Free chapter · Read without an account
EPISODE 8
*RAUNIN ZUCIYA*
*©Zahra Royal Star*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*
EPISODE 8
*Kauyen Tudun Wulli, Kankia local government Katsina State Nigeria*
"An faɗa, ko gani kike bazan iya tuɓewa mu dakun bane?".
Innar su Asabe zatai magana Habiba ta miƙe cike da ƙarfin hali ta ce.
"Dan girman Allah Innar su Asabe kiyi hakuri ki tafi dan Allah".
Innar su Asabe ganin yadda Habiba ke kuka tana roƙonta yasata cizon yatsa cike da tausayinta ta juya ta fice daga gidan.
Tana fita kamar jira Inna take ta wani ci kwalar hijab ɗin Habiba tana kallonta, ta shiƙe mata wuya da hijab ɗin dake jikinta.
Wani irin tari Habiba ta farayi domin shaƙar taji ta har lumfashinta na shirin daukewa, tsabar yadda ta shaƙeta sosai.
"Wato zuwa kike ko ina kina baza ni cewa ga abunda nake miki wato?, to bari na rinƙa miki mai dalili uban kowa yazo dai-dai nake dashi wallahi, ke nifa bari kiji ko uwar data haifeki ce ta dawo ba abunda ta isa tayi min, kamar yadda nake miki a yanzu to haka zan miki koda a gaban idonta ne, ubanda yasa ta aure min miji shi zai sa na ci gaba da cin ubanki, ai ko yanzu nasan duk da bata duniyar tayi nadamar shigowa gidan Lube a matsayin kishiya ta, wallahi harta haihu ta bar min roƙon mugun iri, ai ni wallahi Allah ni Mlm ya cuta".
Inna ta ƙare maganar kamar zatai kuka, sai zuwa can Habiba batai aune ba taji saukar lafiyayyan mari har biyu a duka kumatunta biyun.
Wata irin zabura tayi tana dafe kumatun nata jikinta har rawa yake, saboda Inna zafin hannu ne da ita dama, idan ta bige mutum yadda kasan ya sume haka yake ji.
Cike da tsanar da tayi mata ta kalli Bilki ta ce.
"Ke Bilki ɗakko min dorinar nan tana ɗaki, yau sai kin gaya ma ƴan garinku wallahi".
Kuka Habiba ta ƙara saki tana faɗin.
"Dan Allah Inna kiyi hakuri, wallahi Allah ba gidansu naje ba, gani na tayi kan hanya shine taga yadda banda lafiya shine ta shiga gida zata ɗakko min magani, ni kuma na wuto gida, shine ta shigo har cikin gidan nan".
"Dalla can rufe min baki makira, ke wannan ƴar halittar har kin iya shirya ƙarya har haka ko?, duk abunda kike a tafin hannuna fa kike Habiba, ni har kin isa kimin wayo yarinya, ko uwar data haifeki ai na rigata zuwa duniya, bare ke ƴar baya-bayan haihuwa".
Bilki ta fito itama sai wani zafga mata harara take ta miƙa ma Innar dorinar tana faɗin.
"Inna na rantse da Allah ƙarya take abunda take faɗa miki, baga hannun nata nan ba da magani an saka, ke ma yanzu kin iya shirya ƙarya da munafurci?".
Amsar dorinar Inna tayi ta ɗaga ta iya ƙarfinta tana sauke mata ita a gadon bayanta.
Wata irin gantsarewa Habiba tayi tana jin yadda bugan dorinar yayi mata shigar bazata, wani irin mugun-mugun zafi ne ya dirarma ƙwaƙwalwar kanta, kuka ne ta saki marar sauti tsabar yadda taji zafin bugun dorinar.
Inna ta ƙara rufeta da bugu tana sakinta iya ƙarfinta take sauke ma Habiba dorinar nan, Habiba tun tana daurewa har ta kai da ta kwanta ƙasa tana birgima tana kuka da ihun azo a taimake ta. Sai da Inna taga ta fara fitar mata da jini tukunna ta barta haka nan.
Habiba ta miƙe zaune tana soshe-soshe tana jin kamar har lokacin Inna kawo mata duka take, kuka take amma tsabar yadda hawayen nata suka gaji da zuba babu ma ruwan hawayen, sai sautin kuka da take idonta ya kaɗa yayi jawur.
Inna ta zauna tana sauke lumfashi tsabar yadda ta dake ta itama ta gaji tana wani huce tana dubanta ta ce.
"Ai idan har bazaki daina munafurci ba, ni kuma bazan daina ɗaukar mataki akanki ba, shege ka fasa Habiba tsakani na dake, kinfi kowa sanin wacece ni ai, amma haka kike danne sanin nawa kije ki aikata abu son ranki, to Bismillah ga fili gamai doki".
Ita dai Habiba zafin da jikinta ke mata ma kaɗai ya isheta kukan zuci kawai take tana wata irin shashshaka ta tsabar kukan data daɗe tana yi.
Wani yaro ne ya shigo gidan da sallama yana cewa.
"Wai ance Habiba tazo inji wani saurayi yana waje".
Inna da Bilki tsabar mamaki sun kasa magana,
"to wane marar rabo ɗin ne zai zo kiran wannan bar"
Inna ta ƙare maganar tana duban yaron.
Yaron bai sake magana ba shi dai yana tsaye.
Bilki ta ce.
"Jeka kace gata nan zuwa".
Yaron ya juya ya fice.
Bilki ta kalli Inna ta jawo hijab ɗinta dake akan igiya dake tsakar gidan, ta zura takalminta tana faɗin.
"Inna bari naje naga waye yazo kiran wannan munafukar".
"Yawwa jike ki gano mana waye".
Tana fita Inna ta dawo da dubanta inda Habiba take, ita tunda yaron ma ya shigo wai ya ce wani na son ganinta, abun ya bata mamaki amma saita share tana sake curewa waje ɗaya, tunda tasan ko giyar wake Innar tasha bazata taɓa barinta ta fita kai tsaye ba.
"Kika wani cure waje ɗaya kega munafuka ko?, wato ƙila ma kin san waye kin san da zuwan sa?".
Girgiza kai da sauri Habiba tayi bata ce ƙala ba.
Wani dogon tsaki Innar ta ja tana kallon ƙofar gidan, ganin Bilki ta shigo tana cire Hijab ɗinta tana faɗin.
"Wato Inna wadda yazo neman Habiba shine ya dace da ita wallahi, ai kawai Inna ki yarda ya aureta kowa ma ya huta da ganinta, ta tafi can gidansa".
Cike da mamakin maganar Bilki Innar ke kallonta da mamaki a muryarta ta ce.
"To wai waye ne haka da kiketa nanata na barta ta fita?".
"Yo Inna waye kuwa idan banda Abban Dije mai markaɗe".
Lokacin da Bilki ta furta sunan Abban Dije mai markaɗe, Habiba bata san lokacin data waro idonta waje ba, ƙirjinta na bugawa da ƙarfi.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, waye bai da labarin Abba, ɗan iska ne naƙin ƙari, yayi zaman Lagos, yayi iskanci da karuwai na Lagos, hatta photonsa ansha nuna masu yana zaune akan cinyar mace suna iskancinsu a can Lagos, ya dawo nan garin, babu gidan da baya haurawa idan ya samu rata, yaje yayi sata, hatta dabbobi sata yake, ansha kama Abba a kaishi Ofishin Ƴan Sadda, kai har gidan gyaran hali ansha kai Abba, ga shaye-shaye kala-kala babu kayan mayen da Abba bai sani ba, shan taba kuwa kusan kullum yana tare da ita, ko tafiya yake zaka samesa yana zuƙar Taba.
Tana tunanin halayan Abba da rayuwarsa, tana yi tana girgiza kai hawaye masu zafi ne suka shiga zubo mata a yanzu.
Inna ta wani washe baki tana kallon Bilki ta ce.
"Kai amma duk wadda yaba Abba shawarar zuwa neman auren ƴar banzar yarinyar nan wallahi ni ai ya gama biya na duniya wa lahira".
Inna ta faɗa tana sake dawo da dubanta inda Habiba ke zaune tana hawayen tashin hankali.
Inna tana kallonta ta wani murtuke fuska ta ce.
"To munafuka zaki tashi kije ko kuwa?, baki ji tun ɗazo sallama ake dake bane hamshaƙiya?".
Miƙewa da kyar Habiba tayi tana kallon Inna ta ce.
"Inna ki duba girman Allah ki tausayi min, kimin koma miye amma banda auran mutum kamar Abba, dan......
Da mugun sauri Inna ta ɗaga mata hannu, bakinta har yana kunfar masifa Inna ta ce.
"Ke har kinyi tsaurin ido da zaki kalli tsakiyar ido na kina gaya min haka?, zaki fice kije wajansa ku dai-daita kanku ko kuwa sai na matso inda kike yanzu na idasa sumar dake a wajan nan?, kaga ƴar iskar yarinya, tsintacciyar mage wacce bata mage".
Kuka mai ƙarfi Habiba ta saki tana saka hannunta tana share hawayen dake zubar mata ta nufi waje har bata ganin gabanta tsabar tashin hankali.
Tana fita Inna ta sake cewa.
"Shegiya munafuka ai ko mutuwa zakiyi gaki can kin auri Abba wallahi, ai dama idan ina lumashi keda hutu a nan dai gidan duniya har abada Habiba, yadda Uwarki harta mutu da baƙin cikina kema haka zaki koma a wulaƙanci".
Habiba na fita ta iske shi zaune akan dakalin ƙofar gidan nasu, wani irin abu ta haɗe a maƙoshinta, tana kallon yadda yazo mata sanye da wasu irin ƴan iskan kaya, daga shi sai gajeran wando wadda shima daga wajan cinyoyin duk an wani yayyagashi, ga wata ƴar iskar riga wacce tayi masa yawa, sai wata uwar Sarƙa daya saka a wuyansa, ga wani kwalli daya bauro a cikin idonsa, kai daka kalli Abba zam ɗan iska ne, duk ya cike wasu sharuɗo irin na zama tataccen ɗan iska na haƙiƙa ma kuwa.
Cike da tsantsar takaici Habiba take kallonsa.
Ganinta ta fito ya wani miƙe yana takowa inda take, yana tafe yanzun ma yana zuƙar taba.
Sai da yazo gaf da ita kamar zai shige mata jiki yaja ya tsaya yana wani fesa mata hayaƙin Tabar da yake sha.
Wani tari ne ya sarƙe Habiba da sauri tayi baya sosai dashi, tana rufe kofar hancinta tana dubansa cike da wata irin tsanarsa data ji lokaci ɗaya ta rufeta tana kallonsa ta ce.
"Wallahi Abba ko mutuwa zanyi bazan taɓa bari na auri mutum irinka ba, gara ce na mutu dana bari a lalata min rayuwa da auran irinka, ai wallahi da haihuwar irinka gara ace mahaifiyarka ɓarin cikinka tayi baka zo duniya ba, da baka zo ka addabi bayan Allah ba k......... Maganar ta ce ta maƙale jin wani kyakkyawan mari da Abban ya kwasheta dashi.
Da wani irin sauri ta ɗago tana kallonsa cike da zallar mamakin marin daya ɗauketa dashi.
Idonsa jawur irin na ƴan shaye-shaye yana kallonta cike da ɓacin rai ya ce.
"Ke ƴar gidan matsiyata ni zaki kalla babu shakka ko tsoro kice min da haihuwata gara ɓari na?, to na rantse da rabbil samawati Habiba kin jama kanki, ke ko ana bura uba sai kin auri Abba, naga ubanda ya tsaya miki a garin Tudun Wulli, ke bari kiji ko mutuwa kike ba za'a ɗauke gawar taki ba sai da aure na akanki, muga abunda zakiyi, kin san waye Abba kuwa?, ku kuwa labarinsa kawai kike ji?".
Habiba na dafe da ƙuncinta hawaye masu zafin gaske na zubo mata tana kallon tsakiyar idonsa babu tsoro ko shakkarsa ta sake cewa.
"Babu ruwa na da sanin kai ɗin waye, da an kalleka ba'a buƙatar ƙarin bayani ai akanka ai, mutum ko waye shi daya ganka zai shaida kaiɗin riƙaƙƙen ɗan iska ne, ai ba'a buƙatar ƙarin bayani".
Abba cike da mamaki yake kallon Habibar yadda take faɗa masa magana kanta tsaye, abunda wani ko wata bai taɓa masa hakan ba, hasalima duk yawancin ƴan cikin garin shakkarsa suke.
Wata irin muguwar dariya ce ta rufe Abba ya shiga yinta.
Zuwa can ya tsayar da dariyar tasa yana nuna Habiba da yatsa yana cewa.
"Na daɗe ya ina neman mace irinki ai, marar tsoro dama irinki ce kaɗai ta dace da Matar Abba, ni wannan abun da kike min shike ƙara samin son auranki, dole ma ne saina aure ki Habiba hhhhhhh"
Ya ƙare maganar haɗe da sakin wata dariyar.
Habiba ko bata san ma ya akai ta tsinci kanta da rashin tsoron nasa ba, har take masa rashin kunya da faɗa masa maganganu masu zafi haka ba.
"Har Abada Abba ko zan rasa rayuwata bazan taɓa bari ka zama miji na ba, na faɗa maka na sake faɗa maka".
Habiba ta faɗa cike da ƙara jaddada masa hakan.
Juyawa yayi ya tafi yana dariya yana wani ɗaga mata hannu yana sake faɗin.
"Sai gani na biyu masoyiya, nan ba daɗewa ba zan kawo kudin auranki kuma dole sai an bani ke, ban taɓa neman abu na rasa ba kisan wannan".
Ya ƙare maganar haɗe da barin wajan kwata-kwata.
Habiba na kallonsa harya ɓace ma ganinta.
Duƙewa tayi a wajan tana sakin wani irin kukan tausayin kanta.
Ta ina zata fara ne?, waye zata je ta gaya ma abunda Innar ke sun mata na idasa tarwatsa rayuwarta, idan ta aura mata Abba ai shikenan rayuwarta ta gama aiki, ke koda auran yanzu aka daura shi aka kuma kwance sa, ai dai ta shiga tarihin ta taɓa auran mutum kamar Abba, bata so ko kaɗan hakan ta kasance da ita.
Mi yasa Inna ta tsane ta har haka ne?, miye Mahaifiyata tayi mata har ya kasance abun ya shafeta?, mi yayi zafi shiba wuta ba?, yaya take so tayi da rayuwarta ne?, mi yasa sadda manema wadda zata iya auransu lokacin da suka sha zuwa neman auranta Innar ke hanawa?, sai yanzu kawai dan taga wadda zai tarwatsa rayuwarta shine ta amince ba wani gargada ko tashin hankali, wa'incan saboda taga zata huta da azabar da take mata, zata je inda za'a tallafe ta a lallasheta, a rungumeta a bata kulawa a share mata hawaye, shine tayi duk yadda zatai ta hana abun faruwa, duk da ba masu hali bane, sai dai dai-dai gwargwado suna da rufin asirinsu, kuma mutanen kirki ne, saboda sun kasance haka shine yasa ta hanata auran irinsu, sai mutum ɗan iska kamar Abba ne zata ce ta aura?.
Su Inna dake cikin gida ganin Habiba shiru bata dawo ba har lokaci ya ɗan fara ja yasa Inna miƙewa tana cewa.
"Ke bari naje wajan can naga miye ke faruwa?, kar dai taje nuna masa rashin tarbiyyar tata ne?, ta faɗa masa maganganun da zai gudu".
Murmurshi Bilki ta saki tana kallon Inna ta ce.
"Ai wallahi Inna tayi kaɗan ta kalli tsakiyar idon Abba ta ce zata masa rashin kunya, iyaka ci bazai ji kunyar yi mata dukan kawo wuƙa ba wallahi, shi ai Inna baya ɗaukar raini, yo ko Maza ma tsoron haɗa ido suke dashi ko akan hanya ne da an gansa ya taho darewa ake a basa waje ya wuce, idan ba haka ba kuma jikin mutum ya gaya masa, ita harta isa?, ai Inna bata isa ba wallahi, dama dawowa kikai, kikai zamanki wallahi".
Inna ta nufi kofar gidan tana cewa.
"A'a dai barni naje na gani".
Ta ƙare maganar tana ficewa gidan.
Inna na fitowa idonta ya gane mata Habiba duƙe a ƙasa tana gunjin kuka. Inna ta shiga dube-duben ƙofar gidan, ganin babu Abban a tsaye a wajan yasa Inna saka hannunta ta damƙo Hijab ɗin Habiba ta tayar da ita tsaye tana kallonta ta ce.
"Munafuka kukan ubanmi kike kuma?. Ina shi Abban?, ko kuma kinyi masa baƙin halin naki ya tafi?".
Jan lumfashi Habiba tayi ta girgiza ma Inna kai ta ce.
"Ni ban masa komai ba kawai tafiyarsa yayi".
Wani banza kallo Inna ta jefa mata tana cewa.
"Idan ma ƙarya kika faɗa ai Abban zai dawo dai ko?, ke baki isa ki gaya ma Abba abunda zaiji ya tsani auranki ba, tunda Abba ya zo neman auranki to babu abunda zai dakatar dashi, ki ma sani tun yanzu a'ato, kuma ni nan da kike gani babu abunda zai hanani bashi ke aure yawwa gara ma ki sani".
Innar ta ƙare maganar tana sakar mata Hijab data riƙe mata.
Idon Habiba na zubar da hawaye ta kalli Inna ta duƙa ƙasa tana haɗe hanyanta waje ɗaya alamar roƙo ta ce.
"Inna dan girman Allah Inna kimin rai, ki tausaya min karki aura min Abba, wallahi Allah mutuwa zanyi idan aka ce yau an ɗaura aure na dashi".
Wani mugun kallo Inna tayima Habiba tana kallonta a duƙen, ta nunata da yatsa ta ce.
"To bari kiji ko bindiga zakiyi auranki da Abba ba fashi wallahi, ke bari ma kiji tunda kika ce haka to kuwa ko mutuwar kikai ba'a fita da gawarki sai an ɗaura auranki da Abba, sai kin tafi lahira da auransa akanki, sai naga ta tsiya ko?".
Inna na ƙare maganar ta juya tana sakin wani dogon tsaki tana koma cikin gidan.
Inna na shiga Bilki ta ce.
"Inna naga kin jima a wajen kema?".
Ƙarasowa tayi tana zama kusa da Bilkin, tana zama Habiba ta shigo gidan jikinta a sukwane.
Bilki na kallonta ta ce.
"Wai Inna miye ya faru fitarki waje?".
"Yo mifa zai faru Bilki?. Zuwa nayi na iske ta ƙasa tana kuka, ko ubanmi take ma kuka ohho mata. Zuwa tayi wai tana rokon karna bari a aura mata Abba mutuwa zatai idan aka ɗaura mata aure dashi, kinji fa?, yo ni dama tsoron karta mutu nake ji ne?, shine na sake jaddada mata cewa ai ko mutuwar tayi ba'a kai gawarta Kabari sai an ɗaura auranta da Abba, idan ya so ta tafi lahirar da auran wadda tafi tsana a duniya akanta, idan ana mutuwa sau biyu saita sake mutuwa acan ƙiyamar ai ko?, ni bata san dama haka nake so ba?".
Dariya kawai Bilki ta saki tana duban Inna ta ce.
"To ai Inna bake kaɗai bama, hatta shi Abban banga tashin hankalin da zai hana shi auranta ba, ai tunda yace sai yayi tofa sai yayin".
Habiba dake sauraron abunda suke faɗa ƙirjinta ba abunda yake sai bugawa na tsananin tashin hankali, wata irin fargaba ce ta sake rufeta, tabbas tana ji a jikinta idan har hakan ta kasance to mutuwar zatai, zuciyarta bazata iya dauka ba wallahi, kallonsu kawai take hawaye na zubar mata gabanta kuma na cigaba da faɗuwa..........