Free chapter · Read without an account
3 RANCE
Page 3 RANCE
Samun jari ta hanyar rance ya kasu gida biyu, hanya ta farko ita ce:-
GUN ƳAN KASUWA.
Idan da akwai attajirin ɗan kasuwa da ka sani acikin anguwar ku ko yankin ku, toh sai ka nufe sa da buƙatar ka ta neman rance.
Ka ziyarce sa a gidan sa, ka yi masa bayani dala-dala akan kasuwanci ko sana’ar da kake son farawa.
Ka tabatar ka fahimtar da shi amfanin kasuwancin da kake son farawa da tasirin sa ga al’umma.
Yin hakan zai gamsar da shi, har ya ji zai iya cire kudin sa ya ranta maka.
Idan ganin sa zai ma ka wahala toh ka rubuta masa wasiƙa ta takarda ka kai masa.
SHAWARA
Kada ka cin masa a gun kasuwancin sa, domin a lokacin abubuwa sun masa yawa.
Ka iskar masa a gidan sa bayan ya dawo daga gun kasuwancin sa.
Idan ganin sa ba zai yi wahala ba, shawara ce ka taka da kan ka, ka iske sa a gida madadin ka rubuta masa wasika. (Domin zuwa da kai ya fi aike.)
_______________
A BANKI.
Hanya ta biyu ta samun rance ita ce a banki.
Akwai bankunan ƴan kasuwa da ke bayar da tallafi da rancen jari wa ƙananan ƴan kasuwa.
Bankuna irin su:- SMEDAN, BOI, NIPC da sauran su…
Ka ziyarci shafukan su na yanar gizo ka cicike ƙa’idodin su, domin su ba ka tallafin ko rance da kake buƙata.
DARASI
Ba kowa zai samu tallafi ko rancen jari ta wanan hanyar ba.
Za ku iya ɓata lokaci sosai ta wanan hanyar wajen jiran sakamako.