Free chapter · Read without an account

4

by Aminatu Ibrahim · NUUDARR

NUUDARR 🥀🥀

(A 2025 NOVEL)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

AREWABOOKS@AMINATU IBRAHIM

WATTPAD @UMMU-AMIR

AMEENA IBRAHEEM

(OUM AMEER)

Assalam Alaykum mutanen arziki mutanen kirki mutanena na jahar Zamfara da ma kewaye ina yi muku fatan alheri, Suna na REEDERT SKIN CARE wadda ke zaune a cikin jahar Zamfara Gusau Nigeria.... Ina mai farin cikin tallata muku kayana cikin aminci da kyakkyawar zuciya.......

Shin en uwa Kun dade kuna neman mayukan da zasu gyara muku jiki Baku samu ba???? 😳ina masu fama da sun burn?? ,knuckles?? ,glass?? ,Rashes?? ,spots?? Da sauran su? 😳ina masu qorafin suna shafa mayuka baya karbarsu,???😎ina wadda tayi bleaching ya bata mata fata tanaso fatarta takoma daidai ???🧚🏻‍♀️🧚🏻‍♀️shin kunada labarin REEDERT ORGANIC SKINCARE,dake jahar zamfara kuwa?? to idan baki taba amfani da products dintaba dan Allah ki jaraba kiga ikon Allah cikin qanqanin lokaci fatarki zatayi kyau ta murje tadinga sheqi kamar autar larabawa 👌❤️❤️ munada kaya kamar haka ➡️➡️

Amarya set

Mai jego set

Knuckles and dark spots removal set

Whitening and glow set

Lightening and glow set Etc........

Haka zalika munada supplements masu kyau da qayatarwa kamar haka ➡️➡️➡️

Weight gain supplements

Weight loss supplements

Anti-aging supplements

Whitening supplements

Breast enhancement and enlargement

Hips enlargement.

Reedert Organic skincare tana nan zaune a Gusau Motorgage Area behind masaqa

***,***

Delivery nationwide 🌍🌍🌍

Muna aikawa a duk inda kike cikin faɗin Nigeria da ma kewaye.

PAGE 4

Har na kai ƙofa Aunty Nadee ta fito ta ƙwala min kira na juyo.

Kai tsaye tace.

"Nuudaar ina zaki tafi?"

"Aunty Nadee bakin kasuwa zanje amma sai na fara xuwa gidan Mama Ruke sai mu tafi tare da Fauxa"

"Are you sure??"

Dariya nayi nace.

"Common Aunty Nadee ni fa komai ya wuce wallahi,kuɗin nan da Yah Hadiza ta turo min last week daman ban karɓo kayan ba sai yanzu zanje Fauxa ta rakani sannan akwai sauran jewelries ɗin Aunty Asiyah da ba'a ciko ba kin san kuma kuɗin yana hannuna, shine nike so muje yanxu saboda ina free ita ma haka"

Murmushi ta yi min sannan tace.

"To Allah ya tsare pls kada kiyi dare, and akwai hijabs ɗina wurin Abdullahi ki biya ki karɓo min pls, kuma munyi magana da Emraan kamar yanda kika nema kuma Alhamdulillah! Mun daidai ta shima ya amince. Hakan ma bai fi muku ba kuyi auren ko zaku samu sukuni kunnuwanku su sarara kullum kuna maƙale da waya ko kuma kullum yana hanya yana yawon zuwa kamar wani tsuntsu"

Cikin jin daɗin Kalaman ta nace.

"Thank you so much Aunty Nadeeyah,Allah ya baki farin ciki da ke da Yayah Mansur na har abada"

Ina fita muka yi ido biyu da Emraan, take naji wani irin yarr! Ga dukkan gaɓɓan jiki na....

"Nuudaar Masoyiyah"

Murmushi nayi nace.

"Welcome dear"

"You look beautiful"

Thank you kawai nace masa tare da yin shiru ina wasa da wayata da ke hannu na...

"Yah Mama da Aunty Nadee da sauran mutanen gida"

"Lafiya ƙalau suke Alhamdulillah"

Gyaɗa kansa yayi yace

"masha Allah. Sai Ina haka? Da ban zo ba da shikenan wannan wankan ya wuce ni ko?"

Ɗan murmusawa nayi nace.

"Gidan Mama Ruke zanje daga can mu wuce bakin kasuwa ni da Fauxa"

"Am I permitted to drop you there?"

Ɗan jim nayi ina nazari sannan daga baya nace.

"Sure"

Motar sa ya buɗe min na shiga sannan ya zagaya shima ya shiga.

Gidan Mama Ruke a Igala queters yake yayin da gidanmu ke Unguwar yarima ba mu da nisan da su sosai.

Mama Ruke matar Babanmu ce ta biyu wato abokiyar zaman Mama wadda ita ce ta Haifi Yah Saif, Fauziyya da kuma Hannatu, yayin da Mama ta haifi Yah Hadiza, Yah Halifah, Aunty Nadeeyah ni da kuma Nurudden.

Tun asali Mama ita kaɗai take zaune sai bayan kuma Baba ya auro Mama Rukayyah itama sai ya ajiye ta gidan ta daban, zaman lafiya suke ita da Mama zama na mutunci ba'a taɓa jin kansu ba, Yah Hadiza sai da ta shekara biyar sannan aka haifi Yah Halifah shi kuma wata takwas ya ba Yah Saif shiyasa suka taso kamar yadda muka taso ni da Nurudden....

"Baby zan jira ki ne??"

Girgixa kai na nayi nace.

"Nop! I'm going together with Fauxa..."

"Duk da haka zan jira sai na ajiye ku"

"No thank you, karka damu pls ba sai ka jira ba"

"Wai miyasa kike ta wannan saurin haka? Ko akwai wani abun ne?"

Daidaita nutsuwata nayi ina murmushi nace.

"Ba fa komai,kawai dai sauri nike kada rana tayi mana"

"Pls can you wait for some minute?"

Gyaɗa kaina kawai nayi amma can ƙasan raina tsoro nikeji kada Yah Saif yaxo ya taradda ni a motar nan, daman ya hanamu firar mota sai da mu shiga harabar gida. Jin hankali na bai kwanta ba yasa nace.

"To idan kana da wata maganar da kake so muyi mu shiga daga ciki mana.."

Ƙara narkar da Muryar sa yayi ta yadda sai da ko ina na jikina ya amsa sannan yace.

"I have nothing serious Nuudaa I'm just missing you, ni banƙi mu dawwama a nan ba... Your eyes, your lips and everything about you is burning me when ever I set my eyes on you..."

"Hmm! To kwana nawa ne ya rage baki ɗaya...."

Lumshe idanuwansa yayi tare da jan numfashi sannan yace.

"Haka ne kuma, ni sai yanxu ma na ƙara ganin hikimar barin auren nan watan ni biyu zuwa uku masu zuwa, already daman gidan mu ya zama Ready abu ƙalilan ne ya rage kuma in sha Allah cikin week ɗin nan za'a ƙara sa komai, idan an ƙara sa zan zo na kaiki sai ki gani"

"Allah ya kaimu na rai, Allah ya taimaka"

Daga haka na ɓalle murfin motar na fita hankali na duk a tashe ina yi masa bye bye.

Ina shiga, na taradda Fauxa har ta gama shiryawa, faɗuwa nayi kan cushion tare da kallon Mama Ruke nace.

"Ina wuni Mama"

"Lafiya ƙalau Nuudaa ya Hajiya da su Nadeeyah ?"

"Duk suna nan lafiya ƙalau Alhamdulillah...."

Wai gawa nayi na Kalli Fauxa nace.

"Fauxa Baba yana nan kuwa?"

"Yana nan In dai ba yanxu ya fita ba"

Miƙewa nayi nace.

"Bari na gaishe sa to"

Parloun sa na tarar da shi yayi shirin fita yana duba wasu files da ke gaban sa. Zaunawa nayi a ƙasa gefen ƙafar sa nace.

"Baba ina wuni"

Kallon sa ya mayar kai na yana murmushi ya ce.

"Nuudaa er sababi! Kin wuni lafiya"

"Hmm! Lafiya ƙalau Baba haka dai kace"

"haka ne mana. Idan kika ga hau bori kamar wata yarinya ƙarama Nuudaa, ki daina haka, ya kamata ace yanxu kisan kin girma wani abin ba sai an tsaya ana faɗa miki miye ya kama ce ki ba. Nurudden yaxo ya sanar dani cewa wai kin shirya ki gudu a daren jiya...."

Dum'dum naji ƙirjina ya buga lokaci ɗaya, a raina ina mamakin Nurudden...

" Mamaki kike ko? Nurudden ba zai yarda yana kallo ki cutar da kanki ki cutar da mu ba, wallahi ki kiyayi duniya idan baki yi hankali ba zata yi miki bugun bagaruwar jima, tashi ki tafi ki bani wuri shashashar banxa kawai"

Hawayena na share a hankali nace.

"Kayi haƙuri Baba in sha Allah ba zan sake ba"

Sumui Sumui na miƙe tamkar an sanya kaza a ruwan zafi na wuce ko zama banyi ba na ɗauki Jakata na cewa Fauxa mu tafi kawai, ko Galar da Fauxa tamin ban koma kanta ba tsabar yadda naji kunya ta kama ni, ban taɓa tunanin Nurudden zai iya faɗawa Baba wannan maganar ba. Cikin Muryar sa marar hayaniya yayi faɗa wanda sam banji dadin hakan ba.

Muna napep Fauxa tace.

"Nuudaar Aayaan ya dame ni yana so ya turo magabatansa what did you suggest?"

"While! Ai ni tun tuni nayi miki comment a kansa Fauxa, he's good and well educated, and Yah Saif knows him Kamar yanda Yah Halifah ya gaya mana, saboda haka ni dai matuƙar kin amince da shi to nima na amince, iyaka na ɗauke ki na kai mai ke Bunguɗu..."

"Wai Bunguɗu!.."

Kallon ta nayi nace.

"To miye nufin ki? Kowa nasa fa yana bunguɗu."

"To sai akace miki zaunawa zanyi kai na yayi murfi? wallahi sai dai muka daddaƙe da shi ya tabbatar min da cewa a nan zai ajiye ni sannan na yarda"

Gyaɗa kaina nayi nace.

" I'm just kidding! Nima ba zan goyi bayan ya ajiye ki a can ba nan ɗin yafi, Allah ya sa shine mafi alkaiiri a cikin rayuwar ki"

"Amin sis, na gode sosai"

Dariya nayi nace.

"Fauxa yaran mu fa kamar turawa haka zasu fito"

Kallon rashin ban gane zancen ba tamin sannan tace.

"Me I dnt understand that one, miye yaran turawa kuma?"

"kin rainawa kanki wayau Fauxa ba ni ba, Aayaan ɗin ba fari bane?"

Share zancen tayi tace.

"Emraan ya turomin 20k wai mu hau abin hawa yasan ba zaki karɓa ba"

Dariya nayi nace.

"Shine daɗin mutum biyun ai, yanzu kinga kin ƙwato min haƙƙi na kema idan kika ƙi karɓa sai Aayaan ya turo min da kuɗin in dai shi ba marowa baci bane"

"To wa ya sani, sai mun ƙwanƙwasa munji, ko da yake yanxu ma a bikin nan naku zan gane yana saki ko baya sakin hannu.."

Dariya nayi nace.

"Sosai kuwa, Yanxu idan mungama mu biya Motorgage na sayi cream wurin Reedert nawa ya ƙare daga can mu wuce Teemah fresh mu sayi snacks mu wuce gida"

"Ai bari Nuudaa, kayan Reedert sunyi a rayuwa wallahi cikin sati ɗaya sai jikin ki ya canza babu alamun bleaching ba komai luwui fatarki zata goge kiyi ta glowing mai kyau kamar balarabiya"

Daga haka mukaci gaba da firar mu har muka isa kasuwar, bayan mun kambala kusan ƙarfe biyar na yamma muka wuce na karɓi cream ɗin daga can muka biya Teemah fresh muka yi gida.

********

Asiyah

Wasa wasa sai da ta share kusan sati ɗaya bata sake sanya Halifah a idon ta ba, kuma duk ta kirashi baya picking sai sanda ya ga dama wanda a zahirin gaskiya hakan ba ƙaramin sosa mata rai yake ba, kuma gashi ta kashe hanya a wurin Umma, saboda haka babu wanda ya dace ta faɗawa wannan Maganar idan ba Aunty Zainab ba.

Bayan ta gama shawara da zuciyar ta ne ta shirya ta fito tacewa Umma tayi gidan Aunty Zainab.

Tana shiga ta zauna ta fara hawaye tana faɗa mata duk abinda ya faru tun faɗan su na ranar har yau ba su shirya ba,bayan ta gama kora mata bayani Aunty Zainab taja numfashi tace.

"Asiyah yanxu ina so ki faɗamin ina amfanin hakan da kikayi? Tun ba ki shiga ba miji ya fara yin fushi da ke yana banza da lamarin ki tun ba kuyi auren ba, kuma duk wannan zubar da kan wallahi kece kika janyo shi, manzan da ke rawar ƙafa kamar suyi tsalle su taɓo sama suke ji amma ke kin fara zubar da ƙimarki tun a waje, wallahi idan ba ki zama mai kawar da kai daga sha'anin en uwansa ba har abada ba zaku shirya ba, kuma idan baki zama mai haƙuri da juriya ba ko an kaiki ba zaki jima ba zaki fito domin tun yanxu kin fara ganin sign na wane kalar miji ne kika aura, wannan yana daga cikin maxan da baya ɗaukar rai ni kin fara ganin alamunsa, saboda haka in dai kina son Halifah to dole ki buɗe baki Kisha maganin zama da shi komai ɗacinsa idan kuma kinji bakya so ki aure sa to kiyi magana a gayawa Alhaji sai a san yadda za'a yi magana da magabatansa a fasa kowa ya huta... "

Turo bakin ta tayi tana gunguni tace.

" Nifa Aunty Zainab bance bana son sa ba, kawai dai shine yake min abinda bana so"

Wayar ta ta ɗauko ta kira Halifah a gabanta tace yaxo gidan ta tana neman sa.

Tana gidan kusan hour ɗaya Sai gashi ƴa shigo, suna yin ido biyu ya ƙara tamke fuska ya samu wuri ya zauna.

Bayan sun gaisa da Aunty Zainab ɗin ta kalle sa tace.

"Halifah miye ya ke faruwa ne tsakanin ka da Asiyah??"

Kai tsaye ba tare da ya tsaya yi mata corner corner ba yace.

"Da farko dai Aunty da ace ba ke bace kika kirani wallahi da ba zan zo ba, sannan tsakani da Allah ni naso haƙura da Asiyah kawai domin bata ganin mutunci na ko kaɗan, bata kuma godewa da irin samun da nikeyi wanda hakan yana nuna min cewa ko da munyi aure duk abinda nayi mata ba godewa zata riƙa yi ba sai dai ta zauna tana ganin laifi na,........

OUM AMEER

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.