Free chapter · Read without an account
29
by Aminatu Ibrahim · NUUDARR
NUUDARR 🥀🥀
(A 2025 NOVEL)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
AREWABOOKS@AMINATU IBRAHIM
WATTPAD @UMMU-AMIR
AMEENA IBRAHEEM
(OUM AMEER)
PAGE 29
Assalam Alaykum mutanen arziki mutanen kirki mutanena na jahar Zamfara da ma kewaye ina yi muku fatan alheri, Suna na REEDERT SKIN CARE wadda ke zaune a cikin jahar Zamfara Gusau Nigeria.... Ina mai farin cikin tallata muku kayana cikin aminci da kyakkyawar zuciya.......
Shin en uwa Kun dade kuna neman mayukan da zasu gyara muku jiki Baku samu ba???? 😳ina masu fama da sun burn?? ,knuckles?? ,glass?? ,Rashes?? ,spots?? Da sauran su? 😳ina masu qorafin suna shafa mayuka baya karbarsu,???😎ina wadda tayi bleaching ya bata mata fata tanaso fatarta takoma daidai ???🧚🏻♀️🧚🏻♀️shin kunada labarin REEDERT ORGANIC SKINCARE,dake jahar zamfara kuwa?? to idan baki taba amfani da products dintaba dan Allah ki jaraba kiga ikon Allah cikin qanqanin lokaci fatarki zatayi kyau ta murje tadinga sheqi kamar autar larabawa 👌❤️❤️ munada kaya kamar haka ➡️➡️
Amarya set
Mai jego set
Knuckles and dark spots removal set
Whitening and glow set
Lightening and glow set Etc........
Haka zalika munada supplements masu kyau da qayatarwa kamar haka ➡️➡️➡️
Weight gain supplements
Weight loss supplements
Anti-aging supplements
Whitening supplements
Breast enhancement and enlargement
Hips enlargement.
Reedert Organic skincare tana nan zaune a Gusau Motorgage Area behind masaqa
***,***
Delivery nationwide 🌍🌍🌍
Muna aikawa a duk inda kike cikin faɗin Nigeria da ma kewaye.
Sai da Jariri na ya cika sati biyu cif, a lokacin na ƙara warware sannan a ka yanka masa dabbar suna wadda Abbah ya saya sannan aka raɗa masa suna Abdallah kamar yanda zaɓa masa, bawan Allah ke nan domin banga sunan da ya fi dacewa da shi ba fiye da wannan.
Yankan da ya ke dole shi ka ɗai aka yi min babu wani wanda ya damu ni ballantana har a yi zancen shan ado ranar suna musamman a al'ada irin ta mu ta malam bahaushe na ayi wannan a yi wannan domin haihuwa musamman haihuwar fari.
Ni ka ɗai na san irin taskun da ni ke ciki wanda ko mai ya faru dani ni ce na siya da kuɗi na.
A haka dai na ci gaba da rayuwata ta daga cikin ɗaki sai wajen tsakar gida, daga ni sai Abdallah, haka kowa zai watse a barni ni ɗaya cikin gida.
Duk wani girman kai da jiji da kai da ƙafafar da ni ke ji da ita duk sun tafi. Iyaye na ma ba su da wani kuzari a wurare da dama domin irin maganar da janyo musu, musamman Baba, ga shi mutanen duniya ba su iya juya zance ba, idan ka ji wata maganar muddin ba ka zama mai tawakalli ka kai zuciyar ka ne sa ba sai kaji tamkar ka ɗauki wuƙa ka daɓawa cikin ka.
Ganin irin halin da Asiyah ta shiga ita da danginta yasa su Baba suka yanke hukunci cewa a dakata da zancen Auren Yah Saif a bar shi sai nan gaba idan hankali ya kwanta.
Shiyasa Yah Hadiza ta juya ta koma gida sai yanxu da a kayi kusan wata uku sannan aka tayar da zancen wanda jiya-jiyan nan ta sauko ita da
dukkan yaranta gaba ɗaya.
*********
Asiyah
Ga baki ɗaya rayuwar Asiya ta sauya ganin irin darasosin rayuwar da suka cimmata, ga shi dai ta rasa cikinta wanda sai da tasha baƙar wahala tamkar ba za ta yi ba rai ba da ƙyar aka samo ta, sannan ga abinda ya faru da rayuwar Aunty da Zainab da Ruma wanda sun tafi kenan har abada ba za su dawo ba.
Kullum idan ta zauna babu abinda ta ke idan ba kuka, musamman idan ta kalli Hidayah da Ammar ji ta ke ina ma ace Aunty Zainab ba mutuwa tayi ba.
A haka tayi ta lallaɓa rayuwar ta a gidan har sai da tayi wata uku cif, daman Yah Halifah da kan shi ya ce a barta ta huta ta kuma jinyar zuciyarta kusa da Umma, domin rayuwar ta ta zama abar tausayi.
Ko ranar da za'a mayar da ita gidanta sun yi kuka sosai ita da Umma domin sun san da ace Aunty zainab na nan da ita za ta yi wannan hidimar.
Ranar da labarin abinda ya faru da Hamid ya riske su Umma har da zuba ruwa ƙasa tayi ta sha tana mai jin daɗi da godiya ga Allah da kuma ko wanene ya yi masa haka, shi ke nan an huta da shi.
Suna nan suka ji labarin wai an je kama Sufyan akan zargin abinda aka yiwa Hamid, ganin ba bu wata hujja kamar yanda suka ce ba bu wata hujja da ta nu na Hamid ne yayi wa Ruma fyaɗe suma haka ta kasance ba su da wata hujja, domin dai shi Hamid ya ce bai san su ba bai taɓa ganin su ba, duk wani ƙafafar Iyayen sa sai ta zama ta banza domin ba su da wani maganin da za su yi mai duk da cewa ana kan bincike.
Umma ma baki ɗaya ta yi sanyi, Yanxu babu abinda ya ke gabanta fiye da yaran nan guda biyu Hidayah da Ammar, kullum tana nan a tare da su, komai su ke so dama abinda ba su ce ba komai yi musu ta ke, ta rasa ina zata aza da su, idan kuma sau goma ta tuno ko taji anyi zancen Zainab sai tayi kuka, Sufyan babu yanda bai yi da ita akan ta bari su koma makaranta a satin nan ta ce a'a, ya bar shi idan lokaci yayi zata samu wata makaranta ta kai su.
*********
Washe gari bayan ta kwana ɗaya da dawowa gidanta sai ga ta taxo gidan ba tare da ma Yah Halifah ya sa ni ba.
Har ƙasa ta durƙusa ta gaishe da Mama da Yah Hadiza da Aunty Nadeeyah.
Bayan sun gama gaisawa ta shigo ɗaki na ina zaune ina bawa Abdallah nono...
Yanda na bi ta da kallon tausayi haka itama ta bi ni da shi, wanda bata ankara ba sai ga hawaye shaa! Sun zubo mata, ni ma ganin haka ya saka ni zubo da hawayen ina jinjina kai na nace.
"Asiyah da ciwo ko? Wannan ya isa ya karantar da ke cewa babu wanda ya ke iya rubuta ma kansa ƙaddara, da ace muna iya rubutawa kanmu ƙaddara da kin hana abin da ya same ki ya sa me ki na rasa ɗanki, sannan da kin hana abin da ya faru da Auntyn ki da 'ƴar ta faruwa da su... Duk abinda ki ke faɗa a kaina babu abinda banji ba Asiyah, duk in da kika zauna zagi na ki ke aibata ni ki ke kina yi min wai gwai Allah kin ji daɗi domin kin tsaneni a ranki. Uhm! Ni ban taɓa jin na tsaneki ba ko don son da Yayana ya ke miki ba zan ta ɓa farin ciki don wani abun ƙi ya same ki ba. Ba ke kaɗai ba mutane da yawa suna aikata irin wannan kuskuren saboda wani abu marar kyau ya samu mutum sai su zauna su yi ta yaɗawa wani lokacin har da ƙari akan abinda akayi wanda babu kyau hakan, manzon Allah (S. A. W) cewa yayi;ka faɗi alkaiiri ko kayi shiru ..... "
Hawayenta tare tana mai tariyar numfashi na da faɗin.
" Nuudaar, na fahimta sosai, kuma rayuwa ta koyar da ni darasin da ban taɓa tsammani ba, ki yi haƙuri, ga shi Aunty Zainab ta tafi ta bar ni Nuudaar, da ciwo sosai a zuciyata wanda ban san ranar da zan warke ba..."
Duk yanda ni ke jin tausayin kai na Haƙiƙa bai kai kamar irin halin da Asiyah da ahlinta ke ciki ba.
" Ki yi haƙuri, in sha Allahu suna Aljannah, mun kyautata mu su zato, Allah ya baki lafiya ya ƙara muku haƙuri. "
Dan murmusawa tayi sannan ta jinjina kanta ta ce.
"Amin, na gode Nuudaar, Allah ya raya miki, Allah ya musanya miki wannan jarabawa da mafi alheri"
"Amin. Nuudaar Ina neman wata alfarma, na gayawa Halifah ya ce sai dai na tambaya da kaina, ba zan iya hakan ba domin ina matuƙar jin kunya, dan ki roƙamin su Mama, Ina so a bani Hanna ta ci gaba da zama a tare da ni har zuwa aurenta dan Allah"
"Ba matsala in sha Allah zan gaya musu kada ki damu"
Daga haka ta kwanta akan gado na tayi shiru ni kuma na ci gaba da ninke kayan Abdallah da ke gefe na tun ɗazu.
***********
Washe gari da tasan da zancen zuwan su Yah Hadiza Kaduna tunda sassafe ta zo gidan ta shiga tayani aiki ni da Fauxa ,bayan an kambala wuraren goma da rabi na safe, Mama, Yah Hadiza Maman su Husnah matar Baba Amadu, Nucy, Hannatu, Mama Balki da ƙanwar Babanmu goggo Zuwaira da kuma Su Yah Halifah, su ne suka cika motoci zuwa Kaduna. Bayan sun wuce ni da Fauxa muka wuce gidan Mama Ruke, Asiya kuma daman cewa akayi ta koma gida tunda bata gama warwarewa ba tayi haƙuri ta barshi sai sun dawo.
***********
Hamid
Zaune ya ke da tangamemen gilashin sa wanda yasha baƙi har ya gaji. Shiru kawai ya ke gashi nan dai tunda abin nan ya sa me shi baya cewa um baya cewa Uhm, idan abin ya cizo shi wani lokacin sai dai aga hawaye yana bin kumatunsa.
Cike da karyewar zuciya mahaifiyar sa ta kalle sa, ga hawaye na bin idanuwanta kamar famfo ta ce.
"Hamid Allah ya saka maka da wannan zaluncin da aka yi maka, kullum cikin bincike a ke amma har yanxu ba'a samu wani haske ba, ga shi ka ƙi buɗe bakin ka kayi magana tsawon lokacin nan, babu wanda zai san abinda ya ke zuciyar ka da abinda ka ke so ka faɗi idan har ba ka buɗe baki kayi magana ba Hamid. Kai wannan masifa da mi ta yi kama ni Shamsiyya? Da wata rayuwar ai gwanda a san mutum mutuwa da ya yi, Allah ya isar maka ko waye ya yi maka wannan wallahi ba zamu taɓa yafewa...."
Haka dai ta yi ta sabbatu ita kaɗai yayin da ya koma tamkar kurma a gabanta.
'Hamid dai tunda aka kai shi asibitin Kano sai da Mahaifinsa ya kashe maƙudan kuɗi sosai sannan aka yi masa aiki, tun yana asibiti suka haukace wurin bincike akan sai sun gano wanda ya aika masa haka amma shiru sun je sun sa an kama Sufyan, an kama Abba amma duk a banza domin ba su da wata makama, Ahmad ma da aka je har Sokoto aka zo da shi cewa yayi shi bai san abinda su ke magana a kai ba, Hajiya Shamsiyya ta yi kuka tayi kuka amma a banza. Bayan ya samu sauƙi a ka sallamo shi suka dawo gida akan za su riƙa zuwa check up lokaci bayan lokaci, tun suna Asibiti Hamid baya magana, da farko sun dauka zafin ciwo ne kawai amma sai ga shi daga baya shi kenan ƙarya da gaskiya ya daina magana babu abinda yake sai kuka. Mutanen unguwa duk wanda yaji daga mai tausayawa sai mai tofin Allah tsine'
***********
Su Mama su na isa aka tarbe su cikin mutunci, Mama sai godiya ta ke musu akan taimakon da suka min, kwana biyu da zuwan su aka ɗaura auren Yah Saif da Aunty Meerah.
Bayan kwana biyu da ɗaura aure aka wuto da ita da kayan ta da sauran en uwanta.
Gidan Mama aka wuce da ita direct wanda a lokacin mun riga mun gama gyara gida mun yi girki komai yayi tsab.
Ta na gani na taxo ta rungume ni, ni kuma sai hawaye ina mai jin wani sanyi a raina ban san mi ya sa ba amma jinta ni ke sosai a matsayin wata garkuwa a gare ni......
"Nuudaar! Baki can za kina nan yanda ki ke sai dai ramewa da ki ka yi wanda baya rasa nasaba da shayarwar da ki ke....."
Gyaɗa kai na nayi cikin gamsuwa da kalamanta na ce.
"Bayan en uwana na jini ke ce mutum ta daban da ta fahimce ni ta kuma yarda dani..."
"Nuudaar, in sha Allah zaki yi farin ciki watarana, komai mai wucewa ne in sha Allahu"
Daga haka ta shiru tare da bin bayan Aunty Nadee kamar yanda ta umurceta.
Washegari en uwanta suka je gidan Yah Saif da ke wuri ɗaya da na Yah Halifah suka gyara mata komai na ta wuri yayi barakallah masha Allah.
Da dare bayan sallar magrib aka kai ta ɗakin ta wanda tayi buri da addu'a ita da habibinta Yah Saif.
Bayan an gama komai da sati ɗaya Yah Hadiza ta roƙi su Baba akan a bar ta ta je da ni ko Allah zai sa na sake da su na dawo walwala kamar da can baya,sai ga shi bata sha wahala ba domin tana gama tambayar su baba ya bata go ahead ba ɓata lokaci na haɗa komai nawa muka harba sai Kebbi State.
Muna nan rayuwa na ta tafiya, yau daɗi gobe akasinta har Abdallah ya kai shekara bakwai, wanda zance Yah Hadiza ta daban ce a cikin en uwa. Ta riƙe ni ni da Abdallah tamkar wani abu bai faru ba.
Makarantar sa ya ke zuwa both Islamiyya da boko ni ma kuma na koma fresh degree a fannin Nursing kamar yanda Aunty Meerah ke ƙafafa ni.
Ba na zuwa ko ina ba na hulɗa da kowa Yah Hadiza ita ce komai tawa, ƙawata, uwata, ita da Hudah.
Kuma wani abun mamaki duk da shima iko ne na ubangiji, duk zamana a Kebbi ko sau ɗaya babu mutum guda da ya taɓa fitowa ya ce yana so na ko sau ɗaya wanda ni hakan bai taɓa damu na kullum Yah Hadiza ita ce waya da su Mama suna jajantawa ni kuma banga wani abun damuwa ba.
Wata rana na dawo daga lectures duk na gaji na ɗebo gajiya na dawo, Ina shigowa palour kwatsam mu ka yi ido biyu da Emraan.
Gaba na ne ya yanke ya faɗi ganin shi da nayi bayan lokaci mai tsawo.
Wa su irin hawaye ne ma su zafi suka kwaranyo min daga idanuwana kawai na juyo da nufin barin parlourn....
"Nuudaar pls ki tsaya ki saurare ni dan Allah! Pls ba don hali na ba kada ki duba baya ki tsaya ki ji abinda zan faɗa miki.........."
OUM AMEER