Free chapter · Read without an account

6

by Sadiyamuhammadnasir · RIKON SAKAINA

RIKON SAKAINA

YA FARU A GASKE

NA

SADIYA NASIR DAN

Arewa Book

sadiya Nasir

SHAFI NA SHIDA

A haka har muka d'auki tsawon sati biyu ban sake ganin kiran uncle Naira ko sakon messages ba, sannan kuma baya zuwa gidan. Hakan sai ya samun nutsuwa da kwanciyar hankali saboda nasan yayi zuciya ne. A wannan yanayin muka koma hutun makaranta kuma semester na karshe, hankalina na mayar sosai akan karatu saboda dana fito da results Mai kyau.

Ta bangaren uncle Naira kuwa ganin ba zai samu cikar burinsa akaina ba yasa ya canza salo, Ashe rashin kiran waya da message da baya Aiko min duk shiri ne.

Ranar wata Alhamis Hajiya Indo tana office ita da Aminiyarta Hajiya Turai suna hirarsu da bata k'arewa Musty naira ya ziyarci office din, sosai Hajiya tayi mamakin ganinsa ko meke damun sa da ba zai iya jiranta ta koma gida ba. Bayan sun gaisa Hajiya Turai waje ta basu don su zanta, kallon sa sosai Hajiya Indo tayi tace "Lafiya Musty?". Nisawa yayi ya sauƙe ajiyar zuciya yace. "Lafiya Amma ba sosai ba". Gyara zama Hajiya tayi tace "Ina jinka". "Nazo neman alfarma ce Hajjaju, kuma ina da yak'ini zaki min saboda ke mai son farin ciki nane, sannan kuma akan burin da kike dashi akai nane da kullum kike fatan ki cika sa, wallahi Hajjaju yarinyar gidan ki nake so ki taimaka ki shiga maganar ko Alhaji zai bani ita na Aura, wallahi wannan karo da gaske nake Auren zanyi domin ina sonta, kuma na miki alkawari zan riketa amana". Galala Hajiya Indo ta bishi da kallo na tsawon mintuna kafin tace. "Kana da hankali kuwa Mustapha? Khadijan kake so ka aura? To a dalilin me? Duk matan da suke waje basu isheka ba sai kazo gida na? Kasan ko a mafarki Alhaji ba zai amince da wannan shirmen taka ba, sannan Aliya tana gida Khadija ta rigarta Aure kasan wannan ba mai yuyuwa bane wallahi, don Allah ka janye wannan shirmen karka sake fad'a min". Ta k'arasa maganar ranta a matukar b'ace. "Haba Hajiya kar muyi haka dake, nifa ɗan uwanki ne mai kaunarki mai son abinda kike so, bai kamata ace akwai abinda zan zo nema a wajenki na gagara samu ba, please Hajjaju kiyi nazari, wallahi rasa Khadija a rayuwata tamkar rasa numfashi a jiki nane? K'okarin magana Hajiya tayi yace please kiyi tunani duk abinda kika yanke ina jiran call". Yana gama fad'in haka ya fice. "Mikewa Hajiya tayi daga zaunen da take ta mayar da hanunta baya ta shiga duniyar tunani. Wai ta yaa ma za'a ce ta had'a jini da Khadija? Yarinyar da tsanar uwarta ke zaune a zuciyarta ya kasa goguwa shekara ashirin baya, da ace bata had'a alaka da Musty ba, to tabbas shine dai'dai da Auren Khadija saboda ba mutumin kirki bane, Amma hakan bame yuyuwa bane. Ta furzar da iska mai zafi ta fito tayi office din Aminiyar ta.

Tun daga shigarta Hajiya Turai ta lura da yanayinta. "Kawata lafiya kuwa?". Zama tayi a kujeran gefe tace. "Banda Musty yake so ya caza min kai da ranar nan". Ta kwashe duk yanda su kayi ta sanar da ita. "Kama Baki Hajiya Turai tayi tace. "Wata sabuwa inji masu tallar caca, shi Musty kuma Khadijan yake so?" "Aminiya duk ba wannan ba, nifa bana kaunar had'a zuri'a da wannan shegiyar yarinya mai kama da mayun, ni bazan tab'a bari wannan al'amarin ya faru ba". Murmushi Hajiya Turai tace. "Nida na d'auka ma za kice baki goyon bayan ta Aure shedanin Yaro kamar Musty, koba shi bane mu kaje gidan Luba nema mishi Aure yaje yama y'arsu ciki?". "Kwarai shine amma wallahi bana burin ya Aure Khadija, nifa yanda na tsani yarinyar bana so ta tsaya a haka, ai Musty yana da rufin asiri tunda yana sonta idan ta Aure shi zata huta, babban burina ta Aure talaka fakiri wanda zaici ubanta tsaban wahala a kasa ganeta". "Uhumm Amiya kenan, wani lokaci idan kinyi magana saina raina shekarun ki, yanzu kina da tabbacin idan kin rabata da Musty talakan zata Aura? Al'amarin nan fa a lullube yake, bai kamata ki yanke hukunci da sauri haka ba, komai yana son lissafi da nazari, abinda nake so dake ki nutsu ki kwantar da hankalin ki, batun wai Aliya tana gida Khadija tayi Aure ta barta, ko ba zata Aure Musty ba duk ba wannan bane, amma ina zuwa ta ambata ta jawo wayarta ta soma kiran call, bata jima tana ringing ba aka d'auka. "Allah ya taimaki mai gayya mai aiki, kaina a k'asa kana gida ne yanzu zan taho da bakuwa? Ok gamu zuwa, ta ambata ta kashe wayar ta maida dubanta ga Hajiya Indo, tashi za kiyi muje a bud'e mana aiki akan yarinyar, ki san ma wacece ita da irin taurari da take dashi". Nisawa Hajiya Indo tayi ta mike suka fito a ma'aikatar.

Da isar su gida Malam mai gayya mai aiki kai tsaye ɗakin Magani suka shiga, yana zaune yana tsubbace tsubbacen sa ta madubi suka shigo, waje ya nuna musu su zauna bayan sun gaisa Hajiya Turai ta kora mishi jawabi. Ya jima yana bincike kafin yayi dariya yace. "Wannan Yarinya tana da Baiwa sosai sai anyi da gaske, domin haske ya nuna sosai da alama akwai arziki a jikinta, karshen magana dai Taurarinta masu karfi ne, ko kin rabata da wannan wani zai zo nan gaba kaɗan, domin gashi na gani, mai rufin asiri da nutsuwa da hankali, samun kwanciyar hankalin ki shine ki tashi tsaye ki ajiye batun wai ba kiso ki had'a zuri'a da ita ayi wannan Aure, idan kin ce aa kuma Kashin ki zata hura wuta nan gaba".

"Innalillahi wa'inna ilaihi raju'um! Na shiga Uku ni Indo gaskiya Fatsuma masifa ce, ta mutu ma amma ba zan huta ba ga ɗiyar ta tana neman ta caza kwakwalwa ta, to Amma Malam wani hanzari ba gudu ba, koda na amince da wannan Aure to Miji na zaiyi wahala ya amince dashi, don yayi farin sanin wa Mustapha gashi ya kwallafa ransa sosai akan yaran marigayi, uwa Uba kuma shi mai burin karatu ne, bana jin zai amince da zancen Aure nan kusa koba Mustapha ba".

"Meye sunan shi?" "Kabiru". Ta ambata ya mayar da kansa gefen da madubi yake yayi tsatsubar sa. "Tabbas idan kece ki kaje da zancen ba zai tab'a amincewa ba, akan haka ma zai iya rabuwa dake, Amma naga tausayi da soyayyar yarinyar sosai a ransa, idan har ita ce ta bud'i baki tace ta amince to babu shakka zai mata Auren kuma cikin farin ciki, dole abin yana bukatar taka tsantsa". Dafa kirji Hajiya Indo tayi "Saki fa kake nufi Malam?".

"Eh shi din na gani".

"Tabdijam! to gaskiya Malam na hakura don akan wata shegiya ba zan rasa Aure naba".

Hararanta Hajiya Turai tayi Jin furucin nata tace. "Ke da Allah kiyi shuru, ba kiji meye yace bane? Idan har ita tace wa Alhaji tana so to tabbas za'ayi Aure, ai naga ba abin damuwa bane, ita yarinyar zaki tursasa ko shi Mustapha ya dage har ta shiga ransa, Ina ga hakan shine mafita".

"Shikenan Malam sai a taimaka mana da taimako na yanda zata amince dashi cikin sauƙi". Ba matsala ya ambata ya lissafa musu abinda zasu biya ya basu garin Magani daza taba Khadija a abinci.

Tunda suke fito a gidan mai gayya mai aiki tattaunawa kawai suke al'amarin Khadija, babu abinda yafi komai d'aga wa Hajiya Indo hankali kamar cewa da yayi Taurarinta masu karfi ne. A haka suka iso bakin hanya ko wacce ta shiga adai-daita sahu tayi gidan ta.

Hajiya Indo kai tsaye ɗaki ta wuce saboda kanta dake azabar ciwo, abinci ma Sahura ce takai mata har ɗaki, tana ci tayi wanka tayi sallar Magrib ta ɗan kwanta. Sai cikin dare kusan karfe uku ta farka tayi sallar Isha'i, tana idarwa ta tura message wa Mustapha akan su had'u a office d'inta karfe goma na safe.

Mustapha yana ganin saƙon yayi tsallen murna, yana ji a jikin sa Hajiya ta amince da bukatarsa ce, don haka a shirye yake daya Aure Khadija idan ya samu abinda yake so sati guda ya saketa. Da wannan mummunar kudirin yayi bacci.

Washe gari da safe tsabar zumudi Mustapha ya riga Hajiya Indo isa office, sai da ya zauna na kusan mintuna talatin kafin ta iso, bayan sun shiga office sun zauna Hajiya ta dubi Mustapha. "Tun a jiya na gama nazari akan bukatarka, in dai daga waje nane na Amince ka nemi Auren Khadija, amma ina so kafin Alhaji ya sani kayi k'okari ku dai-dai ta, kaga idan ya tunkareta da zancen za tace mishi ta amince". Murmushin jin daɗi Musty yayi yace. "Kin gama komai Hajjaju tunda kika amince, in dai neman soyayyar Khadija ce wannan ba matsala bace a cikin wata guda zata aminta dani".

"Uhummm".

Hajiya Indo ta sauƙe dogon numfashi. Bai jima a office din ba ya fito, kai tsaye karamin super-market ya nufa ya ɗanyi karamin shopping ya koma gida, bacci yayi karfe d'aya ya farka yayi wanka a gaggauce ya nufi makarantar da Khadija take karatu da ɗan shopping d'insa.

*****

Kasancewar munata hidimar project koda aka tashi office din Dr Maryam muka nufa gaba d'aya wanda muke karkashin ta, sai da taja mana aji ta ajiye mu kusan mintuna Arba'in kafin ta bamu damar shiga, kuma ko minti goma ba muyi a ciki ba ta sallame mu. Makaranta anwatse baifi tsirarru ba, gate na nufa cike da takaici na zafin ranar da ake ga rashin samun abin hawa da ba'ayi, da fitata kamar ance kalli gefe, sai naga motor Uncle Naira. "Yau kuma?". Na ambata nasa kai zuwa bakin hanya. Da sauri ya fito yasha gaba na. "Haba Khadija don girman Allah ki tsaya?". Tamke fuska nayi nace. "Ina jinka domin girman Allah". Ajiyar zuciya ya sauƙe yace. "Kiyi hakuri kizo muje gida tare magana za muyi?". "Nii wai? Har abada na gama shiga motar ka Uncle Naira, saboda tsarin da kake kai sam bai dace da tawa tsarin ba". "Na sani Khadija, na miki rantsuwa da girman Allah ban zo da wancan batun ba, hasali ma ba abinda kike tunani ya kawo niba, wallahi magana za muyi ba kuma a motor ba a gidan ku, please Khadija domin girman Allah na had'a ki?". "Uncle Naira na rantse da Allah ba zan shiga motar kaba, na amince da maganar da kace za muyi kaje gidan ka jirani ina zuwa, Kai musulmi ne nima musulma ce duk mun San hukunci rantsuwa". Sosai yaji zafin magana ta Amma saiya daure yace. "Shikenan barin nemo mai Napep yazo ya daukeki". Bance komaiba yaje ya taro adai-daita ya biya kudin na shiga yacigaba da bin mu a baya......

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.