Yusrah Bukar tazo gidan nan, dafe kanshi yayi yana kallon abinda tayi ta kokarin aikatawa Allah bai bata iko ba ina Nuruddeen yake jiya da abin ya faru, biyo shi dakin Professor yayi ya ga yana ƙoƙarin boye wayar ya ce mishi. "Yusrah Bukar ko?" "Wurgi yayi da wayar." Ya kalli Dad dinsa yana jin kanshi na mishi wani irin ciwo. "Dad Why me?" "Kayi hakuri zan yi magana da Ubanta." Haka yayi ta rarrashinsa, har ya dawo nutsuwarshi, yayi mishi sallama ya fita bai bar gidan ba, sai da ya kira Lauya dinsa ya gaya mishi duk wani partnerships na kasuwanci da yake tsakaninsu da Mr Bukar ya ya janye, kamar wasa babbar maganar ta zama babba.

****

 Rano.


   Kasancewar yau juma'a da wuri Innar Ayuba ta dawo gida, tana zuwa ta samu gidan A rikice ana ta bala'i tsakanin Laraba da Lantana, tana cewa sai ta kashe Babangida yau ko zata ci gidan yari.....

#500

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.