Free chapter · Read without an account
25
*❤️🩹SO da CIWO❤️🩹*
®©Ramlat A Manga
Mai_Dambu
500₦
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
***
Or
***
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 76
Follow this link to join my WhatsApp group: ***
Dakata hajia💃💃💃💃💃 kin Dade kina Neman inda Zaki sai amintattun jaka, da takalma, sarkoki,masu kyau da quality cikin farashi Mai sauki❓
Ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,wannan gidan na RUMIEE UNIQUE BAG'S GALLARY na budeshi ne saboda na Baku damar siyan jaka,da takalma na Yara Dana manya masu kyau da quality da Kuma saukin kudi cikin aminci daga wajena.masu siyan daya da masu sari duk Muna mataba daku
Muna Kano Muna Tura kaya kowanne state da makotan Nigeria cikin yardar Allah,
Uhmm rigi-rigi ko kun san kayanmu sun iso like bags irin wanda Maamah take amfani da shi, Veils, Shoe's, more and more suna nan dasu...... Let go ❤️🩹💃🏻🐾
Paid book
25
Duk abinda yake faruwa sai Mama take ganin bata yi kome ba a kula da ni, don haka ina farkawa ita na fara gani zaune tana kallona. "Mama!" Na kira sunanta. "Wanka zaki yi ko abinci zaki ci?" Tashi zaune nayi ina faɗin. "Bari nayi wankan dai!" "Tow muje na gasa miki bayanki da maran ko?" Zaro idanu nayi ina faɗin. "Mama kema halin Yaya kika koya?" Da yake ina ciwon ciki sosai amma nakan yi skipping month idan nayi wannan watan bai zama dole nayi next month ba har sai na shafe wata biyu zuwa uku nake yi, idan zai zo kuwa da ciwon ciki nake fama da shi a lokacin Yaya take min wanka suyi ta fada da Yaya Mama ta ce a'a kada yaya ta min wanka ta bari nayi da kaina, ita kuwa ta ce mata idan kunyata take ji sai tayi amma wanka sai ta min. Kullum rigimarsu kenan tun da na fara a shekarar da na cika 15yrs. "Ni dai gaskiya ba zaki min wanka ba!" Na fada hawaye na cika min idanu. Harara tayi tana faɗin. "Karen hauka ne ya cije ni da zan barki haka!" Kuma da gaskiyarta domin duk lokacin da Yaya tayi min wanka bana jin kome idan na tashi rigima nace kada tayi min wankan ta bar ni da halina, tow da ciwon baya nake wuni nayi ta tafiya a dudduke sai Mama ta mata magana ta ce ba zata yi ba ai itama hannu ne da ita tayi min mana. "Ni gaskiya ba zan yi wanka ba!" Rike kunnena tayi tana faɗin. "Wuce ko na tsinke shi." "Wayyo Allah na, wayyo Allah na kunnena wallahi ba zan kara ba." Haka muka shige ban dakin ta haɗa min ruwan dumi, ta dibi wani abu abu ta fara gasa min baya, sai zufa nake, tana ganin yadda nake kare kirjina.
"Ke tafi can, idan kika haihu ni ce me muku wanka daga ke har jinjirin karewa ma kenan " "Ni dai ba zaki kara min wanka ba." Na fada ina tura baki da wasu yan matan hawayena ni nan tayi min wanka, yadda ta gasa ni sai nake ji kamar an cire min ciwon jiki da ma cikin, ta fita tare da rufe min nayi wanka sosai, sannan na fito tea ta saka aka kawo min ta zuba min na fara sha kayan kamshi ne sosai har da hulba, sai da na shnye tas sannan na ci farfesun kazan da ta saka Addah Jiddah ta kawo min, ina sha amma barci nake ji. "Innarki ta tafi ta ce a baki wannan gudummawarta, abin dad'i wai tana nimawa danta aurenki." Kallon Mama nayi tana bani labarin, kafin nace. "Shi ne ta tafi babu sallama? Matar tana da kirki." "Eh ta gaya min itama bata da karamar yarinya ta ce mu bata ke a matsayin auta ba suruka ba." Hawaye ne ya zubo min na goge. "Ai kaddara ta riga fata." Na fada a hankali ina shan tea. "Muna da mafita!" Hamma Salim ya faɗa. "Wani irin mafita?" Mama da Addah Jiddah suka tambaye shi. Murmushi yayi ya ce mata. "Wannan mafita akwai hatsari, sannan akwai yiwuwar samun matsala tsakaninmu da Baffanmu." Kallonsu nayi duk muka zuba musu idanu. "Muna jinku!" "Wai dama sace gayen zamu yi mu tilasta shi fasa auren.."
"Wannan lissafin ba naka bane Hamma Salim, lissafin wancan ne." Na nuna mishi Hamma Umar, murmushi nayi na ce mishi. " Da me kuka yi lissafin? Kuna tsammanin zai iya fasawa ne? Hmm ku kawo wani dai." "Princess me yasa kika yi give up?" "A'a ba sarewa nayi ba, kawai abin da zai yiwu nake son su fahimta, abu biyu ne zai saka a fasa auren nan, na farko mutuwa ta na biyu ko b'acewata a duniyar babu labarina, zan roki Allah ya zab'a min abinda yafi alkhairi imma mutuwa ta ko b'acewata bakiɗaya na shiga duniya a nime ni a rasa." Daga haka na mike tare da ɗaukar rigar ruwan da yake cikin wardrobe din dakin, na barsu zaune sun yi jugun-jugun, dake abaya ce a jikina rigar ruwa xan saka na tafi kofar harami na zauna, na gayawa Allah bukatata.
"Kina ganin kika yi haka kin mana adalci?" Inji Addah Jiddah, "Adalcin da ya dace nayiwa kowani bangare kenan." "Kin yi min adalcin kenan?" Juyawa nayi na kalli Mama cikin murmushi na ce mata. "Mama !" "Ya isa haka bayanin da kika yi duk ba zai tafi ba, mutuwa daga Allah ce amma kika bar gidan nan kin ci zarafin Yaya kuma kin wulakanta ni a idanun duniya, na gaya miki ki bar min kome a hannuna kome zai tafi yadda na gaya miki, na rantse da Ubangiji ka'aba zan cika alƙawarin Yaya. Koda shine last chance dina a wannan duniyar believe me." Ta fada tana tawowa tare da riƙe hannuna. Hawaye ne ya zubo min, daga ranar da ta fadi haka ban kara jin wani magana ba, sai da muka kusan dawowa a saura kwana hudu a jere tayi ta azumi har ranar da zamu dawo wato tun ranar Litinin har alhamis, azumi take wanda na lura kamar zuciyarta ta kara yarda da abinda take bukata. Yakininta da tawassalinta hadi da tawali'unta yasa take cikin wani irin farin ciki a ranar da muka sauka Yola.
Ban yarda da cewa nayi kewar yayuna ba sai da suka zo bakidaya tarbanmu, na ji Hamma Jamal yana faɗin. "Saura wata biyu Princess turn to 17 wanda yayi daidai da rasuwar Yaya wata hudu da kwanaki!" Sunkuyar da kai nayi, ina faɗin. "Ba wani murna da wannan ranar ai tun da babu Yaya na daina murnan birthday!" Jan kunnena Mama tayi tana faɗin. "Ban da gulma irin naki Yaya ai adawa take da Birthday dinki, tunda bata son bidi'a," dariya suka yi duk da muna jin kewar Yaya amma kuma mun jajjurce akan lallai sai mun yi farin ciki ko Yaya musamman ni da aka makalawa farin cikin. Kwananmu biyu da dawowa na nufi bangarensu Raheemah na kai mata tsaraba da tace na kawo mata. "Assalamualaikum!" "Waalaikumunsalam!" Inji Heemah fesa min spraying tayi nayi maza na kare idanuna ina faɗin. "Meye haka?" Ina kokarin juyawa. Domin har cikin wuyana na ji abin. "Sorry ina murnan kin dawo ne fa!" Dake Allah ya tsare ni bai shiga cikin idanuna ba sai hancina da wuyana, na ce mata. "Tsaraba ba kawo miki." Na mika mata ina gyaran murya, amsa tayi tana faɗin. "Wow twins na gode duk ni daya wannan himilin bayan na gode sosai." Ta fada tana buɗe kayan. " Wow duk ni daya!" Ta fada tana d'aga wata jalbabba, "eh bari na je gida." Na fita da sauri saboda yadda naji numfashina yana hawa da sauka zan iya samun matsalar Asthma. Dakyar na isa kofar parlourn Baffanmu, nasan na iso amma daga nan ban kara sanin me ya faru ba. Uwani ta fito kitchen ta ganni a wurin shine ta fasa ihu, a cikin kuwa rigima ake tsakanin Baffanmu da Mama, akan a dakatar da auren nan bata ji akwai alkhairi a cikin shi ba, domin kuwa jiya Alhamis Uncle Mehra muna dawowa yasa an mishi bincike akan Yaron shi yasa suka ji shiru, Yaron bai da lafiya sosai. Wai har Baffanmu yake mata gorin don ba ita ta haifi Maamah ba shi yasa take kokarin hada shi rigima da Mahaifinsa, ya tsine mishi ya lalace. Ita kuwa ta ce mishi. "Idan da Alhaji ya yarda da Allah wallahi ba zai tilastawa Maamah dole ta auri Yaron ba, idan ka manta na tuna maka abinda ka rasa lissafinka a kai, ba Yaya Abidah aka so kashewa ba, Ni ce aka zo kashewa. Ni ce kuma ban yi mamaki ba, idan har Yaya ta dauki laifin zubda Jinin Hannatu matsayin nata meye kuskuren haka? Idan har Yaya ta bada rayuwarta domin kare nawa ban ga laifin da zai saka Datti tilastawa Jinin Yaya Abidah Ko ka manta na tuna maka laifinka ne kuskureka ne me yasa yanzu zamu biya bashin abinda bamu aikata ba? Me yasa laifinka da kayi wanka da shi kai da mahaifinka zamu girba?" Ihun Uwani yasa suka fito bakiɗaya, daga nan maganar ta mutu, ganin Maamah kwance jikin Uwani dafara yana zuba a bakinta, a rikice Mama ta fashe da kuka. "Me yasa? Me yasa ne? Me suka kara mata?" Suka dauki Maama a guje aka fita da ita, wannan tashin hankalin da me yayi kama. Kowani rayuwa yana da na shi kalubalen. An taru akan Maamah domin ceton rayuwarta. Mama kuka take kamar ranta zai fita, ita tayi laifi amma bata zaci laifin zai dawo ya samu har haka ba, tun ranar da Innar Ayuba ta tuna mata cewa ba Yaya aka zo kashewa ba, ta fahimci laifin nata ne, amma idan ka mata adalci wallahi bata so faruwar kome ba, asalima abin yazo a bisa tsautsayi ne. Son da bata yi a farko ba shi ya zo mata bazata. Wurin karfe tara na dawo aka samu Maamah ta farfaɗo amma ta koma barci. Kusan kwana suka yi a asibitin bakiɗaya Ahalin Yaya da Mama. Washi gari da safe duk suka tafi gida kafin sha daya sun sake dawowa. Wurin karfe biyu Dr Suraj Sheikh da Dr Hafiz, suka shigo dakin ganin ta farka amma bata magana yasa suka duba tana gyada kai. Zan iya cewa tunda na farka ban ga Baffanmu ba.
Har yamma bai kara dawowa ba, sai da dare na ga ya dawo ya zabge sosai. Hawaye ya zubo min na rike hannunshi. "Rahmatullah!" Lumshe idanuna nayi ina kallonshi share min hawaye yayi yana faɗin. "Am sorry!" Girgiza mishi kai nayi alamar ba kome. Hannuna ya rike yana faɗin. "Hatta yatsunki irin na Abidah ce, kome naki irin nata ne. But akwai laifin da nayi abidah ta dauki laifin a matsayina ta. Please kada ki guje ni idan kin ji laifina da nayi, sai dai ban san yadda zan yi ba ne. Na zabi haka ne domin farantawa Datti yau ga shi ina ji ina gani na gaza kare ki. Yaya tayi iya nata." Hawaye ya zubo mishi yau Baffanmu yana kuka a gabana. Abin da ya faru shekaru sha bakwai yau ya dawo mishi sabo fil, Yaya bata san kome ba amma ta dauki nauyin laifin hatta danginta babu wanda ya sani sai Uncle Mehra.
"Am sorry My little angel!" Hawaye ya zuba mishi. Sunkuyar da kai yayi akan hannuna. "Na rasa da waye kike kama, idan nace tsawo ne dani kike kama idan nayi maganar kyau na halitta mata biyu kika biyo, amma kuma bana ce ba ban san yadda xan yi na gayawa duniya kome ba." "Please forgive me, for my sin." A hankali na cire bututun numfashin nace masa. "Baffanmu wani abu ne?" "Babu kome!" shigowa Mama tayi tana gyara murya, ya mike a hankali zai fita.."kada ka sake wani abu mara kyau ya fito bakinka domin wallahi kowa zai ji mu da kai idan ka shirya ka yaki Datti idan baka shirya ba kome zai fito kamar yadda aka yi shi." Daga haka ya fice a dakin, "Mamana wani abu ne?" Girgiza kai tayi tana faɗin. "Babu kome Princess kawai matsalar auren nane."
"Ok!"
Daga haka na bar maganar, sannan na kwnata ina kallon Mama, barci ne ya dauke ni mai nauyi.
Daga Asibiti gida Alhaji Imam Umar Datti ya wuce, ya same mahaifinsa. Koda ya shiga yana jin muryan Dadah tana kuka ta ce mishi. "Ba yau na gaya maka amsar kudin da ake yi domin jefa Imamu hatsari zai dawo maka, Abidah ta rufa mana asiri ita da dan uwanta da yar Uwarta yanzu kace zaka hankado wannan sirrin bai isa ba sai ka ci zarafin Imamu ta hanyar aurawa Yarinyar da tana da ikon niman hakkin iyayenta. Ka sani nima ina da hakkin akan Rufa'i amma muka kashe muka binne aka bar zancen nan, kasan Abidah ta hanaka sakat akan Yarinyar shine kake jin zafi kai wani irin Uba ne mai matukar son zuciya? Tow daga yau na share Rufa'i da Hannatu a duniyar nan maganar da nake na Abidah da Imamu ce, idan ka sake wani abu ya fito duniya sai ta ji mu da kai mutumin kawai!" Jingina da bango Alhaji Imamu yayi hawaye na zuba mishi. Tabbas yai laifi da ya shiga tare da tauye kome, ya kuma kasa yarda yana da hannu a cikin kome,.yanxu abin da yake kara d'aga mishi hankali shine inherited din Maamah shine zai wanke Maamah daga auren Sharahbil ba haka bane tow ba mamaki sai dai ta auri Sharahbil." Ina ma yana da hanyar da zai bawa Maamah kome, amma a ranar da Yaya zata mutu maganarta na karshe. "Hakkin Maamah yana nan akwai second part da Third part. Idan na gaya maka nasan Alhaji sai ya amsa, ni kuma bana fatan haka." Ta fadi haka ne lokacin da ta ce ya bata ruwa ta sha. "Hakkin Maamah yana nan!" "Ka kula da Maamah ka rufe kome kamar bai taba faruwa ba!" "Ka fahimci wani abu Maamah yar baiwa ce zata gano kome amma sai ta wani silan jinin da yake yawo a jikinta mai daraja ne domin na mutumin kirki ne da babu ruwansa. Tsakanin da ta tsaga na nagartacciyar mace wacce nasan ni kaina ina kwadayin haka. Danginta zasu zo domin nima nasan zasu zo."
Rintsa idanun yayi da karfi hawaye na zuba mishi, yau yayi danansani haka yayi danasanin abinda ya faru. Kuka yake kamar ranshi zai fita. Allah yaso shi da arziki bai hada dukiyarshi da ta haram ba balle ya ga tashin hankali, yanzu babban damuwar shi su waye suka kashe Abidah idan har lokacin da aka ayi mutuwar can ba mutuwa ce ta Allah da Annabi ba zai iya cewa wannan kashe Abidah akan abu biyu ne, tsuntsu biyu aka jifa da dutse daya an biyo kan Yaya ne domin ayi reaching Hassanah, sannan an tab'a ne domin jikakkiyar gabar da ta gauraya da SO da Ciwo, Maamah ita ce abin harin gaba idan yayi lissafin wanda yayi wancan kisar da wannan tow abin harin gaba Mama ce da Maamah zunubi ce da kowa ya aikata ba tare da saninsu ba amma Datti ya san kome kuma yasan abinda ya faru....