Free chapter · Read without an account
28
by Aminatu Ibrahim · NUUDARR
NUUDARR 🥀🥀
(A 2025 NOVEL)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
AREWABOOKS@AMINATU IBRAHIM
WATTPAD @UMMU-AMIR
AMEENA IBRAHEEM
(OUM AMEER)
PAGE 28
Assalam Alaykum mutanen arziki mutanen kirki mutanena na jahar Zamfara da ma kewaye ina yi muku fatan alheri, Suna na REEDERT SKIN CARE wadda ke zaune a cikin jahar Zamfara Gusau Nigeria.... Ina mai farin cikin tallata muku kayana cikin aminci da kyakkyawar zuciya.......
Shin en uwa Kun dade kuna neman mayukan da zasu gyara muku jiki Baku samu ba???? 😳ina masu fama da sun burn?? ,knuckles?? ,glass?? ,Rashes?? ,spots?? Da sauran su? 😳ina masu qorafin suna shafa mayuka baya karbarsu,???😎ina wadda tayi bleaching ya bata mata fata tanaso fatarta takoma daidai ???🧚🏻♀️🧚🏻♀️shin kunada labarin REEDERT ORGANIC SKINCARE,dake jahar zamfara kuwa?? to idan baki taba amfani da products dintaba dan Allah ki jaraba kiga ikon Allah cikin qanqanin lokaci fatarki zatayi kyau ta murje tadinga sheqi kamar autar larabawa 👌❤️❤️ munada kaya kamar haka ➡️➡️
Amarya set
Mai jego set
Knuckles and dark spots removal set
Whitening and glow set
Lightening and glow set Etc........
Haka zalika munada supplements masu kyau da qayatarwa kamar haka ➡️➡️➡️
Weight gain supplements
Weight loss supplements
Anti-aging supplements
Whitening supplements
Breast enhancement and enlargement
Hips enlargement.
Reedert Organic skincare tana nan zaune a Gusau Motorgage Area behind masaqa
***,***
Delivery nationwide 🌍🌍🌍
Muna aikawa a duk inda kike cikin faɗin Nigeria da ma kewaye.
Har aka gama addu'ar Uku hawayen Umma na rashin Zainabu ba su dai na kwaran ya ba, ga Hidaya da Ammar ta sanya su a gaba ta rungume gam tamkar wadda aka ce za'a raba ta da su, ita da ke bai wa Zainab baki akan rashin Ruma yau ita ce ake bai wa baki Sufyan ma haka. Shi abun na shi kamar ma ya so ya taɓa ƙwaƙwalwar sa domin ba abinda ya ke sai sabbatu ya kasa yarda da cewa wai Ruma da Zainab sun mutu kenan har abada ba za su dawo ba......
Abbah ne ya shigo ɗakin baƙi da ke waje domin ya duba Sufyan idan ya gama shiryawa daman ya nemo Malam azo a raba gadon ta kamar yanda shari'a ta tanada.
Lulluɓe ya cimma sa, ya rufe har kansa da duvet, da sauri Abba ya ce ya yaye zanen ya na mai kiran sunan sa.
Ko iya ɗago kansa ba ya yi sanadiyyar wani irin zazzaɓi da ya turnuƙesa, ga hawaye na yi masa tsiyaya tamkar ba namiji ba.
Jin zafin jikin ya yi yawa sosai ya sa Abba ya kira yayansa Alhaji Lawali da ke waje ya shigo tare da taimakon Ahmad suka ɗauke shi zuwa asibiti. Komai rashin tausayin ka ka kalli Sufyan sai ka zubar masa da hawaye tsabar yanda ya susuce yake kuka domin shi kaɗai yasan irin raɗaɗi da azabar da ya ke ji akan rasa matar kirkin sa, matar rufin asiri, mata ta gari da yayi, ya sa ni har abada ba zai taɓa samun mace irin Zainab ba.
*********
Maman Salima ta na zaune a tsakar gida ta na yiwa wata mata kitso, daman sana'arta kenan, sai ga yaronta ya shigo ya kalle ta jiki sanyaye ya ce.
"Mama!"
Ɗagowa ta yi ta kalle sa ta ce.
"Ya akayi Ukasha?"
"Mama Maman Hidayah ta ra su kuma ma Ruma ta rasu...."
Ture matar da ke gabanta tayi da ƙarfi tana mai miƙewa tsaye ta dafe ƙirji cikin tashin hankali ta ce.
"Kai Ukasha! Bana son ƙarya..."
"Na rantse Mama, yanzu Baban su Ubaidu ya dawo ya ce daga can gidan su ya ke yana magana da baban su Suhailu, har baban su Ruma ma ba shi da lafiya an kai shi asibiti, wallahi na ji yanxu ya na gaya mai..."
Kuka ta ratsa tare da ɗora hannun ta aka tana faɗin.
" Na shiga uku na na lalace ni Huraira ni yau mi zan ji haka! InnaLillahi wa inna ilaihiraji'un...Allah na tuba ka yafe min... Wayyo Allah wayyo ni kaina.... "
" Kuma Mama na ji ya na faɗai mishi wai Hamid ɗin gidan Alhaji Bilya mai Sudan ne ya yi mata fyaɗe har ta mutu... "
" InnaLillahi wa inna ilaihiraji'un! Ni yau na ga baƙar rana ni Huraira Hamid Allah ya tsine maka albarka, Allah ya walaƙantaka, Allah ya ruguxa ka.... "
Kishiryarta ce ta fito daga madafar abincin su ta kalle ta a sheƙe sannan ta ce.
" Ba haka ki ke so ba? Ai ni tun jiya na ji, kuma har na je gidan iyayenta na yi musu gaisuwa, ke kuma ki jira ranar da zaku tsayu domin hisabi, duk unguwar nan ba ta hulɗa da kowa sosai kamar yanda ta ke yi da ke, kin ji ɗan maƙota na shirin cutar ma ta da 'ƴa sai kika yi shiru wai kada ki faɗa ma ta ta ƙi amincewa, to yanxu ina zaki ganta ki roƙeta Maman Salima??... "
Ƙara sautin kukanta tayi jin Kalaman Maman Aslam,lallai ta yi kuskure, kuskuren da ba za ta iya gyarawa ba, Yanxu Maman Hidayah ta ra su??
Miƙewa tayi da sauri ta zari hijabinta da ke sagale jikin igiya ta zura, takalmi a birkice ta sanya ta fito sai gidan Alhaji Bilya Mai Sudan.
Cikin baban Palourn Hajiyar ta yi wa tsinke, zaune ta tarar da Hajiyar Hamid ɗin ta na kallo a TV ga waya a hannun ta ta na dannawa.
Cikin kakkausar Murya ta kalli hajiyar da kyau ta ce.
"Hajiya Shamsiyya na san ba ki rasa jin irin aika-aikar da ɗanki Hamid ya yi wa Yarinyar gidan Maman Hidayah da har ya yi sanadiyyar mutuwar ta ta sanadin wannan ɗin yasa uwar ta baƙin ciki ya kashe ta washe gari bayan mutuwar 'ƴar ta, wallahi tallahi sai kun gurfana gaban alƙali domin sai an bi mi su haƙƙin su.... "
Wani irin kallon wulaƙanci Hajiyar ta bi ta da shi tun farkon shigowar ta har sai da ta dasa Aya sannan ya buɗe baki ta ce.
" A gidan ubanwa aka gano cewar Hamid ɗin shi ne ya aikata ma ta haka? Wai ku mutane miyasa tsoron Allah ya yi muku ƙaranci ne a zuciya? Yarinya ta mutu uwar ta ta mutu kuxo ku rasa wanda za ku maƙalawa sharri sai yaro na? Duk yaran da ke unguwar nan ku rasa wa za ku yiwa sharri sai Hamid ɗa ɗaya tilo? Don dai kunga ya na samun gata shi ne zaku ɗauki ƙahon zuƙa ku aza masa?miye shaidar ku akan hakan?... "
" Wallahi tallahi mu nan duk shaida ne unguwar nan ɗaɗɗaya ba su nan cewa Hamid na cutar da Ruma ba, kuma wallahi a shirye mu ke domin mu tsaya shaidata in sha Allahu sai an ƙwatar ma ta haƙƙinta... "
Wani murmushi Hajiya Shamsiyya ta yi tana mai jinjina kan ta tace.
" Wato duk mutanen unguwa da ke yin maganar suna ƙus-ƙus ba su iya sun tunkare ni sai ke da kika fi su tsaurin ido ko? Ba dai kotu ki ka ce ba? Ku je muna nan muna jiran ku "
Cikin ɗacin rai Maman Salima ta ce.
"In sha Allahu sai an bi musu haƙƙin su, Hajiya Shamsiyya sai kin yi kuka kamar yanda Maman Hidayah ta yi, kuma baƙin cikin wannan Yaron da ku ka ɗaure wa gindi ya ke abin da ya ga dama wai don shi kaɗai kuka mallaka shi ne zai yi ajalinki ke ma"
"Naji, Malama ki fitar min gida wallahi ko na sa ka yanzu a yi miki dukan tsiya dukan kawo wuƙa, matsiyaciya er neman gindin zama"
Fitowa Maman Salima tayi tana mai jin wani irin jiri yana ɗibar ta tamkar zata faɗi, mashin ta tare direct sai gidan su Umma.
Duk abinda su ke faɗa a kunnen Hamid ya na laɓe ya na sauraren su, daman tun da ya ji labarin mutuwar Ruma hankalin sa ya tashi daga baya kuma ya sa ke jin mutuwar mummynta, Suhail da kansa ya zo yana tuhumar sa cikin ɓacin rai kamar yanda yaji labari na yawo a unguwa, amma haka ya bushe idonsa ya ce shi sam bai san an yi ba, bai san mi ke faruwa ba.....
"Miye ka ke wani tsayawa a bayan ƙofa? Fito nan ka gayamin idan da gaske ne... "
Fitowa ya yi yana muzurai ya ce.
"Ni fa Mum ban san ma mi su ke magana a kai ba, wallahi ban san yarinyar ba, kawai mutane ne hassada da baƙin ciki sun yi musu yawa..."
"Bar ni kawai da su sha kuruminka, bari Alhaji ya dawo mu zauna domin dole ya kamata ayi wa wannan abin tubkar hanci"
Hamid na ji wannan zance na mahaifiyar sa, sai ya ji ya samu nutsuwa shike nan hankali sa ya kwanta ba shi da wata sauran fargaba.
*********
Ba ta ƙara shiga tashin hankali ba sai da ta isko Asiya wadda dawowar ta kenan daga asibiti an yi discharging na ta sai kuka ta ke mai ban tausayi tana kiran sunan Aunty Zainab ita da Ruma.
Su Umma ma sun bi bayanta sai kukan su ke ga Ammar rungume a hannun ta Hidayah kuma na jingine da jikinta ita ma.
Gefe Maman Salima ta rakuɓe tana ta darzar kuka tamkar uwar ta ce ta mutu.
"Wallahi tallahi Hamid ne, shi ne ɗan gidan Alhaji Bilya Mai Sudan, Yah Allah ka isar muku da isar sa, Allah ya gafarta mu su, Allah ya yi musu Rahma... Kai co!"
Girgiza Kai Umma ta yi a hankali ta ce.
"To ya za'a yi? Kunga dai shike nan Zainabu ta tafi ta barni ko? Hmmm! Wai ta na cewa ta yafe wa Ruma ba ta taɓa yi ma ta laifin komai ba, to ni a duniyar nan wane Laifi zan ce Zainabu ta taɓa yi min ni Murja? Wallahi tallahi duk cikin yara na babu mai yi min biyayya kamar ita, babu mai gudun zuciyata kamar ita, duk yanda ni ke hantara da yi mata faɗa sai dai ta yi shiru tana mai bani haƙuri, komai ta samu sai ta zo gidan nan ta kawo min kuma ko kafin tayi aure haka ta ke, dama ban yi mata abinda na ke yi mata ba, ga shi lokaci ya ƙure mini domin ta tafi ta barni a duniyar, ba bu ita ba bu Rumaisa kamar an yi ruwa an ɗauke. To kundai gani... "
Wani kukan Asiya ta sa ke fashewa da shi ta na mai kwantawa jikin firdausi ta na faɗin.
" Aunty Zainab! Wayyo Aunty ta, wallahi tallahi duk abinda ki ka ce nayi shi zan riƙa yi na yi miki alƙawari, in sha Allahu ba zan sake yin duk abin da bakya so ba"
Jinjina kai Umma ta yi ta ce.
"Hmm! Zainabu in sha Allahu ta na Aljannah, ba ta son rashin gaskiya ba ta zama da mai rashin gaskiya, kullum ba ta da aiki sai yi wa mutane nasiha da hana su aikata laifin da ubangiji ba ya so, mijinta ma ya shaide ta ya yabe ta ya kuma yafe mata nima haka Mahaifin ta ma haka, to miye kuma ya rage? Shaidun duniya shi ne shaida sai dai kuma abinda ya ke tsakanin bawa da ubangijin sa, muna fata da addu'a Allah ya yafe mata kusakuranta ya kai haske ƙabarinta yasa mutuwar ta zama hutu ne a gare su"
"Amin amin yah Allah. Wallahi Maman Hidayah duk katafanen unguwar nan ta mu ba ta da abokin faɗa ba ta da abokin gulma, shekara goma sha biyar da tayi a unguwar nan babu wanda zai ce ga laifin da baiwar Allahn nan ta yi masa. Allah dai ya yafe mata amin. Umma ni ce maƙociyar ta maman Salima idan ta taɓa gaya miki "
Jinjina kai Umma ta yi ta ce.
" Ina jin Maman Salima a bakinta, can ta ce ta ke ajiye yaranta watarana idan za ta fita, ta ce ke kaɗai ta ke iya amincewa "
Wani irin abu Maman Salima ta ji ya dokar ma ta zuciya jin furucin Umma na cewa ita ka ɗai ta yarjewa, 'kai ni Huraira na shiga uku na! Ya zanyi da rai na? Yanxu ta ina zan Maman Hidayah ta yafe min? InnaLillahi wa inna ilaihiraji'un. Allah na tuba! Allah ka yafe min Allah. Da ace na gaya ma ta da yanxu hakan ba ta faru ba ko?....
Yan da ta ke wani irin matsanancin kuka shi janyo hankalin su musamman Firdausi da taji ta bata tausayi ta ce.
"Ki yi haƙuri baiwar Allah, mu ma dai dole mu ɗau dangana, ba bu abinda ta ke buƙata da ga gare mu yanxu fa ce addu'a"
Ganin shigowar Abbah ya sa duk suka bi shi da ido. Gefe ya samu ya zauna Maman Salima ta gaishe shi ta yi mi shi gaisuwa sannan ya kalli Umma ya ce.
"Hajiya Murja yanxu muka dawo tare da Halifah wurin shigar da ƙara kamar yanda muka yi shawara, musamman Halifah, ya ce idan har aka biyewa shawarar ita Zainabun aka ce a ƙyale Yaron nan to tabbas an ba shi lasisin da zai ji daɗi gobe ya sake komawa ya yi wa wata.... "
Girgiza kai Umma ta yi ta ce.
" Hmm! Alhaji irin wannan na wa akayi? Babu abin da za'a masa ina faɗa maka dama kun janye kun bar su da Allah can gobe yayi muna hisabi, Ina tabbatar ma ka ko da munyi shari'a da su ba zamuyi nasara ba, musamman da ubansa ya ke ji da kuɗi ga shi yana tare da manyan en siyasa kasan babu abinda za'a iya yi masa kawai mu bar su da Allah da za ku ji shawara ta... "
" To Hajiya, Yanxu dai mu jira mu gani, kin san wani lokacin shari'a saɓanin hankali, sai kiga kuma watarana an da ce ɗin,yanxu sai mu jira Sufyan ya warke daga asibiti idan Allah ya nufa sai mu ga mi ya dace. Allah ya gafarta musu"
"amin amin"
Bayan Abba ya fita da ɗan jimawa Hannatu ta miƙe, daman ita ke kwana da Asiya a asibiti tunda abinnan ya faru, sai yanxu da aka sallamo su suka taho a tare.
"Aunty Asiya ni zan tafi gida, Allah ya sanyaya ya ba da haƙuri..."
Idanunta ta ɗago da suka yi ma ta suntum tsabar kuka, murya a dishashe ta ce.
"Haba Hannatu! Dan Allah ki yi haƙuri mana kar ki tafi ki barni kinji, kiyi hakuri..."
Cikin tausayawa Hanna ta ce.
"ki yi hak'uri Aunty Asiyah Lectures ne da ni, kuma ina so in je gida in ƙara duba jikin Aunty Nuudaar, in sha Allahu idan na gama zan dawo da dare"
"To shi kenan na gode sosai Allah ya saka miki da alheri, ki gaishe da Nuudaar ɗin da su Mama kinji, ki ce musu na gode sosai da hidima Allah ya biya"
Gyaɗa kai Asiyah tayi tana mai fadin in sha Allah, daga haka ta fi ce tana mai matuƙar mamakin Canjawar Asiyar nan ta ke, matar da idan ta gan su ta ke jin kamar ta kashe su amma wai itace ke cewa kada ta tafi kuma ga ta ma cikin gidan iyayenta.
Maman Salima ta na gidan sai da akayi sallar Asr zuwa ƙarfe biyar sannan ta ta shi ta koma gida cikin alhini da da na sani marar amfani.
*********
Ahmad.
Zaune ya ke cikin wani tsohon kango ga Hamid durƙurshe a gaban sa an nannaɗe sa hannaye an ɗaure su a baya, fuskar sa Lulluɓe da ƙyalle.
'Mafari....
Ahmad dai tunda ya ji dalilin abinda ya samu Ruma kuma ya ji labarin wanda ya yi mata wannan ɗanyen aiki, tun ranar ya baza yara shiryayyi ya biya su akan su kamo masa Hamid idan sun samu dama, idan sun kama shi kuma su naɗo masa shi su kawo a nan sannan su kira shi,tun daga ranar suka shi ga bibiyar duk wani motsin sa har Allah ya ba su sa'ar sa suka cafko shi ya tsaya akan hanyar sa ta zuwa school motar sa ta tsaya ya fito yana dubawa'
A hankali Ahmad ya janye kwance masa ƙyallen fuskar sa ya kalle sa da kyau ya ɗauke sa da wani irin gigitaccen mari.
Zuciyar sa na yi masa wani irin raɗaɗi ga hawaye na bin fuskar sa ya kalle sa ya ce.
"Ka san kuwa wacece Zainab a wurina? Kasan girma da matsayin Aunty Zainab a cikin rayuwar ahlina?? Babbar yayata ce kuma ita ɗin uwa ta ce, yanda ta ke kulawa da tarbiyyata da duk wani abinda ya shafi rayuwata ko uwata da ta haife ni bata kulawa da ni hakanan, ita ce ta ke bani kuɗin yin provision na school tun ina secondary school har yanxu da nike ɗan-fodiya ko Abba ya bani sai ta bani, duk girmannan nawa duk sallah ko wata hidima sai ta yi min ɗinki ta bani kuɗin kashewa don kawai kada in ji abin wani yana burgeni har in yi sha'awar sata, ba ni kaɗai ba, Abba, Umma, firdausi, Asiya duk tana kulawa da mu bata bari damuwa ta hana mana bacci muddin ta na da hanyar da zata iya taimaka mana walau ta kuɗi ko ta magana da baki,amma kai... Kai ɗin nan dai.... "
Ya ƙara she maganar ya na mai fashewa da kuka, sai da yayi mai isar sa sannan ya share hawayen sa yana jinjina kai ya ce.
" Ruma.. Babbar ɗiyata Rumaisa da ni ke ji da ita, duk lokacin da taji muna waya da maman ta sai ta ce Daddy Ahmad ya makaranta, daddy Ahmad Allah ya taimaka..... ,ita ce wadda na ci buri a raina duk sanda auren ta ya tashi ni ne nan zan saya mata kayan ɗaki domin kawai na sanya Aunty Zainab farin ciki.. Yarinya mai ilmi da tarin baiwa, kai ɗin nan wai kai ne ka yi mata fyaɗe.. To da ta yi maka me? Na ce da ta yi maka me? Duk tarin en mata da yaran da ke garin nan tunkiyar ƙwaƙwalwar ka da arniyar zuciyar ka ba su nuna maka kowa ba sai ita ko??"
Yanda ya ke nuninsa da sharɓeɓiyar wuƙa sai ƙyalli ta ke shi ya ɗagawa Hamid hankali, cikin tsananin tsoro murya na yi masa rawa ya ce.
" Dan Allah dan girman Allah kayi haƙuri wallahi tallahi sharrin shaiɗan ne.... "
Wani mugun mari ya sa ke sauke masa sai da ya hantsila sannan ya ɗago shi ya dangwarar da shi akan ƙafafunsa shi kuma ya zauna suna facing juna cikin ƙunar rai ya ce.
"Sharrin shaiɗan ko? To nima yanzu shi ne zai sanya na aika ta maka abinda har abada ba za ka sake sha'awar yi wa er wani abinda ka yi wa Ruma ta ba. Ba ance wai kai ubanka mai kuɗi ba ne? Kuma wai ba zamu iya shari'a da ku ba domin ko anyi ba zamu yi nasara ba? Na san ma ko da mun yi nasara duk tsanani kayi en shekaru ka fito ka dawo ka na yawon ka cikin nishaɗi da farin ciki. To ba haka za'a yi ba, a'a! Sannan ni B zan kashe ba, domin idan na kashe ka ba zan taɓa hucewa ba, I will do you what would make you to suffer for rest of your life, Wanda da an ganka ga ka nan dai ka na rayuwa amma kuma ba ta da wani amfani a gareka"
Daga haka ya sanya wuƙar ya danne sa da ƙarfi ya caccake masa idanuwansa, yana ihun fitar rai yana magiya yana komai, sannan ya kamo yatsunsa hannuwansa tamkar wani mahaukaci yana faɗin.
"Bayan na gama halaka idanuwanda suka hango maka ita har ka ji ta burge ka waɗan nan hannayen kuma su ne suka janyo Ruma har ka iya cire mata kayan jikinta ka yi mata fyaɗen ba.."
Haka ya sanya wuƙar duk ya yanke masa en yatsun hannun sa guda goma ya bar sa da gundun-bulai.
Jinjina kansa ya fara ya na faɗin.
" Daga rana mai kamar ta yau ba zaka sa ke sha'awar yi wa er wani fyaɗe ba...kaii?.. Ku ɗauki wayar sa ku kira rubutawa uwar sa ko ubansa text su zo nan su ɗauke sa su kai sa asibiti domin ni bana so ya mutu, Ina so ya ɗanɗani rayuwa cikin wannan yanayin ya ji irin daɗin ta"
Daga haka ya karɓi ruwa ya wanke hannun sa da wuƙar ya sanya ta cikin mashin ɗinsa sannan ya haye ya yi tafiyar sa ran sa fes!.....
Ya na zuwa ya haɗa kayansa ya cewa Umma shi ba zai iya ci gaba da zama nan ba, zai koma makaranta sai dai idan ya dawo, daga can ya je ya samu Abbah ya karɓi kuɗi ya wucewar sa Sokoto ba tare da kowa ya san abinda ya aikata ba.
OUM AMEER