Free chapter · Read without an account
23
by Aminatu Ibrahim · NUUDARR
NUUDARR 🥀🥀
(A 2025 NOVEL)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
AREWABOOKS@AMINATU IBRAHIM
WATTPAD @UMMU-AMIR
AMEENA IBRAHEEM
(OUM AMEER)
PAGE 23
Assalam Alaykum mutanen arziki mutanen kirki mutanena na jahar Zamfara da ma kewaye ina yi muku fatan alheri, Suna na REEDERT SKIN CARE wadda ke zaune a cikin jahar Zamfara Gusau Nigeria.... Ina mai farin cikin tallata muku kayana cikin aminci da kyakkyawar zuciya.......
Shin en uwa Kun dade kuna neman mayukan da zasu gyara muku jiki Baku samu ba???? 😳ina masu fama da sun burn?? ,knuckles?? ,glass?? ,Rashes?? ,spots?? Da sauran su? 😳ina masu qorafin suna shafa mayuka baya karbarsu,???😎ina wadda tayi bleaching ya bata mata fata tanaso fatarta takoma daidai ???🧚🏻♀️🧚🏻♀️shin kunada labarin REEDERT ORGANIC SKINCARE,dake jahar zamfara kuwa?? to idan baki taba amfani da products dintaba dan Allah ki jaraba kiga ikon Allah cikin qanqanin lokaci fatarki zatayi kyau ta murje tadinga sheqi kamar autar larabawa 👌❤️❤️ munada kaya kamar haka ➡️➡️
Amarya set
Mai jego set
Knuckles and dark spots removal set
Whitening and glow set
Lightening and glow set Etc........
Haka zalika munada supplements masu kyau da qayatarwa kamar haka ➡️➡️➡️
Weight gain supplements
Weight loss supplements
Anti-aging supplements
Whitening supplements
Breast enhancement and enlargement
Hips enlargement.
Reedert Organic skincare tana nan zaune a Gusau Motorgage Area behind masaqa
***,***
Delivery nationwide 🌍🌍🌍
Muna aikawa a duk inda kike cikin faɗin Nigeria da ma kewaye.
Wani fitsarin wahala ne naji ya kubce min tsabar tashin hankali. Cikin tsantsar ruɗewa na kalle sa laɓɓa na har suna harɗewa tsabar kaɗuwa na ce.
"Yah Saif...."
Ba tare da ya kalle ni ba ya yi saurin katse ni da faɗin.
"Shut up. Kawai ki fito ki biyo baya na"
Jiki na na ɓari na buɗe motar na fice kamar yanda na ga yayi na fara tafiya tamkar bana son yi muka nufi cikin gidan yana gaba ina bayansa.
Mama ce zaune akan kujerar tsugunno riƙe da buta a hannun ta, Baba kuma yana kan kujera zaune kamar ko yau she domin lafiyar ta zama sai a hankali.
Ji fa Mama tayi da butar da ke hannun ta taxo cikin azama ta rungume ni gam tare da fashewa da kuka tana mai faɗin.
"Na gode ubangiji da ka ji tausayi na ka karɓi addu'a ta ba don hali na ba. Astagfirullah, Alhamdulillah ya Allah"
Yanda ta ke kuka haka nima na ke yi tamkar yau ne muka fara ganin juna.
Hannu na Yah Saif ya kama wanda yayi sanadiyyar janyeni daga jikin Mama ya jani zuwa gaban Baba, na faɗi a gaban sa ina mai sake rushewa da kuka, wato wani abin yasha gaban wani, a wannan lokacin bana ma wani tunanin cikin da ke jiki na domin hankali na yayi matuƙar ɗagawa wanda bana ganin komai sai iyaye na.
Kallon Saif Baba Ya yi kamar yanda shi ma ɗin shi ya ke kallo babu wanda ya cewa wani uffan. cikin wata irin jarumta ya buɗe baki still yana mai ƙure baba da kallo ya ce.
"A duniya babu wani Uba ko wata Uwa da ta ke yiwa ɗanta fatan mummunar ƙaddara, duk wanda ka gani da irin wannan to hukunci ne da ƙaddarawar ubangiji... Idan yayi mana jarabawa sai mu gode masa domin duk abinda ya yi dai ne shine sarki guda wanda baya zalunci kuma abinda ya so ya kasance shi ya ke kasancewa. Nuudaar ta aikata kuskure, maimakon ka barmu a tare da ita a nuna mata kuskuren ta sai ka hau dokin zuciya ka kore ta Baba, wanda hakan kuskure ne,kuma na san kayi hakan ne wai don ka manta da ita da kuma zunubinta wanda hakan ni na sani ba mai yiyuwa ba ne domin har abada ba zaka manta da ita ba Baba... Haihuwar ta kwanaki ne suka rage mata, a yanxu tana a tsakankanin siradi guda biyu, ko dai ta haihu ta tsallake wurin haihuwar ko kuma ta mutu wurin haihuwar, ba zan iya barin ta a wata duniyar ba a wannan hali bayan kuna nan a raye a cikin duniya ɗaya.... "
Faɗuwa yayi shima akan ƙafafunsa tare da fashewa da kuka ya harɗe hannayensa alamar roƙo ya ce.
" Ban sani ba ko har yanxu kana akan bakanka, amma don Allah don girman Allah ka yi haƙuri ka barta ta haihu a gaban ku ko zata samu sassauci daga baya koma wane irin hukunci kaga yafi muddin zai saka zuciyar ka ta huce ni na amince ka zartar da shi... A madadina da na sauran en uwana muna neman alfarma da kuma nemawa er Uwar mu gafara dan Allah don girman Allah ka yi haƙuri ka yafe mata Baba "
A hankali ya zauɗo zuwa gaba ya matso dab da Saif ɗin ya ɗora hannayensa akan na sa yana mai zubar da hawaye ya kalli Saif ɗin ya ce.
" Saifuddeen Na ɗauka idan na kore ta shikenan na huta da ita zan kuma manta da wata Nuudaar a duniya da zunubinda ta aika ta min, ashe ba haka ba ne, tunda ku ka sanya ƙafa kuka fice a kowace rana mutuwa ni ke yi Saifuddeen, al'amarin ko kaɗan bai zo min da sauƙi ba.... "
" Kayi haƙuri Baba, ka yi haƙuri dan Allah... "
" Saifuddeen duk tsawon lokacin nan kuna ina a duniyar nan?? Miyasa ba ku dawo ba?? "
" Muna Kaduna Baba, Nuudaar tana gidan iyayen wadda zan aura Baba, bamu dawo ba domin mun ɗauka baka da buƙata da mu Baba... "
Girgiza kansa yayi sannan ya ce.
" To ya zanyi Saif? Nuudaar ce ta ɓata sunanta ta kuma ɓata suna na, ta zubar min da mutunci na tayi min godiyar Mayu akan irin tarbiyyar da na gina ta a kai,Saifuddeen taya zan zo na ganta....."
Ƙara zauɗowa nayi da ƙyar zuwa dab in da hannunsa ya ke, hannun na kama tare da ɗora fuska ta a bayan hannun nasa ina mai ci gaba da kuka na ce.
" Kayi Hakuri Babana... Kayi haƙuri! Na tuba Baba, rashin ku a cikin rayuwata yana mini wahala sosai, bana iya bacci Baba"
Janye hannunsa ya yi ya ɗora ɗaya a kaina, ya janyo kan nawa zuwa ƙafar sa. Ƙara kwantar da kai na nayi da kyau ina mai jin wani irin sanyin rahma na tsaga ɓargo da dukkan gaɓɓan jiki na.
Muryar sa ta ratsa dodon kunne na da faɗin.
"Na yafe miki Nuudaar, tabbas yau na yafe miki duniya da lahira, Allah ya yafe miki zunubin da kika aikata ya sauke ki lafiya, ki yi ta istigfari ki kuma yawaita sadaka domin sadaka tana maganin masifa"
Zuwa Mama tayi ta ɗaga ni ta sake rungume ni cike da tsantsar tausayin yanayinda ta ganni.
Ƙara kwantar da kaina nayi a jikinta a hankali ina faɗin.
"Na gode mu ku Mama, Allah ya saka muku da alheri ya ƙara muku tsawon rai mai amfani da lafiya mai amfani da kuma albarka"
"Amin Nuudaar"
Ɗakin ta ta jani har bakin gado ta zaunar da ni, ta kawo min tuwo, fura, nama, fruit... Komai da tasan ta mallaka sai da ta dire min shi a gaba na, bayan haka kuma tambaya ta take ko ina son wani abin ta tashi ta haɗamin,maganar ta ke tun ɗazu ba tare da hawayen ta ya tsaya ba.
Hawaye na na share domin ta bani matuƙar tausayi, uwa kenan! Ba abinda ni ke idan ba Kallonta ba.
**********
Saif kuwa, ji ya yi tamkar an sauke masa wani gingimemen dutse da ke ƙwaryar kansa.
Ya ɗan jima tare da Baba suna tattauna zance sannan daga baya ya tashi ya nufi gidan mahaifiyar sa zuciyar sa ci ke da kewarta.
Zaune suke ita da Hanna suna auna lallen Hausa a robobi wanda suke saidawa da yankan soletef.
Suna jin sallamar sa kamar a mafarki Hannatu ta je da gudu ta rungume shi cike da murna ga hawayen farin ciki da suka wanke mata fuska.
"Yah Saifuddeen Oyoyo!"
Shima dariyar ya yi yayin da ya ji wani farin ciki ya lulluɓeshi.
"Hanna, ai kun sarara kwana biyu mai takura mu ku yayi ne sa da ku...."
Da sauri ta girgiza kanta tana mai share hawayen ta ta ce.
"Yah Saif, ba wani zancen takurawa, munyi kewar ka."
"Ina Fauzah da Nurudden?"
"Aunty Fauxa tana wurin lectures ta na 400level ta bar Aunty Nuudaa a baya. Nurudden yana shago, Yah Halifah ma yanxun ya bar gidan nan ya ce Aunty Asiya na jiran shi.... Yah Saif na kawo maka abinci..."
Girgiza kai ya yi ya ce.
"a'a, Thank you Hanna"
Wurin Mama Ruke ya nufa wadda ta kawar da kanta gefe daga barin kallon sa tana mai share hawayen ta lokaci baya lokaci.
Durƙusawa yayi a gabanta tare da kama hannunta ya riƙe murya a tausashe ya ce.
"Kalaman baki na sun yi matuƙar yin kaɗan wurin baki haƙuri ya ke mahaifiyata, na san ko a gare ki ban aikata kuskure ba kawai da sharrin zuciya ne da kuma rashin son nesantar abinda ta saba da shi, amma ko ke Hajiya na san a duk lokacin da za ki tuna da Nuudaar kuma ki tuna da cewa ina tare da ita sai hankalin ki ya kwanta, ni ban san komai ba sai kyakkyawan ɗabi'un da kika koyar da ni na so da ƙaunar en uwana da kuma tsaya musu a kowa ne irin yanayi.... "
Sautin Kukan ta ne ya ƙaru, yayin da ta jimƙe hannunsa sosai a na ta tana mai jinjina kanta ta ce.
" Da farko hankali na ne ya nemi gushewa Saifuddeen domin tunani idan ka ta fi ba zaka dawo ba har abada ko kuma ka kwashe tsayin shakaru ba ka dawo gare ni ba wata ƙila ma sai na mutu, shi ne kawai tsoro na, ga shi ka bar aikin ka Saifuddeen ka bar komai na ka wanda na san yanxu sun jima da korar ka.... "
" Kar ki damu Hajiya, Allah ya ga niyyata ta alheri,in sha Allahu in dai domin sa nayi da kuma zumunci har abada ba zan taɓa kunya ba, ko sun kore ni shi zai bani wata hanyar wadda ma tafi wannan ka da ki damu"
"Saifuddeen, Haƙiƙa ba ka yi kuskure ba, kayi abinda ya da ce, Ina nuudaar ɗin da fatan tare ku ka dawo da ita?"
Zaunawa yayi a kan ɗuwawunsa tare da tanƙwasa ƙafafuwansa ya ce.
"Ta na gida na kai ta, Baba ya ce yafe mata...."
Nan ya gaya mata duk yanda suka yi,itama ta tambaye shi a ina suke tsawon lokacin nan ya yi mata bayani tiryan-tiryan kamar yanda ya yi wa su Baba. Bayan ya gama ta jinjina kanta ta ce.
"Haƙiƙa sun yi sadaukarwa ko mu da muke iyayen ku mun kasa yi muku, waɗannan mutanen samun irin su kaɗan ne a cikin duniyar nan ta mu ta yau, yarinyar ma taci 'ƴa, ka ji tsoron Allah ka riƙe ta da amana kamar yadda ta riƙe ka da er uwarka"
Cikin jin daɗin furucin ta ya ce.
"Amin amin. Na gode sosai Hajiya da kika fahimce ni, Allah ya ƙara lafiya"
Daga haka ya tashi zuciyar sa fes! Ya wuce ɗakin sa ba tare da sauran wata damuwa ba. Tsayawa yayi ya na mai bin ko ina da kallo... Sababbin kayansa ya gani nan kan makekiyar katifar sa. Kayan da ya ci burin cin bikin ɗan uwansa kuma amininsa da su wato Halifah, ga hula na nan a gefe da takalmi da komai na shirin ɗaurin aure,ga saƙon Meerah da ta aiko masa a lokacin ko buɗewa bai yi ba. Hannu ya miƙa ya ɗauko ledar murmushi kwance a kan kyakkyawar fuskar ya buɗe ledar domin ya ga miye ne a ciki.
Ɗinkin babbar riga ne a ciki Complete set da takalmi da hula masu matuƙar tsada. Er ƙaramar paper da ya gani ciki an yi folding ya buɗe.
'Abokin ango, ka gayawa matar ango bashi na bayar da kayana idan an tashi na mu auren to ta rama mini taƙwarƙwara'
Faɗawa ya yi kan katifar yayi shiru yana mai tunanin Meerah a ransa.
Bai fi minti goma da kwanciya ba yaji an banko ƙofar tamkar za'a ɓallata ya ɗago da sauri domin ya ga waye.
Murmushi yayi ganin Halifah a tsaye yana kallon sa.
"Ba za ka ta so ka rungume ni ba Saif! Kasan irin yanda nayi bala'in kewar ka a zuciya t....."
Hugging ɗinsa da ya yi shi ya katse masa maganar sa sai shima ya saka hannayensa ya zagaye sa yana mai zubar da hawayen farin ciki.
Janyewa ya yi a hankali yana mai ƙure kallon saif ɗin cikin wata irin raunatacciyar murya mai nuna gazawa ya ce.
" Thank you Saif.."
"Thank you for what Halifah?"
Girgiza kan sa yayi ya ce.
"Ni ne wanda ta ke gani a matsayin mutum na farko da zai tsaya mata a dukkan komai, amma banyi hakan ba Saif...."
"OH! Wato baka yarda cewa ni da kai duk ɗaya muke a wurin Nuudaar ba?"
"No! Ba haka ba ne...."
"Halifah Musayyib Alƙali yanxu mu bar wannan zancen domin ya wuce ya zama tarihi har abada in sha Allah. Yanxu ka zauna ka jira ni nayi wanka in shirya mu tattauna"
********
Ko da ƙarfe takwas tayi na dare, gidan mu ya cika cinjim da en uwana, da masu yimin fatan alheri da kuma ma su gulma Waɗanda suka yi ta yaɗa ni a fai-fain talla.
Kwance na yi lamo! Na ɗora kai na a kan cinyar Aunty Nadee kowa sai faman sannu ya ke min, Fauxa ma tana gefe na ta kasa matsawa ko ina tamkar wadda aka ce za'a ƙwace mata ni.
Yah Halifah ma sun jima sosai da Yah Saif, sai da suka kambala sallar Isha sannan ya koma gida da nufin ya ɗauko Asiyah.
Yana shiga ya cimmata tayi shame-shame a ƙasan center carpet ga robar rufaida-yorghurt a gabanta da alama sha ta ke domin robar a buɗe ta ke.
Cikin farin cikin da ta jima bata ganshi a ciki ba ta kalle shi ta ce.
"Lafiya dai?"
Cikin tsantsar farin ciki ya ce.
"Alhamdulillah Asiyah! Nuudaar ta dawo Saif ma ya dawo"
Murmushi ta yi tana mai miƙewa zaune ta ce.
"Masha Allah, congratulations! Allah ya tsare gaba. Ta haihu?"
"A'a...."
"Yanxu Shi Emraan ɗin ya san ta dawo?"
Nan girgiza kai yayi ya ce.
"Miye ya kawo zancen Emraan a nan Asiyah? Yanxu dai ki tashi mu tafi ki duba ta ki mata sannu dawowa.."
Kallon bakin shi ta ke yanda ya ke maganar har ya ƙarasa. Ƙasa tayi da murya tana mai yatsina fuska ta ce.
"Halifah ka fa san bana jindaɗi, ka bar shi zuwa kwana biyu in ɗan samu sauƙi tukun...."
Cikin mamaki ya ce.
"In bar shi kwana biyu? Bakya jin daɗi? A ina ne bakya jin daɗin? Ai na san bakya jin daɗin Asiyah amma ai baya hana miki fita a duk sanda kika so"
"Halifah Nuudaa fa tana tare da mu ba ɓacewa za ta yi ba, ko sa ke komawa za ta yi in da ta fito??"
Miƙewa ya yi kawai ya bar gidan direct ya wuce gidan Mama. Zuciyar sa na raya masa abubuwa ma su yawa akan Asiya.
OUM AMEER