Free chapter · Read without an account
8
A bangaren Asim yana jiran kiran ta dan ya kira ya ji wayar a kashe har gari ya waye bata kira ba ko da Asuba da ya kira ta wayar a kashe hakan na nufin bata daga waya ba, ya girgiza kan sa tare da yin murmishi yana jin kara son ta a zuciyar sa.
Bayan sun shirya kasan cewa yau juma'a sun yi shiga iri daya, light ash gazna tare da hula, ba abin da ya ban banta.
Asif ya tambaye shi in dan yayi wa Umma maganar Halimatu?
Ya girgiza masa kai tare da ce wa "Bari nayi sai na dawo daga tafiya kafin nan mun kara jituwa da ita."
Asif yayi dariya yace "Asim ke nan, kar ka damu we will all fight for it. Ya mika mashi kunckles,. They chop knucles.
Suka fito suka wuce part din Hajiya shafa suka gaishe ta sannan suka wuce part din umman ta su.
Suka yi sallama suka karaso ciki, Safna ta ce "Yau kuma shiga daya a ka yi.
Murmishi dukan su suka yi suka karasa wurin Umma suka rintsuna suka gaishe ta sanna suka zauna.
Umma ta ce "Yau zaku ba mutane wahala koh."
Asif ya ce "Ba haka ba ne, mun kwana biyu ba mu zama tagwaye ba."
Asim ya ce "Wanda ya sa ka aikin office da kullun kake cikin suit."
Asif ya ce "Kai ma miyasa ka tsaya a kasuwa da ka hada biyu."
Asim yace "Sai kuma naki, ra’ayi riga."
Asif ya ce "Kai ka so."
Umma ta katsai su "Ni kar ku fara rigamar ta ku, kun girma ba kusan kun girma ba."
Asif ya ce "Umma kin san kullun shi ke da jan fada."
Asim ya ce "Ashe ma sai ka fada min da wata igyar na jaka."
Umma ta ce "Ku dai ku ka sani."
Asim ya ce "Umma gobe ne zan yi tafiyar."
Umma ta ce "Ah ah ba yau banei ganin kun sa kaya daya na ma dauka tare za ku tafi."
Ya dubi Asif yace "Wannan miyasa ni kan kasuwa."
Asif yace "Sannu gwani na gwanaye."
Asim ya ce "Ka ma dai ji abin da ka ce gwani na gwanaye."
Asif ya ja kuntu tsaki tare da cewa "Kan ka ake ji yaban kai jahilci."
Asim zai yi Magana Umma ta dakatar da shi dan yanzu sun hawa samaa kuma kai ba ka isa ka shiga tsakani ba ka sha kunya.
Ta ce "Yanzu dai kun ji maganar Abban ku ta jiya fatan kowannan ku na da budurwa dan na ga take taken shi ya na nema muku matayen aure.
Asim ya ce "Umma maganar da jiya muka gama yi ke nan musanmaman mijin ayana wai kin sa da tsohon cikin dukan ta yake yi.
Cike da mamaki ta ce "Ismail din?
Asif ya ce "Shi din fah."
Umma ta ce "Shiyasa fah ni lamarin Abban na ku yake ban tsoro, kin ga Safna ki wa Allah ki fito da mijn aure, ganin yayi shiru bai bi ta gan ki ba na tabbata bai samu wanda yake so ba, ki wa Allah ki fiddo miji kafin ya kawo nashi."
Safna ta ce "Umma aure fah lokaci ne, sannan ko ka kawo wanda ka ke so in ya ga bai mai ba korar shi fah yake yi."
Umma ta ce "Ay ba duka yake kora ba da daga na ayyana sai na Sadiya.
Safna ta ce "Umma mazan kwarai yanzu wiya suke, ji fah yayye na kullun cikin rigima ake basu da kwnciyar hankalin cikin su daga Aunty zulaiha sai maman khaili ita ma ita ke kula da gidan ta.
Umma ta ce "ke dai ki ka sani shawara ce na ba ki."
Asim ya ce "Safna tayi gaskiya aure lokaci garai shi, sannan jinkiri al-khairi ne."
Umma ta ce "Da wannan amma a ce kuna kannanta kunyi aure ita bata yi ba."
Asif yace "Umma kar ki damu da lokacin yayi zaki ga an yi shi kila a hada duka ayi sa December."
Umma ta ce "Allah sa. Suka mike tare da cewa umma mun tafi." Suka fadi a tare.
Umma ta ce "Toh sai kun dawo. Suka amsa da Amin suka wuce.
Suna cikin tafiya Asif ya tambaye shi; "Miyasa ba ka fadawa Umma ba ay yanzu ya kamata ka fada mata tin da ta tambaya."
Shima ya tambaye shi "Kai kana da tsayyar budurwar?
Asif yayi dariya ya ce budurwowi ma sai wadda na zaba, ba kai ka ki yarda mu auri twins ba ka je ka naimo wata Halima, mai sunnan Umma.
Nan take rain shi ya baci yace "Kana naman wuce gona da iri ina ruwanka da rayuwa ta, ba zan auri twins ba ko dan ina twins sai a aka ce dole sai yan'biyu zan aura." Ya ja tsaki ya wuce.
Asif ya bi shi da cewa "Ikon Allah har ka yi fushi ah lallai."
Ya bi shi a baya ko da suka isa wurin packing mota, ya shiga motar shi batare da yayi ma Asif Magana ba kuma sun shirya akan za su fita tare dan dama mota iri daya Alhaji Inuwa ya siya masu.
Yayi gaba ya bar Asif. Shima Asif ya na fita ya wuce office shi kuma Asim ya wuce kasuwa.
Kafin sallah azahar har yasako ya naimi dan uwan sa suka wuce masallaci dakanan suka koma gida suka ci abinci ya koma daki dan duk Friday yana barin yaro a shagon.
Bayan ya gama cin abinci ya wuce dakin su ya kwanta saman gado ya jawo wayar sa ya kara trying number ta a kashe, sai ya tuna da aikin da ta bashi hakan ya sa ya koma chrome ya yi searching gamaida aure. Har sai da akyi la’asar ya fito.
Ko da manaiman auran sadiya suka zo bai fito ba.
Dagan masallaci suka dau mota shi da Asif suka shiga gari dan zumunci daman duk Friday sukan fita ziyara gidan yan'uwa shi da Asif ciki hr da gidan ayana wanda gidan ya haska layin sosai,duk wanda zai wuce ta gaban gida sai gidan ya birge shi yayi sha’awar dama shi ke cikin gidan ko kuma shike da mallakin gidan.
Yayi park motar a gate din gidan tare da yin horn.
Mai gaidin ya fito ya karaso wurin su. Asim ya sauke window , mai gadin ganin Asim fara’a shinfidai a fuskar sa ya ce "An gaishe ku tagawaye, anbiyu kyautar Sllah.
Asim ya yi murmimshi ya tambaye shi "Ta na nan?
Mai gadin ya ce "Ranka ya dadai kai da ka san ba ta zuwa ko ina."
Asim yace "Toh budai mana mu shiga."
Mai gadi ya koma ciki ya dannan mabudin gate din, Asim ya shigo da mota yayi parking a parkig space suka fito.
Mai gadin ya karaso wurin su yana masu kirari. Asif ya fiddo kudi daga aljihun sa ya mika mashi. Mai gadin ya masu godiya sannan suka wuce wurin second gate suka karasa ciki, a gefan kofar shiga wata hadden hut ce tare da karamin garden sai kuma saman baine gidan glass ne. Kofa biyu ce ta shiga gidan da wadda zata kai ka underground da kuma wadda zata kai ka cikin gida.
Suka wuce ta gefen daman su wadda ita ce aynayin main door din.
Asif ya yi knocking ba jimawa mai aikin ta ta budai ma su. Ta rintsuna ta gaishe su suka amsa suna karasowa ciki.
Ta rufe kofar ta na ce masu bari na kira ta. suka wuce parlourn na ta wanda bai da gima karamin palour ne dai dai da baki maza main parloirn ta ya na sama, parlourn dauke yake da golden turkey furniture with turkey carpet mai laushin gaske, sai rabar da kamshin turaren hutan M&N àttar dake tashi wanda kamshin ya riga da ya kama gidan.
Suka karasa suka zauna.
Mai aiki ta wuce saman wanda staircase din was curved ga hasken fitila daga kasan sa, ta wuce sama a nan ma parlour ne mai dauke da royal furnish da kuma tv set sannan dakuna uku ta yi knocking na gefen daman ta sannan ta karasa ciki ta na sallama.
Ayana da ke kwance saman royal bed din ta ta budai idon ta ta na tambayar shatu lfy.
Shatu ta ce "Kin yi baki, yan'biyu ne."
Farin ciki shinfidai fuskar ta ta tashi zaune ta na ce wa ce masu gani nan ki kai masu drinks.
Shatu ta amsa mata da toh ta wuce..
Ayyan ta mike har zata wuce sai ta dawo ta dubi kanta a mudi fuskar ta da ke dauke da shatin belt ta jawo powder ta dan shafa amma a banza dan ba zai boye shatin ba hakanan ta fita dan ta na farin cikin ta ga wani ya zo gidan ta tin da mashayin mijin na ta sai dan banzan kishi har na innalilahi wa inna’ilahir rajiun. Sai dai a kullun ta na godai wa Allah da baya neman mata shi dai in dai zai sha ya ji ya haw sama shi ke nan ba Ruwansa da wasu mata, giya ita ce kawar rayuwar shi.
Ta sauko kasa fuskar ta ta dauke da fara’a ta ce "Yau ku ne a gidan na wa."
Asif ya ce" Muna ziyara muka ce bari mu kawo wa yayar ta mu ziyara."
Ta karaso ta zauna tare da ce wa "Gaskiya kun kyuata kuma naji dadi sosai."
Asim ya ce "Ina boy di nan?
Ta yi murmishi kafin ta ce ya na ciki shi da shatu kasan yau ba isalamiya."
Asim ya ce "Eh."
Ayana ta kwala wa shatu kira. Shatu dake kitchen ta na kokarin sa snack a cikin bowls ta amsa ta sannan ta dau try din drinks ta fito da shi.
Ta aje saman center table ta nace wa "Gani."
Ayyana ta ce "Kira min Mahir ki ce mashi ga baban alewa."
Ta amsa mata da toh sannan ta wuce kitchen ta dauko bowls uku da ke dauke da chinchin danbun nama sai kuma cup cakes ta dora su bisa tire ta kawo masu ta aje ta wuce sama dakin da ke tsakiya ta shiga.
Mahir dan shekara 3 da ke zaune saman baby carpet yana wasa da car toys duk ya zubar da kayan wasan sa, da ga gefen daki haddaen gadon yara blue sai kuma mini table.
Ta shigo ta ce mashi mahir ga baban alewa ya..
Kafin ta ida ya mike da sauri yana cewa "Da gaske??
Ta ce "Eh." Ya wuce da gudu ya bar dakin cike da murna zuwan uncle din na shi ya sauka kasa ya karasa wurin su ya rungumai Asim.
Asim ya rungumai shi. Sannna suka saki juna. Asim yace mashi chop knucle. Ya mika mashi suka yi .
Ayyana ta ce "Ba ka gaida su ba."
Mahir ya gaishe su suka amsa.
Asim ya jawo karamar leda ya mika mashi.
Farinciki cike a zuciyar sa ya amsa ledar yana mashi godiaya.
Asim ya ce "Maza ka je ka sha Friday gift ne from I and Asif.
Ya dubi Asif ya mashi godiya sannan ya mikawa mahaifiyar ta shi ledar yana ce mata ta budai masa ledar.
Ta amsa ledar ta budai mashi sannan ta ce ya wuce sama."
Ya yi wa uncles din na sa weaving hannu sannan ya wuce sama.
Asim ya fara tambayar ta ya jikin na ki?
Ta amsa shi da sauki
Asim ya ce "Jiya ayan ke fadi mana abin da ya maki gaskiya ismail bai kyautaba bai duba halin da ki ke ciki."
Ayyan ta yi murmishi mai cike da radidi ta ce "Ina zai gani."
Asif ya ce "Gaskiya ya kamata a san abin yi dan ba zamu zuba ido ya na zaluntar ki ba."
Ayyana ta ce "Toh mi ne abin yi fa ce in yi hakuri har Allah ya raba ni da shi lfy."
Asim ya ce "A'a hakurin da ya ga ana yi shi yasa ya ke abin da ya ga dama, yarje-jeniya za ayi a kotu daga rana da ya kara daga hannu ya duke ki ya duki auren ki.
Asif ya ce "Mun ma gama yanke shawara haka dan ayan so yayi a kai shi kotu a raba auren.
Ayyana jin su kawai ta ke dan ta san wannnan sharadin da za asa aikin banza ne bai hana mai hali chanzawa.
Suka dai bata hakuri suka wuce kasan cewa duk in da suka je shaf shaf suke yi a gaisa a wuce.
Sun fito daga gidan ayyana sun na kan hanya Asif ya tambaye shi saura wuri daya ya rage mana.
Asim yace "Kai na gaji mu bar wa wani satin."
Asif ya ce "Dadi na da kai alan kosa ne duka ina muka je da zaka ce ka gaji."
Asim ya ce "Miya shafe ka."
Asif ya ce "Ba ka ma tambayi in da zamu har ka ce ka gaji toh daman gidan su Halimatu za mu."
Da sauri Asim ya juyo ya kalle shi sannna ya ce "Impossible."
Asif da ke tuki ya juyo ya kalle shi "Why? Ba ka so nima in mika gaisuwa ta. Ya mai da idon sa saman titi.
Asim yace "Ba a bukata.
Asif ya ce "Malan ka fada min a wata unguwa ne nima in je ka sa ni ko nima in sa mu mata a unguwa ka ga shike na sai mu samu karfin tinkaran Abba."
Asim ya ce "Ba inda zamu."
Asif ya ce "Toh shike nan kai ma yau ko ba za ka je ba."
Ya dubai shi ya ce "I don’t get you."
Asif ya ce "Badai ka ha na ni ganin ta ba shi ke nan."
Asim ya ce "Kayi duk abin da zakayi dan rainin sense da kai."
Asif yayi dariya kafin ya ce "Miyayi zafi mai da wukar daga nace zan ganta shike nan sai ka tada jijiyoin wuya sai ka ce na ce zan ma snatching
Reders mi kuke tunani; Asim zai je wurin sahibar shi ko A'a??
Ina sauraran ra ayoyin ku.
Kat ku manta, vote, react comment & share.
Halimatussadiya (Sakayya) daga Meenamajeed.
C.E.O MEEMAJ love you💋❤️