Free chapter · Read without an account

12

by Aminatu nazeer · HALIMATUS'SADIYAH

Tin da ya dawo at around 12:00pm bai fita daga gidan ba, sai bayan yayi sallah magriba ya shirya dan zuwa ganin masoyiyarsa da yake daukin gani.

Leda biyu da ke saman mirrow ya dauki karamar ya bar babba sannan ya fito. Hamza ya iske da abokansa suna biga PS, suka gaishe shi ya amsa cikin sauri ya wuce.

Da isar shi gidan su Halimatu yau layin na su babu giccin yaro, ya zaro wayar shi daga aljihun gaban rigar shi yayi dailing number ta.

A cikin gidan Umma na zaune saman sallaya kamar kullun sai Nusaiba da Asee da ke karatu Huzaifah kuma na cin abinci, Halimatu kuma ta na ciki ta na guga.

Her phone’s rang, the chiming of the phone made her pause. Ta aje iron din ta jawo wayar ta, ganin shi ne ke kiranta ran ta ya bata yana kofar gidan su. Ta dau kiran tare da mashi sallama.

Ya amsa. Ta gaishe shi ya amsa, sannan ya ce mata ta fito yana kofar gida. Ta amsa shi da ya bata 5 to 10 minute. Ya amsa mata da toh. Ta aje wayar ta kashe iron din ta fito waje. Ta ce "Umma ga Asim ya zo kuma yau ya ce "Zai shigo gaishe ki.

Umma ta dago ta kalle ta bata bata amsa ba.

Halimtu ta dubi si Asee ta ce "Asee dan Allah ku koma ciki kai ma Huzaifah koma ciki ka ida cin abincin.

Nusaiba ta ce "Mu ina Ruwan mu da shi ba Umma zai gaida ba."

Halimatu ta ce "Da Allah na hada ku, kuma in ya shigo bisa tabarmar ku zai zauna."

Umma da ta yanke wudrin ta ce "Nusaiba ku koma daki bana in ya tafi sai ku dawo."

Huzaifah da ya mike yana cin tuwon sa ya ce "Halima yauma su biyu suka zo?

Halimatu ta ce "Ban san ni  ba tambayo da kai."

Huzaifah ya aje kwanan twon ya juya ya nufi hanyar waje ya na tsidai hannunsa, tin da ta ki ba shi amsar tambayar sa zai je ya gani da kansa.

Ta kira shi da ya dagata amma ina ko dagata wa bai yi ba. Yana fita ta dau kwanan tuwon ta maida shi kitchen ta rufe shi ta koma daki ta sa hijab din ta sannan ta yi waje.

Huzaifah kuma na isa wurin Asim ya rintsina ya gaishe shi.

Asim ya amsa shi. Huzaifah ya tambaye shi ina da’uwansa.

Asim yayi murmishi ya ce "Ya na gida."

Huzaifah ya ce "Ka gaishe min shi."

Asim ya ce "Zai ji." Sannan ya mika masa ledar hannun sa.

Huzaifah yayi tsaye yana kallon ledar tare da jin tsoran amsa.

Asim ya ce "Amsa bana."

A lokacin Halimatu ta fito ta na mashi sallama. Da sauri huzaifah ya jiyo yana girgiza kan sa, Ya wuce ciki da sauri.

Asim ya bi shi da kallo. Bayan ya wuce ya dubai ta ya ce "Kin kyauta."

Ta mashi alamar tambaya ya ce "Kin hana shi amsa ba na."

Ta ce "A'a ni ba ni na hana shi ba."

Ya ce "Toh gashi ki kai mai tinda ke kin ce kin girma da tsaraba.

Har ya mika mata kafin ta amsa ya ce "Na ma fasa da kai na zan bashi daman mun yi dake yau zan gaishe da Umma, fatan kin fadi mata."

Ta gyada mashi kai, ta ce "Bismillah." Ta juya ya bita a baya suka shiga ciki.

Yayi sallama Umma ta amsa shi. Suka karaso ya tsugunna ta gefenta tare da saddar da kansa. Ya gaishe ta ta amsa sannan ta mashi ban gajiyar hanya.

Bayan sun gaisa ya aje ledar a wurin ta yana ce wa "Umma ga tsarabar hanya a ba Huzaifah."

Umma ta ce "Har da diwaniya."

Ya ce "Ba komi."

Umma ta ce "Huzaifah kam ya godai." Ta kira huzaifah. "

Huzaifah ya na cikin daki ya na jin sallamar shi ya wuce daki da sauri.

Umma ta kira sunan sa har sau biyu a na ukun ne da Nusaiba ta takura shi ya amsa sannan ya fito ba tare da ya bari sun hada ido da Halimatu ba dan shine agent din ko wani saurayin da Halimatu ta yi ita kam ba ta mashi da wasa da ya sake ya kuskusra ya amshi abin da Asim ya bashi dazu ya san in ta dawo gida Allah kadai zai cece shi.

Ya rabe a gefen Umma. Umma ta ce "Ka mashi godiya ya kawo maka tsaraba."

Ya kalli Asim yana son yin murna amma yana jin tsoran Halimatu. Ya mashi godiya.

Asim ya mike tare da ce wa Umma sai anjima. 

Ta mashi godiya ya wuce.

Ya na fita Huzaifah ya kara shigewa wurin Umma ganin harara da Halimatu ke mashi.

Umma ta ce "Ki bi shi mana ba zance yazo wurin ki ba."

Halimatu ta turo baki ta nace wa "Umma ni fah bana son shishiigewar nan, ba na son halakar mu tayi nisa har ta kai yana kashe mana kudi."

Umma ta ce "Daga ya mashi tsaraba shi ke nan ya zama laifi. Kin shiga uku da wannan bakin halin na ki." Ta jawo ledar ta budai ta, biscuit, and confectioneries, sune cikin ledar.

Huzaifah farin ciki cike da zuciyarsa ya kira Asee ya na ce mata ta zo ta ga ikon Allah ta zo ta ga kayan dadi.

Asee ta fito da ga dakin ta na ganin alatu ta karaso da sauri ta na ce wa "Umma yallabai Asim ya kawo su?

Umma ta ce "Eh tsaraba ya kawo wa Huzaifah."

Ta kalli Halimatu ta ce "Kin ga ni da kin bar ni na gaishe shi ya san ni nima yanzu da ya kawo min tsaraba."

Halimtu ta mata kwanya a kai Umma ta ce "Ban san sakarcin banza, ki bar mutun a waje haba Halimatu, mtsww ke shike nan ba za ki yi hankali ba."

Halimatu ta turo baki tana jan kafa ta na tafiya har ta isa bakin kofa. Umma ta bita da Allah ya shiryeki.

Ta na isa wurin shi zai yi Magana ta ce "Ba san haka." Ta daure fuska ta na rungumai hannun ta.

Ya ce "Ikon God what did I done?

Ta ce "Abinda ka kawo mashi yayi yawa, ka dai na."

Ya ce "Tuba na ke rankiyadadai amma ina jin nauyi in je gidan da ke da yara hanunu biyu ba tare da komi ba, biki ga su shiek(jikan mummy) suna kira na da baban alewa.

Ta ce "Su daban Huzaifah daban."

Ya ce "Ni kuma a wurina babu banbanci sai dai a wurin ki kuma kin san babu kyau nuna banbanci a matsayin mu na musulmai, mi nene dan na ma shi karamar sayyaya."

Ta ce "A wurin ku ba, bana so kuma kar ka kuma."

Yayi shiru bai ce mata komi ba duba da yanayin fushin da ta yi ko tantama babu Huzaifah tsoran feedback din ta yake shiyasa bai amsa ba haka ma da ya fito yi mashi godiya.

Shiru na wasu mintina da ba za su wuce minti 5 ba ya ce "Shi ke nan na yi laifi tuba nake."

Ta ce "Ya wuce." Ta furta ba tare da ta motsaba tana nan tsaye ta rungumai hannu.

Kiran sallah da a ka fara yi ya ce "Dare na yi ni zan wuce, take care."

Ta ce "Sai da safe." Ta juya ta wuce shi kuma ya juya ya tafi yana tunanin Halimatu wata kalar macece ita ke nan yar kyaututuka na saurayi bata amsa ko kuma shine bata son nashi.

Ta na da wani saurayi ko samari bayan shi shiyasa bata saken mashi fuska ko mi.

Haka ya cigaba da Nazari gab da isa motar shi ya hadu da Haidar suka gaisa sannan ya wuce mota. Har ya isa gida yana tunanin haka a kan sa ya na jin ba ma zai iya hakura da ita ba ba ma zai iya bari ya zama losser ba ko da samarin ta sun kai dari he will be the winner.

A wurin Halimatu da ta shigo ciki ta iske Umma, Nusaiba, Aseey da Huzaifah suna watanda da snacks din da Asim ya kawo. Ta karaso ta ja karamar kujera ta zauna saman kujerar ta daure fuska.

Ba wanda ya tanka mata chan sai Aseey ta kalle ta ta ce "Halima na dauko maki waya ki budai min??

Ko kallo ba ta samu ba, ta kama kanta. Huzaifah kuma  yace "Kaii Umma Allah yiwa yallabai albarka, kin ga wata chakulate mai dauke da kwakwa, ta kuma umma ta na dauke da gyada."

Tsaki ta yi ta tashi za ta shiga daki umma ta kirata. Ta juyo umma ta ce zo nan.

Ta dawo ta tsaya a kanta. Umma ta ce "Zaki zauna ko sai na bata maki rai sai wani shan kunu ki ke yau ga doluwa."

Halima ta zauna fuskar ta a daure umma ta fara mata fada. "Ke shi ke nan ba damar a masu kyuta sai ki nuna ba ki so, minene a ciki, roko su kayi ne da ki ke wani bata rai da har za su miki mgn ki ki tanka su ba na san sakarcin banza." Ta na cikin yi mata fada Haidar ya yi sallama. Ya karaso yana tambayar mi ta yi.

Umma ta amsa shi "Daga wannan yaron yayi tafiya ya dawo sai ya kawo su Huzaifah tsaraba shi ke nan ta ke wani bata rai."

Haidar yayi karamar dariya kafin ya ce "Umma na ce maki Halima ba ita kadai ba ce ku mata rukiyya ba zata rasa almasutsai ba."

Umma ta ce "Waya sani dan na ga abin ta na nema ya wuce iyaka."

Nusaiba ta ce "Lfy ta lau wulakanci ne irin na ta."

Halima ta wulla mata harara.

Umma ta ce "Ay sai tay tayi tin da wulakanta mutun abin birgewa ne a wurin ta." Ta ja kuntu tsaki.

Halima ta mike ta wuce daki. Ta jona socket din iron ta cigaba da gugar ta ko da malan Yakubu ya shigo a ka nuna mashi shima ya yaba sannan ya tambayi Halima in ta yi bacci.

Umma ta fadi mai abin da tayi shima ya dora a kan na Umma. Ta na daki ta na guga ta na suraran karatu ta na fatan ta gama guga kar su dauke wuta. Har ta gama ba su dauke wutar ba.

Ta maida kayanta cikin akwati sannan ta kwanta saman ledar dakin dan katifar dakin an fidda ta waje, ta yi matashi da wasu kunshi kaya. A haka ta nitse a tunanin Asim da kuma gudan saurayin ta Nura, duk da ba ta tsayaye wanda za ta ce wai da shi ta ke soyayya sai dai kowa ya zo ya kafa tutar sa.

A bangaren Asim da ya koma gida part din su ya wuce ya shiga daki, gudar ledar da ke saman mirrow ya dauki biscuit biyu da chocolate daya ya sa su a aljihu ya fita ya wuce part din hajiya shafa bata karamin parlour ya karasa ciki.

Ya na sallama Hajiya shafa ta ce "Yauwa kazo a daidai damn tin da zu Lubna ta cika min ihu da kunne."

Asim yayi dariya ya ce "Mama yar yaye ce fah." Ya zauna.

Hajiya shafa ta ce "Ni wannan yayen ba da ni ba da gangam Meena ta kawo min ita ta san tana kwiwa."

Ya ce "Maama ke dai ta ke wa kwiwa."

Ahmad da ke zaune ya ce "Daman ya za ayi ta ma kwiwa kana mata hassafi."

Yayi dariy ya ce "Je amso ta."

Ahmad ya ce "Duk ta bi ta cika mana kunne, tin dazu umaimah(mai aiki) ke lallashin ta."

Ya karasa maganar yana mike wa ya wuce ciki ya amso lubna de ke bori tana kiran sunnan Mummy.

Ya fito ya mika mashi ita ta na kuka ta na bankarewa. Asim ya mike ya amshe ta yana cewa 'It’s okay crying baby. " Tamkar ya ce mata ta kara himma ta kara fasa wata jiniya. Ya ce "Mu je wurin Mummy.'

Daga haka ya fita da ita. Hajiya shafa ta ce "Daman sai kai za ka iya."

Asim ya fito da ita waje bata yi shiru har nan waje gida wurin majalisar su amma lubna ta kafe ita mummy. Ya wuce da ita wurin motar ya budai ya shiga ciki, ya dora ta bisa cinyar sa dan ta ma ki yarda ta zauna saman sit.

Ya tada motar ya fara tuki a hankali sannan ta rage kukan ta ya fiddo biscut din aljihun sa ya bata da farko ta ki amsa sai da ya lallabata sannan ta amsa.

Ya cigaba da tukin ganin ta cigaba da kuka ya hau da su babban titi hakanan yayi zagaye da ita har sai da tayi bacci sannan ya maido ta gida.

Ya dora ta bisa kafadar shi ya shigo da ita ciki hajiya har ta kwanta dan babu kowa a parlour ya wuce dakin ta ya kunan fitila tare da nufa wurin gadon.

Hajiya ta yi hamma ta na ce wa har tayi bacci.

Asim ya nuna mata da tayi shiru. Ya aje ta bisa gado a hankali za ta tashi ya dan shafa bayan ta a hankali. Ganin baccin ya dauke ta ya tashi da ga gadon ya ce 'Maama ga sauran biscut din da choclate a ba ta in ta tashi gobe."

Ta ce "Mmm sai da safe kashe min fitilal."

Ya amsa mata da toh ta wuce wurin swith ya kashe fitilal ya fita ya koma part din Umma. Ita ma har ta yi shirin kwanciya.

Safna ya iske a karamin parlour ta na kallo ya tambaye ta Umma ta ce mashi ta na ciki ya karasa cikim baban parlour ya iske Jannat ta na waya ya wuce dakin Umma yayi sallama ya shiga.

Umma da ke zaune bisa gado ta yi Shirin bacci ta ce "Yawwa daman ina son Magana da ke, dazu Buba ya ce min ka fita da lubna."

Ya ce "Eh Umma na shiga part din maama sai na iske lubna na kuka."

Ta ce "Kai kuma sarkin san yara ka fita da ita."

Yayi karamar dariya ya ce "A’a Umma kawai.."

Umma ta ce "Ni da na san hali, Zauna ina son Magana da kai."

Ya zauna a cushine da ke kusa da gadon. Ta ce "Wata maganace ka ce sai ka dawo za ka min ita dan I can't belive wai Asim ne da soyaya, duk da dama ranar za ta zo kuma gashi na ganta."

Murmshin sa mai kara mashi kyau yayi wanda yanzu har da na soyaya.

Umma ta ce "Ohh Allah, see how you'er blushing daga na ce a bani lbrn ta."

Ya ce "Umma ki taya ni da addu’a."

Umma ta ce "As in?? ba ta san ka ne ko mi?

Ya ce "Nima ban sa ni ba."

Tayi karamar dariya kafin ta ce "Ba ka sa ni ba toh ita ta san kana san ta?

Ya ce "Eh Umma dan har gidan su na je kuma mahaifin ta ya yarje min."

Umma ta jinjina kai kafin ta ce "Ok. Yar in nace? Kuma wa cece?

An zo wurin, ya dubi Umma sai kuma ya dan kauda kai ya ce "Yar nan kano ce, kuma Umma ta hada All qualities sirikar da ki ke fatan mana, Umma she is well trained, family din su ba su dau duniya da zafi ba ko kudi, suna da rufin asiri, kin san mi Umma ta na da ilimi both Islamic and western, ga nitsuwa kunya da kamin kai, ba ta da hayaniya, kuma Umma.."

Umma ta dagatar da shi "Ka ga ya isa haka, wai wacece da kake ta xuba bayani kanta?¿

"Umma da dai kin cigaba da min addu'ar samun mace ta gari."

Umma ta ce "Ka ce she has all the qualities what else?

Yayi shiru yana tunanin taya zai fadi mata Hlimatu ce mai aikin Mummy, matar kawu mala.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol