Free chapter · Read without an account

11

by Aminatu nazeer · HALIMATUS'SADIYAH

Ta sadaqas ta ce "Kai ne Asim."

Asim yayi mamaki da ta gane shi sai ya mata alamar ta fadi. Gaban ta ya fadi ta kara dan haska su in dai ba wanda ta zaba ba ne Asim kenan.. kai Asim ta zaba ta kara cewa kai ne dai."

Asif break the game ta hanyar tafa mata ya ce "Gaskiya na jinjina maki, but taya ki ka gane mu?

Asim kuma murmishi yake ya na dade farin ciki a zuciyar sa kasancewa Halimatu ta gane shi.

Asif kuma ya cigaba "Ko da ya ke kuna masoya ya za ayi ki kasa gane shi."

Asim ya wulla mashi Harare dan ba ya son abinda yake mashi. Asif da ganin haka ya ce "Mai sunan Umma ni zan wuce kar in ci ma ku lokaci."

Halimatu ta ce "Toh sai anjima."

Har ya juya zai tafi sai ya juyo ya ce "Zan bashi kyauta ya kawo miki dan gane mu da ki ka yi."

Murmishi kadai ta mashi ya juya ya wuce.

Bayan wuce war sa ya ce "In ga wayar?

Ta mika mashi ya kashe torch light din sannan ya ce "Miyasa tin da na ba ki ita baki kunnata ba in na kira a kashe?

Duk kunya ta dauke ta sai a lokacin ta ga bata kyauta ba ko godiya ba ta mashi ba sai ta wayin ce a kan ban iya amfanin da irin wayar ba.

Da mamaki ya tambaya "Ba ki iya ba?

Shi dai bai yar daba mutumin da yayi NCE bai iya android ba kai ko iya kar primary a zamanin yanzu za ka iya amfanin da android. Ya ce "To wace ki ka iya amfani da ita?

Ta ce "Keypad."

ya ce "Toh wannan ma za ki iya." Ya dan matso gab da ita though ya bar tazara tsakanin su ya ce kin ga bari na fara nuna maki in za ki yi kira.

Jin shi kawai take dan ta iya duk abubuwan da ya ke nuna mata. shi ko ya dage ya na koya mata.

Bayan ya gama ta mashi godiya da ta wayar da kuma koya mata da yayi.

Yayi murmishi sannan yace ba komi, again ya a kayi ki ka gane mu.

Ta ce "Nima na yi mamaki."

Ya ce "Gaskiya kina da baiwa ta musanman."

Tayi murmishi ta nace wa "A’a kawai dai na chanka sai Allah ya sa na chanki daidai."

Ya ja hular kan sa kasa wurin keya sannan ya haska gefen kan goshin sa ya ce kin ga wannan mark din da shi a ke ganai mu. So da mun sa hula na rufe sai ta hanyar maganarmu, shi yana da katuwar murya. Ya ida maganar yana dariya.

Ta ce "Kar ka mashi sharri."

Ya ce "Toh murya ta dai ta fi ta shi dadi."

Ta ce "Amma da kuna yara fah, ko daman da wannan shatin a ka haifai ka."

Ya ce "Ko daya, zancen gaskiya mun yi rishin ji, a school teacher ya fita kafin ya dawo muka mai da ajin upside down so muna wasa irin dai na yarinta wani yaro ya turo ni kaina ya bugu da egdes din desk din mafarin kenan aka min stitches ya bar min wannan tabo, so ka fin tabon nan bamai ganai mu dan wani loakcin har rikita Umma muke, misali kamar in yayi laifi sai ya ce ni na yi shi in a ka tambaye ni nima in ce shi yayi shi.

Ta ce "Kar in cika ka da tambaya amma da kuna yara.

Yayi murmishi ya ce "Lokacin da muna babies Asif na da birthmark a bayan kafar sa daga giwa ta nan ta ke banbace mu sai kuma my unique smile. Ya kare maganar ta re da mata kyawatacen murmishin da ke kara bayyana masa kyawun da Allah ya bashi.

Ta jaddad kai ta ce"Allah raya ku."

Ya amsa da Amin

Shiru na dan seconds kafin ta ce "Kai ka na son twins?

Ya ce "Eh ina so amma ba nawa ba  dan ban so su chaza min kai yanda muka chajawa Abba da Umma kai musanman Abba dan shi bai ma ganai mu sai lokacin da na ji ciwon nan haka ma yan gidan mu.

Tayi murmishi ta ce "An ce abin da kayi wa iyayen ka kai ma sai an ma ka ke nan na ka nan na zuwa wanda za su chaja ma kai."

Ya ce "A'a su sha zaman su, su zo a wurin Asif ni na yafe, dan ban so su chaja miki kai."

Da jin haka tayi shiru dan a wannan gabar ba ta abin cewa balle ta amsa shi.

Ya ce "Ya kika yi shiru? hmm a ganin ki ni ke kidina ina rawana koh??

Tayi shiru, ya ce "Toh shike nan sai ranar da na aure ki za kiyi mamaki dan in tabbatar maki bani ke kidi na ba ina rawa. Kuma insha Allah ke ce nan uwar ya’yana."

Har yanzu ta mashi shiru dan ita ba ma ta iya hango kanta a matsayin shi, ya ma za ayi a ce itace matar shi.

Ya ce "Daman yau na zo maki sallama dan gobe zan je lagos, yau na so zuwa ban maki sallama ba kuma ban samai ki a waya ba shiyasa na bari sai gobe. Tsarabar mi zan maki?

Ta ce "Sai ka ce Huzaifah, ni na girma da tsaraba."

Ya ce "Toh, ni kuma kin ga har gobe in Umma zata yi tafiya sai na ce ta min tsaraba kuma ta na min."

Ta ce "Kai daban ni daban."

Ya ce "Eh mana yanzu dai dare na yi bari na kyale ki koh, kar ki damu zan maki tsaraba ke da Huzaifah da kowa. Ki mika min sakon gaisuwa wurin Umma in sha Allah in na dawo zan shigo mu gaisa."

Ta ce "Toh shike nan sai ka dawo Allah ya kai ka lfy ya maido ka lfy."

Ya amsa da amin sannan ya ce sai anjma. ya wuce ita ma ta koma ciki.

Ya isa wurin motar ya budai, ya na shiga Asif ya ce "Baban soyaya ka manta ka bar ni ni kadai."

Asim ya rufe kofar yana cewa "Malan ja motar mu tafi."

Asif ya tada motar yana ce wa "Gaskiya yarinyar nan ta ban mamaki, kasan har yanzu I can't belive ta gane mu anya baka bata sign ba."

Asim yayi tsaki kafin yace "Toh an gaya ma za ta kasa gane mijin ta."

Asif ya saki baki kafin yace "Ikon Allah har ma ka zama mijin ta toh Allah amin, kai ma ka san ka ibo ruwa wurin Abba."

Asim ya ce "Sai dai in Allah bai sa za ta zama matata.'

A bangaren Halimatu ta na shiga ciki direct kitchen ta nufa ta dau tuwon ta wanda duk dare in Umma ta gama zata raba a zuba ma kowa nasa. Ta dawo nan tabarmar ta zauna tayi bismillah zata fara cin tuwon Haidar ya ce "Allimo har yanzu ba ki bude wayar ba?

Sai da ta sa lomar tuwon bakin ta ta hadiye sannna ta bashi amsa "Dazu na budai ta."

Asee da ke kwance bisa katifa cikin net din sauro ta ce "Haidar ay dazu yallabai Asim ya zo shi da dan’uwansa sai ta daw wayar ta fita."

Umma ta dubai ta ta ce "Oh abin da ki ka dauka ke nan a dakin."

Halimatu ta dubi Asee ta ce "Sarkin gulma."

Haidar ya ce "Mu ki ba mu waya mu yi amfani da ita I dan ke baki so dubu na so."

Nusaiba ta ce "Wlh."

Halimatu ba ta ce da su komi ba ta gama cin tuwon ta ta maida kwano kitchen ta fito ta wanke hannun ta ta koma daki ta cire kayan ta ta sa marasa nauyi sannan ita ma ta fito waje ana firar dare da ita har malan Yakubu ya dawo shima yayi joining firar ta su.

Su Asim da zuwan su gida part din Abba su ka shiga suka gaishe shi sannan suka wuce na Umma suka ci abinci daga nan suka koma part din su kasancewa yau yar’mutunci ake ji.

10:24pm

Zai kwanta ya kira number Halimatu, a bangaren Halimatu suna zaune suka ji ringin din wayar ta. Ta dau wayar ta duba wanda ya kira ta ga an sa Asim ita dai ba ta yi saving number sa ba ba ma ta san number sa ba, sai ta ki daga kiran ta dannna power buttom. Har ta gama ringing ba ta daga ba.

A ka kara kira a karo na biyu ta dube su suma su ka kalle ta. Nusaiba ta tambaye ta wa ke kira.

Ta ki amsata.

Umma ta ce "Halimatu Magana fah ake maki."

Ta turo baki ta ce "Shi ne."

Umma ta tambaya "Shine  wa?

Ta ce "She dai, shi mai wayar."

Kiran Asim ya kara shigowa a karo na uku. Umma ta ce ta daga.

Ta ce "Umma 10 fah da rabi dare yayi."

Umma ta saki baki ta na kallon ta malan Yakubu ya ce "Daga ki ji mi zai ce."

Ta ce "Ay ya katse."

Saifullahi ya ce "Ba akwai kati ba."

Ta ce "Ay ya kare."

Haidar ya ce "Wa ki ka kira da katin dubu?

Malan Yakubu ya ce "Kun ga ku kyaleta ba ta so ta daga shiyasa ta ke kamai kamai kuma dare yayi daman ba son wannan wayar daren na ke yi ba."

Malan Yakubu yana ida maganar ta shiga cikin net din ta ce masu sai da safe ta yi addu’a ta kwanta.

Asim kuwa yana kira na uku ya ga bata dauka ba sai ya yi tunanin ta kwanta shima ya kwanta kasancewa gobe flight din safe zai bi.

Washe gari da safe ya shirya ya wuce part din Umma yayi breakfast da tea, bread and omelet sbd bai son cin abu mai nauyi in dai zai yi tafiya. Yayi wa Umma sallama suka wuce part din Hajiya shafa suka gaishe ta ya mata sallama  daman jiya ya riga da yayi sallama da Abba.

Da Asif da Buba su ka kai shi airport. Ya masu sallama. Kafin jirgin na su ya tashi ya kara kiran number Halimatu gab da zata yanke ta daga nan ma Umma ce ta sa ta dagawa.

Ta mashi sallma ya amsa. Kafin ta gaishe shi ya tambaye ta jiya bacci ta yi da ya kira ba a daga ba.

Ta ce "Wayar na daki ban ji kiran ba."

Ya ce "Toh ya kike da su umma?

Ta amsa "Lfy qlau muke."

Ya ce "Daman na kira mu yi sallama nan da mintuna kalilan jirgin mu zai tashi da na isa zan kira ki."

Ta ce "Allah tsare ya sauke ku lfy."

Ya amsa da Amin kafin ya kashe wayar.

Suna aje wa umma ta tambayeta kiran mi yake maki?

Ta ce "Umma kira na kwai yayi mu gaisa sannan ya min sallama yau zai..

Umma ta katse ta "Ina zai je?

Ta ce "Lagos zai je siyo kaya."

Umma ta ce "Masha Allah Allah ubangiji ya dawo da shi lfy."

Bata amsa ta ba amma a badini ta amsa da Amin.

Jirgin sun ya sauka karfe 10am.

Ya kira ta ba a daga ba sai ya kira Umma ya sanar da ita sun sauka daga nan ya wuce kasuwa yayi siyayar kayan provision ya dora su a mota. Bai dawo hotel ba sai gabannin magriba.

Yayi sallah ya sauka kasa ya siya abinci ya ci sannan ya koma sama ya kira Umma bayan sun gama waya ya kira Halimatu dan a kasuwa ya ga kiranta amma ba halin dauka. Bayan sun gaisa ya ce "Sorry dazu ina kasuwa ki ka kira."

Ta ce "Eh na dawo naga miss called din ka."

Ya ce "Good ya kanon."

Ta ce "Kano lfyl qlau, ya hanya kun sauka lfy?

Shima ya amsa da "Lfy qlau."

Shiru na dan wani seconds kafin ya ce "Ina nan ina kewarki yau ban ga kyakyawan fuskar ki ba."

Ta yi shiru ba ta amsa shi ba.

Chan kuma sai ya ce "Kunna data ki shiga whatapp ay ba ki manta ba ko, in ma kin manta yanzu sai na tuna maki."

Ta kunna data ta shiga ta ce "Na yi.

Ya ce "Okay I will hang up the call for some second karfa ki yi nisa. "

Daga haka ya kashe ya koma whatsapp ya kira ta vidioe call, ta na gannin haka sai da yan’cikin ta suka kadu sai ta ki dagawa ta mashi text da bamu da huta.

Ya na ganin haka ya kira ta. Ta na daga wa ya ce "Yanzu shike nan ba zan gan ki ba."

Yanzu ma ba ta amsa shi ba sai ya tambayi Huzaifah ta ce mashi yayi bacci

Ya ce "Nima kam baccin na ke ji dan na gaji.

Ta ce "Toh ka kwanta ka huta."

Ya ce "Ya za ayi in samu nitsuwar bacci bayan ban gan ki ba.

Ta ce "Gashi kuma muna Magana.

Yayi hamma kafin ya ce "Toh zan kokarta in yi baccin tin da yau kin hanani ganin ki."

Ta ce "A’a masu wuta ne suka hana ka."

Ya ce "Toh ni zan kwanta ki kula min da kan ki kin ji. I love you sweethe.."

Kit ya ji ta kashe wayar ya bita da murmishi. Ya aje wayar ya shiga ya watsa ruwa ya Shirin baci dan ba karamar gajiya yayi ba.

A bangaren ta tana jin wannan kalmomin jikin ta ya kada ba ta san miyasa duk tarukan samarin ta Asim ya fita daban, miye dalilin da ya sa ta ke bashi privillage da yawa. Dole ma ta nisantar da zuciyar ta daga garai shi duk da shi yana maton ta da shi. Amma abinda zaiyi wahala sosai a ce ya aure ta.

Kwana daya, biyu yayi a lagos ya dawo gida. Asif da Abokinsu Ubaid suka dauko shi da ga airport suka wuce gida.

Direct part din Umma suka wuce shi da Asif, Ubaid kuma ya na sauke su ya wuce.

Umma ta mashi maraba da zuwa. Ya gaishe ta.

Ta amsa, ta kira binta mai aiki.

Kafin ta karaso Asif ya mike yana cewa Umma ni zan koma office.

Asim ya ce "Ko kai ne alhudda hudda ka bari mu ci abinci ayi sallah."

Asif ya ce "Rufa min asiri I just excape without taking permission." Umma i'm leaving. Ya wuce da sauri dan yasan Umma na iya tsaida shi.

Binta ta karaso tare da cewa gani Hajiya.

Umma ta ce a kawowa Asim abinci.

Ta rintsina ta na cewa toh hajiya, ta wuce.

Asim ya ce "Umma wannan tafiya na dauko gajiya." Ya karasa maganar yana mimike kafafunsa.

Umma ta ce "Ay dole, Allah yayiwa kasuwa albarka, ba kudin ba albarkarsu."

Yayi karamin murmishi ya ce 'Ay Umma muna gani falalal adduar ki a cigaba da mana budi na ta zuwa ta ko ina."

Umma ta ce "Masha Allah haka a ke so sai dai na sha gaya maku kuma har gobe bazan ki fada maku ba, kar ku shafawa dukiyar kazanta, kuyi tsarkaken kasuwanci bacin amana ba riba."

Binta da Indo suka kawo mashi abinci suka aje a gefen sa. Sai da su ka wuce ya ce "In sha Allah. Ina su Aysha? Ya ida mgn ya na sauka daga kujera ya jawo plate da serving spoon.

Umma ta amsa shi, suna mkrt Safna kuma ta je kasuwa.

Ya ce "Umma da zaman nan da ta ke yi dama kasuwanci ta fara ji dai Yaaya meena( iyar hjy shafa'atu)ta na aure kuma ta na kasuwancin ta amma ita sai ta tsaya komi sai an mata." Ya na ida mgn ya sa abinci a baki.

Umma tace "Ko wa da ra’ayinsa ba ga Asif ba shi yana son aikin gwamnati kai ba ka so. Everyone has his on passion."

A daure a tashi a naimi sana'ar yi, a yanzu zama ba na mu ba ne, kar ki zauna ko mi sai an maki ki tashi ki naimi sana'ar yi kai ma ka tashi ka naimi sana'ar yi.

Muna da tarukan sana'a phsical da online sai wanda mutun ya zaba.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol