Free chapter · Read without an account

6

by Aminatu Ibrahim · NUUDARR

NUUDARR 🥀🥀

(A 2025 NOVEL)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

AREWABOOKS@AMINATU IBRAHIM

WATTPAD @UMMU-AMIR

AMEENA IBRAHEEM

(OUM AMEER)

Assalam Alaykum mutanen arziki mutanen kirki mutanena na jahar Zamfara da ma kewaye ina yi muku fatan alheri, Suna na REEDERT SKIN CARE wadda ke zaune a cikin jahar Zamfara Gusau Nigeria.... Ina mai farin cikin tallata muku kayana cikin aminci da kyakkyawar zuciya.......

Shin en uwa Kun dade kuna neman mayukan da zasu gyara muku jiki Baku samu ba???? 😳ina masu fama da sun burn?? ,knuckles?? ,glass?? ,Rashes?? ,spots?? Da sauran su? 😳ina masu qorafin suna shafa mayuka baya karbarsu,???😎ina wadda tayi bleaching ya bata mata fata tanaso fatarta takoma daidai ???🧚🏻‍♀️🧚🏻‍♀️shin kunada labarin REEDERT ORGANIC SKINCARE,dake jahar zamfara kuwa?? to idan baki taba amfani da products dintaba dan Allah ki jaraba kiga ikon Allah cikin qanqanin lokaci fatarki zatayi kyau ta murje tadinga sheqi kamar autar larabawa 👌❤️❤️ munada kaya kamar haka ➡️➡️

Amarya set

Mai jego set

Knuckles and dark spots removal set

Whitening and glow set

Lightening and glow set Etc........

Haka zalika munada supplements masu kyau da qayatarwa kamar haka ➡️➡️➡️

Weight gain supplements

Weight loss supplements

Anti-aging supplements

Whitening supplements

Breast enhancement and enlargement

Hips enlargement.

Reedert Organic skincare tana nan zaune a Gusau Motorgage Area behind masaqa

***,***

Delivery nationwide 🌍🌍🌍

Muna aikawa a duk inda kike cikin faɗin Nigeria da ma kewaye.

PAGE6

Sati biyu da kai kayan Yah Halifah aka kawo kayan Aunty Nadee daga gidan su Yaya Mansur. Duk da cewa ta na da yaro ɗaya hakan bai sa suka yi mata lefen banza ba, itama set ɗaya ne mai 5pcs. Kuma naji daɗin hakan a raina ba kaɗan ba. A rayuwar auren ta na baya sam bata ji daɗin zama a gidan Sabeer ba, lafiya ƙalau yaxo ya ne mi aurenta bayan sun kwashe tsawon shekaru biyu suna soyayya ƙarshe ya koma yi mata wulaƙanci haihuwa ɗaya yana biye biyen mata ga rashin mutunci ga kuma zagin iyayenta kamar shi ne ya haife ta, tun tana hak'uri har sai da ta kai zancen gida wurin su Mama, ga Mama ba sauƙi tuni ta buɗe mai aiki, bayan alƙawarin da ya ɗauka na cewa ya daina suka koma aka ci gaba da zama sai kuma abubuwa suka ci gaba har da duka a wannan karon, ba shiri Mama ta saka su gaba sai da ta rabe auren sannan Aunty nadeeyah ta samu sukuni bayan shekara huɗu tana shan wahala. Bayan ta dawo gida tana ci gaba da zuwa aikinta na lecturing a FCET ta haɗu da Mansur wanda shima lecturer ne a nan yana da mata ɗaya. Sai gashi an samu Allah ya daidaita tsakanin su har maganar iyaye ta shigo ciki. Jin an saka rana yasa Yah Hadiza ta ce a bata Abulkairi ya koma hannun ta don kada ma Sabeer ya zo bayan yaga tayi aure yace a bashi ɗansa tunda a farko cewa ya yi ta je har ɗan baya so ya bar mata. But a yanxu in sha Allah muna kyautatawa Yaya Mansur za to domin babban mutum ne kamili a fuska muna kuma fatan Allah yasa haka ya ke har zuciyar sa.

Bayan kwana biyu da kawo na Aunty Nadee Emraan ya kira ni ina tare da su Mama a parlor ya ce su Sumayyah za su zo su kawo kaya da yamma.

Kallon Mama na yi bayan mun gama wayar na ce.

"Mama Emraan ne ya ce wai za'a zo daga gidan su a kawo kaya"

Fuska ba yabo ba fallasa ta ce.

"Allah ya kawo su lafiya?"

Ƙara yin ƙasa da murya nayi na ce.

"Mama su Sumayyah ne ya ce da yamma za su zo?"

Sai yanxu ta ajiye atamfar da ke hannun ta tana dubawa ta kalle ni da kyau ta ce.

"Su kuma har yanxu ba su daina wannan yayin ba?.."

Aunty Nadee ce ta ce.

"Wallahi kuwa Mama. Ni ma dai yanzu tsarin nan da aka fito da shi yana burgeni, iyaka maza su sallama su ajiye kaya suyi tafiyar su ba tare da kowa yasha wahala ba. Amma komai na malam Bahaushe baya so a samu sauƙi a rayuwa an fi so ayi ta wahala"

Kai tsaye Mama ta ce.

"To ku kira Hajiya Ruke ku gaya mata ke Nadeeyah sai kije can ni dai wallahi sisina ba zan bayar ba, amma ita idan zata iya to ba zan hana ba"

Aunty Nadee ta miƙe da sauri ta ce.

"To Mama bari naje muji yadda za'a yi"

Ni dai shiru nayi tare da yin ƙasa da kaina raina yana min ba daɗi domin sam bana jin daɗin yanda Mama ke yi idan taji zancen Emraan.

Nadeeyah kuwa tana fita daman da wankanta kaya kawai ta sauya ta fice ta hau napep sai gidan Mama Ruke.

Tana shiga ta tarar da Mama Ruke na kwashe tuwo tana magana da Nurudden shi kuma yana mulmula tuwon a Leda yana sakawa a kula.

Zaunawa tayi a kujerar robar da ke jikin bango ta ce.

"Ina wuni Mama Ruke"

"Lafiya ƙalau Nadeeyah ya garin ya kuma shirye shirye?"

"Lafiya ƙalau"

Kallon ta Nurudden yayi ya ce.

"Aunty Nadee ta wa, Ina wuni"

"Murmushi ta yi ta na kallon sa ta ce.

" Lafiya ƙalau wato kayi mana tawaye tsawon sati biyu ko? Har aiken ka nayi gidan Samee baka je ba"

"Wallahi na je, cewa tayi zata tura miki ta account sannan kuma waɗannan kayan ba su iso ba ne da ta aiko miki"

Mama Ruke na dariya tace.

"Ya ce min yaji yayi wa Nuudaa faɗa suke, to baya so ma suna haɗa ido saboda kada yayi saurin saukowa"

"Hmm! Ƙyale su kawai Mama Ruke kina nan za su shirya baki da labari"

"Shiyasa ai na share sa nima, kuma a nan ɗin ma kullum sai sun yi faɗa da Hanna ke ko ɗazu kafin ta fita sai da sukayi"

"A haf! Nurudden kuma. Amm! Daman Nuudaa ce ta sanarwa Mama cewa wai su Sumayyah ƙanwar Emraan za su kawo lefe anjima da yamma, to shi ne kin san halin Mama, tace ba ruwanta kuma sisinta ba zata bayar ba amma in zo in sanar miki"

Girgiza kai Mama Ruke tayi ta na murmushi ta ce.

"Kai! Hajiya Sadiya! Har yanxu ba zata daina halin nan ba na fushi"

"Wallahi kuwa"

"Su ma dai sun taushe Hannu gaskiya, Yanxu ƙarfe ɗaya a ke magana. To miye shawara ke Nadeeyah?"

"Ni dai shawara ta a nan shi ne yamma tayi ba zamu iya ƙirƙirar ko wane aiki ba a yanxu, kawai dai muyi ordering na snacks da drinks sai mu ɗora musu 50k"

"Eh, haka ne gaskiya"

Nurudden yace.

"Kun san halin mutanen nan maƙarya ta ne na ƙarshe, harakar ƙarya ita kaɗai suka iya kuma itama hakan ta nuna masa sai suka zama ɗaya. shawara ta a nan, a bincika aji idan za'a samu naman kaji da na Rago wanda ba'a ɓalla ba a siyo a saya mata girma"

Mama Ruke ta ce.

"Kuma in don da wannan da maganar ka Nurudden, Yanxu bari na kira Saifuddeen yaxo su kawo kuɗi ko kuma a faɗa musu su siyo ke kuma ki kira Hadiza itama sai a samu wani abu wurinta a haɗa."

Kafin kace mi sun haɗa sun abinda suke buƙata har naman an bincika kuma an samo.

Ƙarfe biyar suka iso da kaya akwati goma sha biyu har da mukullin mota.

Kaya kuma sun kai kala ɗari biyu.

Ganin haka Nadeeyah ta kira Yah Hadiza suka ƙara shawara tare da Mama instead of su ba su 50k kamar yadda suka tsara dole su ka sauya zuwa 100k da sauran kayayyakin sha tara na arziki.

Ni dai ina gida Su Fauxa sai kirana suke suna ta yimin santin kayan da aka kawo wai harda mota, hmm! Lallai Emraan ƙarshe ne.

Bayan an kambala komai Aunty Nadee ta dawo gida ta shaidawa Mama duk yadda akayi a gabana. Kallo na Mama tayi ta ce.

"Ba tulin kaya ba Nuudaa ba kuma mota ba, ni dai ya riƙe min ke da mutunci da daraja duk ya fiye min wannan."

Gyaɗa kai na na yi alamar assurance na ce.

"In sha Allah Mama"

Miƙewa nayi wata irin zazzafar ƙaunar Emraan na cizon raina na wuce ɗaki na faɗa kan katifa ta ina ta murmushi na janyo waya na kira shi, shi kuma kamar jira ya ke tana shiga ya na cafkewa.

Ina murmushi na ce.

"Kamar mai jira na"

Cikin calm voice ɗin sa ya ce.

"I'm always ready and available for Nuudaar"

Lumshe idanuwana nayi ina jin wani abu mai matuƙar tasiri yana yawo a ƙirji na muryata a ƙasa na ce.

"Thank you Emraan"

Ajiyar zuciya ya sauke ya ce.

"You deserved more than that Nuudaa"

"Emraan even Mama request a favour from you cewa ba duk wannan ta ke buƙata ba kawai ka riƙe mata ni da mutunci and nima kuma kawai abinda nike so kenan, pls kada ka juya min baya a ko wane irin yana yi"

"Nuudaa I'm giving you my word as I always do, mutuwa ce ka ɗai za ta iya rabani da ke, girman ki da darajar ki sun sha gaban na ko wace irin mace a duniyata"

"Ina jin salama a raina duk lokacin da mu ke irin waɗannan maganganun amma da zaran na tuna irin lokacin da Aunty Nadee ta buga ita da Sabeer kuma ƙarshen labarin su bai yi kyau ba duk sai na ji guiwa ta ta sage, sai in ji kamar kai ma watarana haka za ka min... "

" Nuudaa pls count me out from those kind of people, I assure you I'm different kema Kuma kinga alama, ni ban san komai ba son ki kawai na sa ni"

"Ba'a yabon ɗan kuturu Emraan sai ya shekara goma da yatsa..."

"Irin wannan karin maganar is Haram Nuudaa, domin ta ke ta hurumin ubangiji, shi ya ke halitta bawan sa duk yadda ya so ko a farko ko a tsakiya ko kuma a ƙarshe"

"Astagfirullah! In sha Allah ba zan sa ke ba"

Kiran Mama da najiyo yasa na miƙe da sauri na ce masa two minute.

Ɗakin Baba ta kirani suka ƙara Jamin kunne musamman Mama wai ita hankalinta ya ɗaga sosai ganin irin waɗannan kaya kamar hauka, sai da Yah Hadiza da Baba suka kwantar mata da hankali da kuma ba ta misali da cewa ba komai ba ne wannan domin kowa ya san gidan Mashfiq Moriki irin kuɗin da ke gare su musamman wannan auren ɗan su ne na farko.

Bayan na dawo daga ɗakin Baba na tarar da Nurudden a parlourn Mama yana saka cajin wayar sa.

Hugging ɗinsa nayi Ina dariya na ce.

"I'm sorry twiny.."

Ƙara ɓata rai ya yi tare da tura ni yana faɗin.

"Dan Allah ci kani Malama kinji..."

"Haba! Nurudden babban aboki na kuma ƙanina kayi haƙuri mana..."

"Ba zan yi ba, wai har ni zaki wulakanta ko?"

"To ba kai ne ka fara ba, miye na kiran Emraan da banza??"

Tsaki yaja sannan yace.

"Ke ni fa bana ma wani ganin girman sa domin ba girma ta yayi ba, kema kuma don rashin sanin ciwon kai namiji mai shekarun ki zaki Aura, to idan baki sani ba ki sani yanxu Mama Ruke ta sanar min komai"

"To sai me? Kai ne ba ka sa ni ba amma ni na daɗe da sanin he's my age mate, Kuma ba abun kunya ba ne domin ko girmar sa na yi bai zama haramun ba ballantana ya ba ni watanni. Saboda haka ba zan yi fushi da kai ba ni dai na gama nawa kayi haƙuri idan abinda nayi bai maka daɗi ba in sha Allah ba zan sa ke ba"

Hugging ɗi na ya yi back murya a rauna ne ya ce.

" Shi kenan tunda kinyi alƙawarin ba za ki sa ke ba, ya wuce"

"To Nurudden gobe ka ɗan ajiye ni school mana.."

Waje ya nufi yana faɗin.

"Ba zan ajiye ki ɗin ba, duk kwanakin nan da ki ke tafiyar ki waye ya ke kai ki?"

*********

Aunty Zainab

Da sassafe ta ta shi ta kambala duk wasu aikace aikacenta ta shirya ta nufi gida, daman firdausi taxo tun daren jiya za su tafi Kaduna tare wurin siyo kayan Asiyah. Ɗokin ganin ƙanwar ta Firdausi ta ke amma kuma fargabar Umma duk ta cika mata zuciya, ta san yanxu da ta je gidan nan zata fara hantarar ta, abu kaɗan da zaran tayi shi za ta ce ta aikata mata kuskure. Tana jin kewar gidan a ranta shiyasa wataran haka zata daure ta je domin kawai ta ga Umma.

Da wannan tunanin ta isa gidan.

Tana shiga ta tarar da kowa yana nan, Asiyah, Ahmad, Firdausi da yaranta guda biyu Khalid da Khadijah.

Da sauri firdausi ta ta so ta rungume ta cikin farin ciki ta ce.

"Oyoyo Aunty Zainab"

Itama cikin jin daɗi ta ce.

"Sannu da zuwa Firdausi.."

"Aunty Zainab ina kwana?"

"Lafiya Lau Ahmad, kuna nan kuna ta shirye shiryen biki ko?"

"Kamar ya suna shirye shiryen buki! ke fa?"

Da sauri ta juya wurin Umma da ke wannan maganar ta ce.

"Umma ina nufin ai har da ni. Ina kwana Umma"

Fuska ba yabo ba fallasa ta ce.

"Lafiya"

"Ummah na ce baban su Hidayah ya kawo su nan idan sun dawo school ga kayan su nan naxo mu su da su kafin mu dawo..."

Yatsa Umma ta ɗaga tana karkaɗawa ta ce.

"A'a a'a a'a! Ki dai bar su gidan uban su tunda yana nan.."

"Haba Umma! ba ga su Khadijah ba, sai su taru suyi zaman su kuma ma tafiyar Kwana ɗaya ko biyu"

"Ni dai Zainabu ki bar su gidan su tunda uban su na nan, kinfi kowa sanin halin Hidaya shegen kukan tsiya ne da ita..."

Firdausi ce ta ce.

"To Umma ga Rumaisa ga Khadijah sannan ga Asiyah miye matsalar ki da fitanar ta..."

Ahmad shi ma ya ce.

"Umma dan Allah ki bar yaran nan a gidan nan, wai miya sa dan Allah kike musu haka ne??"

"To ubana da ke ni? Da ke ni na ce tunda har gano ina yin ba daidai ba"

Miƙewa yayi yana gunguni ya nufi hanyar fita ya na faɗin.

"Ni dai dan Allah ki daina haka ba kyau wallahi. Duk baiwar Allahn nan taxo gidan nan sai ta fita tana kuka wanda ban san dalilin hakan ba"

"Wallahi tallahi Ahmad da ni ka ke zancen nan kaji na gaya maka, ka ji min ɗan kaza uba mai juya zance zuwa in da ba nan mutum ya nufa ba. To tayi kuka da aka mata uban me?"

Ita dai Aunty Zainab komai ba ta ce, wuri ta samu ta zauna tare da ciro kuɗi dubu ɗari biyar en rafar 100-100k ta bawa Umma ta ce ga na ta.

Tamkar wadda aka ba wa ka shi haka ta karɓi kuɗin tace an gode can ciki ciki ta wuce da su ɗaki.

Daga zainab ɗin har firdausi da Asiyah kallon Umma suke har ta shige ciki, murya a ƙasa firdausi tana zare ido ta ce.

"To ni Aunty Zainab da na kawo 200k ban san ya za'a min ba"

Jarumta ta aro ta yafawa zuciyarki tare da yin wani murmushin yaƙe ta kalli Firdausi ta ce.

"Godiya zata yi mana, ko yanxu ai ba ta ce muku ba ta gode ba, kawai dai Ahmad ne ya ɓata ma ta rai shi yasa ku ka ga tayi reacting haka"

A ƙasa ƙasa Asiyah ta ce.

"Aunty Zainab kala talatin na kai ɗin ki amma duk da haka Umma sai faɗa ta ke min wai in ɗunka duka, idan ban ɗunke ba zai saya min wasu ba"

Zaro ido firdausi tayi ta ce.

"Me? Wallahi kada ki soma ɗin ke su duka, na miji ko da ya san kina da su muddin yayi niyar yi miki yi zai yi, sannan ba kowa ne namiji ba ne ma yake da wannan rayuwar bin diddiƙi na bura'uba"

Nan dai suka yi ta tattaunawa around 10:30am Ahmad yazo su ka kama hanyar Kaduna.

OUM AMEER

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.