Free chapter · Read without an account
028
*BAYA DA ƘURA.*
Fitattubiyar2025
©️Nana Haleema.
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11
*BOOK 1*
*Page 028*
Bebi kuwa yana kwance a gida baya son fita a ranar kwata-kwata, ya jawo wayar sa ya kira Huzaifa bayan ya ɗauka yace, "Yau bazan shigo ba, in akwai wani abun ku yi kar ku jira ni." Huzaifa yace, "Lafiya?."
"Baba jin daɗi ne."
"Sannu, Allah ya ƙara Lafiya." Ya amsa da amin kafin yace, "Mama ta amince da maganar aurena da Manal, amma tace da sharaɗin in na auri Manal da shekara ɗaya zan auri Rumana."
Huzaifa yace, "kuma dai!." Bebi bai iya magana ba jin haka Huzaifa yace, "to Allah yasa hakan shine mafi alkhairi, kar ka sake mata musu a wannan lokacin kawai ka amince tunda tana so."
"Na amince ma ai Huzaifa, na amince har zuciyata ta saboda ita."
"Hakan yayi, Allah ya kai mu lokacin" ya amsa da amin ya yanke wayar ya koma ya jingina da kujera.
Manal ya kira bata ɗauka ba ya sake kira a lokacin ta ɗauka tayi sallama yayi shiru na wani lokacin idanun sa a kulle kafin ya amsa tace, "an tashi lafiya?."
"Lafiya lau, ya jikin Mama? Ina fatan ta samu Lafiya?."
"Da sauƙi sosai, yau ma tace min tana ganin hasken rana."
"Ma sha Allah, a hankali komai zai dawo in sha Allah. Ki gaishe ta."
Manal tace, "zata ji in sha Allah." Yayi shiru baice komai ba itama bata ce ba na wani lokaci, sai da ya sauke ajiyar zuciya ya katse shirun yace, "kin cemin kina da Yaya, ban taɓa ji kin min maganar ta ba ban kuma taɓa ganin ta ba. Bakya so na santa?."
Tayi murmushi tace, "Yaya Mubeena wai? Tana school, cikin kwanakin nan ne ta dawo gida kuma bata jin daɗi shiyasa baka ganin ta."
"Ohhh” Abinda ya furta kenan kafin yace, "ita tana zuwa makaranta amma ke bakya zuwa, meyasa bakya so?."
"Ina so sosai, kawai dalili ne ya hana ni zuwa."
"Meye shi?."
"Mama, bazan iya tafiya school na dinga barin Mama ita kaɗai ba gaskiya. Shiyasa na ajjiye duk wani burina a gefe, tana da lalurar ido in muka tafi duka waye zai kula da ita?."
Lumshe ido yayi yana jin wani irin bugun zuciya a lokaci ɗaya, Allah ya sani yadda take son mahaifiyar ta yana daga cikin abinda yake jan hankalin sa zuwa gare ta, soyayyar ta yake ji sosai a zuciyar sa fiye da yadda yake tunani, bai taɓa tunanin zai so wata mace kamar haka ba, shi ko a yaushe burin sa kar soyayya tayi masa mugun kamu, sai gashi a lokacin da bai yi tunani ba ya faɗa tarkon ƙaunar ta, ƙauna mai tsanani ma kuwa. Har bugun zuciyar sa yake ji a kunnen sa saboda soyayya, bai san lokacin da yace, "ina sonki Manal" ya faɗa cikin shauƙin so da kuma ƙauna.
Murmushi yaji tayi jin abinda yace, yadda yake furta kalmar ma abin jin daɗi ne balle yadda kalmar take ratsa ta sosai, tace, "Nima haka Dr."
“Kema me?.”
Tayi murmushi ta kulle fuska kamar tana ganin sa bata ce komai ba yacw, “ina jin ki, kema me?.” Tayi dariya tace, “nima i love you.” Ƙaramin tsaki yayi yace, “Da hausa zaki faɗa min.” Manal cikin shagwaɓa tace, “kunya nake ji.”
Ya gyara zama sosai shagwaɓar ta na ratsa shi sosai yace, “shiyasa nace ki faɗa.” Manal tace, “to ba na faɗa ba?.”
“Ban amince da wanda kika ce ba, da hausa nake so ki faɗa.”
“Ina son ka.” Ƴar dariya yayi cikin farin ciki ya wara idanu yace, "wow! Finally yau dai kin ce.”
Tayi murmushi shima shi yake yi yace, "sake faɗa naji pls." Ƙi tayi sai ta canja maganar tace, “meyasa ake ce maka Bebi?.”
"Sunan gida ne" Ya faɗa a taƙaice kafin yace, "bakya zuwa makaranta saboda Mama, amma yanzu zaki aure ki bar Mama."
Tayi shiru na wani lokacin muryar ta ta raunana kafin tace, "tuna hakan yana saka ni ciki damuwa" ta faɗa murnar ta na rawa sosai alamun kuka zata yi. Da sauri yace "wasa nake miki, meye na kuka Manal?."
"Da gaske ne ko baka ce ba itama tana faɗa min, don Allah babu ta yadda za'ayi na zauna a wajan Mama? Wallahi bazan iya zama a ko ina in bata nan ba, ko Ina zanje bazan ji daɗi sa kamar wajan ta ba."
Kuka take sosai nan take yayi dana sanin faɗa mata haka yace, "Manal relax please, ki daina kuka ki tsaya kiji abinda zance miki." Bata yi magana ba hakan ya saka yace, "Manal kina tare da Mama a ko yaushe in sha Allah kar ki damu, aure ai ba mutuwa bace." Manal bata ce komai ba jin tayi shiru yace, "ki nutsu ni da wasa nake faɗa miki ba da wani abun ba, naga alama kina son kuka baya miki wahala ke kam."
Manal tace, "duk yadda zan faɗa baza ka gane ba, Mama na kira na" Tana faɗa ta yanke wayar shi kuma yabi wayar da kallo yana jin wani iri a zuciyar sa da ya saka ta kuka. Ba jimawa ya kuma kira amma bata ɗauka ba, ya sake kira ba'a ɗauka ba, babu daɗi zuciyar sa haka ya ƙyale ta ya cigaba da harkokin sa.
A ranar Bebi ya samu kiran Baba akan Manal ta sanar dashi ta amince da auren sa ya turo iyayen sa, da yamma yaje ya samu Yaya ya faɗa masa yayi masa bayanin gidan su Manal da komai, shi kuma yace in sha Allah da safe zai je ya samu Yayan mahaifin su y sanar dashi a saka rana su je.
Rumana hankalin ta ya tashi ta gigice jin labarin da yazo kunnen ta na auren da Bebi zai yi kuma ba ita zai aura ba. Ammi tana zaune kusa da ita tana rarrashi tace, "Haba Rumana, wai akan Adnan kike wannan koke-koken?.
"Ammi ina son sa sosai, inaa son Adnan” ta faɗa tana kuka. Ammi tace, "nasan kina son sa, kuma yanzu ma ai ba fasa auren ki yayi ba zai aure ki amma ba yanzu ba.”
Ta girgiza kai tace, "Wallahi da zarar yayi aure bazai aure ni ba, ni kawai ya fara aurena kafin ya auri waccan ɗin. In ya fara auren wata bani ba mutuwa zanyi." Ammi tace, "kin cika rigima wallahi, ke ba auren ki ka yi ki ka barshi ba ne wai? A lokacin wanne irin so ne Adnan bai nuna miki ba?, Amma kika saka ƙafa kika yi fatali dashi kika ce ke Jawad kike so aka aura miki shi, to shi yanzu dan yace a bashi dama ya auri wacce yake so shikenan sai ya zama laifi?.”
Rumana ta goge idon ta tace, "Rabuwa ta dashi tsautsayi ne, kuma yanzu Ina son sa fiye da baya, don Allah ki taimaka min." Ammi tace, "taimakon naki ne ya saka zai aure ki nan gaba ai.” Rumana ta tashi tace, "wajan Maman zanje ni gaskiya a canja shawara, matuƙar ya auri wacce yake so shikenan na gama yawo wallahi, bazai aure ni ba kamar yadda yace. In ya auri wata ba ni ba kafin lokacin da aka bashi na aurena yayi na mutu.” tana faɗa ta ɗauki mayafi da key ɗin mota Ammi na mata magana amma ina bata ji ba ta fita.
Kaii tsaye gidan su Adnan ta wuce ta shiga wajan Mama ta same ta ita kaɗai kuwa tana zuwa ta zube a cinyar ta tana tace, "Mama don Allah kar ace Adnan bazai aure ni ba, in bai aure ni mutuwa zan yi" ta faɗa tana kuka sosai.
Hankalin Mama ya tashi cikin rarrashi tace, "Haba Rumana, zai aura ki mana, waye yace bazai aure ki ba?." Bata ce komai ba sai kuka da take yi a jikin Maman, Mama tace, "ki nutsu ki daina zubar da hawaye muyi magana."
Hawayen ta goge tana jan numfashi Mama tace, "in dai ina da rai kina da rai sai kin zama mallakin Adnan in sha Allah, ki daina wannan kukan, ɗan lokaci ne kawai na bashi damar ya auri waccan ne saboda haka hajiya tace, amma na tabbatar miki da zai aure ki kuma matsayin ki zai wuce matsayin waccan saboda kece wacce ya fara so tun bai girman haka ba, a duniya abinda ka fara so yafi tasiri a zuciya.”
"Mama ni nake so ya fara aura, in ya auri waccan shikenan bazai aure ni ba Mama." Mama tace, "nace ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai faru, zai aure ki in sha Allah ke matar Adnan ce amma sai kin daina tayar da hankali. Ki fara shirin zama matar sa daga yanzu dan shekara kwana ce."
Ta kwantar da kanta jikin Mama tace, "Mama..." Mama ta dakatar da ita tace, "kiyi haƙuri a bashi dama kamar yadda aka baki taki damar, ke mace ce bazai yu ki auri maza biyu ba amma shi namiji ne zai auri mata biyu har sama da haka. Ki yi haƙuri ayi hakan yafi kwanciyar hankali."
Rumana ta girgiza kai bata ce komai ba, ba haka taso ba, ba kuma haka take so ba amma hakan za'a yi babu yadda zata yi. Taso ace ita ya fara aure domin ta ƙure cika bakin sa amma hakan bai samu ba dole ya fara zama da wata kafin ita. Numfashi ta saukar zuciyar ta nayi mata zafi tana tunani kala-kala.
Hankalin Maryam ya tashi sosai tunda sukayi waya da Kamal ya shaida mata bashi da lafiya yana kwace ta rasa nutsuwa so take kawai taje inda yake, sai bayan ta fita da mota sannan ta kira shi tace, "Kana ina gani nan zan zo?." Daga can ɓangaren yace, "ina gidan mu dake." Kashe wayar tayi ta nufi gidan da ta zauna dashi matsayin mata da miji.
Gidan babu mai gadi dan ba’a ciki matar sa take ba, a ƙofar gida ta ajjiye motar ta fito ta tura gate ɗin ya buɗe ta rufe ta shiga ciki da sauri. Baya falon hakan ya saka ta masa waya tace, "ka sakko gani a falon, Sauri nake zan koma."
"Bazan iya sakkowa kowa ba, ki hau saman kawai ina ɗakin ki" Daga haka ya yanke wayar ta sauke ajiyar zuciya ta hau saman jikin ta yayi sanyi rayuwar ta ta cikin gidan yana dawo mata hankalin ta.
Ɗakin ta buɗe ta shiga an saka sabon furniture yana kwance a kan gado jin ta shigo sai ya miƙe daƙyar ya zauna yana kallon ta yace, "Barka da zuwa my love." Da sauri ta ƙaraso gab da kan gadon tace, "ya jikin naka?."
"Gani nan dai kawai."
"Meyasa ka zauna kai kaɗai a nan? ba ga gidan matar ka ba?."
"Nan ma gidan matata ne." Tayi shiru ya tashi tsaye sai tayi saurin kawar da kai daga kallon sa domin daga shi sai gajeren wando ko riga babu a jikin sa.
"Maryam ƙaddara ce ta jawo na furta saki a kan ki, amma wallahi Ina son ki ina ƙaunar zama dake, wannan damuwar itace ta haifar da zazzzaɓi, ina so mu sake zama matsayin mata da miji”
Ya matso daf da ita yana magana a hankali yana kallon ta.
tace, "ƙaddarar kenan, babu wanda zai canja ta tsakanina da kai. In Allah ya yi nida kai zamu sake zama tare zamu zauna ko bayan shekara nawa ne.”
"Ina son kasancewa dake, babu macen da nake kwaɗayi sai ke Maryam" ya faɗa yana komawa da baya ya zauna ya dafe kai yace, “Na rasa abinda yake min daɗi, kiyi wani abun dom Allah Maryam."
Maryam tana tsaye jikin ta yayi sanyi ta kalle shi kafin tayi magana yace, "Maryam ya zanyi?." Kallon sa tayi tace, "haƙuri” ta faɗa a taƙaice zuciyar ta na bugawa. Da azama ya taso ya riƙe kafaɗun ta ƙirjin ta yana gugar nasa yace, "Haƙuri Maryam? Wallahi zan iya mutuwa yanzu in ban same ki ba” ya faɗa yana jan ta da ƙarfi zuwa jikin sa ya rungume ta sosai yana sauke ajiyar zuciya.
Ƙoƙarin kwacewa tayi amma ta kasa saboda ya riƙe ta sosai a kunnen ta yana cewa, "ki bari Maryam, nasan kina son kasancewa dani kema don Allah ki bari mu ji ɗumin juna." Yadda yake maganar ya saukar mata da kasala sosai ta daina ƙoƙarin ƙwace kan ta tayi shiru tana ji yana sake matse ta a jikin sa.
"Ina son ki Maryam, ƙaddara ce ta raba mu da ban muna so ba, ina son ki Maryam kema na san kina sona, bana marmarin ko wacce mace in ba ke ba" ya faɗa yana sake matse ta sosai a jikin sa.
Ita dai taji ɗumin bakin sa a wuyan ta daga nan baza ta sake cewa ga abinda ya faru ba ta tsinci kanta ne kawai a kan gado a kwance ita dashi a cikin bargo guda ɗaya tamkar ma'aaurata.
A firgice ta miƙe tunawa da abinda ya faru ta cure a waje ɗaya hankalin ta ya tashi sosai ta gigice, ganin hakan sai ya ƙaraso inda take yace, "Haba maryam meye haka?."
Kuka take yi sosai yana rarrashi amma taƙi bada damar hakan, yayi yayi tayi shiru amma abin yaci tura shi kansa hankalin sa ya tashi bai ɗ'auka zata ruɗe haka ba. Ya san tana son sa sosai bai ɗauka dan wannan abun ya faru tsakanin su hankalin ta zai tashi sosai har haka ba.
Haƙuri yake bata amma taƙi sauraren sa kallon doguwar rigar ta tayi a gefe a ajjiye, tana kuka ta zira hannu ta ɗauka ba tare da ta cire abinda rufe jikin ta ba ta saka rigar tana daga zaune ta miƙe tsaye ta saka da takalmi da mayafi ta ɗauki key da wayar ta fita a guje.
Bin bayan ta yake yana mata magana amma inaa ta shiga mota ta bar unguwar da gudun gaske. Da sauri ya koma gidan ya ɗauko nasa key ɗin ya hau mota yabi bayan ta, saboda gudun da take yi bai iya tarar da ita a hanya ba sai da yaje har gidan mai gadin gidan ya tabbatar masa da ta shiga sannan hankalin sa ya kwanta ya koma. bashi damuwa akan abinda ya faru dan yasan zata yafe zai kuma wuce, wataƙila ma a sake maimaitawa in soyayyar ta sa ta motsa a zuciyar ta.
Bayan kwana biyu.