Free chapter · Read without an account
EPISODE 5
RAUNIN ZUCIYA
©Zahra Royal Star
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION
EPISODE 5
House No: 23, Ahmadu Belloh Sardauna Estate, Katsina State Nigeria
A hankali ta miƙa hannu ta amshi kofin da Mama ke miƙa mata, tana ɗan taɓe baki.
Mama ta kalleta cike da takaicinta, ta saki tsaki tana banka mata harara ta ce.
"Har yanzu baki da hankali Hamda, ke kin san waye Mubarak kuwa?, wallahi da kin san shi waye a yanzu bazaki tsaya ina miƙa miki maganin da zai saka ya soki ko bai shirya ba, da baki tsaya kina taɓen min baki wajan amsa ba, sana kina kwaɓe min fuska. Lokacin da Mubarak yabar Nigeria baki ma wayo shi yasa baki san waye shi ba, hatta gidan nan da muke zaune nashi ne muka zo muka tare, domin dama muna jiran wannan ranar ta dawowarsa ƙasa Nigeria, munyi babban shiri da dawowar tashi".
Zama Hamda tayi tana idasa shanye ruwan ta kalli Mama ta ce.
"Mama tuni fa nasan shi a photo, ni kawai bai.....
Mama da wani irin sauri ta ɗaga mata hannu tana cewa.
"Wallahi har yanzu shashasha ce ke, wannan photon da kike gani ai ba ainafin kyan nasa bane, ki bari ki gansa a zahirin gaskiya shine zaki iya yanke hukunci, shida bama ya son yana yin wani photo, idan kinga photonsa to bai sani ba aka ɗauke shi, dan haka ki bari zaki bani labari zuwa ƙarfe sha biyu na rana idan kuka je ɗakkosa a Airport".
Murmurshi kaɗan Hamda ta saki tana kallon ƙofar babban parlon gidan, zatai magana mai aiki ta shigo, basu kalleta ba, ta fara kawo masu gaisuwa, cike da rainin wayo da alamar sun saba yima na ƙasa dasu hakan, tashi tayi domin nufar ƙofar kitchen, Hamda ta tsaida ita ta ce.
"Ke dawo nan"
Dawowa tayi kanta a ƙasa Hamda ta ce.
"Kije yanzu nan a fara shirya abinci mai kyau domin Y Mubarak zai sauka ƙasar zuwa an jima".
Ɗan duƙawa tayi alamar girmamawa ta amsa ta wuce zuwa ƙatoton kitchen ɗin gidan.
Hamda dake kallon Mama ta ce.
"Mama wai duk cikin ƴan uwan Y Mubarak sai mu kaɗai ne ya yarda mu zauna a cikin gidansa koda baya ƙasar?".
Murmurshi kaɗan Mama ta saki tana kallon Hamda ɗin kamin ta ce.
"Har yanzu ke yarinya ce Hamda, ni kaɗai na rage masa a cikin ƴan uwan Mahaifiyarsa, ƴan uwan Mahaifinsa kuwa ko wannensu yana basa kulawar data dace, mu kaɗai ne makusantanshi, kuma kema tun kina yarinya da Mahaifinki ya rasu shine musabbabin abinda yasa ya dawo damu a hannunsa, ni kuma banda buri sai na ganin ki zamo Mata a wajan mutum kamar Mubarak Khabeer Ƙanƙara, ko ina zan iya shiga a duniyar nan domin dai naga kin auri Mubarak Khabeer Ƙanƙara, koda hakan zaisa na saɓa hanyar Ubangiji ne kuwa".
Shuru Hamda tayi tana satar kallon Mama, itafa rayuwarta rayuwar ƴanci take so, bata son takura ko kaɗan, shi yasa Mamar ma ta barta duk ta sangarce ita ce yawo can ita ce yawo nan, shi yasa yanzu hatta ma'ala da maza ta sani, idonta a buɗe yake, ita kanta Mamar tasan ƴar tata ta san maza da daɗin namiji, shi yasa kullum cikin ɗora mata maganin hana ɗaukar ciki take, shi yasa kuma take son ƙaƙubama Mubarak ɗin auranta, saboda tasan da wuya wani yazo neman auranta, ba'a samu wani ya zigesa ba, duk da rayuwar birni suke amma fa yanzu kiwon mutum ake ba dabba ba, Hamda bata magana ko kaɗan, tunda ta taso ta gansu a wannan kantameman gidan shikenan take ɗagawar sune keda kuɗin, ita bata ma tashi sanin ainafin waye mai wannan uwar dukiyar ba sai kwanakin da Mubarak ɗin zai dawo ƙasar, amma Mamar bata taɓa sanar da ita waye mai wannan uwar dukiyar da suka zo suka hakimce akanta ba, duk ɗaukarta kota Mahaifinta ce wadda ya mutu aka bar mata gado shine suka taso cikin dukiya haka, tunda sadda Mubarak ɗin ya ɗakko su ya kawo cikin gidan nashi ita Hamda na ƴar karama ne lokacin ma tana rarrafe, ko yayeta ba'aiyi ba.
Hasalima da ƙanin Mamar wani mai suna Abubakar, wadda suke kira da Abu, harda shi aka taho shike tsare duk wasu abubuwa daya shafi gidan, komai shike kula da shige da fice na ma'aikatan gidan da abunda ya shafi wasu al'amura na cikin gidan, ko kuɗi zai aiko a ba wani daga cikin ƴan uwansa ko wani ta hannun Abu yake biyowa, ko kuɗin ma'aikatan gidan ta hannun Abu suke biyowa.
Mama ce ta shiga ta fita har ya yarda dasu haka ya damƙa masu ragamar komai nasa dake Nigeria, sai dai wasu abubuwan dashi ne kaɗai ya sani na Companys nasa dake nan Nigeria shi kaɗai ya sani sai P'A ɗinsa, da suke gudanar da komai a can yana tafiya yadda ya kamata, iya abubuwan dake gidan nasa ne kawai ya bari suka sani, kuma suke kula dasu.
Mama da Abu wasu mutane ne masu mutuƙar son kansu, kansu kawai suka sani, duk wani ai'ke da Mubarak ɗin ke yowa dan aba ƴan uwansa, basa ba wadda aka ce ɗin, idan ma sun bada saboda ko zai gaine, baza su bada yadda ya turo da saƙon ba, sai sun ɗebe rabinsa sana suke ba mutum, shima sai sadda mutum ya kawo kansa domin a bashi saƙon da Ƴallabai Mubarak ɗin ya bada.
Duk wani asiri da kulle-kulle da Mamar keyi Abu ne ke zuwa wani Ƙauye da suka taɓa zama a can, ko nace garinsu da suka baro, can yake zuwa ya amso asiri a cewarsu taimako ne yake amsowa, duk da sun san ko sunyi asirin nasu baya wani kama Mubarak ɗin, amma duk da hakan basu taɓa yarda cewar bai kama shi ɗin ba, saboda komai suka tambaya basu yake ba gardama, ko kuma suje masa da wata buƙatar kai tsaye yake biya masu. Sai dai abunda basu sani ba, ba asirinsu ne ke kamashi ba, hasalima gani yake ai sune kaɗai wadda suka rage masa ƴan uwa na kusa-kusan nan, shi yasa kawai yake kyautata masu domin gani yake idan yana kyautata masun kamar ya faranta ma Mahaifiyarsa rai ne duk da bata raye.
A hankali Mama ta ɗaga kanta tana duban Abu daya shigo afujajan, yana faman zare ido.
"Kai kuma Abu lafiya zaka faɗo kamar wadda ƴan Sanda suka biyo".
"Haba Yaya ai dole ki ganni a ruɗe fa, kin fa san Ƴallabai yau zai dira ƙasar nan fa".
Mama ta nisa tana dubansa sosai ta ce.
"Na sani mana to sai akai yaya?".
Kallon Hamda yayi ganin tasa abun kunne a kunnanta bata jinsu yasa shi cewa.
"Yawwa Yaya, kinsan fa ba'ayin wata Ƴallabai Mubarak bai turo saƙo zuwa Rimaye ba, kin san abokinsa Baba Mlm ne yake zaune a can Rimaye, duk wasu kuɗin da yake turowa harda na Baba Mlm ɗin, domin nasa ma na daban ne, ke yasha kira na waya ma na haɗa sa da Baba Mlm ɗin, amma sai na samu wata ƙarya nayi masa, shi kuma da yake yayi mugun yarda da mu, bai tsayawa wani jin dalili yake yarda da duk abunda zan sanar dashi. To kin san idan ya dawo dole ya nema Baba Mlm yaje inda yake, ni tsoro na kar Baba Mlm ɗin ya sanar dashi ba'a kai masa komai fa".
Mama itama da hankalinta ya ɗan tashi, sai zuwa can ta ce.
"Kai ka kwantar da hankalinka, babu abunda ya isa yayi mana, bai dai isa ya ce zai kore mu ba, mun riga da mun zame masa ƙarfen ƙafa babu yadda ya iya damu, ni nasan miye zance masa"
"Yawwa Yaya ai shi yasa ma nazo tuni na ƙara tunasar dake, nasan ku mata akwai dabara sosai, ni bari naje wajan direbobin gidan nan su shirya domin da mota kusan biyar za'a je ɗaukarsa, ai harda ke Yaya ko?".
Murmurshi kaɗan Mama ta saki ta ce.
"Noo da dai Hamda za'aje, amma fa saika kula da ita, kar taje tayi masa wannan shirmen nata Please".
"Karki damu Yaya, ai idan ta gansa ma kwarjininsa kaɗai ya isa yasa ta natsu wallahi, ai Ƴallabai duk yadda take ɗaukarsa ya wuce nan, duk yadda za'a baka labarin kamaninsa bai kai ya ka gansa da idanuwanka ba, yo Yaya ko can Ƙasar wajan fa Mata rububinsa suke bare ace ga nan Ƙasa Nigeria. Yaya fa dole sai mun sake dagewa wallahi, ayi-ayi mu samu Hamda ta auri Ƴallabai Mubarak, idan ta auresa ai mun ƙara warkewa wallahi, domin ƴan matan yanzu kota ina kawo masa hari ake, danma sunga shi ɗin baya son raine, kuma ya daɗe baiyi aure ba kusan shekara arba'in, shi yasa kowa ke kallonsa da ko neman mata yake, ko kuma wai aljana ce ta hanasa auran, basu san shi Matan ne kawai basa gabansa ba, sai kace wadda baya jin sha'awar Mace, wato Yaya ban taɓa ganin mai tsananin kame kansa irin Ƴallabai Mubarak ba, duk tsawon shekarun nan bai taɓa kusantar zina ba, hasalima ya tsani duk wasu masu yinta, yana da wani irin mugun kyamar masu kusantar ta, ni ina gudun ranar da zai gane Hamda.....
Mama tayi saurin ɗaga masa hannu tana zaro ido waje.
"Abubakar wai mi yasa idan ka kama ratatu zance baka iya kwanturorin bakinka ne?, sai zuba kike kamar kanyar data lalace, so kake ƴan aiki ko mutanen dake gidan nan suji ka ne?, a samu wani ɗan baƙin cikin yaje ta bayan fage ya sanar dashi, kuma kake ta wannan ya ma za'ai ya gane cewar ba budurwa bace?, ni nasan ai irin gyaran da zan mata namu na mata, ta dawo kamar budurwa. Kaga mubar zancan nan kamar ma tsautsayi wani yaji mu".
Ɗan dafe bakinsa Abu yayi yana ɗan murmurshi ya ce.
"Ayi hakuri Yaya, kin san bakin nawa ne baida linzami".
"Ni ko na san hakan. Yaa kamata kaje a fara shirin zuwa Airport ɗin nan, domin naga sha ɗaya da ƴan mintoci yanzu kuma sha biyu jirginsu zai sauka".
Mama ta ƙare maganar tana duban agogon dake maƙale a bangon parlon.
Hamda da idonta ke kulle dama tana kwance ne a kujera, ta ɗan mike ganin Kawu Abu ne yasa ta cire abunda ta maƙala a kunnan nata, da duk bata ji shigowarsa bama sai lokacin.
"Kawu Abu ashe kaine ka shigo?".
"Nine Hamda, ya kamata ki tashi ki shirya dake za'a je tarbo Ƴallabai, Please Hamda kisan irin shigar da zakiyi wajan zuwa Airport ɗin nan, kiyi shiga irin ta mutumci dan Allah".
Ɗan taɓe baki tayi kaɗan tana jin an takurata sosai, domin harga Allah bata son sa manyan kaya, kullum cikin ƙananun kaya take, domin yanzu haka ma daga ita sai wando sai wata riga fara ko Cibiyarta bata rufe ba.
Tashi tayi tana faɗin.
"Bari to na saka Abaya irin ƴar ƙasar Dubai ɗin nan, saboda bazan iya saka atamfa ba ko Hijab gaskiya".
Mama dake kallonta tana hawa saman benen ta ce.
"Ai ko Hamda da kinyi hakuri kin san kayanmu irin na hausawa atamfar, domin Mubarak yafi son yaga Mace da kayan hausawa wallahi, bare ace kisa kayan masu ɗan duhu haka, saboda yana son kalar baƙi da fari a rayuwarsa".
Bata ma jita ba tayi saurin ƙarasa hayewarta saman.
Mama ta dawo da dubanta wajan Abu tana cewa.
"Waccan yarinya bata da hankali amma ina jin idan ta gansa dole ta gyara dabi'unta. Ni ba wannan bama, ka tabbatar dai an gyara masa part ɗinsa?".
"Haba Yaya ai tun jiya aka gama gyara shashinsa, komai ya zama radi nake gaya miki".
"To yayi zaka iya zuwa ku shirya domin tafiya yanzu nasan itama zata fito".
Da to ya amsa yana ficewa daga parlon...
Unguwar Yammawa Rimaye, Kankia local government Katsina State Nigeria
Ummi ce kwance akan katifarta, tana ɗan latsa wayarta sai Halima dake kwance itama akan nata gadon, itama dai wayar take yi da wadda zai aureta.
Ummi ta kalli cikin wayarta Datarta dama a buɗe take tana ɗan kallon photos a cikin facebook da videos data ke cin karo dasu.
Tana cikin kallon auran da Ahmed XM yayi da Safeera, da aketa yayato a social media, kota ina ka shiga maganar dai auran ake, itama bikin ne take kallo yadda ake kashe naira wajan bikin, haɗe da shiga comments ɗin mutane tana karantawa, yadda wasu ke kushe auran nasu, wai yaci amanar matarshi Safiyya da auransu da shekara ɗaya yayo mata kishiya, kishiyarma da tsohuwar budurwarsa, wani idan ta karanta comments ɗin dariya ma yake bata, tana mamakin yadda mutane suka maida hankalinsu ga auran Ahmed XM ɗin, mai makon su maida hankali akan tasu rayuwar, da abunda ya dami tasu rayuwar ko kuma ma suyi magana akan matsalolin ƙasar, yanzu suna nan gashi ƴan bindiga kusan koda yaushe zasu iya shigo masu gari da makwabtan garuruwansu, baka taɓa ji anyi magana akan haka, sai wani abun da baima kamata a maida hankali akansa ba, shine mutane ke tada jijiyoyin wuya akansa, ta tabbata maganar auran da suke yi shi kansa Ahmed XM ɗin da Safirar bama su san anayi ba, koda sun sani sun maida wa'inda suke kushe auran da magana akansa mahaukata, to tunda basu san dai da zamanka a duniyar nan ba, kai wani ma harka mutu baza kaga wani Ahmed XM ba, to na miye kazo kana tada jijiyoyin wuya?.
Tana cikin kallo da tunanin abun, taga an turo friends, ta facebook ɗin, wajanta shiga sai taga namiji ne mai suna Usman, samun kanta tayi da danna masa Confirm itama, hannunta ne ya kuskure ta tura masa hey, da yake da ka danna Confirm ɗin hey da ɗan emos zasu fito.
Dafe kanta tayi da sauri ta shiga wajan chatting ɗin hannunta na rawa ta kai domin gogewa, sai dai kashh tana gogewar taga an turo mata da amsa na Hi.
Huci mai zafi ta firzar kawai ta fita daga facebook ɗin bata maida amsa ba.
Washe gari bayan ta gama duk ayyukan gidan da daddare kamar yadda suka saba kowacce da wayarta, ita Hali tafi yin waya itama ba wani daɗewa take yi tana wayar ba.
Ummi tafi shiga facebook dama, tunda Whatsapp ɗin nata bata chatting da kowa, duk numbers ɗin dake cikin wayar tata bata fi ta mutum uku ba, daga ta Hali sai ta Tasiu, itama ta tasi'un ta gogeta, yanzu kuma saita halin kawai a ciki sai kuma ta Umma, wacce da wuya ma suyi waya da Ummar, idan ba fita Ummar tayi ba, tana so ayi mata wani abu a gidan kamin ta dawo, shine zata kira Ummin ta bada Umarnin hakan, daga haka kuma zata yanke kiran, dan ko gaisawa ma Ummar bata bari suyi, abunda za'ai mata kawai zata faɗa ta kashe wayarta.
Yanzu ma Ummi sake gani tayi Usman ya sake aiko mata da saƙo.
Shiga tayi, sai taga ashe status ne data ɗora a facebook ɗin na Kuku Mazuru wacce take bada dariya, ɗazo da safe ta ɗora shi, domin tana son Kukun nan tana yawan sata nishaɗi idan tana cikin ƙunci.
Gani tayi ya ce
"Ai ko kunyi kama da ita"
Dariya ta saki kawai ta turo masa da murmurshi.
Sake aiko mata da message yayi na cewa
"Ummi".
Da yake ko a facebook ɗin da Ummi kawai tasa a shafin nata na facebook.
Amsa masa tayi da
"Na'am ykk?"
"Alhmdllhi"
"Masha Allah"
Kawai tace masa ya sake cewa.
"You from?"
Ummi ta saki murmurshi kaɗan ta sami kanta da maida masa reply da cewa.
"Rimaye Kankia local government Katsina State Nigeria"
Murmurshi ya saki haɗe da tabbayarta photonta, samun kanta tayi da tura masan.
"Ah Masha Allah. A Kankia ɗin kike kenan?"
Yayi reply ɗin da photon data tura masa da cewa.
"Kinyi kyaw, thanks".
Shima a kansan saƙon ya turo da photonsa. Kyawawan gaske ne son kowa ƙin wadda ya rasa, domin har yama fi Tasiun data rabu dashi kyau, nesa bama kusa ba.
Wani irin murmurshi Ummi ta saki, lokaci ɗaya taji ta sake dashi sosai.
Ta maida masa reply.
"A'a a Ƙauyen dai Rimaye".
Sai reply na photonsa daya tura mata da cewa.
"Masha Allah".
Ta sake aika masa da reply na sakonsa da ya ce tayi kyau.
"Thanks dear".
Shima reply ya maido mata inda ta ce a Rimaye take, da cewa.
"Ohh Ayya. Thanks"
Ya sake mata reply inda ta ce thanks dear.
"Awwwn" da ɗan alamar kiss.
Ya sake cewa.
"Kina zuwa Katsina amma ko?"
Ta aika masa da reply
"Eh amma ba sosai ba"
Ya ce.
"Ohh Allah sarki
I used to live in kano too ina aiki anan".
Ummi ta ɗan saki murmurshi kaɗan ta maida da amsa.
"Ohhh Allah sarki, ashe Kano kake aiki?"
"Yes Ummi"
"Allah ya taimaka tohm"
Ummin ta maida masa da amsa.
"Ni ki bani number ki to Please?"
Samun kanta tayi ta tura masa number ɗin, shima nan take ya tura mata tashi number.
Ya sake aiko mata da message
"Allah ko kunyi kama da Kuku. Send me morw More pictures".
" uhum uhum Allah bazan yarda ba dear, saina haifa maka irinta kuwa"
Ummi ta samu kanta da maida masa da reply da hakan.
Ta sake tura masa reply.
"Kana WhatsApp da number saina tura maka ta can"
Ya aiko mata da reply ɗin data ce saita haifa masa irin Kuku da cewa.
"Hahahahahahaha maza maza bismillah"
Sai ya sake reply ɗin data ce masa, yana WhastApp zata tura masa photon ta can
"Okay I’ve sent my no already"
Ummi ta yi masa reply.
"Uhum uhum shine ka sake min dariya ko?, da gaske sai na haifa maka irinta"
Yayi reply da
"Auxubillahi kika haifi mage ai munshiga uku ai"
Murmurshi kawai Ummi keyi ta shiga WhastApp ba tunanin komai ta tura masa ƴan photos idanta da wasu bane, ta dawo facebook ɗin ta ce masa.
"Kaje WhatsApp na tura Maka"
Yayi reply
"Nagode I’ve seen it"
Ummi tayi reply da inda ya ce idan ta haifa masa mage an shiga uku da cewa.
"Wasa nake yi, Baby zan haifa ma mai kyau, mai kama da kai"
Reply yayi da.
"Mai kama dani? ba zatayi kyaw ba kuwa anshiga uku,
tabiyo mamanta daii"
Reply Ummi.
"Kai Y Salam baka son ta biyo ka. Karfa shiga uku ta kama bakinka fa, ba kyau faɗa".
Ummi ta ɗan waiga inda Hali take ganin har tayi bacci, yasa Ummi dafe kanta tana tunanin miye ya shiga kanta bata san mutum ba haka kawai ta sake dashi.
A tunanin kawai ta kawo ai Allah ne yayi mata canji da Tasiu, Allah ne ya kawo mata wani.
Reply ɗinsa ta gani.
"eh gaskia tabiyo ki nake so ai zatayi kyaw"
Reply Ummi.
"Haka kafi so?"
Reply Usman "Yes Please".
Reply Ummi. "Ni Kai nake so tabiyo, kai ɗin ma ai kana da kyau ai ko?".
Reply Usman. "Touuu shikenan za'a haifi iri na. Next one sai ayi irinki"
Reply Ummi. "Hhhh Allah Hayatyyy farin ciki kake kawai yau ko"
Ta samu kanta da ƙaƙuba masa suna Hayatyyy, ta rasa miya shiga kanta.
Reply Usman. "hmm angodema Allah dai always, sai kuma ta dalilin haɗuwa da ke, please Ummi zaki aure ni?, tunda naga photonki naji kin kwanta min, Please Ummi ki soni".
Wani irin daɗi ne ya rufe Ummi, ko bata faɗa ma tasan itama ta faɗa soyayya lokaci ɗaya, soyayyar Usman saita mantar da ita wani Tasiu, zuciyarta mai rauni ce da saurin kamuwa da son wani, da kuma wuyar mance wani, amma fa idan ta tsani mutum ta manta dashi har abada bata waiwayarsa, tunda tun lokacin data kira Tasiu ta fara jin haushin kanta, ta fara dagewa da addu'a har taji kwata-kwata Tasiun ya fice mata a rai, sai ga Usman kwatsam shima ya shigo rayuwarta, amma fa tana ɗari-ɗari karta taje ta faɗa sonshi da yawa shima wani abun ya zo ya lalata komai.
Sauka kawai tayi daga facebook ɗin ta kashe wayarta ta juya ta kwanta, tana jin wani irin farin ciki haka kawai ya rufe mata zuciya......