Free chapter · Read without an account
8
💞💞💞💞💞💞💞💞
*AMATURRAHAMAN*
_*By*_
*_OUM FATIMA_*
_*(Hakimar D. A. W. A)*_
💞💞💞💞💞💞💞💞
_*DASHEN🌲ALLAH*_
_*WRITER'S📚ASSOCIATION*_
_*TEAM*_
_*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*_
*BOOK 1*
*PAGE 8*
_*بسم الله الر حمن الر حيم*_
*Bayan sati ɗaya*
Bayan sati ɗaya da rasuwar Abba Mukhtar mutanen gidan kowa ya manta da shi ya koma harkokin gabansa, rayuwa ta ƙara yiwa su Amaturrahaman tsanani ga jikin Umma da kamar jira yake Abba ya mutu nata ya fara nunawa don ciwo ta kwanta sosai. A hankali abinda zasu saka a bakinsu ya fara gagararsu.
Mahaifiyarsu bata da sauran dangi a nan, dangin Mahaifinsu kuwa babu wanda ya damu da halin da suke ciki. Kamar abinci wannan sai mai sauran ɗan tausayi yake basu irin su Rakiya matar Isma'il. Ganin fa idan suka zauna zasu mutu da yunwa ne, ga jikin Umma na ƙara tsananta basu da kuɗin saya mata koda paracetamol ne yasa Nafisa yanke shawarar fita ta nemi taimako.
Tun daga kan su Kawu Isa ta fara waɗanda sune ya kamata su jawosu a jiki su kula da ci da shansu da ilimin su da suturarsu a matsayinsu na ƴan'uwan Mahaifinsu na jini, amma sai suka kasa hakan suka wofantar dasu suka ɗauki ƙiyayyar da sukewa Mahaifinsu suka mayar kan Iyalansa.
Ko zasu kwana su yini basu ci ba babu abinda ya dame su, koda Nafisa taje kewayen Kawu Isa samu tayi an zubawa yaran shinkafa da miya da nama har da Salat da tumatir. Ji tayi yawun bakinta ya tsinke yunwar da suka yini da ita ta murɗo mata.
Wata muguwar harara Salaha ta wurgo mata ganin yanda ta kafe kwanon da kallo, "mayya kawai, sai dai kici kanki ba dai abincin nan ba." Ta faɗa tana ɗauke kwanon suka shige ɗaki.
"To jarababbu, uban miye ya faru kuma?." Kawu Isa ya faɗa lokacin da yake fitowa daga banɗaki ya aje butar hannunsa kusa da mazubin ruwansu. Da sauri Nafisa ta ƙarasa ta tsuguna kusa da shi tana faɗin "Ina yini Kawu."
"Ajiyarsa kika bani? Nace aniyarsa kika bani da zaki tambaye ni iye?."
Sunkuyar da kanta tayi tana tura baki sabo da itama bata da haƙuri tace "Dan Allah Kawu ka taimaka mana da abinda zamu ci, tun safe ba abinda muka ci ga jikin Umma yayi tsanani?." Ta ƙare maganar hawaye na zuba saman fuskarta.
"Kar Allah sa kucin man, nace kar Allah yasa kuci ina ruwana da cinku, ko Ni na ajeku tsabar munafurci zaki zo min da koɗaɗɗiyar fuskar ki. Jikin uwarku kuma ai daman tasan hakan zai faru tunda ta auri mazinaci ɗan tasha, fice ki bani wuri sha-sha-sha mara amfani!."
Tashi Nafisa tayi ta fice tana jin ɗacin kalaman kawun nata, shekarunta goma sha biyar a yanzu kuma tana da wayonta. A yanzu ta gama fassare duk irin magan-ganun ɓatanci da ake faɗa akan Mahaifinsu, tana jin ɗaci da ciwo a zuciyarta idan taji ana zaginsa a kan ƙaddararsa.
Hawayen daya silalo mata ta ɗauke da yatsanta ta idasa ficewa a gidan tana jin surutan da Kawu Isa keyi tamkar ya auri baki. Ɓangaren Kawu Isma'il taje shima ya shafawa idanunsa toka ya korota da baƙaƙen magan-ganu, haka ta dawo tana kuka share-share.
Umma dake kwance saman lamusashshiyar katifar da ita kaɗai tayi musu saura a ɗakin ganin yanda Nafisa ta shigo tana kuka ta zauna kusa da Amaturrahaman dake fama da zazzaɓi ta ƙara fashewa da wani matsanancin kukan na rashin samun mafita yasata tsiyayar hawaye daga kwancen da take.
A halin da take ciki yanzu yaranta kawai take tsananin tausayawa sabo da ta san mutuwa zata iya riskarta ako wane irin lokaci, gashi babu wani kyakykyawan hannu da in ta barsu za'a kula mata da su. Ƴan'uwan Mahaifinsu basa ƙaunarsu ko kaɗan, yanzu da take raye ma banda kyara da hantara babu abinda suke fuskanta bare kuma bata raye. Ƴar'uwar Mahaifinsu ƙwara ɗaya da zata riƙesu ta kula dasu tsakani da Allah bata kusa, don tunda yazo musu sallama ta ɗaga suka tafi wata ƙasar ita da mijinta basu ƙara jin koda ɗuriyarta ba.
Ita kuma bata da kowa a nan dangin Mahaifinta tunda ya rasu suka zo suka raba gadonsa suka kama gabansu ba wanda ya ƙara wai-wayar abinda ya bari. Mahaifiyarta kuwa dama marainiya ce bata da wani gatan da ya wuce mijinta. Sallamar da aka yi ce tare da shigowa ɗakin yasa su kallon ƙofar baki ɗayansu.
Rakiya ce ta shigo tana ɓoye da kwano tana wai-wayen baya gudun kar wani ya ganta ya faɗawa mijinta "Sannu Asiya, ya jikin?." Rakiya ta faɗa lokacin da take aje musu kwanon abincin da ta kawo musu a ɓoye sabo da tausayin halin da suke ciki da irin wulaƙancin da mijinta yayi wa Nafisa ya korota lokacin da taje neman taimako, kasa jurewa tayi da ya fita shine ta ɗebo abincin a ɓoye ta kawo musu da kanta gudun kar ta bawa yara su fito suna nunawa har maganar ta koma masa bayan duk kashedin daya mata.
Zuwa tayi ta taɓa jikin Amaturrahaman dake kwance tana rawar sanyi sabo da zazzaɓin daya zubar mata, taɓa jikin tayi tayi da zafi sosai nan take tausayin yarinyar ya ƙara kamata. Yarinya ƙarama amma tana da wani irin hankali da natsuwar da tafi ta wasu manyan, bazaka taɓa jin ana hayaniya da ita ba irin ta yara koda yaushe tana liƙe da Mahaifiyarta da kuma ƴar'uwarta.
Naira ɗari ta kwance a haɓar zaninta ta miƙawa Nafisa tace "Tashi maza kije ki sayo musu paracetamol a chemist in kunci abincin ki basu su sha, ni bari in koma kar Babansu ya dawo." Godiya suka shiga yi mata har Umma da take buɗe baki da ƙyar.
Ficewa tayi cikin sauri yayinda Nafisa ta kama Umma ta tashi zaune, ta ta tada Amahh itama ta shiga basu abincin suna karɓa da kyar. Amaturrahaman kaɗan taci ta fara sheƙa amai, riƙeta Nafisa tayi cikin tausayawa har ta gama ta gyarata sannan ta matsa mata ta ƙara karɓar loma biyu kafin ta barta taci sauran ta fita nemo musu magani Umma tana saka mata albarka.
***
Dokajo Mansion...
Yanzu Momy kina kallon yanda nake shan wahala akan soyayyar Ya Zayyad amma ko kallo ban ishe ba kuma ke kin kasa yin komai a kai, kuma ga wannan jarababbiyar Aunty Zaheeran kullum shige masa take tana ƙara cusa kanta a wurinsa, kar fa aje ya fara kulata in shiga uku!." Anisa ke wannan maganar ƴa a wurin Uncle Maina da Hajiya Sha'awanatu. Ita kaɗaice ƴa Mace a wurinsu sai yayunta Maza biyu Mujahid da Aarif.
"Ki kwantar da hankalinki Anisa in dai ina raye baza ki taɓa neman wani abu a duniya ki rasa shi ba, kar ki wani damu kanki da batun Zaheera zan san yanda zanyi wa Dadynku maganar nasan in har shi yayiwa Zayyad maganarki to ba musu zai amince tunda yana jin maganarsa."
"Yauwa Momy shi yasa nake sonki, don Allah kiyi wani abu a kai."
"Kar ki damu, maza Kije uzurinki." Momy ta faɗa tana shafa kanta.
*** Fitowarsa kenan daga wanka yana goge lafiyayyar fatarsa da take sheƙi, baƙa ƙirin ɗin sumar kansa irin ta Fulani yake tsanewa da wani karamin fari ƙal ɗin towel. Ƙaran da wayarsa ta ɗauka ne yasa shi ɗaga lumsassun idanunsa ya aza saman wayar.
Ganin sunan Tariq na yawo saman wayar ya sa shi janye idanunsa yaci gaba da abinda yake yi. Sai da ya gama shirin sa cikin ƙananun kayan da suka karɓi tsarin halittarsa kafin ya ɗauki wayarsa da Car key ya fice yana amsa wayar Tariq data sake shigowa.
"On my way." Shine kawai abinda ya faɗa ya yanke kiran, yana fita kai tsaye wurin da motocinsa suke ya nufa yana danna key ɗin wacce yake son fita da ita. Cikin sauri Samuel ya taso daga wurin zamansu zai amshi key ɗin a hannunsa ya ɗaga masa hannu ya shiga motar aka buɗe masa gate ya fice. A dai-dai general parking space ɗin dake gidan ya hango Salim a cikin Motarsa yana busa sigari dabi'ar daya tsana duk da kasancewarsa Jami'in Soja.
Kansa ya ɗauke yana ƙara ɗaure fuskarsa yana ɗagawa sojojin dake tsaron babbar ƙofar da suke sara masa lokacin da aka buɗe masa ya fice, kai tsaye inda zai haɗu da Tariq ya nufa don amsar bayanai dan gane da wani aikin sirri daya bashi.
***
Matazu...
Ganin dai ba wanda zai taimaka masu a cikin dangin Mahaifinsu yasa Nafisa fara fita neman aiki koda shara da wanke-wanke ne a gidajen dake da hali a unguwar, sabo da matuƙar suka ci gaba da zama a haka zasu mutu da yunwa ne ga jikin Umma kullum gaba yake.
Da ƙyar bayan tasha matuƙar wahala ta samu aikin a gidan wani mai kuɗi da ake kira da Alhaji Tanimu, aikin gyara ɗakunan yaran gidanne da kula da duk wani abu da ya shafe su zata yi. Kullum zata riƙa zuwa tun da safe zuwa la'asar za'a biyata Naira dubu talatin (3000k) duk wata.
Cikin farin ciki ta ƙarbi wannan aikin ta koma gida da albishir mai daɗi wa Ummanta da ƙanwarta.
# Oum Fatima