Free chapter 路 Read without an account

Thirteen

by Aisha Abbakar 路 RANAR YABO..!

*_馃挃RANAR YABO馃挃_*



*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*



   By

Mom muhsen

   &Asaad



      Thirteen




Tunda suka isa class d'in suka same su Shida Jamil, suka zauna tsawon minty goma ba alamun Fareed zai yi wani abu Jamil yace, "Aboki lafia kuwa,"


Fareed ya bude idonsa da sunyi wani kala, yace "Yau babu karatu inhar wannan rigimammiyar yarinyar bata zo ba,Kama gaya musu"


Zaro ido Jamil yai yace "Kuttt,yau lalata ka shirya mana kenan"


Ya juyo yana sanar dasu sakeena, suka kyalkyale da dariya tace "to itama d'in bata da lafia kanta ke ciwo na barota zata sha magani"


Fareed ya jiyo yana marairaice fuska yace, "Nima kaina I'm not feeling well,amma sbd ita dole na fito pls kiyi mata dubara tafito,yanzu haka ma ba wani ciwon kai pretending ne"


Merry face"ohh hakane ko?Sakeena karki kirata in ya cika ya damu da ita yaje ya taho da ita mugani"


Ya kalli Merry yace "haka kika fad'a,"


Sun san dokar mkrntar inhar namiji ya shigo hostel wajen wata to ba shakka ko d'an waye za'a kore su sudukan, Jennifer tai saurin cewa "She is joking fa Fareed"


D'an murmushi yai yace, "ko Ku kirata tafito ko kuma wallahi inshiga har dakin naku"


Suka kalli juna,jamil mizai ba dariya ba yace "ashe ka iya rigima kaima"


Ya dage kafadarsa yana b'ata rai, "Ya zanyi ita ta koya mun ai"


Su sakeena suka fara tsara yadda zasu kirani,merry tace "nasan dubarar da Zan mata"


Ta fita waje tana daukar wayarta ta kirani, Ina kwance nayi rubda ciki ina kallon system na kasa karatun, wayar Merry ta shigo na kalli kiran saida yazo tsinkewa na dauka, "Ya dai?"


Abunda na fada mata kenan,sai naji tace cikin damuwa sosai "Bia kiyi sauri kizo Fareed ya fad'i fa ya suma bamu san abunda ke ya same sa ba,gashi dai munata son kiran guard Dinsa........ai ban sake sauraren mi zatace min ba na saki wayar na diro daga gado na dauki veil d'ina na yafa bisa gown din jikina ban tsaya daurawa ba,rigar ta wani material ne d'inkin ya zaunu a jikina ta fidda shape d'ina sosai sbd rud'un da nake ciki yasa ban lura ba na fita a hakan gylen iyakarsa kirjina da bayana amma bai kai bom bom dina ba,jikina har rawa yake na saka hills dina na fita da sauri wayata rik'e ga hannu.


Kamar an jehoni na fad'o cikin class d'in idona cikin nashi ya fara sauka,kafin nabisu da ido daya bayan d'aya na sauke akan Merry wacce ta mun karyar, "I have no option Bia,"


Sai kawae na juya a fusace nabar class din,banyi nisa ba sosai nasha gabana yana hakin saurin da yayi, "Allah inkikai yunkurin guduwa saidai kiji na daukeki"


Idona a warwaje na nuna kaina, "ni zaka dauka?"


Ya jinjina kanshi yana dafa ginin dake kusa damu ya jingina bayansa, "kin ban wuya wlh"


Na kawar da kaina daga gujema wannan lalataccen kallon nashi, "kasa anyi min karya don in fito to gani"


Murmushi yai yana cewa, "to tsoron mi kike ji da ba zaki fuskance ni ba,ki jiyo ki min mgnr ido da ido"


Na hararesa na sake dauke kaina, "Kaga dare nayi kuma ni Daddy ya hanani kaiwa dare a wajen Hostel"


"Washh bayana,kinga ma na gaji da tsayuwar wlh ko zamuje mota........wlh ba zanje wata mota ba ka fadi abunda zaka fad'a anan in tafi ni"


"Fitina dai kikeji Bee'a to ba dani zakiyi ba,mu shiga wannan class din mu zauna Allah kuwa na gaji kin sanya nayi gudu sosai fa"


Na murgud'a bakina ina kallon wani wajen,ala dole bazan kallai ba bacin idanuna hakan suke so, "pls kinji yar gidan Daddy"


Na b'ata fuska ina duba wayana naga nine saura minty ashirin, na d'an dafe kaina k'adan nace "To gaskiya thirty minutes zan baka, kaina ke ciwo haka nan na fito"


Cikin nuna damuwarsa yace, "Ayya Sorry kinji, nima d'in fa banda lafia"


Yanda yai mgnr cikin langwab'ewa saida zuciyata ta ansa sosai,na saci kallon sa naga ni yake kallo, nai saurin cewa "anci five minutes fa"


Saurin tashi yai daga jikin bangon yana cewa "let's go"


Class din baida sanyi sosai amma duk da haka saiya ciro jacket d'insa mai d'an kauri hadda hularta ina zaune cikin sit d'in yazo ta bayana ya rufa min ita,dago kaina nayi idanunmu suka sark'e cikin na juna,bai cire hannunsa daga kan rigar ba a haka muke kallon junan, mgnrsa ta dawo dani cikin hayyacina.


"Miyasa kike guduna?jiya fa kince kin yafe mun"


Saurin juyar da kaina nayi gabana yana bugawa, nama rasa bakin mgn to mi zan ce masa?wlh banda abunda da zance masa, "RABEE'ATU"


saida na lumshe idona kafin na had'iye busashshen miyau na ansa muryata bata fitowa sosai, gabana ya dawo ya zauna muna fuskantar juna har nakan jiya jin yadda yake jan numfashi, kamshin turarensa yana dukan hancina yana ratsa min har xuciyata.


"Kinji miyasa kike gujemun bayan kince kin yafe mun"


Runtse idona nayi ina jujjuya hannuna,na rasa abun cewa sai na bud'e baki zanyi mgn sai in kasa, sai zuwa can na iya cewa "uhm kawae......ni bana guje maka,kawae dai......banajin dad'ine shiyasa"


Inajin kaifafun idanunsa akaina baice komi ba, zuwa can muryarsa tayi kasa sosai kuma tayi sanyi kamar ba tashi ba yace, "Rabee'atu kina jin irin abunda nakeji don Allah???"


Da ace yadda zuciyata ta buga za'ajisa a zahiri sai ka ji tsoro,duk sanyin da ake zuba wa alokacin sai naji zufa na tsatstsafo mun,har bakina nakejin kamar babu miyau ciki na gaza d'ago da kaina duk yadda nakejin idanunsa akaina na kasa dagowa na kallai, shiru ya ratsa tsakanin mu na tsayin lokaci nida nake cewa thirty minute na bashi nayi imanin zuwa yanzu ya riga ya wuce sosai, ya sake cewa cikin wata irin murya mai karairaya zuciyar duk wata lafiyayyar mace, "Please talk to me Bee'a I'm confuse na rasa gane kaina ne,komi kwace mun yake ban san ma taya zan miki explaining ba amma I swear bana da natsuwa duk inba ina tare dake ba.......

"Faa.....Fareed dare yayi,Ina.....inaso naje na....na kwanta"


Mgnr ta firfito mun a duburce na mik'e tsaye jikina yana yar rawa kad'an,rik'e mun gefen gyalena yayi idanun sa sun kad'a kadan yana kallona dasu da,basa bud'ewa sosai nai saurin dauke idona zuciyata na sassarfa sosai, sai ya taso ya iso gabana sosai har ina jin hucin numfashin sa a fuskata, ji nake kamar inb'ace a wajen haka nakeji kirjina bugawa yake ba k'ak'k'autawa........"wannan mgnr taki kad'ai ta sanya na yarda kema.......Aa,Aa ba....ba haka bane,bana jin hakan ba irin haka nakeji ba,kawae dai.....kila ka kasa fahintar kanka ne,amma......ba haka bane gaskiya"


Gefe ya furzar da iska yana kokarin saita kanshi yace muryasa tana dishewa sosai, "Still mgn ta haka take,amma bazan miki musu ba nasan watan watarana yadda na gaji,yadda na kasa cigaba da hkr kema........cikin sauri na d'ago idanuna da suke cike da wani irin firgicin halin da nake ciki,da kuma mgnr sa ta yanzu.


Kallona yake sosai kamar zai cinyeni, ya matso da fuskarsa sosai yana cemun, "Yes,ranar tana zuwa ko kink'i ko kinso,tunda kin k'i tsayawa muyi mgn sosai,and one more thing idan har kika cigaba da guje mun,idan har kika cigaba da k'in daukar kirana,idan kika cigaba da treating d'ina like this........yadda idona suke akanshi yasa ya d'anyi smile mai fitinannen kyau, "to ya tabbata kina jin fiye ma da abunda nakeji a cikin zuciyana,kin yarda"


Yadda ya narke idonsa cikin nawa yasa na fizgi numfashi a hankali,Ina danne abunda ke hank'oro a cikin zuciyana, muryata kamar ma ba tawa ba wlh, nace "Naji kuma na yarda,yanzu dai zan tafi daki"


Ajiyar zuciya yaja yace, "lemme escort you"


Haka muka fito muna tafiya tare ba mai mgn cikinmu saidai zucikatan mu ne kurin keta azabtuwa da tunani,har bakin get d'in mu ya kawo ni saida na shiga na tsaya jikin get d'in,inajin sa har sannan bai tafi ba kuma kallona yake, a hankali na jiyo Ina cewa "Ur jacket"


Na nuna ta da hannuna,rungume hannunsa yai ga kirji yana cewa "na bar miki ta tayaki bacci yau"


Murmushi mgnrsa ta sani,na rausayar dakaina nace "OK,Good night"


Bye yayi mun sannan na juya na shige cikin Hostel d'in,ban sanma na iso daki ba sbd tsananin yadda zuciyata tayi zurfi a cikin tunani, Jenny na iske tana goge kayanta Sakeena na waya da alama saurayi tayi wanda bansan da zaman sa ba,Merry ce tayi bacci.


Cikin kasala da mutuwar jiki nayi shirin bacci na nazo na kwanta bamce ma kowa komi ba, jacket d'in tashi dana aje gefen filona na dauko Ina d'orata akan fuskata fitinannen k'amshinsa yana ratsa ko ina na ilahirin zuciyana da gangar jikina.


Cikin ikon Allah sai bai kirani ba hakan ya samun salama,ba dan bana son jinsa ba sai don kaucewa abunda ke shirin faruwa damu,ko kuma yafarun ma amma dole komi zai gyaru ban sbirya ma hakan ba,nayi ma Baba alkawarin bazanyi soyayya ba har saina kammala karatuna,inhar na biyewa wadannan abubuwan ba makawa zan rufta irin ruftawar da bazan tab'a iya fita ba,

A haka baccin yai nasarar sace ni cike da tunanin Faa.


*******


Haka muka cigaba da kasancewa tare dashi kowa yana hidden abu a kasan ransa,duk yadda naso in danne in nuna kamar babu komi hakan ta faskara,shi daga garesa ban sake ganin wani abu dazai kawo mun zargi ko kokonto ba,har yawan kallon da yake mun duk ya rage sosai,yawanci mgnr mu duk akan karatune in ka dauke karatun to Zaka same mu kamar kurame,koda a class ne mun gama karatu to ba zakaji muryata wajen firar ba sai ta kama inyi sentence d'aya ko biyu.


Shi kuwa shida Jamil firar su duk akan ball ne,kamar ma yanxu yafi da sakewa da walwala babu alamun komi akan fuskarsa balle Inyi tunanin something like that,sannan yadda yake kirana a baya yanzu ana iya wuni ma baimun kira guda ba, sai hakan ya riga azabtar dani amma karfin zuciyata da karfin hali ya hanani in nuna masa koda a fuska ne,haka kuma mun rage k'ebewa da juna ko karatu muka ta shi idan su Sakeena sukayi gaba suna jirana,daya fito zai ce min "Goodnight Bee'a"


Wani lokacin wani irin kududu hakan ke mun,amma sai nuna kamar ba komi nima inyi masa saida safen, a hakan har muka cinma exam d'inmu wacce batafi sauran sati mu gama ba, rashin zuwan Fadeel da yana d'an damuna dana tuna zai iyayin ta online sai hakan bai sake damuna ba, yau kuma da ya kasance kowa yasan malamin baya exam d'insa online sai hankalina yayi kanshi da son sanin zaizo ko bazai zo ba,ba wai don na damu ba aa bana son kamar yadda ya maimaita wannan shekarar irin last year wannan dinma ace saiya maimaita sbd tsarin mkrntar yanada wuya duk da kasancewarta a turai hakan baisa wasu abubuwan sunyi wasa dasu ba. 


Karfe hud'u zamu shiga mu fito six kuma daya ce shiyasa yini nayi ina karatun,duk da cewar da daddare ma munyi amma hakan bai hanani cigaba da dubawa ba, sbd course d'in yawanci duk mathematics ne duk Fareed yayi mun kokari sosai akan course d'in,saida ya tabbatar na iya kuma zan iya sannan ya kyaleni,tun safe ya mun text cewar idan anfito exam zamuje cikin gari bandai bashi ansa ba har lokacin, ban sauko daga gadona ba saida lokacin ya taho sannan na shirya cikin doguwa riga gown mai fitinannen kyau,sabuwa ce rannan muka fita shopping da safe nida su Sakeena Daddy ya turo mun yan kudin provision,shine fa daga yaji zamu fita yace mujira zaizo ya kaimu.


Wata mall ya kaimu wacce duniya ce kurin acikinta, tama fi waccen da muka taba zuwa da sakeena,shike driving d'in ina baya Sakeena ke gaba nida merry muna baya Jenny taje gida weekend d'in.


Haka yaita kallona cikin center mirror har muka iso,duk inda mukaje tare dashi muke zuwa,wasu sabbin new design muka gani nida Sakeey muka tsaya muna yaba kyansu,bamu fito mall d'in ba saida Fareed ya dauko mana rigunan nida Sakeena,sai naji babu dad'i kamar zaiga rok'a mukai kuma har ranmu ba haka bane, bayan rigunan haka ya ringa jidar mana tarkacen kayan cinye cinye, Fareed baya gajiya ko misk'ala zarratin wajen kashe mana kud'i, duk yadda na nuna masa bacin raina akan hakan baisa ya fasa ba,wani lokacin har rasa inda zan saka kaya nake sbd yawansu,haka sutura ba laifi inada kaya sosai wasu har mancewa dasu nake.


Kallon rigar nake yadda tayi masifar yima jikina kyau,kamar daman danni akayita tabi ko ina najikina ta lafe ta kuma fidda shape d'ina ma sha Allah, "Kai Kai kai,Bia irin wannan had'uwa haka?Billahi rigar nan tayi masifar yi miki kyau"


Sakeena data fito wanka take fadar hakan,Jennifer tace "Kin rigani fad'a,wallahi ta miki kyau sosai kamar dai ya aunaki kuma yasan kalar zata fito dake"


Nace "Amma bazan iya fita da ita ba dubi yadda ta fiddo jikina fa........ke wallahi ba kauya ce dakin saka veil shikenan fa"


Girgiza kaina nayi jin abunda Jennifer tace, Sakeena ta anshe da cewa "gaskiya ta fiddoki sosai amma inkika saka ya ganki zaiji dad'i sosai,sai ki daura babban veil da zai saukar miki sosai"


Sake kallon kaina nayi Ina jin nauyi da kunyar fita haka Fareed ya ganni,amma miyasa nake jin kunyar shikadai???


Na kalli Sakeena nace cikin marairaicewa "Wallahi kunya nakeji ya ganni haka"

Suka kyalkyale da dariya su dukan, Jennifer ta ce "To su sauran mutanen bakya jin kunyars?"


Na b'ata rai bance mata komi ba, haka dai suka matsa mun na hkr da rigar,amma duk juyin da zanyi saina kalli kaina a madubi har sadda time ya cika sannan na yane kaina da babban veil kuma ba laifi ya rife mun jikina sosai sannan muka fita.


********


Fitowa yai cikin shirin sa na fita zuwa mkrnta,yai kyau har ya gaji daman kuma Fadeel badai iya tsara gayu ba,shiyasa mace ko baice yana yi ba ita kawo kanta, Allah ya masa zubin halitta mai kyau daidai son kowane d'a namiji ya kasance, haka ma mace duk abunda take buk'ata ga namiji intazo ga Fadeel ta samu, saidai abunda baka rasa d'an adam dashi ba sbd tara muke bamu cike goma ba.


Falon Mami ya shiga ya isketa ta buga tagumi ta abincin rana nan tun da ranar aka kawo mata bata tab'ashi ba, ya jima tsaye kanta yana kallonta duk ta firgice ya isa ya zauna gefenta yasa hannu ya cire ta gumin, ta jiyo tana kallonsa "Mami please stop thinking is too much,"


Jitai kamar ta rushe da kuka ta rungumeshi ta gaya masa damuwarta,amma ba zata so rauninta ya bayyana haka ba ta danne ma zuciyarta tace "Ina zakaje"


"School"


"Waye zai kaika?"


Ya d'an dora kanshi bisa kafad'arta yana lumshe ido kafin a hankali yace "I'm waiting for Bilal"


Ta shafa kanshi tana cewa, "Kasha drugs d'inka?"


Kai ya jinjina mata yana sake lafewa jikinta, "Kayi karatu sosai dai ko?kaga kun taho shiga aji uku kuma daga sai final year d'inku in baka dage ba bazaka cimma point din da kake so ba"


"mami nayi karatu fa"


"OK Allah ya bada sa'a"


Sukai shiru na wani lokaci kafin Bilal ya kirasa yace ya iso, ya dago yana kallon Mamin cikin shagwab'a, "Mami inason Pepe fish kafin na dawo,pls yayi dad'i irin na........sai yaji mgnr ta mak'ale,sunan ya kasa fita daga bakinsa, ya had'iye abu a makoshin sa kafin yace, "Mami I'm missing Daddy too,pls kice yayi hkr ya dawo kona kira baya picking"


Ajiyar zuciya ta sauke tace, "Don't worry Son,zai dawo as soon as possible"


Ya tashi ya nufi waje ta bisa da kallo ta na nazartar sa,tana kokwanton rashin walwalarsa, definitely akwai wani abu dake damunsa a rai wanda ya kasa fadar sa ga kowa,tasan yaronta ba haka yake ba sannan shi baya boyen damuwa duk abunda yakejin ya damai fada yake,yasan zatai masa magninsa ko kuma Daddynsa ya shiga ya fita ya masa abunda yakeso, 


"Miyasa wannan karon ya zab'i ya boye abun duk da yadda yake damunsa?"


Wannan tambayar tayi ma kanta,kuma ta nanata yafi a kirga amma bata da ansarta,haka tatashi ta shige bedroom dinta don yin wanka sbd tunda ta dawo daga wajen Daddy ta zube falo tana hakin bacin rai, kallon dakin nata take tanajin takaicin duk gyaran akai masa baya yi mata yadda takeso,kasan ranta tanajin gyaran Rabee'atu yafi kwanta mata yafi yi mata,har siff dinta tafi jin dadin gyaranta sbd komi tana ajesa a muhallin daya dace, gajeran tsaki taja ta wuce toilet ta rufe.











Mom muhseen鉁嶏笍

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.