Free chapter · Read without an account

13

by Aminatu nazeer · HALIMATUS'SADIYAH

Ta ce Kayi shiru kai na ke saurara.

Ya sauke ajiyar zuci ya ce "Umma na san ko na fada maki ita ba zaku yi amanna ba shi yasa kwara na cigaba da addu'a ke ma kin min duk da ina son yarinyar nan ina son ta da gaske kuma ina son in aure ta sai dai nasan ba zai yu ba.

Umma ta sauko daga gadon ta koma wurin sa ta zauna ta nace wa wacece I want to know her?

Ta san kai dan waye da zata ki ka, ita wacece da zata ki amsar tayin soyayar ka?

Kana dan Alhaji Inuwa wanda garin kano ke hannun su, ka na jikan tsohon sarkin Borno d'a ga current king, kuna da Kano kuna da Borno da Maiduguri, wa ta yarinya ce ta ke son sa maka dafin so ba ta isa ba. "

Ya yi murmishin ciwo ya ce "Umma ba iyar kowa ba ce, mtsl na daga wurin ku na san ba za ku bari na aure ta ba musanman Abba dan su din talakkawa ne, ba masu kudi bane, ba masu matsayi ba ne ba masu gata bane ba masu sarauta ne sai dai kuma suna da abin da suka fi mu duniya da lahira wato ilimin addini.

This is a bolt from blue, bata tsanmani haka ba.  Ta ambaci sunan sa sau biyu cike da mamaki kafin ta ce "Kai ma ka san zancen nan ba dan’uwansa bane."

Ya marairaice ya na cewa "Umma shiyasa nace ki taya ni da addu'a dan wlh ta ma riga da ta sa min dafin son ta da har ina ji rayuwa ta ba cike ta ke ba in ban samaita ba."

Da farko Umma ba ta so ba ganin yanda yayi sanyi ya na Magana hakan ya sa ta tausa maganar ta. Ta ce "Fadi min ina kuka hadu? Har yanzu ba ka fadi min ba."

Yayi shiru yana fargaban abin da za ta ce.

Ta ce "Ba shiru za ka min ba mgn za ka yi kila in na gamsu in taimakeka wurin Abban ku."

Dafe goshin sa yayi yana kallen kasa yayi shiru. Tabbas Umma ta fuskanci damuwar sa hakan yasa ta kara tausasa lafazin ta "Ta ce Asim you should open it to me ba wai ka boye ba, ko da ya ke ban kai matsayin da zan ji ta cikin ka ba bari na kira Asif."

Da sauri ya dago kansa wanda umma tayi mamakin chanjin launin idon sa daga fari ya koma jaja-jaja. Ta  ambaci sunan sa.

Ya ce "Umma ba zaku taba fahimtata ba musanmana Abba, dan Allah ki min addu'a, Allah ya cire min ita a zuciyata na san ba matsayi na ba ce amma zuciya bata da kashi ta rasa wadda zata so sai iya talakka, talakkan da bai aje ba sai yafita ya naimo, and the worst thing wai yar aiki a gidan kannen mahaifina wanna wata irin jarabawa ce Umma?

Ya  rufe mata baki ba ta da ta ce wa jin mai aiki. Ya cigaba; "Umma kin tilasta sani na so a ce in kashe in birne in zan iya sai dai a bune mai wiya a wuri na, umma yarinyar nan ba kowa ba ce fa ce Halimatu mai aikin Mummy matar kawu mala.

Saukar mari ya ji a kunchin sa. ya rike wurin ya sadda kai.

Rai bace ta ce "Ba ka isa ba gwara tin wuri ka ma cire ta a zuciyar ka dan kai ba tsaran ta ba ne. Mai aiki ina kai ina mai aiki. Zancen nan ba dan'uwansa ba ne gwara tin wuri ka cire ta a zuciyar ka dan abin da bazai yu ba ko ni ba zan aminta da haka ba balle mahaifin ku. Mtsww shasha-shasha.

Ta mike ta koma gado kafin ta ce "Kashe min fitila ka tafi.

Ya mike kwantakwata bai da kwari jikin sa ya kashe fitila ya koma dakin su.

Umma da fitar shi ta kasa gane haka, mai aiki da gaske dan ta yake so, sai kace a rubutun zubai.

Dole ta dagatar da shi dan wanan zubar da mutuncin su zai yi, mai aiki.. haka har ta yi bacci tana tunani.

Ya na shiga part din su, Ayan ya iske shi kadai a parlour ya mashi sallama ya wuce cikin dakin su.

Ba wanda ya tanka ma wa ya chanza kayan shi ya kwanta tare da juya masu baya.

Ya rufe idon sa yana jin zuciyarsa na masa nauyi ga zafin da ta dauka lokaci daya, Umma ce hope din sa idan ta yarda ya san za ta shawo kan Abba sai dai a wannan karon ita kanta bata goyi bayan shi ba.

Har su ka kwanta yana tunani kala kala har dai gari ya waye. Sai bayan ya dawo daga Asuba ya samu bacci.

Asif kam ya lura da yanayin sa tabbass yasan Umma bata aminta da maganar Halimatu ba daman yasan abu ne mai wiya dama ita din ba mai aiki ce ba a gidan Mummy da abin ya zo da sauki. Ya shirya ya tafi aiki.

Asim kuma da ya tashi ya shirya ya shiga part din Umma ya gaishe ta sannan ya wuce part din hajiya shafa ya gaishe ta yaba lubna hassafi sannan ya wuce kasuwa amma kwatakwata bai jin dadin jikin sa.

A chan yayi breakfast, ya na gama sallah la’asar ya koma gida ko part din ta bai shigaba ya wuce daki ya kwanta bai tashi ba sai da a kayi magrib ya tashi yayi sallah a dakin sannan ya sa Hamza ya kawo mashi abinci yana gama ci ya shirya ya wuce wurin masoyiyar sa.

Ya na karasowa ya ci karo da Halimatu a waje ita da wani, mumunar dakawa zuciyarsa tayi sai dai yayi kokarin rike kan sa dan tabass mace kamar Halimatu ba za ta rasa saurayi ba.

Ya karaso wurin su ya mikawa Nura hannu suka yi musabaha. Shi dai nura bai san waye ba ita kam ta fauzai.

Ganin haka ya kara karyas masa da gwiwa sai ya wuce wurin kofar gidan su dan ya jira ta.

Nura ya tambaye ta waye shi?

Ta ce "Wai so na ya ke."

Nura ya dubai shi sai ya kalleta ya ce "Ki ce a zage damke kar ya min tawaye.

Ta amsa shi da uhmm.

Ya ce "Amma tin yaushe kuke tare??

Ta ce "Ba a jimaba ko wata daya ba muyi ba."

Ya jinjina kai ta ce "Ina zuwa bani minti daya. Ta wuce wurin Asim. Ta na karasowa ya tambaye ta waye shi.

Ta amsa shi "Nura ."

Ya maimata sunan kafin ya sa ke tambayar ta  "Ya fi ni matsayi a wurin ki."

Ta dan yi shiru kafin ta ce "Matsayin ku daya da man na zo in baka hkr in zaka iya jira har ya tafi in kuma ba zaka iya jira ba shike nan." Ta wuce.

Asim ba karamin zafin maganar ya ji ba ya bi ta da kallo har ta isa wurin Nura.

Nura ya ce "Yana ga yana bin ki da kallo bai san kin kusan zama tawa ba."

Ta ce "Nima ban sani ba."

Ya ce "Kin ki bani dama in turo magabata nan."

Ta ce "Na ce ma sai na ida kammle karatu na."

Ya ce "Amma kin yi NCE, degree kuma ko ki na dakin ki zaki iya yin sa."

Ta ce "Bari dai muga yanda halli zai bada."

Ya ce "Gaskiya zuwan sa ya sa mun zeal din daure damara kar ya min talala."

Bata dai bashi amsa ba dan ita yanzu ba ma ta da zabi duk da zuciyarta ta bi kwanciya da nura wanda shi ne daidai matsayin ta amma kuma Asim soyayr sa a fili ta ke wanda idon sa kadai ya isa mutun ya gane haka.

Haka ya tsaya ya na jiran ta shi kuma Nura ganin haka ya rike ta kusan hourn su daya ta ma manta da Asim na jiran ta. Dan dakalin gidan da ke gefen su ya zauna yana jiran ta.

Nura na komawa saman maschine da niyar tafiya ya tashi daga dakalin zata wuce gida ya yi saurin shan gaban ta.

Ta dagata. Ya ce "Amira kin ce na jiraki kuma zaki wuce ciki."

Ta ce "Baka ga dare yayi ba, zan kwanta." Da ga haka ta wuce ta gefen sa ta shiga ciki.

Nura kuma na ganin haka ya ja machine din sa ya wuce.

Ba karamin zafi yaji ba sai dai ba yanda ya iya tinda shi ya gani kuma ya ce ya na so.

Haka ya koma gida jikin sa duk ba dadi ya na shiga dakin su ya wuce ko part din Umma bai shiga ba. Ya wuce daki. Yau ma bai kula kowa ba wanda hakan ya fara damun dan’uwan sa.

Ya fita ya je part din Umma. Ta na zaune a parlour ya tambaye ta mike damun Asim.

Umma tace bai lafiya ne?

Ya ce "Eh, tin jiya jikin sa ba dadi."

Ta ce "Nima ban sa ni ba ka tambaye shi ba kun fi kusa ba."

Ya juya ya wuce ya koma dakin na su. Buba da ke dakin ya roke shi da ya dan basu wuri.

Tsaki buba yayi ya mike ya na cewa "Kun gama in dai tayi tsami zamu ji." Ya na fita Asif ya zauna a wurin gefen sa. Ya ce Asim what wrong with you? Please tell me. Mike damun ka?

Asim ya ce "Asif let it be."

Cike da damuwa ya ce "No ka fada min.

Asim ya ce "Ka taya ni da addu’a."

Asif ya ce "Kai ka sani tin da ba zaka fada min ba duk da raina ya bani Amira na da sanadi a ciki."

Asim ya ce "Ko daya ba ruwanta, kawai dai ka taya ni da addu’a."

Ya ce "Okay, Umma ta sa ni did she approve?

Ya girgiza masa kai. Asif ya ce "That is the point, ni na san duk yanda za ayi rinshi lafiyar ka na linking da Amira, Umma ba ta yarda ba ina ga Abba.

Asim ya kwanta tare da rufe jikin sa da bargo ya ce "Ni dai kawai ka taya ni da addu’a." Ya ida rufe jikin sa da bargo.

Ganin haka Asif ya koma dayan side din ya kwanta shima ya na tunanin yanda zai billo wannan lamarin, shin hakura Asim yakamata yayi da ita ko mi? B,ut it’s a sheme ya auri yar aiki, dolle zuciyarsa ta hakuri da ita though zai shiga damuwa na wani halai kafin Allah ya hada shi da wata amma rabuwar shi da ita shi ne alkhairi da ita kanta yarinyar ba dadin gidan za ta ji ba.

Washe gari abu kamar da wasa zazzafi ya rufe shi.

Asif ya yi yai da shi su je clinic amma Asim ya kiya ga jikin sa sai kara daukar zafi yake.

Buba ma yayi yayi ya kiya yarda sai Buba ya wuce kasuwa ya barshi da Asif.

Asif ganin jikin sa na kara daukar zafi numfashin sa na dade nauyi ya bar dakin da sauri ya wuce part din Umma ya ce mata Asim bai lafiya sosai kuma yaki yarda mu kai shi asibiti Umma dan Allah mu je ki mashi magan zai ji maganr ki.

Umma ta ce " Ya sha magani bana, rishin lfyr ay ba ta yi tsananin xuwa asibiti ba

Ya roke ta da ta su je ta mashi magana.

Tamike tare da cewa ka wani damu kanka muje in gani.  Suka wuce part din su suna shiga dakin Umma ta karasa tana ambaton sunansa amma shiru bai tanka ba ta karaso ta ja blanket din da ya rufa ta daddadbai shi amma ya yi shiru bai yi Magana ba.

Da sauri ta kai hannun ta wurin hancin shi.  Jin yana lumfashi ta sauke tagwayen ajiyar zuci. Sannan ta ce kama shi muje asibiti.

Suka kama shi suka fita waje a kan hanya Abdullahi ya rike shi Umma kuma ta koma ta dauko key din motar ta ta yafa gyalen ta suka wuce wurin mota. Shi da Umma a baya sai Abdullahi da ke tuki.

Suna isa asibitin Abdullahi ya fita ya samo mashi bed da nurses suka fito aka fiddo shi a ka wuce da shi emergency.

Doctors suka haw kan shi. Bayan wasu mintuna suka mai da shi amenity room. Bayan sun fito Asif ya tambayi Dr Nawfal mi ke damun sa Dr Nawfal ya ce "Biyo ni office." Daga haka ya wuce.  Ya bishi a baya.

Bayan wucewar su Abdullahi ya ce da umma ta ki kwantar da hanakli ta ba abinda zai sami shi.

Suna isa office. Dr nawfal ya zauna bisa kujera ya ce da Asif shima ya zauna. Asif ya zauna tare da tambayar mike damun shi.

Dr nawfal da mamaki ya tambaye shi Daman yana da ciwon zuciya?

Asif yayi mamakin haka ya girgiza kai ya na cewa "A’a"

Dr Nawfal ya ce "Toh ya samu heart bradycardia.

Ta kara da "Wata damuwa ke damun sa ne da har zata yi zamai heart palpitation

Asif ba karamin mamakin haka ya yi ba ya ce "Dr kana nufin he is depressed?¿

Dr yace "Kusan haka amma heart beat din sa was very low da at any moment zai iya rasa ran sa, sai dai wani ikon Allah amma in sha Allah tin da yana under traetment kuma kun kawo shi da wuri zai samu sauki."

Asif da gaba ki daya ya rude jin an ce dan'uwan na sa zai iya rasa ransa.

Ya ce "Dan Allah Dr you should do all the possibilities, dan Allah kar ya mutu ya bar ni dan Allah."

Dr nawfal ya ce "In sha Allah ba zai mutu ba ka kwantar da hankalin ka a shawarce ka yi duk yanda zaka iya ya daina sa damuwa mai nauyi ko bakin ci a zuciyarsa."

Asif ya ce "In sha Allah zan yi." Na godai.

Ya mika mashi hannu suka yi musabaha sannan ya fita. Ya koma wurin su Umma. Kafin ya karaso ta tambaye shi mi likita ya ce.

Ya karaso ya zauna ya ce "High fever ne kawai."

Jin haka Umma ta samu nitsuwa dan tunani ta ke kala kala a zuciyarta kar dai a ce soyyar wannan yar aikin ce ta kwantar da shi.

Ya ce "Umma ki kwantar da hankalin ki."

Umma ta ce "Shi ke nan amma ba za su masa tests ba hign fever kadai??

Ya ce "Eh haka yace min he asure min he will be well Ta ce "To Allah ya tashi kafadun sa."

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol